Showing 6001 words to 9000 words out of 176868 words
Chapter 3 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
By
*GARKUWAR FULANI*
8/
*NAKASA BA KASAWA BACE*
*PAGE 3*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
_Wannan page ษin nakune gaba ษayanshi ฦดan Hukuncin Allah fans Especially Mom Asas, Zee Ya'u, Jannart Salis, ina muku fatan al'khairi._
~Gareku masu buฦatan biyan kuษin littafin ,turo katin mtn na ษari uku, ta wannan layin 09097853276 ko transfer ta nan 0005388578 jaiz bank Asha Aliyu Garkuwa~
Cikin tsananin razana da tsoro jiki na rawa mai jan motar ya fara kiciniyar taka birki.
Amman ina abin ya gagara, tuni birkinta ya kubce mishi, ido ya zaro da sauri lokacin da yaga motar tashi ta nufi kan Nuruddeen gadan-gadan
ji kakeyi k'uuuuuiyyyyhh.
motarnan ta bugu machine d'in Nuruddeeen bugu mai tsanani wanda yasa, Nuruddeen yayi tsalle yayi sama kana ya fad'o kan bump d'in tsakiyar titin,
"Innalillahi'wa'illaihi rajiun. Hasbunallahu wani'imal wakil."
Shine abinda tarin mutanen dake zageye da Nuruddeen suke fad'i,
yayinda wasu suka ma kasa mgna sai d'aura hannu sukayi a kai, kana wasu sai jujjuya kai sukeyi.
mai mota kuwa da ker ya samu ya fara sarrafa motar har ya samu ta tsaya,
yana fitowa da gudu ya nufi inda dandazon mutanen suke,
kutsawa yayi tayi tsakiyar mutanen har ya samu ya isa,
ido ya rumtse da k'arfi cikin tsananin fargaba ya sunkuyo kan Nuruddeen da yake konce lib bisa titi, ida nunshi a rufe kirib sai numfashin shi dake korar juna,
da sauri ya tallaboshi tare dagowa ya kalli mutanen cikin tashin hankali yace.
"Ku taimaka min mana in d'agashi in sashi a mota."
wani k'ak'k'arfan matashi ne,
yayi maza ya sunkuyo ya ciccibi Nuruddeen kana cikin, d'aga murya yace.
"Biyoni."
yana fad'in haka ya juya ya tsallaka titin zuwa d'aya hannun kana ya nufi cikin asibitin MUSABA dake fuskantar tashan Dukkun,
cikin rawan jiki mutumin ya mik'e kana yabi bayanshi.
suna shiga Reception suka nufa,
ganin sun shigo hajaram majaram yasa Nurse's yin kansu da tambayar meke faruwa,
cikin kad'uwa mutumin nan yace,
"Accident ne ku taimaka doctor ya dubashi."
juyawa sukayi suka kalli juna, kana d'aya daga cikinsu tace.
"Ko an gayawa doctor bazai dubashi ba sai an nemo police."
jin haka yasa mutumin nan juyawa da sauri ya fita,
gudu-gudu sauri-sauri ya tsallaka titin kana ya nufi wurin motar tashi, yana shiga ya nufi Gombe division yana zuwa ya musu bayanin abinda ke faruwa,
ba b'ata lokaci suka had'ashi da police d'aya, kana suka tafi tare,
suna zuwa Doctor in ya amsheshi bisa sa hannun hukuma kana fara bashi taimakon gaggawa, sannan daga bisani ya ce su tafi Medical Center.
Ba b'ata lokaci suka amshi shawararshi suka tafi can,
suna zuwa aka amsheshi.
shi kuwa police yasa d'aya police d'in yaje ya d'auki machine d'n nashi ya kaishi officensu.
kana sun samu wayarshi y'ar Nokia dake jikinshi tanan aka kira Bappa Ali aka sanar mishi meke faruwa.
Lokacin da aka gayawa Bappa Ali yana cikin garin kurugu da yake ranar larabace,
to yaje cin kasuwa,
ana gaya mishi bawan Allah ya bar duk abinda yakeyi ya nufi cikin Gombe kai tsaye Medical Center din ya nufa, inda yana zuwa fargabarshi ta k'aru domin tunda Nuruddeen ya fad'i bai sake bud'e idanunshi ba kuma uwa uba yana konce tamkar gawa komai sai an mishi ga roba a hanci da baki da k'asanshi wannan abu yayi matuk'ar firgitashi, duk da k'arfin zuciya irin na bappa Ali sai da yayi ta kuka,
mutumin daya bugi Nuruddeeen ma sai kukan yake sabida kukan da Bappa Ali keyi ya matuk'ar karya mishi zuciya sai hak'uri yake bashi da neman yafiyarsu.
