Showing 18001 words to 21000 words out of 176868 words
Chapter 7 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
leda a Ramadan kaga sai ka karb'eshi bayan salla in an dawo sai ka bashi sana'arshi kai ka koma pure waternka ko?."
Ido suka zuba mishi baki d'aya,
shi kuwa ba tare daya bi ta kan kallon da duk suke mishiba ya matso kusa da Dottijon cikin nitsuwa yace.
"Kana ji ko baba Bello shi Balarabe ruwa yake sedawa da kayan zak'i irin namu na yara,
to kuma kaga ga Ramadan yana zuwa to duk abin saidawa in dai na cine cinikinshi ya mutu da rana sai dai in darene,
to kaga ita kuma kasuwa da rana takeci,
shi kuma d'an dukkune kullum zuwa yake da safe bayan sallan isha yake komawa,
toh shine yaketa nazarin wani abu zai fara saidawa cikin azumin,
da yayi zaton zaike saida dabino da kwakwa to gsky itana sana'ar yawace kuma kada yaje garin talla ya tsalli dabino ya afa a baki."
Ya k'arishe mgnar cikin tsokana da wasa,
k'eyarshi Saifuddeen ya bugi tare zare mishi irin yadda akewa yara masu surutu,
dariya sukayi baki d'aya ganin yadda Jabeer ya tura baki tare da cewa.
"To nayi shiru."
shi kuwa ogansu Jabeer gyara zama yayi tare da cewa.
"Baba Bello bananma da wuri zaka shiga itikafin ne?."
cikin kauda zancen Dottijon yace.
"Waya ce da kai itikafi nake shiga,
kawai dai ina ajiye kasuwancin ne da ramadan sabida tsufa yazo kuma azumi na wahaldani."
Murmushi kawai Alhaji Adamu yayi sabida yasa Baba Bello itikafi yake shiga shi kuma yana b'oyewa sabida gudun riya,
shiyasa yake ce musu hutun Ramadan kawai yakeyi.
shiko Dottijon cikin kulla ya kalli Saifuddeen kana murya a tausashe yace.
"Yaro na zaka iya yawon bin shago layi-layi kana raba musu ledodi, suna yi maka biyan bashin daddawan k'auye?."
murmushi yayi tare da gyad'a mishi kai alamar zai iya.
Shiko Dottijon sauk'owa yayi daga kan keken nashi kana ya zauna kusa da Saifuddeen cikin tattausan lafazi yace.
"Kullum in azumi yayi ina barin kasuwa duk costomomina sai dai suyi ta kame-kamen sayan leda wurin wasu,
anayin salla kuma da kwana biyu zan dawo to duk masu kawo musu sai su bari inci gaba da kawo musu kamar kullum to amman tunda gashi bana Allah ya had'ani da kai, in dai ka amince kayi al'k'awarin rik'e amana to zan kaika wurin babban dilanmu da yake bamu talla bisa farashi mai sauk'i,
zaike baka kaya ba tare da ka bashi ko asiba,
sai kai kuma ka tallata ka d'ora ribarka,
misali yau in ka kawo bazasu baka kud'iba sai gobe in ka kawo musu sai su baka kud'in na yau,
na yau kuma sai ka kawo musu na gobe.
to wasu ba ruwansu kana kai musu zasu biyaka,
wasu kuma dole sai goben,
to anan amanar da nakeso ka rik'e zan kaika gaban dilanmu amatsayin kai jikanane dan in baisan wani nakaba bazai bakaba,
in ya amince zai baka kuma zan had'aka da costomomina baki d'aya, nasan duk masu amana da gsky ne, suma kuma zan basu amanarka kada su ganka bakaji su cuceka, nasan zaka iya kasuwancin kam tunda kayi karatu zaku rink'ayin komai a rubuce."
cikin lumshe ido Saifuddeen ya had'e hannunsu wuri d'aya kana ya jinjina mishi sannan ya zaro biro ya fara rubutu a tafin hannunshi saida ya gama kana ya nunawa Jabeer nan Jabeer ya fara karanta abinda ya rubutan.
"In sha Allah Baba bazan kasance mara gsky ba a cikin had'akarmu,
nayi alk'awarin rik'oda gsky da amana bazan kunyataka ba,
ga Oga Adamu da abokina Jabeer da sauran maikatan shagon nan su zama shaida, Allah kuma ya bamu sa'a ngd matuk'a Allah ya k'ara lfy da wadata."
