Showing 129001 words to 132000 words out of 176868 words
Chapter 44 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
ne".
Murmushi kawai Zaleeha tayi tare da sakai ta fice daga cikin falon, da kallo Maman nata ta bita aranta tana mejin wani sabon buri na ƙara ɗarsuwa acikin zuciyarta, don ayanzu tunaninta ya fara haurawa sama don kuwa har Abdussalam ɗinma tanaga Zaleeha ta zarce ajinsa.
Ita kuwa Zaleeha tana fita, tayi kicibis da Ya Habu,
cikin had'e fuska yace.
"Kina dai sane haramunne in mace baliga zata fita ta zabga irin wanna turaren naki mai shegen k'amshi, na hanaki yafi a k'irga amman da yake kunnen k'ashi gareki kink'i ki bari ko?."
ya k'arishe mgnar cikin zaro mata ido.
cikin yin rau-rau da ido tace.
"Ya Habu bazan sake ba."
kwaffa yayi kana ya wuce yayi cikin gida.
Motarta ta shige, maigadi na buɗe mata gate ɗin gidan ta cilla motarta kan titi. Cikin nutsuwa take murza steering motar tata yayinda daddaɗan ƙamshin turarenta ya cika gaba ɗaya motan.
Hancin motartane ta kunno kai cikin gidan nakasassun inda ta tsaida motar a parking lot, daga can wani babban falo kuwa nakasassune acike sun shirya tsab suna me jiran zuwanta.
Cikin nutsuwa take takunta ƙwas-ƙwas yayinda takun takalminta ke bada wani sauti, saura bai wuce taku biyu ta samu kanta acikin babban falon ba taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin iska na shiga jikinta, addu'a ɗauke abakinta ta sanya ƙafanta acikin falon, mutanen dake zaune da waƴanda ke gani da waƴanda basa gani tuni sun shaida da zuwanta saboda jin sallamarta da sukayi, waƴanda basaji kuwa hancinsu ne yasanar musu da zuwanta tahanyar shaƙan daddaɗan ƙamshinta, cikin mutumtawa haɗi da rashin ƙyama Zaleeha ta gaishe da kowannensu, Ishaq ne yashigo cikin falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Sannunki da zuwa Hajiya Zaleeha!".
Murmushine yafaɗaɗa akan fuskar Zaleeha cike da kulawa tace.
"Yauwa Malam Ishaq ya fama da jama'a?".
Da. "Alhamdulillah ya amsa mata alokacin dayake ƙoƙarin zama akan kujera tare da gyara rik'on da yayiwa system d'inshi da wayarshi. Sosai ƙwazon Ishaq ke burgeta saboda yana aiwatar da komai nasa tamkar wanda yake gani.
Yau da wani Gurgu zata gudanar da shirin nata don haka tuni ta tafara ƙoƙarin soma yi masa tambayoyi kamar yanda tsarin shirin nata yazo dashi, ko mintu 10 ba ayi da fara shirinba a hankali taji wani irin ni'imtaccen iska na ratsa ko ina dake jikinta yayinda bugun zuciyarta ya tsananta,
lumshe idanunta tayi sakamakon wani irin daddaɗan ƙamshi da taji ya ratsa cikin hancinta ya kuma cakuɗa da numfashinta, wani irin mimmiƙewa taji tsikar jikinta nayi, wani irin sanyi me daɗine taji yana kusanto ta tamkar wanda ake hurosa, hakan yasanya akasalance ta kai dubanta ga inda takejin kamar tanan sanyin ke fitowa, dai-dai lokacin shikuma ya shigo cikin wajen, zaune yake akan kekensa fuskarsa na fitar da annuri haɗi da ƙyallin kyau sajenshi yayiwa fuskar k'awanya mai jan hankali.
Wani irin duka da harbawa zuciyar Zaleeha tayi, yayinda ta kafesa da idanunta masu rikita maza, cikin nutsuwa yake sarrafa kekennasa wanda kuɗinta kaɗai ya isa yasai wani gida, sam ya kasa ɗauke kyawawan idanunsa daga kan kyakkyawar fuskar da yajima yana bege dason gani, wani irin yawu Zaleeha ta haɗiye wanda ya tsaya mata amaƙoshi, zata iya rantsewa bayan mutumin daya taimaketa bata taɓa ganin wani kyakkyawa aduniya ba bayan wannan mutumin dake zaune akan kekensa in dai ido da idone, cikin tsananin dauriya da kama ajinta bawai don ta ƙoshi da kallonsa ba ta kawar da idanunta gefe, ƙarasowa cikin babban falon yayi tare da tsayawa adai dai inda Ishaq ke zaune,
A fakaice ta D'angelo kalle fararen yatsun hannunshi da yaketa musabaha da mutanen nasu da suka kewayeshi tamkar sarki a fadarsa,
ƙamshinsa kaɗai yasanya Ishaq ganesa, nan ya ɗauki wayarsa ya rubuta masa saƙo kamar haka.
