Showing 39001 words to 42000 words out of 176868 words

Chapter 14 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

ne yasashi sa hannu,
ya amsa tare da yin murmushi cikin kurma-kurma yayi mata godiya tare sa hannu ya karb'i kwalin wayar da Ishaq ke mik'a mishi wanda SIM card d'inshi na mtn yana ciki da yana cewa.
"Dama ai na san halinka kai komai aka baka sai kace baka so har yau baka d'aukeni d'an uwanka ba,
sai kayi ta nuna min fulaku ni kuma da yake banda zuciya duk abinda na gani a wurin Ummi amsa nakeyi."
amsar woyar yayi tare da yiwa Ishaq d'in alamun to ya isa sarkin k'orafi,
sai ya kuma kalli Mama tare da mata alamun ta mishi godiya a wurin Ya Rabi'u,
sai ya kuma amshi wayar Ishaq ya rubuta sak'on godiya ya turawa Ya Rabi'u babban yayansu Ishaq kenan,
daga nan kuma suka nufi d'akin ishaq nan sukayi ta hira.
Suna cikin hira Saifuddeen ya duba time ganin lokacin salla ya kusane ya sashi mik'ewa ya shiga wonka yana fitowa ya shafa mai tare da canza kaya yasa kayanshi daya cire jiya ya wonke imran kuma ya goge mishi.
Shima ishaq wonkan ya shiga yana fitowa ana kiran sallan magrib,
suna shirin fita imran ya shigo d'auke da tire yana cike da kayan bud'a baki,
dabino sukaci sannan suka sha kankana da abarba daga nan suka fito, suka nufi masallacin fadar masarautan Gombe bayan an idar da salla ne kuma suka dawo gida,
nan sukaci abinci sannan suka zauna suna hira a parlour Mama nan ishaq ya ware mishi d'inkunan da Ya Rabi'u ya musu d'aya riga da wondo ne da babbar riga sai takalmi da hula,
sai d'aya kuma riga da wondo d'inkin zamanin sai boxers and vest guda uku-uku,
sai ledar da Mama ta bashi kuma atampa ce da shadda sunsha d'inki atampar dai-dai Adda Rahma shaddan kuma dai-dai Ummi,
godiya yayi sosai,
daga nan ya had'a komai sannan sukaci gaba da hira,
dan yau ana tsumayin ganin wata.
A dukku kuwa su Warisu da Mudassir kamar kullum sukaje sukaci abinci a gidansu Saifuddeen.

Shi kuwa Saifuddeen a Gombe ganin lokacin sallan isha yayi ne yasa suka fita sukaje masallaci akayi sallan isha rashin samun labarin ganin wata yasa akayi asham d'inma.
Bayan an idar ne sun dawo gida suka shiga parlourn Baban Ishaq zaune suka sameshi yana kallon tv, ganinsu yasa ya maida hankalin shi a kansu,
cikin nitsuwa suka gaida su nan yayi musu bayanin k'ungiyar su ta nakasassu da yake son su shiga wato (Jonapwd), sosai ya musu bayani ya k'ara da ce musu.
"Shi abu na taron jama'a yanada amfani da fa'ida domin hannu d'aya baya d'aga jinka,
shiga k'ungiyar yanada amfani domin tamkar taimakekeniyace a gareku dan saida had'in kanku zai zama maganarku zatayi tasiri wa kunnuwan jama'an gari dama gwamnati,
saida had'in kan k'ungiya da zaku samu damar yak'an barace da k'arfafawa mutanenku guiwa ta yadda zaku fahimtar dasu Nakasa ba kasawa bace."
Cikin gamsuwa suka gyad'a kai dan shi Saifuddeen yana gane abinda Baba yake fad'a da matsin bakinshi shi kuwa Ishaq yana jinshi, ganin sun gamsune yasashi ci gaba da cewa.
"Dama naje nayi mgna da shugaban k'ungiyar na mishi bayaninku, kuma na shaida mishi in anyi salla lfy zan kaiku."
still kansu suka gyad'a cikin alamun amincewa,
daga nan yayi musu nasiha da basu k'arfin guiwa daga bisani Saifuddeen yace zai tafi,
nan ya mishi addu'an komawa lfy,
shi kuwa ishaq ya rakashi parlour Mama ya d'auki kayanshi sannan ya rakashi har woje saida ya hau machine yaja ya tafi sannan ya koma cikin gida.