Cikin raunin murya yake cewa.
"Ku gafar ceni tsautsayine, nayi iya k'ok'arina inga na tsare motata bataje ta bugeshi ba amman ina Allah ya k'addara faruwar hatsarin bani da tsumi ko wayo bare k'arfin hanawa."
sai ya kuma sharte hawayenshi kana yaci gaba da cewa.
"Tunda nake ban tab'a shiga cikin tashan Dukku ba, sai yau, ashe ashe ban saniba masifa ke kirana."
shi kuwa Bappa Ali ya gaza cewa komai domin da ganin mutumin ya girmeshi kuma bisa dukkan alamu mutum ne mai daraja da ka ganshi kasan mai kamalane,
shi kuwa mutum shirun Bappa Ali sai ya sa mishi rauni yana ganin shike nan ya cucesu,
yana bashi hak'uri yana tuno dalilin zuwanshi tashan,
dan matarshi da ta kasance yar Ngalda to kullum shi ke kaita to yau kuma har ya shirya zai kaita sai kuma motocin kayanshi suka iso, so shiyasa yace bari ya kaita tasha ta shiga motar kasuwa, to shinefa ya kaita kenan yana fitowa wannan hatsarin ya auku.
Bappa Ali kuwa ganin yanata bashi hak'uri ya sashi yin k'arfin halin cewa.
"Ba komai Allah ya bashi lfy, ai shi tsautsayi ba ta inda baya wakana."
sosai mutumin ya d'anji sanyi kana yace.
"Wacce uguwa kuke ne?."
cikin sanyi Bappa Ali yace.
"Har Dukku muke."
da sauri yace.
"Ina mamanshi?."
kai ya jinjina kana yace.
"Mamanshi da babanshi duk basu saniba, suna Dukku ni kuma dama ina Kurugu to da aka kirani sai na taho nand'in.
Yanzu in ba matsala in akwai masu kula dashi zan wuce Dukku inje in sanar musu."
cikin kad'uwa yace.
"To kai waye d'inshi ne?."
"Ni bappanshi ne k'anin mahaifinshi kuma mahaifin nashima baida lfy."
kai ya jinjina kana ya zaro kud'i a aljihunshi sannan ya mik'a mishi tare da cewa.
"Ba matsala zan kula da komai kayi maza kaje ka sanar musu."
k'in amsar kud'in yayi, shi kuwa mutumin ya sashi karb'a a dole.
Haka dai ya amshi kudin badon ya soba ya tafi,
shi kuwa mutumin shida kanshi ya zauna wurin kana ya bada duk abinda ya dace na jinyar Nuruddeen.
Shi kuwa bappa Ali daya koma Dukku jiki a mace yayiwa Ummi bayani sai dai ya boye mata hak'ik'anin halin da Seyojinta ke ciki, yace mata da sauk'i sosai baiji ciwoba an dai mishi allurar bacci ne dan ya huta.
To shiyasa hankalin ta bai tashi sosaiba,
Saifuddeen kuma tun lokacin da Yayan nashi ya tafi sai yaja hannun Hayatuddeen suka tafi gidan Goggo Dada, to shiyasa bappa Ali bai tarar dashi a gidaba,
kuma gidan Goggo Dada nada d'an nisa don ita a Shabewa take.
Abba kuwa baida lfy ba damar yaje,
haka yasa Bappa Ali ya juya shida Adnan babban abokin Nuruddeen d'in,
kana sai Rahma.
Koda sukaje gaba d'aya hankalinsu ya tashi ganin yadda Nuruddeen ke kwance tamkar gawa Rahma tayi ta kuka tamkar ranta zai fita,
Adnan yanata rarrashinta,
Bappa Ali kuwa mutumin ne keta rarrashinsa.
Ganin dare ya fara nisa yasa Bappa Ali cewa Rahma ta koma dan har takwas na dare yayi,
jin haka yasa mutumin nan k'iran d'anshi mai suna Arabi yazo.
Kana yace ya maidata Dukku da motar da yazo,
ba musu ya d'auki Rahma ya maidata Dukku,
yana ajeta ya juyo Gombe.