"Gafa Zaleeha nan tana gudanar da shirinta wani sati dakai za ayi".
Murmushi kawai Saifuddeen yayi tare da yiwa abokin nasa rubutu inda yace.
"Allah ya kaimu,"
kana shiko Ishaq ya gyara zama tare da cewa.
"Zaleeha ga aboki na kurman da na tab'a gaya miki naje Indian dubashi da jiki."
ba tare da ta kalleshi ba tace.
"Ayyah."
Shiru yayi tare da kafeta da idanunsa kowani motsi da zatayi tare da bugun zuciyarsa yake tafiya amman da yake ya iya sarrafa kanshi babu mai ganewa sai ita da takejin kwayar kekyawan idanunshi na yawa a surar jikinta.
Hakan yasa gaba ɗaya nutsuwarta ce tayi ƙaura daga jikinta, cikin rashin kuzarin dayazo ya lulluɓeta haka take gudanar da shirin, ɗan ɗago da mayan idanunta tayi da niyar satan kallonshi karab idanunsu suka haɗe dana juna, da sauri tayi ƙasa da kanta, sakamakon wani irin shock da taji acikin jikinta, gaba d'aya taji wani abu na dark'efe kwayan idanunta,
bayan kamar minti 7 tasake ɗago da kanta don ta dubesa still idanunsu ne ya sake sarƙewa acikin najuna, sake yin ƙasa da kanta tayi aranta tana cewa.
"Na shiga uku waye wannan kuma ne wai da yazo ya hanani sukuni, irin wannan kallo saikace maye hegen gurgu mai jajayen kunnuwa, dama ai ance gurgu yafi mai k'afa iya shege!".
bayan kamar 8 minutes a hankali tasake ɗago kanta, har yanzu dai kallonta yake baya ko ƙiftawa sai dai ya rage girman idanun nashi, ɗan jim tayi tare da yin mgnar zuci.
"OK tsaurin ido ko tam zanyi mgninka yanzu".
kana itama ta tattaro tsaurin idonta da jarumta ta tsaida kwayar idanunta cikin nashi kwayar idanun,
dib-dib taji zuciyarta na bugawa da k'arfi-k'arfi kuma da sauri,
wani irin kwarjini da haibar fuskarsa da surarshi suka cika mata idani cikin one second ta janye idanunta cikin idanunshi da sauri ta maidasu akan surar kansa zuwa gefen sajenshi, ganin bai ɗauke nasa idanun daga cikin nata ba yasanya ta sakar masa harara tare da murguɗa masa baki, wani irin dariyane ya kama Saifuddeen don sosai hakan da tayi ya ƙarawa fuskarta kyau, lumshe idanunsa yayi yana mejin wani abu ya dark'afe ƙahon zuciyarsa.
Adaddafe haka Zaleeha tagama gabatar da shirinta inda gaba d'aya kallon da Saifuddeen ke mata ya dagula mata lissafi, ita sam batason yawan kallo musamman ma shida ya kafeta da ido kamar zai cinyeta kuma idanun nashi wani haiba suke dashi na musammam.
a hankali taja gajeren tsaki tare, kallonshi a fakaice kana tace.
"Maye kaci Kanka!."
ido ya lumshe a hankali dan ya gane me ta fad'i mishi,
ita kuwa hararanshi ta kumayi kana taci gaba da aikinta.
Shi kuwa Saifuddeen cikin lumshe ido da shak'ar sassanyar iskar AC mai cike da k'amshi a ranshi yace.
"Uhummmm bazan ci kaina ba in sha Allah ke d'in dai zan c...!
Duk fa masu bin labarin nan kunsan sashi sashi muke binshi, to da ganin yanzu kun san mun shigo wani sashi na musamman kuma. Wasan yanzu zai fara.
Dan Allah da darajar iyayenmu da girman Al'arshi Kada ki fitarmin da littafi na, in kin fitarba ba sai nace Allah ya isaba ko inyi zagi da tashanci ba damn tijar maguzawa ba, No da Allah isasshene kuma shi yana sane daku in ni bana sane daku, kuma shine zai mana hisabi. Dan haka ni bazan zageku ba bare in zagi iyayenku, dan nasan darajar nawa iyayen ko k'abilata bana so a zaga bare iyayena shiyasa bazan zagi iyayen wasuba🤗🤗🤗
BY
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:56 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*NAKASA BA KASAWA BACE*
*Page 26*
*NA*
*AISHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Lumshe ido yayi tare da yin magana a cikin zuciyarshi.