Shi kuwa Saifuddeen yana isa kasuwa ya had'a kayanshi duka sannan ya dawo bakin kasuwa inda yasan Salisu zaizo ya d'aukeshi,
bai jima da zuwaba kuma Salisu ya iso daga nan suka kama hanyar Dukku.

To a wannan shekaran dai azumi talatin akayi.
Ranar salla duk al'ummar musulmai kowa da ko ina ana cikin farin ciki,
duk inda ka gibta ido cikin garin dukku zakaga kowa cikin cikar sura da haiba.
K'arfe tara dai-dai akayi sallan idi,
ana idarwa Saifuddeen da abokanshi da suke cikin shiga iri d'aya suka kama hanyar gida,
kasan cewar sun canza hanyar komawa ne yasa suka fito gab da k'ofansu Saminu,
dan haka nan suka shiga suka gaida iyayen Saminu daga nan suka shiga parlour Hajja Mama mahaifiyar Saminu,
inda k'anwarshi Sakina tayi ta jero musu abin ci da sha,
nan suka zauna suka d'anci,
suna fitowa gidansu Saminu suka wuce gidansu Warisu.
Dalinshi tana ganinsu tai ta farin ciki tare da sa musu al'barka nan ta kawo musu fura da nono, sunsha nonon sosai daga nan suka fito suka shiga gidansu Mudassir nan suka samu ya Adnan ya dawo jiya da dare,
yana ganinsu yace.
"Iye Umma zo ki ga 'yan samarinku, wlh yarannan sun girma sosai fa kalli duk sun kusa kamoni tsawo fa."
Bud'a kafad'u sukayi tare da had'a baki sukace.
"Kai Ya Adnan mun kamo ka dai kawai zaka ce."
Umma dai sai murmushi takeyi,
shi kuwa Adnan kamo hannun Saifuddeen yayi tare da cewa.
"Duk baku da kunya Saifuddeen ya fiku mutunci, dan ku gani kuke kunma fini."
sai ya kuma kalli Ahmad dake tsare fuska cikin raha yace.
"Kai Ahmad me na had'e fuska haka?."
tab'e baki yayi tare da cewa.
"Au ashe dai baka mance niba ai wlh ya Adnan baka da kirki, kullum Dada sai tayi cekiyarka in taga Mudassir tace wato kai kam tunda Ya Nuruddeen ya rasu ka yanke zumuncin dake tsakani."
da sauri ya juyo ya kalli Ummanshi dake cewa.
Ai wlh shi Adnan sam baida k'afa dama Nuru shike sashi ziyara,
kullum in yazo sai nayi ta binshi yaje amman sai ya zama ko fitan baya so."
da sauri ya katsesu tare da cewa.
"Kinga ko Umma wlh yanzuma niyata shabewa zan tafi dan wlh nima kaina nayi kewan goggo Dada tun rasuwar Abba ban kuma ganintaba."
shi dai Saifuddeen baibi ta kansuba,
shiko Ya Adnan bayan sun shiga d'akin Umma ne shi kuma ya fita.

Kai tsaye gidansu Saifuddeen ya nufa,
yana shiga ya samu Ummi a tsakar gida cikin shiga ta salla,
tana ganinshi ta fad'ad'a fara'arta cikin jin dad'i tace.
"Lale marhabin da Ya Adnan yaushe a gari mutanen Zaria."
cikin sakin fuska ya zauna bisa taburmar data shimfid'a mishi cikin sakin fuska yace.
"Jiya da dare ne Ummi shiyasa ban shigoba."
gyara zama tayi tare da cewa.
"Ayyah sannu da hanya."