Ita kuwa Rahma jiki a mace ta shiga gida,
Ummi dasu Saifuddeen da Abba dasu Raihana suka tasats a gaba da tambayar ya jikin nashi.
sanin in ta gaya musu gskyar halin da yake ciki ba mmki jikin Abba ya tashi, Ummi ta k'ara shiga damuwa dan haka sai tai ta ce musu jikifa da sauk'i,
koda Ummi ta bata abinci sam ta kasa ci, sai hawaye da take zubdawa time to time, kana tana sa hannu tana goge hawayen dan kar Ummi ko Saifuddeen su gani dan sam ta lura hankalin su a tashe yake.
haka dai sukayi ta jimantawa juna kana sukayi shirin bacci da nufin gari na wayewa Ummi da Saifuddeen zasu shirya suje.
Rahma kuwa har ta konta Ummi ta kuma biyota d'akinsu tana k'ara tambayar yanayin jikin nashi nanma dai boye mata gskyar tayi.
a haka dai suka kwana da fargaba.
A can Gombe kuwa k'arfe d'aya dai-dai na dere Nuruddeen yace ga garinku,
Allah sarki rai bak'on duniya,
bayan likitan ya sanar musu ya cika,
Bappa Ali kam sai ya rasa inda zaisa ranshi kawai sai ya shiga d'akin da gawar yake yayi ta zagaya gadon yana wani irin azabebben kuka maicin zuciya da tada hankalin mai sauraro,
Adnan kuwa kanshi ya kife gefen kan Nuruddeen yana wani irin sassayan kuka mai zazzafan hawaye,
hakan mutumin nan tunda aka gaya musu ya zame a wurin ya zauna bisa kujera yana kuka mai ban tausayi yanayi yana tasbihi da hailala,
sabida hankalin shi yayi matuk'ar tashi tunda yasan shine sanadin mutuwarshi.
Bayan an d'auki gawar an kaita macuwari,
su kuwa duk su uku sai suka nufi masallacin dake cikin asibitin bayan sunyi al'walane suka fara nafifili da k'auna Qur'an tare da yimishi Addu'a.
Koda gari ya waye mutumin nan yayi duk kan abinda ya kamata kafin a basu gawan,
Aka yi mishi wonka aka shiryashi kamar yadda musuluncin ya tanadar mana,
bayan an gama kimtsashi ne, suka barshin nan cikin asibitin tare da Adnan kana shi kuma ya d'auki bappa Ali ya nufi gidanshi dake Fantami,
nan ya sanar musu abinda ke faruwa,
kana ya fara gaiyatar jana'izar,
bayan ya gama abinda ya sauwaqa sai kuma suka nufi Dukku.
Suna isa sukayi cikibus dasu Saifuddeen da Ummi da suke shirin tafiya yanzu.
ganin Bappa Ali da wani mutum a cikin zazzafar mota yasa zuciyar Ummi karaya,
sai tayi maza ta koma cikin gida,
yayinda Saifuddeen kuma ya zubawa Bappa Ali idanu tamkar zai mannasu a jikinshi duk sun kasa yin Magna tuni mak'ota sun taru a wurin anata tambayar jikin Nuruddeen,
amman ba mgna Bappa Ali sai jujjuya kai yakeyi yayinda mutumin nan kuwa yaketa zubda hawaye,
ganin haka duk aka gane cewa Nuruddeen baya raye.
Ita ku Ummi tana shiga cikin gida da sauri Rahma dasu Raihana sukace.
"Ummi meya faru." duk da taji abinda sukace amman ta kasa mgna sai nufar inda Abba ke zaune tayi yayinda shi kuwa yayi mutuwar zaune,
cikin rawar murya tace.
"Bappan Saifu ne ya dawo shida wani mutum."
wani irin zabura Abba yayi sai ya kuma koma ya zauna da sauri sabida azabar da yaji mak'ogoronnshi na mishi.
Dai-dai lokacin kuma Bappa Ali da mutumin nan suka shigo,
gefen Abba suka zauna kana Ummi kuwa ta matsa can gefe ta zauna bisa kujera yar tsuguno gaba d'aya jikinta tsuma yake zuciyarta na harbawa da sauri-sauri,
shi kuwa Abba ido ya zubawa mutumin da ya tasashi gaba yana kuka da shesshek'a a hankali,
cikin firgita da rauni murya can k'asa Abba ya kalli k'anin nashi da matarshi da yaranshi baki na rawa yace.
"Innalillahiwa Inna'ilaihi rajiun."
sai ya kuma rumtse idanunshi wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo mishi masu tsananin k'una murya can k'asa yace
"Mutuwa ta barni ta d'auke Seyo na ko?."
cikin zubda kolla bappa Ali ya gyada mishi kai,
ido ya rumtse kana yayi murmushi tare da cewa.