"Uhmmm bazanci kaina ba insha Allah keɗin dai zan ci!".
Sake ɗago idanunsa yayi ya watsa mata su, ita kuwa Zaleeha daketa ƙoƙarin tattara kayan aikinta ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, duk da cewa ba kallonsa takeyi ba amma tabbas tanajin idanunsa na yawo ajikinta, tana gama haɗa kayan aikin nata taɗan ɗago da kanta,aikuwa idanunsu ne ya sake sarƙefe acikin na juna,
"Anya wannan ba maye bane!".
ta kuma faɗa cikin ƙasa-ƙasa da murya tana me wurga masa harara da kyawawan idanunta.
Lumshe idanunsa yayi tare da dafe saitin zuciyarsa dake beating, tabbas yau yasamu nutsuwa irin wacce yajima bai samu ba, bakomai ke tafiya da hankalinsa ba face yanda take kaɗa idanunta wajen hararansa, harshe yasanya ya ɗan lashi red lips ɗinsa, yanaji ajikinsa inama da yana da damar da zai kusan tota garesa, tabbas daya jawota jikinsa yayiwa wannan bakin tsiwannanta shan tom-tom.
hand bag ɗinta ta rayata abisa kafaɗanta tare dakai dubanta ga jama'an dake gabanta, sallama tayi musu akan cewa zata wuce, cikin takunta dake matuƙar ɗaukar hankalin maza ta tako harzuwa inda Ishaq yake, ƙarasowanta garesu yayi dai-dai da kusan ɗaukewar numfashinsa sakamakon daddaɗan ƙamshinta daya samu cakuɗa da numfashinsa, cikin wani irin kasala ya lumshe beautyful eyes ɗinsa.
Saura bai wuce taku huɗu ba ta ƙaraso garesu ta tsaya cak tare dayin ƙasa da kanta, sam batajin zata iya kallon cikin idanun Saifuddeen dan wata azababbiyar fitina take hangowa cikin kwayar idanshi mai kama da maganad'isu haiba da kwarjinshi yana sa zuciyarta cikin wani yanayi, hakanan ƙarasowarta garesu ya haifar mata da faɗuwar gaba yayinda ƙirjinta ke duka da sauri-sauri.
Cikin tausasa murya ta dubi Ishaq daketa faman murmushi kamar yana ganinta,
"Malam Ishaq nizan wuce sai kuma idan munsake haɗuwa wani sati Idan Allah yakaimu!"
Murmushin dake kan fuskar Ishaq ne ya faɗaɗa, inda ya sanya hannunsa ya dafa kafaɗan Saifuddeen cike da ƙaunar Saifuddeen ɗin yace "To bari nai miki rakiya Malama Zaleeha, amma fa wani sati kishirya don kuwa baƙonki na musammanne, abokina Saifuddeen kenan!".
Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya daki zuciyar Zaleeha cike da haushinsa ta ɗago fararen idanunta ta watsa masa harara, inda still ta kamasa yana kallonta, "Nasani ae dama kallona kake maye kawai!".
tafaɗa cikin ƙasan maƙoshi tana me mulan-mulan da bakinta,
Murmushin daya ƙara bayyana zallan kyau da kwarjininsa yayi, sarai ya fahimci me take faɗa cikin ransa yace.
"Zakisan kuwa ni maye ne na gaske duk randa kika shigo hannuna!".
Sake gayara zaman jakarta akan kafaɗarta tayi inda ta juya cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta nufi hanayar da zai fitar da ita daga cikin falon, tare da Ishaq suka jera suna tafiya, suna ɗan hira sam idan kaga Ishaq bazakayi tunanin makaho bane.
Da wani irin kallon So, haɗi da shauƙi tare da zallan k'auna Saifuddeen ya bita, komai nata abun burgewane, idanunsa ne suka sauƙa akan tsararren hips ɗinta da cikin salo suke juyawa, saurin lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa, don kuwa wani irin harbawa yaji jikinshi da zuciyarshi sa nayi, wata irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da buɗe idanunsa, dai-dai lokacin ita da Ishaq suka fice daga cikin falon, murmushi yayi tare da ɗan sanya hannu ya shafi lafiyayyen sajen dake kwance akan fuskarsa.