"Yauwa sannu Ummi ya gida yasu Saifuddeen ina auta Hayatuddeen."

juyawa ta d'anyi ta kalli k'ofar d'akin Rahma cikin d'an d'aga murya tace.
"Auta ga Ya Adnan d'inku."
jin haka yasa Hayatuddeen fitowa da sauri,
ita kuwa Ummi juyawa tayi ta kalli Adnan tare da cewa.
"Yanzu ya dawo idi shida Faruq to wai zai tafi shabewa wurin Goggo Dada da yake Adam da Raliya suna can shiyasa suketa d'okin zasu tafi can."
shi kuwa Hayatuddeen yana zuwa ya ruggumi Adnan yayinda Faruq ke bayanshi da sauri ya iso ganin Adnan na mik'o mishi hannu ruggumesu yayi baki d'aya yana jin tausayin yaran da k'aunarsu yana tuno irin so da k'aunar da Nuruddeen ke musu.
ita kuwa Ummi cikin sanyin sautin da ganin Adnan ya tuna mata d'anta ta kalli Rahma da yanzu ta fito ganin Adnan ne yasa ta koma cikin d'aki da sauri,
jin muryar Ummi na cewa.
"Rahma fito mana kizo ki kawo mishi abinci."
cikin sanyin murya tace.
"To Ummi bari insa hijabi."
daga nan sukaci gaba da hira,
cikin kula Ummi tace.
"Ya karatu yanzu kam ka kusa gamawa ko?."
gyara zama yayi tare da cewa.
"Alhamdulillahi Ummi ai nama gama."
cikin jin dad'i tace.
"Alhamdulillahi nayi farin ciki Allah ya taimaka ya baka aiki cikin sauk'i."
ido ya lumshe ganin Rahma data rutsuna gabanshi,
sai ya kuma kauda kai daga gareta tare da sauk'e numfashi kana ya kalli Ummi tare da cewa.
"Amin Amin Ummi aiki kam ya samu ma da yake karatun likitanci ne samun aikin ba wuya,
next week zan koma gombe dan na samu gurbin aiki a medical senta gombe harma sun bani gidan zama a can a jerin gida jen ma'aikatan su."
Sosai Ummi tayi farin cikin wannan labarin,
daga bisani ta tashi taja hannun Hayatuddeen da Faruq da tace.
"To muje in had'a muku kayanku,
kai Auta baka ganin girmanka sai kayi ta zama jikin mutane."
murmushi yayi tare da zaro kud'in 'yan ishirin-ishirin ya bawa Hayatudden guda goma hakama Faruq aifa nan sukayi ta tsalle suna murna, cikin had'a fuska Rahma tace.
"Baku iya godiya bako?."
da sauri suka juyo tare da cewa.
"Ya Adnan mun gode Allah ya saka ya k'ara bud'i."
Amin Amin yace,
tuni su kuma sunbi bayan Ummi,
shi kuwa Adnan idonshi ya d'an lumshe tare da sa yatsunshi biyu ya d'an ja jelan kitson Rahma dake har bisa kafad'unta,
da sauri ta d'an juyo tare da cewa.
"Wash Allah na ya Adnan zafi."
girarshi d'aya ya d'aga mata tare da cewa.
"Raguwa kawai."
ido ta lumshe da sauri jin yana cewa.
"Kinji na gama karatu har na sama mana aiki,
bakice komaiba."
idon ta ta d'an bud'e tare da cewa.
"Nayi mana addu'a ai ya Adnan."
gyara zamanshi yayi ya kalli gefe ganin Ummi ta fito zata shiga d'akinta cikin yin k'asa da murya yace.
"Kinga sauran burinmu na gaba,
yanzu dai na kusa in baiyana kaina gaban bappa Ali ya aura min ke in rik'e 'yar k'anwata in sata farin ciki."
da sauri ta kuma rufe ido,
shi kuma sai ya d'an d'aga murya tare da cewa.
"Yunwa fa nakeyi bani abinci inci."
hararanshi ta d'anyi sannan ta zuba mishi abincin ganin zai fara cine yasa ta yunk'ura zata tashi,
sai kuma ta koma ta zauna jin ya kamo hijabinta,
dole ta zauna suna d'an hira yana cin abinci.
har saida ya k'oshi sannan yace.
"Nafa yi amarya."
ido ta d'an zaro alamun tambaya,
murmushi yayi tare da cewa.
"Bafa amaryar da za'ake konciya da ita a gadoba machine ne kasia na saya mana."
cikin jin kunya tace.
"Masha Allah, nayi farin ciki."
juyawa yayi ya shiga d'akin Ummi kud'i ya zaro yan d'ari-d'ari rafan dubu uku ya mik'awa Ummi,
amsa tayi tare da sa mishi al'barka ta kuma yi godiya,
daga nan ya fito tare da cewa su Hayatuddeen su fito ya kaisu gidan goggo Dada aifa da murnarsu suka fito,
suna fitowa Raihana kuma dake k'ofan bappa Ali tana taya Aunty Nina kirba fura itama ta fito nan tace zata bisu,
nan take ta shirya suka fita suka nufi shabewa.