Murmushi sukayi baki d'aya,
daga nan Dottijon nan yayi gaba Saifuddeen na binshi a baya har shagon babban dilansu na leda,
nan ya gabatar dashi ga Alhaji Babayo,
ba wani dogon bincike Alhaji Babayo ya aminta da Saifuddeen sabida ganin Baba Bello ne ya kawoshi Dottijon da sunfi shekaru 20 suna tare a harkar leda.
shi kuwa Baba Bello ya musu bayanin Saifuddeen kurmane amman yana gane duk abinda ake cewa in yana ganin bakin mutun.
an yarda tuni an rattaba sunan Saifuddeen a jerin sunayen masu amsar talla,
yasa hannu shaidu sun saka hannu.
daga nan suka juya Baba Bello ya tasa Saifuddeen a gaba duk inda yasan yana kai ledodi saida ya nuna musu Saifuddeen yana ce musu jikanshi ne, kuma shi zai rink'a kawo musu Leda cikin azumi har sai bayan sallah shi zai dawo,
to dama duk kostomominshi sun san da baya kawo musu leda cikin azumi to sai sukaji dad'in wannan ci gaban koda sukaje shagon Alhaji Ibrahim baban Hisham yaji dad'in abun sosai ya sanya albarka haka dai duk wunin wannan ranar kam sukayi shi ranar bag d'in pure water takwas kawai ya saida sai dai ya saida su Coca-Cola sosai.
Sun bari akan sai ana gobe azumi zai fara tallan ledan tunda ranar Baba Bello zayi zuwan k'arshe sai kuma bayan sallah.
Anayin sallan magrib Salisu yazo ya d'aukeshi kamar kullum,
yau wurin mai shayi sukaje kwai aka soya musu da indomi kana sai ruwan tea,
bayan sunci ne sukayi sallan isha, kana suka kama hanyar Dukku.
Koda suka isa Saifuddeen na sauk'a Salisu ya zaro dubu biyar d'in balance ya mik'ashi,
amsa yayi kana ya zare 2k ya bashi yace yaje ya sayawa Mamanshi sugar da Lipton baiso karb'a amman dole ya amsa,
shi kuwa Saifuddeen yana shiga gida kai tsaye d'akin Umminshi ya shiga inda ya sameta ita da Aunty Nina suna hirarsu.
Bayan sun gaisane ya mik'e tare da yiwa Ummi alamun bari yaje yayi wonka.
To tace mishi kana sukaci gaba da hira,
shi kuwa solle jikinshi yayi suk'al kana ya shafa mai tare da fesa turare,
canza kaya yayi sannan ya nufi tsank'aya wurin Bappa Ali duk da yasan yau al'hamis ne ba karatu so ya kuma san canne wurin zaman Bappa Ali ko yaushe bayan sun gaisane ya mishi bayanin canjin sana'ar da zaiyi da tsarin kasuwancin da dokokinshi,
sosai Bappa Ali ya gamsu da hakan addu'a yayi da fatan al'khairi.
Koda ya tashi tafiya sai ya kwaso cinikinsa na yau duka da riban da jarin duk dubu 3 ne.
sai ya kuma zaro da sauran dubu ukun balance d'in ya had'asu inda suka bashi dubu shida kenan.
Cikin nitsuwa ya mik'awa bappa Ali.
Cikin tsuke fuska da fad'a bappa Ali yace.
"Me zanyi dasu? shin ba nacema Ka dena bani kud'iba in dai ban bakaba to ai baici ka baniba,
fatana Allah ya bud'a maka yadda zakayi kaci gaba da rik'e marayun k'annenka dani bappanku na gaza rik'ewa."
da sauri ya girgiza mishi kai kana ya rubuta mishi.
"Dan Allah Bappa Ali ka amshi kud'innan in dai ba rainawa kayiba, meyasa kullum in na baka abu baka amsa,
to in ban makaba waye zanyiwa kainefa uba a garemu ka sanya al'barka a lamarinmu in bani dashi zan baka ne?."
to ganin ranshi ya b'acine yasa Bappa Alin amsar tare da samishi al'barka.
Har ya tashi sai ya kuma zauna ganin Bappa Alin ya rik'o hannunshi bayan ya zaunane yake shaida mishi wannan mutumin daya kad'e Nuruddeen ya kawo musu kayan azumin.
