Showing 111001 words to 114000 words out of 176868 words

Chapter 38 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

mall malad west Mumbai* kasancewar nan yaje yayi musu sayayyan ƴan abubuwan buƙatansu dangin kayan sawa da duk wasu abubuwan da baza'a rasa ba shida Saifuddeen. 

Aje ledodin yayi akan gado yana me duban Dr Adnan da Ahmad wanda yake ƙoƙarin zuge jakan kayansa.
Murya asanyaye yace.
"Ya Adnan lokacin tashin naku yakusa ko?".
Murmushi Dr Adnan yayi tare da dafa shoulder ɗinsa cikin kulawa yace.
"Badai kuka zakamana ba".  Ɗan murmushi yayi tare da son maida hawayenshi tare da cewa
"Sai kace ɗan ƙaramin yaro, kawai dai zanyi missing d'inku".
Dariya Ahmad da Adnan sukayi Ahmad ne yace.
"Ehem dakai ɗin babbane? sakalallen Ummi kawai! Ba gashi har idonka ya ciko da ruwan hawaye ba".
Dariya sukayi su dukansu kana suka nufi hanyar fita. Hayatuddeen ne ya riƙewa Dr Adnan jakansa, kana suka fice daga cikin ɗakin hotel ɗin.
  Kaitsaye asibiti suka nufa don yin sallama da Saifuddeen.

Kamar koda yaushe kwance yake akan gadonsa yayinda kyawawan idanunsa ke rufe, ahankali Dr Adnan ya turo ƙofar ɗakin ya shigo kana su Ahmad suka biyo bayanshi,   Jikin gadon ya ƙarasa tare da sanya hannunsa yaɗan taɓa Saifuddeen. 
Ahankali ya ware idanunsa wanda samansu ke ɗauke da zara-zaran eye lashes da suka matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau, ganin Dr Adnan ya sanyashi sakin tattausan murmushi, shima Dr Adnan ɗin murmushi yayi tare da cewa.
"Zamu wuce Saifuddeen lokacin tashin jirginmu yakusa."
Sai kuma ya d'an kalli sajenshi kana yaci gaba da cewa.
"Allah Ubangiji ya ƙara maka lafiya! Yasa nanda wata d'aya ka mik'e tsaye da k'afafunka".
  still murmushi Saifuddeen yayi tare da jinjina kansa kana yayi masa alamar godiya.
   Kallonsa ya maida kan Ahmad tare da miƙo masa hannu, hannunsa Ahmad ya kama idanunsa cike tab da ƙwallan tausayin abokinsa kuma d'an uwansa, ganin hawaye kwance a idanun Ahmad yasanya Saifuddeen girgiza kansa alaman kada ya bari hawayen idanunsa su zubo, da sauri Ahmad ya shanye hawayensa tare da juyawa da sauri yafita daga cikin ɗakin don bayajin zai iya jure tsayuwa agaban Saifuddeen batare daya zubda hawayensa ba.

  Cikin dakiya Dr Adnan yayiwa Saifuddeen bankwana don shima hawayenne cike a idanunsa kawai dai shanyewa yake dan kada ya raunata zuciyar Hayatuddeen.
Tare da Hayatuddeen d'in suka fito kuma shi ya rakasu har airport saida yaga tashinsu sannan yadawo asibitin domin zuwa yanzu Hayatuddeen ya zama ɗan gari a india.

Nigeria k'asarmu ta gado.

Su Dr Adnan sun dawo gida cikin halin ƙoshin lafiya yayinda dawowarsu ya ɗan sanyaya zuƙatan masoyan Saifuddeen kasancewar sunji kyakkyawan labari daga garesu, inda hankalin Ummi ya ɗan daɗa kwanciya musamman da Dr Adnan da Ahmad suka shaida mata cewa ayanzu Saifuddeen har ɗan iya motsa jikinsa ya keyi, sannan kuma sauƙi yana samuwa sosai, inda kuma suka shaida musu cewa sun bar asibitin dake new delhi sun koma wanda ke garin Mumbai.
   Adda Rahama kuwa ganin mijinta da jin labarin jikin ɗan uwanta yasanya hankalinta ya ƙara kwanciya don dama takusa shiga watan haihuwarta gab take da fita a wata na takwas. 