"Hmmm Seyo na ya tafi ya barni! nasan nima bazan kai bad'i iwar hakaba, zan bishi zanbi bayanshi, Aliyu na tausaya maka zan tafi in barka da nauyi,
Saifuddeen zai d'auki nauyin da shekarunsa basu kai ya d'aukaba."
kawai sai suka had'e kai suna kuka,
hakama su Raihana da Raliyya da Hayatuddeen Amman Ummi da Saifuddeen da Rahma sun gaza kuka domin ance wani zafin ya wuce inda hawaye yake.
Mutumminan kuwa shima kuka yakeyi cur-cur da hawayenshi yana basu hak'uri.
Ita kuwa Ummi wani abu mai tsananin k'arfin taji ya tsoki k'afon zuciyarta ya danne kukan da takeji tana son yi,
hakama Rahma sai d'anta Faruq daya tasa a gaba yana kuka ita kuwa sai dafe zaciyarta dake barazanar tarwatsewa tayi kana zuba musu idanu tamkar zautacciya.
Aunty Nina kuwa matar bappa Ali fargaba yasa cikin jikinta b'arewa.
Saifuddeen kuwa Allah ne kad'ai yasan abinda yakeji a ranshi, in ya kalli Ummi da Rahma ji yakeyi tamkar zai fad'i ya mutu dan tsananin zafin da k'una da zuciyarshi ke mishi.
shi ko Abba yunk'ura yayi a hankali ya tashi kana ya kalli k'aninshi yace.
"Ina gawar take?."
cikin tausayawa mutumin nan ya mishi bayani kana duk masu zuwa jana'iza a dauko motocin a tasha ya biya kudinsu,
nan aka dugguzuma aka nufi Gombe.
bayan sallan azahar aka sallaci gawar, sannan akaje aka binneshi,
motocin nan suka jidi mutanen Dukku suka meda su, kafin su dawo duk yan uwa da abokan arzik'i an hallara tuni Goggo Dada ma da tazo,
dama Ahmad da babanshi kam dasu akaje gombe.
Nan sukayi zaman makoki na kwana bakwai,
mutumin nan shima yayi zaman makoki a gidanshi na tsawon kwana uku,randa akayi sadakan bakwai yaje Dukku ya k'ara basu hak'uri,
nan sukace sun yafe, domin k'addarace ta rigayi fata sannan shi kuma yayi musu al'khairi sosai dan harda kayan abinci ya kawo musu
tuni kuma ya fara azumi settin d'in da zaiyi.
Rayuwa dai taci gaba da tafiya a haka.
Yau da dad'i gobe akasin haka.
Abu da dama ya faru cikin watanni ukun nan.
Bayan wata uku
Ranar wata asabar bayan sallan magrib,
duk suna tsakiyar gida, Ummi ta tasa Rahma dasu Raihana da Raliyya suna d'an hira,
Saifuddeen kuwa da Hayatuddeen suna gaban Abba.
mik'ewa Abba yayi kana ya kalli Ummi da yaranta da suke shawarar a saida kayan d'akin Rahma a kaishi asibiti ai mishi aikin mak'ok'on .
murmushi ya d'anyi kana ya d'auki butar dake gefenshi tare da nufar hanyar ban d'aki yana mai ce musu.
"Uhumm Rahma kenan, kada ku yarda ku saida wani abunku a kaina fa, domin wannan ciwon nawa tabbas wata rana shine ajalina."
d'an tsayawa yayi jin Rahma na cewa.
"Dan Allah Abba kayi hak'uri mu kaika asibiti, bazamu iya ganinka hakaba."
murmushi ya kumayi kana yace.
"Rahma iyayena mafa haka sukayi ta nema min mgni k'arshe har suka rasu ban samu lfy ba, hakama k'annena gaba d'aya Ali ya saida gonakinmu da filayanmu na gado,
a kan nema min mgni yanzu du-du du gonaki ukune suka rage sai wannan filin da ke can bayanmu wanda shi kuma dama nine na sayeshi da sunanku.
dan haka ku dena wahal da kanku ai sauk'in yazo."
yana fad'in haka ya juya ya nufi bayan gidan,
a dai-dai bakin k'ofar ya fad'i.
Wanda kafinma a d'agashi ya cika.
Wannan rana anga tashin hankalin wannan ahlin,
dole Abba kwanan keso yayi,
washe gari da hantsi akayi mishi sutura, wanda tuni k'ofar gidansu ta cika da al'ummar annabi.