Su Saifuddeen kuwa ranan sun zazzagaya gidan yan uwa da abokan arzik'i,
sai bayan sallan magrib suka dawo gidan Ummi inda dama sukace tayi musu miyar kuka da tuwon semo wai sun gaji da cin kayan maik'o,
aifa sukaci sukayi hanik'an,
har sha d'aya na dare Ahmad yace shifa zai koma aiko sukace yasin bazasu rakashi ba,
dole Salisu ne ya maidashi.

Ishaq kuwa ranan wuni yayi yana zura idon ganin Saifuddeen,
yayi ta gwada kiranshi kuma woyar tashi bata shiga,
haka ya hak'ura ya kwanta da niyar gobe da sassafe zai tafi dukku.

Washe gari kuwa Saifuddeen yayi kolliya na gani na fad'a dan zaije gidan Abokan Abbanshi Baba Hamisu kakansu Faruq kenan da kuma Malam Ashiru,
yana gama kimtsawa ya d'auki turare ya feshe jikinshi dashi kayan sunyi matuk'ar mishi kyau shida Hayatuddeen da Ahmad ne wanda Ahmad d'inne ya d'inka musu shi,
yad'in voyel ne mai ruwan madara yadin mai gidan dara-dara, sai surfani bak'i da akayi aikin d'inkin,
sai kuma takalmi bak'i mai ratsin fari da hula zanna bukar bak'i da ratsin farin,
sosai kayan sukayi d'as da jikinshi yayi wani irin mashahurin kyau da korjini.

Pillows inshi ya d'an d'ad'ad'aga alamun yana duba abu,
sabuwar woyarshi ya d'auka sannan ya fito ya nufi d'akin Ummi yana kunna woyar,
gefen Ummi ya zauna wacce take shan fura da nono mai sanyi.
da sauri ta mik'a mishi kofin kai ya jingina da gado kana ya amshi kofin,
kurb'a ya d'anyi sannan ya fara rubutu a woyar da tun randa ya dawo daya sata a caji ta cika ya cireta ya ajiye bai kuma bin ta kantaba sai yanzu,
rubutu yayi sannan ya nuna mata fuskar woyan.
"Ummi zanje in gaida su Baba Ashiru kuma zan isa gidan Baba Hamisu ma, kuma ya kamata inje dasu Faruq da Hayatuddeen,
gashi kuma suna gidan Goggo Dada."
bayan ta karanta ne ta d'an gyara zama kana tace.
"To kaje ka cewa Salisu ya d'aukosu mana."
kai ya gyada cikin gamsuwa daga nan yasha fura da nonon sannan ya fita yaje ya gayawa Salisu, cikin k'ank'anin lokacin Salisu ya d'aukosu.