Sannu ahankali gaba ɗaya mutanen dake cikin falon suka soma watsewa kowa ya kama gabansa.
Har bakin motarta Ishaq ya rakata, inda sosai taji daɗin rakiyar tasa, cikin muryarta dake nuna jin daɗin rakiyar tasa tace.
"Godiya dubu Malam Ishaq!".
Murmushi Ishaq yayi tare da cewa.
"To Malama Zaleeha kigaida mutanen gida!"
Da "To" ta amsa masa, kana ya juya yakoma inda yabar Abokinsa Saifuddeen.
Murfin motar ta buɗe ta shiga tare da murza mata key, dai-dai-ta tsayuwar motar tata tayi, cikin tuƙinta me ɗauke da nutsuwa ta fice daga cikin harabar ofishin ƙungiyar ta (Jonapwd), cikin salo take murza kan steering motar tata, tunaninsa ne ya faɗo cikin ranta, hakan yasa ta saki wata ƴar siririn tsuka tare dayin ƙwafa, cike da haushin irin kallon daya dinga yi mata ta murguɗa baki tare da yin guna-guni acikin ranta inda tace "Mutum gurgu sannan kurma amma sai shegen sa'ido, no wonder akace gurgu kafi me ƙafa iya shege!".
tafaɗi haka adai-dai lokacin da take shan wata kwana.
Ishaq na dawowa cikin falon, ya iske Saifuddeen wanda ke zaune cikin matsanancin shauƙinta.
Hannayen Saifuddeen ɗin Ishaq ya riƙo cikin nutsuwa yace.
"Saifuddeen kaga Zaleeha ko, tana da kirki sosai sannan akwai nutsuwa atattare da ita, sam kyawunta baisakata yin ɗagawa ba".
Murmushi Saifuddeen yayi tare da zaro wayarsa daga cikin aljihu, inda ya rubutawa Ishaq saƙo kamar haka.
"Nayaba da hankalinta matuƙa ishaq, saboda hakane ma na zaɓeta a matsayi. Matar aurena uwar ƴaƴana in Allah ya yarda,
ba dama nace maka nasamu matar aure!".
Waro idanun Ishaq yayi bayan yagama sauraran wayarsa inda ta karanta masa gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta, cikin tsananin mamaki yace.
"Wai kana nufin Zaleeha?"
Still murmushi Saifuddeen yayi inda ya rubata cewa.
"Inasonta Ishaq, haƙiƙa ina tsananin sonta, harma inajin kowani bugu na zuciyata tare da zallan soyayyarta yake tafiya, Inaso na Aureta! Ishaq tun randa na fara ganinta sonta ya zame min abokin rayuwa,
shiyasa kullum mukayi mgna da kai sai na tambayeka ita da lfyarta".
Koda Ishaq yagama sauraran batun wani irin tsananin farin ciki ne ya lulluɓesa, haƙiƙa baya gani da ido amma yana gani da zuciya, kuma tuni zuciyarsa ta gama karanta masa kyawawan halayya da kuma nagarta irin na Zaleeha, tabbas zaisowa abokinsa Saifuddeen samun mace irin Zaleeha amatsayin mata, cikin jin daɗi tare da son ƙarfafawa Saifuddeen ɗin guiwa Ishaq yace.
"Naji daɗi Saifuddeen, kuma zanfi kowa so da muradin kasantuwar aurenku da Zaleeha, saidai kuma baza muyi gaban kanmu ba, zaifi kyau mu fara sanar da manya don baza muje haka kawai ba sai da ƙarfin mu, ma'ana sai munsamu amincewar manyanta, tabbas ayanda nasan Zaleeha nasan tanada nagarta, kuma zata soka".
Ya k'arishe mgnar cikin karsashi domin su basu sawa ransu cewa nakasarsu zata zame musu kasawa ba, bare ta hanasu neman duk wani abinda mai cikar halitta zai nema kuma ishaq bai san dakon son dake ran Zaleeha ba.
Wani irin ƙwarin guiwa kalaman Ishaq suka ƙarawa Saifuddeen, nan suka cigaba da tattauna hira atsakaninsu ta hanyar gudanar da text message.
Zaleeha kuwa daga Jomapwd kai tsaye gidan redionsu na vission FM. ta nufa, tundaga fitowarta acikin motarta gaba ɗaya kallo ya dawo kanta, haƙiƙa Zaleeha cikakkiyar mace ce dake iya ɗaukar hankalin kowani ɗa na miji, cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta ƙarasa babban ɗakin da suke tantance shirye shiryensu kafun su turashi izuwa ɗakin watsa shirye-shirye, saida aka tantance shirin nata na wannan rana kafun aka watsashi tayanda kowa zaijisa raɗau batare da wata matsala ba.