Kama daga shinkafa, taliya, doya, Couscous, indomi, mai, manja, magi, gishiri, onga, kwai madara da Milo sugar Lipton, da kud'i 10k.
wani irin tsuke fuska Saifuddeen yayi tare had'e rai sai ya kuma yiwa bappa Ali alamun tambayar sun karb'ane?.
kai bappa Ali ya gyad'a mishi alamar eh sun amshi kayan,
cikin takaici ya...
By
*GARKUWAR FULANI*
8/
*NAKASA BA KASAWA BACE*
*PAGE 5*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
πππππππππππππ
_Wannan shafi gaba Ιayanshi tukuicine da saudaukarwa ga Umar ibrahim Wambai, Allau rabbi ya baka lafiya!_
Free pageπ€π»
A hankali ya koma ya zauna, rai a b'ace ya fara rubutu.
"Meyasa kuka karb'a ne? Bappa Ali wancan karonma da ya kawo saida nace muku kada ku amsa!
ai tunda muka rasa Ya Nuruddeen mgna ta k'are munce mun yafe mishi to me sa zayi ta d'awainiya damu, ko yana zaton abinda yake mana zaisa mu manta tabon daya zama sanadin samuwarshi a ah'linmu ne?."
Gyara zama bappa Ali yayi kana ya fuskanceshi cikin sanyi yace.
"Kana tuhumarshi kan shine ya kashe mana Seyo ne?."
da sauri ya girgiza kansa alamar a a.
Shiko Bappa Ali ido ya kuma zuba mishi tare da cewa.
"To haushinsa kakeji ne? Kodai baka yafe mishi bane? Ko baka yarda cewa k'addara bace da tsautsayine ya rufta mishi?."
cikin lumshe ido yake jujjuya kai,
sai kuma ya bud'e idanun nashi da tuni sunyi jazir dan tuno d'an uwanshi da k'unar da yakeji a ranshi.
murya a tausashe Bappa Ali yaci gaba da cemishi.
"Nima da Umminka k'in amsar kayan mukayi,
koda aka shigar da kayan su Mudassir nasa suka fara fitar da kayan,
ganin ana fidda kayanne ya sashi cewa aiyi mishi sallama dani,
niko sai blnace ya shigo daga ciki sabida lokacin akwai yara a wojen suna karatu."
shiru Bappa Alin yayi tare da sharte guntayen hawayenshi kana yaci gaba da cewa.
"Yana shigowa gaban Umminka dasu Rahma ya durk'usa duk da girmanshi da shekarunshi da arzik'inshi ga d'anshi Arabi wanda zai kai sa'an Seyoji yana ganin mahaifinshi ya rusuna a gabansu shima sai ya rusuna."
Cikin zubda hawaye Bappa Ali yaci gaba da cewa.
"Suna durk'usawa sai Alhaji Gid'ad'o yayi ta zubda hawaye cikin rawan murya ya kalli Umminku dasu Rahma hawaye na zuba yace.
"Kuyi hak'uri ku gafarceni, nasan duk abinda zan muku bazaku tab'a farin ciki dashiba,
nasan na cutar daku cuta mafi muni tunda na kashe muku Garkuwarku,
wlh bawai dan in biyaku bane ko wani abu yasa nazo na kawo muku yan wannan kayan ba a a,
sai dan nasan nine na kashe me ciyar daku kullum hankali na baya konciya in na tunaku saina rasa sukuni tunda na buge Nuruddeen dan Allah ku gafarceni ku dena k'in abinda nake kawo muku halal inkune tunda na kashe mai cidaku."
cikin rawar murya da zubda Hawaye Ummi tace.
"Ba kaine ka kasheshiba dan babu mai rayawa da kashewa sai Allah, nasan kwananshi ne ya k'are,
amman in mun amshi kayan Saifuddeen zaiyi fad'a ranshi zai b'aci shiyasa bazamu amsaba."
da sauri Arabi yace.
"Dan Allah Ummi ku amsa ku bawa Saifuddeen hak'uri hankalin Abbana a tashe yake tunda ya buge Nuruddeen please Ummi ku amshi abincin nan wlh in baku amsaba zaiga kamar baku yafe mishi bane."
rumtse ido Bappa Ali yayi kana yaci gaba da cewa.
"Jin haka yasa ni cewa ba komai mun yafe musu mun kuma gode Amman kada ya k'ara kawo mana wani abun.
haka yasa sukaji dad'i sukayi ta godiya suka tafi suna k'ara bamu hak'uri.