Bayan sun dawo ne ya tasasu a gaba suka tafi Katafila inda nan gidan Baba Ashiru yake,
suna shiga matarshi ta tarbesu a mutunce bayan sun gaisane tace su isa yana k'ofanshi tare da abokanshi
nan ya tasa keyarsu Hayatuddeen suna isa suka samesu a harabar wurin yana tare da abokanshi a ciki harda Malamin isilamiyar su Saifuddeen,
yana ganin Saifuddeen ya saki murmushi tare da cewa.
"Masha Allah Saifuddeen d'alibina, yanzu kuwa nake mgnarka."
da sauri ya isa inda suke cikin girmamawa ya basu hannu duk ya gaidasu d'aya bayan d'aya,
Baba Ashiru kuwa rik'e hannun Hayatuddeen yayi yana shafa kanshi,
shi kuwa Malaminsu Saifuddeen cikin iya mgnar kurame yayi ta tambayar Saifuddeen bayan rabuwa nan yake sanarwa Saifuddeen shima ya k'aura ai yanzu baya Dukku jiya da yamma yazo dan ziyartan 'yan uwa da abokan arzik'i,
hira sukayi sosai dan Malamin nasu yana tsananin son Saifuddeen dan ya yarda da tarbiyarshi tun yana ji gashi yasan yaron yanada tsananin ilimi da fahimta.
koda suka tashi tafiya sai Saifuddeen ya d'an sunkuyo kud'i ya zaro a aljihunshi 'yan d'ari bibbiyu kimanin dubu bakwai dubu biyu ya ware ya ya ajiye a gaban Baba Ashiru sannan ya kuma zaro dubu biyu ya ajiye a gaban Malamin nashi ya kuma ajiye a gaban d'aya abokin nasu dubu biyu kana ya maida dubu d'aya cikin al'jihunshi,
kusan a tare suka had'a baki wurin cewa.
"A a haba dai Saifuddeen in bamu baka ba ai baza mu karb'a daga gareka ba."
kai ya rink'a jujjuya musu alamun dan Allah kada suk'i amsa su karb'a su samishi al'barka.
Cikin sanyi Baba Ashiru yace.
"Deen ai sai ka sani jin kunya ni ya cancanci in taimaka muku, amman na gaza sabida lamarin yau da gobe ya hana."
kanshi ya rinka jujjuyawa alamun kada yak'i karb'an kud'in,
sai ya kuma kalli Malamin nasu dake cewa.
"Kud'in sunyi yawa ai Deeen."
wayarshi ya d'an zaro yayi rubutu kana ya bawa melanin nashi wayar,
amsa yayi tare da fara karantawa yana karatun yana murmushi cikin dottaku yace.
"Bodd'i ta girma ai yanzu ta bar kukan zuwa makaranta ta daina genged'i in zata bada hadda,
to ta gode niko zan saya mata sweet dan har yanzu tana nan da son shan zak'i tunda ka koya mata."
murmushi Saifuddeen yayi tare da nuna Hayatuddeen yayi alamun tambaya ko ta kai Hayatuddeen d'in tsawo,
da sauri ya gyad'a mishi kai tare da cewa.
"wai ai tafi Hayatuddeen tsawo yanzu kusan shekaru biyar fa rabonka da ita tun randa ka bar zuwa Islamiya, nima tunda ka fara spacial education ban kuma ganinkaba saida ka gama daka gama d'inma sai rasuwar Abbanku na kuma ganinka."
murmushi yayi kana yayi alamun a gaidata daga nan ya sallamesu ya tafi.