Zama tayi akan wata kujera wanda keda ƙafafun taya, ahankali take jujjuyawa yayinda ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayarta ta ciro tare da saƙala earpiece acikin kunnenta, cool music na Edsheeran ne ke tashi acikin earpiece ɗin nata, ahankali take jujjuya kanta alaman waƙan na taɓa zuciyarta sosai, luf tayi ajikin kujeran tare da kwantar da bayanta kana ta lumshe kyawawan idanunta, tunaninsa ne yayi mata tsaye acikin ranta, wani irin ƙauna haɗi da begensa ne suka cika zuciyarta, bazata taɓa cire rai da rabo ba akansa saba, haƙiƙa ita mai raunice hakanne ma yasanya soyayyarsa ke wahalar da zuciyarta, inama da ace wani zaiji abun da takeji, inama da ace ƴan uwanta zasu fuskanci mai takeji tabbas tasan da kowa sai ya jinjinawa girman soyayyar da takeyi masa, tanajin sonsa har cikin ƙashi da bargo, haka kuma tanajin soyayyarsa tamkar jinine dake gudana ajikinta ako yaushe, hawayene suka cika idanunta sakamakon rauni irin nata.
Ajiyar zuciya Raveel yasauƙe, wanda tun ɗazun yake tsaye yana kallonta, ayayinda tayi nisa cikin begen masoyinta, shikuma alokacin yakejin kamar zuciyarsa zata tarwatse saboda ƙaunarta, son Zaleeha yake da duka zuciyarsa, hawayene suka cika idanunsa, hango manager dake ƙoƙarin tahowa garesu da yayi yasanyashi saurin shanye hawayensa, tare da komawa cikin wani ɗan balcony ya tsaya don sam bayason manager ɗin ya gansa, saboda rauninsa ya bayyana sosai ta yanda bazai iya ɓoyewa ba.
Yana sako ƙafarsa cikin babban falon wanda yakasance kamar ɗakin hutu ga ma'aikata gidan radio'n vission FM ɗin wani irin walagigin ƙaunarta ne ya daki ƙahon zuciyarsa, yayinda ya lumshe idanunsa tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin ta da ya cika ɗakin, ahankali ya buɗe idanunsa tare da sauƙesu akanta, sam batasan da zuwansa ba kasancewar haryanzu idanunta arufe suke, sannan zuciya da ƙwaƙwalwarta sunyi nisa wajen tunanin abincin ruhinta, ahankali yatako ya ƙaraso gareta, cikin kulawa yaƙira sunanta, sam bata jisaba don tayi nisa atunanin da takeyi, kujera yajawo tare da zama yana facing ɗinta, hannunsa yakai ya zare earpice ɗin dake kunnenta, da sauri ta ware idanunta da sukayi ja ta sauƙesu akansa, cikin mamakin ganinsa da kuma yanda ya cire mata earpiece ɗin kunnenta taɗa kallesa kana tayi ƙasa da idanunta.
Murmushi Manager yayi tare da cewa.
"Barkanki da hutawa gimbiyar mata".
Cikin takura ta amsa masa da yauwa acan ƙasan maƙoshinta, hakanan ganinsa yasanya taji ba daɗi acikin ranta, itafa yanzu hakanan ta tsani duk wani mahluƙin da zaizo mata da zancen soyayya, ayanzu mutum ɗaya kawai take muradi kuma tana nan tana jira ya taho mata da soyayyarsa,
"Zaleeha!" Manager yaƙira sunanta murya asanyaye.
Bata amsa masa ba bata kuma ɗago kanta ta kallesa ba, sam ayanzu batason damuwa, hutu da nutsuwa kawai take da buƙata.
Ganin cewa bata amsa shibane yasanyashi cewa "Kiyi haƙuri Zaleeha, bansan da yaushene kuma tayaya bane nakamu da sonki, amma tabbas inasonki sosai, ina fatan zamo warki mata agareni Zaleeha, nasan kina ganin girma ƙima da kuma mutumci na, amma banda yanda zanyi akan soyayyarki Zaleeha, inajin kaina tamkar ƙaramin yaro akan soyayyarki, bazan gaji da fallasa miki sirrin zuciyata ba, don ina fatan samun nasara agareki!".
Sai alokacin Zaleeha ta ɗago idanunta ta kalleshi, inama da ace shine zaune agabanta haka yake furta mata daɗaɗan kalaman soyayya? inama da ace zata kasance da masoyinta kasantuwa