To kaji yadda akayi dan haka ba laifin kowa bane fashe ni Aliyu in kuma na maka laifi sai in kwashi kayan in meda musu."
da sauri ya jujjuya kai kana ya rubuta mishi.
"Kayi hak'uri bappa Ali, duk abinda kayi ya zauna."
to daga nan ya shaida mishi dama yau zai fasa asusunshi da niyar gobe in zai tafi yaje da kud'in ya sai musu kayan abinci mu samman cefenen ramadan da cin kud'i.
bayan ya karanta ne ya kalleshi cikin gwarin guiwa yace.
"Yanzu dai to kada ka fasa asusun ka bari sai azumi ya d'anyi nisa in yaso ka fasa kayi hidiman kayan sallah."
cikin gamsuwa ya jinjina kai tare da cewa.
"Ba matsala hakan zanyi."
daga nan suka d'an tattauna shirye-shiryen Ramadan,
nan Bappa Ali yake sanar mishi an gayyaceshi cewar zaiyi tafsir a masallacin Fada har zuwa saba'an watan ramadan d'in.
nan kuma yace Saifuddeen d'in zaike fassarawa kurame kuma da hannu tunda da dare zaike yin tafsir d'in zai fara k'arfe 8 a tashi 9 nan dai suka gama tsara komai yadda zai tafi.
Daga nan wurinshi kai tsaye woje ya fita wurin abokanshi Mudassir k'anin Ya Adnan sai Salisu da Saminu dan gidan sarkin Dukkun sai kuma Warisu,
duk su lafiyayyune sai dai sun matuk'ar iya body language sabida abokanshi ne tun na yarinta,
bakin titi sukaje suka zauna iska na kad'awa suna tsaka da hira Ahmad yazo d'an Goggo Dada cikin body language Saifuddeen yace mishi.
"Kai a daren nan ka ratse wannan dajin naku,
to ni dai bani raka."
sai ya kuma duggure kan Ahmad dake dariya tare da cewa.
"Yaseen sai kun rakani, yo kewarkuce ai ta sani zuwa,
tunda ka fara zuwa Gombe ka rage zuwa Shabewa Dada ma sai cekiyarka takeyi."
Sai ya kuma harari su Warisu da Saminu yace.
"Su dama wad'annan al'barkacinka suke zuwa,
shine wai Dada tace ai dama saida karenka kake ganin karen wani, ba gashi yanzu tunda ya Seyo ya rasu bata kuma ganin abokanshi ba."
sai kuma yayi dariya kana yaci gaba da cewa.
"Shine yanzu da zan fito nace to Dada bari inje in cekinta miki karnukan naki tunda kice saida karenka kake ganin karen wani."
dariya sukayi baki d'aya kana suka kai mushi bugu,
Mudassir ne yace.
"Hege Ahmad d'an iya juya mgna,
ai hausace haka ba wai tana nufin mune karnukanba."
shi kuwa Saifuddeen mik'a yayi tare da lumshe ido kana ya amshi wayar Saminu rubutu yayi kana ya bawa Warisu karantawa ya farayi da d'an sauti.
"Hege mai dogon k'afa yau zamuyi mgnaninka yaseen bazamu rakaka ba,
dan ni baccima nikeji."
suna jin haka duk sukayi dariya.
Nan dai suka zauna sukayi ta hira,
daga bisanu dole suka raka Ahmad har shabewa suna tafe suna hirarsu ta abokai tamkar ba dareba.
So koda suka dawo dare ya d'anyi nisa basu wani tsayawa ba kowa ya nufi gida.
Shiko Saifuddeen yana shiga gida ya samu Umminshi da Rahma suna hira inda Rahma take goge mishi kayanshi data wonke mishi
tsakiyarsu ya zauna ita Rahma tana k'asa ita ko Ummi tana kan kujera,
haka yasa ya zauna k'asa kusa da Rahma sannan ya jingina kanshi kan cinyar Ummi wanda take rik'e da k'afafun Hayatuddeen tana yanke mishi farce.
numfashi ya furzar kana ya d'ago ya kalli Umminshi dake shafa kanshi,
murmushi yayi kana ya lumshe ido tare da bud'esu ya zuba matasu alamun yana sauraronta
Cikin kula tace.