Bayan an mishi sutura an kimtsashi kamar yadda musulunci ya koyar damu
anzo za'a d'auki makar ne za'a fiddashi.
da sauri Bappa Ali ya kalli Saifuddeen daya rik'e makarar yanayin wani irin kukan da yasa dukkan bani adam dake wurin zubda zazzafan hawaye,
tuni shima Bappa Ali sai ya zame kana ya ruggumi Saifuddeen da Hayatuddeen dake ruggume dashi, kuka sukeyi wanda duk kan mai imani zai tausaya musu.
shi kam Saifuddeen duniya ta mishi zafi ji yakeyi tamkar bai tab'a farin cikiba, fata yake inama shima mutuwar tazo ta d'aukeshi.
tausayin kanshi da mahaifiyarsu da k'anneshi da yayarshi yakeji tamkar zai d'auke numfashi sa.
Man Liman ne suka janye bappa Ali kana Baba Hamisu yasa hannu ya janye hannun Saufuddeen daga rik'on da yayiwa makarar.
Baba Ashiru kuwa da wani abokinshi wanda kuma malamin islamiyarsu Saifuddeen ne sune suka kamashi ganin yanayin da yake ciki,
cikin sanyi Baba Ashiru ya cewa Hayatudden.
"Deen je ka kawo min ruwa.
cikin kuka ya mik'e kana ya kawo ruwan amsa yayi kana ya kalli Saifuddeen da idanunshi sukayi jazir tamkar zasuyi aman wuta, ganin bazai k'arb'a bane yasa Malaminshi amsar ruwan ya kai mishi har baki,
kana cikin sanyin murya yace.
"Saifuddeen kasha ruwa zakaji sanyi a ranka."
a hankali ya fara shan ruwan domin jin zuciyarshi yake tamkar ana soya mishi ita,
ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa akai akai kana hawayenshi suka tsagaita,
Ya Nuruddeen d'inshi ne ya fad'o mishi a rai, tabbas da yana raye da bazai bari kukansu ya tsanantaba,
wani numfashi yaja kana ya kalli Malamin nashi da yake ce mishi.
"Tashi muje woje Saifuddeen muje ka tsaya a sallaci gawan mahaifinka,
kayi mishi addu'a a madadin kukannan da kake mishi, ka sani dukkan tsanani yana tare da sauk'i in sha Allah muna zatawa d'an uwanka da mahaifinka rahama, kada kayi musu kuka domin su mutanene na gari musu imani da tawakkali basu da abakan musu bare na fada ko gaba,
ka sani babu maraya sai rago, kuma nakasa ba kasawa bace.
Kada kayi ta kuka domin kukanka shi zaisa yan uwanka kuka, kuma kukanku shi zaisa mahaifiyarku kuka har ta kai ga ta kamu da wata cutar ka daure ka jumre ka zama Garkuwarsu."
Cikin tsanani rauni ya mik'e tare da yi mishi alama da yaji zai bari,
daga nan sukaje suka sallaci gawar kana aka kaita makwancinta.
Nan aka zauna zaman makoki.
Yau akayi sadakan Uku, duk da haka Bappa Ali dasu Malam Ashiru da Baba Hamisu dasu Saifuddeen d'in suna zama dan akwai masu zuwa gaisuwa.
Bayan sallan azahar ne duk suna zaune a gindin bishiyar limis dake harabar massalacin k'ofar gidan nasu,
wasu maza su uku sukazo wanda kusan abokan Abban ne bayan sun gaisa ne d'aya daga cikinsu ya zurawa Saifuddeen idanu yana kallonshi ido cikin ido,
shi kuwa Saifuddeen bai kauda idanshi bane dan ganin mutumin yana jujjuya kai alamun zaiyi mgn to sanin in ba kallon bakinshi yakeyi ba bazai gane abinda yake fad'anba shiyasa ya tsurawa mutumin ido,
shi kuwa mutumin cikin jujjuya kai yace.
"Allah sarki duniya mutuwa bata zabi,
Allah bai barin wani dan wani yaji dad'i."
sai ya kuma kalli su Bappa da Malam Ashiru da suke jinjina kai sannan ya meda hankalin shi ga Saifuddeen tare da cewa.
"Da ana bawa mutuwa zab'i ai da an bata zab'i ta d'auke wannan nakasasshen ta bar Nuruddeen da shike kula da rayuwar k'annenshi."
da sauri su Bappa Ali suka zaro ido tare da cewa.
"Subahanallahi Mala Bala wannan wanne irin mugun furuci ne?."
kai jinjina musu tare da jaddada musu cikin rashin iya mgna yace.
"A ai gsky ne Malam Ashiru shi wannan dame zai amfani kanshi ma bare ya amfami wasu,
yaron dashi da dutse bashi da banbanci ai su Rahma sun tagaira da mutuwa ta d'auke Nuruddeen