Kai tsaye gidan Baba Hamisu ya wuce dasu Faruq,
bayan sun gaisa ne ya bashi sauran dubu d'ayan nan sannan ya bar Faruq da Adam anan dan suyi d'an kwana biyu.

daga nan ya tasa keyar Hayatuddeen suka nufi gidan su Aunty Nina dan yi musu gaisuwan salla,
suna fitowa yaji alamun saqo ya shiga woyarshi dake cikin aljihunshi,
yana dubawa kuwa yaga sak'on Ishaq ne yana ce mishi yazo Dukku fa gashi ga Ummi,
so jin haka yasa suka kama hanyan gida.
Yana shiga ya samu suna zaune a tsakar gida bisa taburma,
Ishaq sarkin surutu sai hira suketayi da Ummi da Adda Rahma,
suna shiga imran yayi sauri ya mik'e yaje ya ruggumi Saifuddeen tare da cewa.
"Oyoyo Hamma Saifuddeen yau kam nima nazo gidanku, Umminka ta bani fura da nono nasha."
kanshi ya shafa tare da jinjina mishi,
Hayatuddeen kuwa tuni ya isa jikin ishaq sunata surutu dan duk masurutane,
Ummi da Rahma kuwa sai murmushi sukeyi,
yayinda Ishaq yake cewa Hayatuddeen.
"Yauwa Autan Ummi kaga yau na kawo maka abokinka imran autan Mama."
da sauri Hayatuddeen ya juyo ya kalli Imran tare da cewa.
"Shima autane?."
cikin dariya ishaq yace.
"Eh shima autane kuma sakali irinka."
aifa daga nan Hayatuddeen da imran suka d'inke dan sakalcinsu iri d'aya ga tsawonsu dai-dai.
ranan Ummi da Ishaq da Saufuddeen da Adda Rahma da Aunty Nina tare suka wuni koda yamma tayi Ishaq yace dole Saifuddeen ya rakashi Shabewa dan zaije ya gaida Goggo Dada ya kuma ga Raihana da Raliya dan yayi missing d'insu,
aifa haka suka d'unguzuma da su Saminu da dama yake son bin bayan
Raihana nan sukaje suka gaida Goggo Dada,
daga bisani suka dawo dole Ummi tasa Ishaq da Imran suka kwana.

Washe gari suka tafi da Saifuddeen.
saida yayi kwana biyu a gombe sunje gidansu Jabeer da Hisham har gidansu Ibrahim duk sunje, kana Baban Ishaq ya tasasu gaba shida kanshi ya kaisu k'ungiyar (Jonapwd) nan take sukayi duk abinda ya kamata na shaidar suna cikin members d'in k'ungiyar.
Daga nan suka ziyarci abokan su da suka yi makaranta d'aya.
Sannan ranar da zai koman yaje ya wuni a kasuwa dan hutun salla ya k'are.
to a ranar ya tambayi Alhaji Aliyu gidan baba Bello ina yake,
to cikin sa'a ya samu Alhaji Aliyu da kanshi ya d'aukeshi sukaje gidan Baba Bello dake cikin jeka da fari,
nan suka samu ashe baida lfy shiyasa tunda akayi salla bai dawo kasuwa ba,
yayi farin cikin ganin Saifuddeen sosai bare da Alhaji Aliyu ya yaba mishi nagartan Saifuddeen d'in,
shi kuwa Saifuddeen wannan 10k d'in ya zaro ya bashi ya yace ya nemi mgni sannan ya d'anyi cefene,
yayi godiya sosai hakama matarshi Inno sunji dad'in sosai,
sannan yace ba matsala Saifudddeen yaci gaba da kasuwancin shi, sai in Allah yasa ya samu lfy, in ya dawo sai suci gaba da kasuwancin.

Da haka dai sukayi sallama suka tafi.

Tun daga ranar Saifuddeen yaci gaba da kasuwancin sa ba kama hannun yaro, sosai fa harkan leda ta amsheshi harkalla taci gaba, ya k'ara sabawa da mutane sosai,
duk sati yakan ware ribar kwana biyu ya yiwa baba bello sayayyan kayan abinci,
na dubu goma sannan ya bashi dubu biyu ya rik'e wannan abu yasa sam Baba Bello bai kuma sha'awan komawa kasuwancinsa ba tunda yanaga ya huta da wahala kuma ya lura hannun Saifuddeen yanada al'barka duk abinda ya kama yana cin gaba.

Shi kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login