Daren randa suka dawo bayan Ahmad ya gama kontarwa Ummi hankalin ganin dare ya tsala ne ya mik'e tare da kallon Raliya cikin sanyi da begen matarsa wata uku har an shiga na hud'u kenanfa.
"Tashi muje ki hada min ruwan wonka."
yace da ita,
kai ta rausayar tare da mik'ewa tabi bayanshi dan tabbas ta hango wutar begenta da sha'awarta a idanunshi.
Suna shiga bedroom nata yasa hannu ya jawota suka fad'a kan gado blanket ya jawo ya rufesu tare da cewa.
"Hak'uri nafa ya k'are ina gab da macewa in ban samu d'umin jikinki ba."
ido ta lumshe tare da shigewa jikinshi.

Hakama Ya Adnan sam ya kasa d'agawa Adda Rahma k'afa duk da tsohon cikinta.

Sati ɗaya da dawowan su Dr Adnan Ummi da Ishaq da kuma mahaifiyar Ishaq ɗin suka shirya tsab don zuwa India,
   wata ranan Asabar da sanyin safiya jirginsu ya ɗaga zuwa India.

India.

Hayatuddeen ne zaune akusa da gadon Hamma Saifuddeen d'inshi wayarsa dake cikin aljihun wandonsa tasoma ƙara, ciro wayar yayi tare da duba sunan me ƙira "Zakari".
shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, murmushi yayi dan tuno kullum sai Zakariyya yayi ta musu fasifar su dena yanke mishi suna suna medashi sunan wani abu da ban dariya yayi tare da amsa ƙiran kana ya kara akan kunnensa tare da cewa.
"Zakari namu ina kake ne?."
Zakariyya dake jingine da jikin motar Zaliha yanajin Hayatuddeen ya ɗaga wayan yaja tsaki tare da cewa.
"Yana cikin wondonka banzaye kawai, masu mgnar banza."
dariya sosai Hayatuddeen yayi kana yace.
"Yi hak'uri Ya'u namu."
tsakiya ya kuma ja kana yace.
"Gwara dai ba indiye ya akayi ne? Don katashi daga ba gombe ka koma ba indiye mai katon z!".
Dariya Hayatuddeen yayi tare da ɗan gyara zamansa kana yace.
"Amma Zakariyya baka da mutumci.
To Oho dai koma dai menene ina lafiya".
Dariya Zakariyya yayi tare da cewa.
"Masha Allah to yajikin Hamma Saifuddeen Ina fatan da sauƙi sosai ko?".
"Jiki Alhamdulillah da sauƙi sosai wlh,."
Masha Allah. Allah ya kara sauk'i."
"Amin Amin." yace cikin jin dad'i tare da ci gaba da cewa.
"Ya Nigeria?".
"Kai da kake ƙasar Indiyawa mene haɗinka dawani tambayar Nigeria?".
Zakariyya yafaɗa cikin tsokana.
"Ko madai mene ae Nigeria ƙasatace kuma nanne tushena abin al'fahari na."
"To Nigeria tana lfy."
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Ina hajia Zaleeha masifaffiyar yar jarida?".
Hayatuddeen yatambaya cike da neman tsokana.
Dariya sosai Zakariyya yayi tare da cewa.
"Kana zancenta sai gata ta iso".
Duban Zuleeha Zakariyya yayi wacce tasha ado cikin wani tsadadden pink shadda me kyaun gaske, cikin rausayar dakai gefe yace.
"Adda Zaleeha Hayatuddeen ne please gashi ku gaisa".