"Yau Alhaji Gid'ad'o yazo."
ga mmakinta sai taga ya gyad'a mata kai kuma fuskarshi ba fushi,
sai ta kuma sa yar yatsarta manuniya ta shafa gashin girarshi ta kontar dashi kana tace.
"Na k'i amsar kayan nida bappanku, to kuma sai yayi ta kuka yana bamu hak'uri dole bappanka yace mu amshi kayan."
murmushi yayi kana ya gyada mata kai sannan ya amshi rezar hannunta ya juya ya fuskanceta da kyau kana ya kamo hannunta ya fara yanke mata farcen hannunta,
saida ya yanke na yatsu biyu kana ya kalleta tare da dungule hannunshi ya mik'ar da babbar yatsarshi yayi alamun jinjina,
sannan ya jujjuya mata kai alamun karta damu ba matsala.
sai ya kalli Rahma ya lumshe ido ya d'aga hannu yasa bisa goshinta ya sharte mata zubafar data tsastsafo mata sabida zafin anyon.
Murmushi tayi tare da zare bakin igiyar daga jikin kuros d'in,
dan ta gama gugar nashi har ta goge uniforms d'insu Hayatuddeen da Faruq na boko da islamiya.
gyara zamanta tayi suna fuskantar juna,
a hankali ya bud'e bakinshi kana ya had'a lips enshi da alamu furta.
"Sannu Addana ngd."
lumshe ido tayi tare da cewa.
"Godiya kuma a kan me?."
zuba musu ido Ummi tayi tana jin so da k'aunar yaran nata da tausayinsu na ratsa mata zuciya musamman Saifuddeen,
hannu ta d'aura bisa kan Saifuddeen d'in, shafawa takeyi a hankali tare kallon yadda ya manna kanshi bisa cinyarta murya a tausashe tace.
"Babana kayi shiru kamar ranka baiso mu amshi kayan bako?."
jujjuya mata kai yayi kana suka juyo suka kalli Rahma data shafa k'afarshi tare da jan 'yan yatsunsi biyu kana tace.
"Kada ranka ya b'aci muma bisa dole muka amsa bawan Allah nan har durk'usa mana yayi yana kuka yana bamu hak'uri,
k'in amsar kayan zaisa yayi ta zaton ko bamu yafe mishi bane."
murmushi yayi tare da lumshe ido cikin kurma-kurma dayin body language ya had'a hannunshi duka biyu ya karkad'a kana ya shafa gemunshi tare da nuna musu kunnenshi alamun yace.
"Ba komifa na fahimta, ai Bappa Ali yamin bayani."
sai ya kuma kalli Ummi kana ya gyara zama sannan yayi mata bayanin canjin kasuwancin da zaiyi,
haka nan Ummi ta tsinci kanta cikin farin ciki dan wannanma wata alamace dake nuna Saifuddeen inta yana tare da mutanen kirki nagari kuma wannan ya nuna mata kasuwa tasan da Saif d'inta.
"Alhamdulillahi Babana Allah ya sanya al'khairi yasa ka fara harkar a sa'a rabbi yasa ka shiga da k'afar dama."
Amin Amin suka amsa shida Rahma,
kana ya mata bayanin fasa asusunshi nanma tace.
"Hakan yayi yadda bappankun yace haka zakayi,
ka bari tukun kaga yadda kasuwar ledan take."
kai ya gyad'a mata kana sukaci gaba da hirarsu har zuwa 11:36 pm sannan sukayi saida safe,
Rahma ta tafi d'akinsu ita dasu Raihana Ummi kuwa ita da Autanta da Faruq,
shiko Saifuddeen d'akinshi ya tafi,
koda yaje buta ya d'auka al'wala yayi sannan yazo yayi nafilfili daga bisani ya fara karatun Qur'an yayi kusan awa biyu sannan yayi addu'o'in da neman sa'a da nasara a kasuwancinsa ya rok'i Allah ya tsareshi da cin amana sannan daga bisani ya mik'e ya kashe wutan d'akin kana ya matso da fankanshi kusa da gadon tare da k'ara gudun fanka,
gefen katifar ya zauna tare da yin addu'o'in bacci qulhuwa 3 falaqi 3 nasi 3 sannan ayatul kursi'u 1 ya shafa sannan ya konta da hannun dama,
a hankali ya gyara konciyarshi tare da yin mik'a ido ya lumshe yana mai mamakin Al'amarin halittarshi a ranshi yake cewa.
"Anya kuwa ni lafiyeyye ne."
sai ya