Zaleeha wacce take ƙoƙarin buɗe murfin motarta kana ta tab'e baki ta amshi wayan batare da tayi masa musu ba dan tasan sai in zai tsokaneta yake ce mata Adda,
cikin zazzaƙan muryarta tace "Hello Hayatuddeen!".
Jin muryan Zaleeha yasanya Hayatuddeen sake gyara zama kana yace.
"Adda Zalees ina wuni ya aiki?".
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
"Alhamdulillah ya mai jiki?"
"Jiki da sauƙi sosai" Hayatuddeen ya bata amsa.

"Allah yaƙara sauƙi".
tafaɗa tare da miƙowa Zakariyya wayarsa. Nan Hayatuddeen da zakariyya suka ɗan taɓa hira daga bisani sukayi sallama.

Jirginsu Ummi na dira aƙasar ta india taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin fargaba, tsoronta ɗaya kartaje tasamu Saifuddeen ɗinta awani hali, Ummun Ishaq ne ta tara musu taxi inda kae tsaye suka faɗa masa inda zai kaisu sabida kwatancen dasu Dr Adnan suka musu,  agaban katafaren asibitin mai taxi ɗin ya sauƙesu, batare da wani shan wahala ba suka isko ɗakin da Saifuddeen ke kwance.
Ɗaya daga cikin nurses ɗin dake kula dashi ne tayi musu jagora zuwa cikin ɗakin,   kwance yake flat akan gado kamar wani wanda yake bacci.
Hayatuddeen dake zaune yana charting da Amina wayarsa ya ɗago da saurin jin muryar Umminsu, wani irin tsananin farinciki ne ya bayyana akan fuskan Hayatuddeen cike da tsananin kewarta ya mik'e da sauri ya ƙarasa gareta tare yana isa ya fad'a jikinta tare da cewa.
"Oyoyo Ummi na!".
Murmushi Ummi tayi tare da sanya hannu ta shafa kansa, cikin ƙaunar ɗannata tace "Na'am Autan Umminshi". dariya yayi tare da duban Umman Ishaq cikin girmamawa yagaida ta, fuska asake ta amsa masa gaisuwan tare da tambayarsa ya mai jiki.
"Da sauƙi, Umma ina Imran" ya bata amsa yana me duban Ishaq dake tsaye yana murmushi tamkar wanda yake kallon abun da sukeyi, ƙarasawa yayi ya kama duka hannayen Ishaq cikin son abokin hamman nashi yace "Ya Ishaq sannunku da zuwa".
  murmushin dake kan fuskar Ishaq ne ya faɗaɗa hannunsa yasanya ya dafa kan Hayatuddeen cike da kulawa yace.
"Auntan Ummi Me jinya barkan ka dai, ya jikin Saifuddeen?!".
Ƴar dariya Hayatuddeen yayi cikin yanayin dayake ciki najin daɗin ganinsu da yayi yace.
"Jikin Hammana da sauƙi sosai Ya Ishaq, don zuwa yanzu yana ƙoƙarin yin wasu abubuwa da kansa".
cikin tsananin jin daɗi su dukansu sukace.
"Masha Allah- Allah yaƙara mishi lafiya".
Ummi ce taƙarasa jikin gadon da Saifuddeen ɗin ke kwance, idanu ta zuba masa tana mejin tausayi haɗi da ƙaunar ɗan nata na ratsa ko ina na jikinta.
Ahankali ya buɗe manya manyan idanunsa, tarwal ya sauƙe ganinsa akan fuskar mace mafi soyuwa agaresa wato UMMI'n sa, cikin tsananin farin cikin ganinta ya sanya hannuwansa ya kamo nata hannun.
Murmushine ya bayyana akan fuskar Ummi'n cikin jin daɗi tace.
"Ashe ma ba bacci kake ba"
Gane abun data faɗa yasanyashi kaɗa mata kai, tare dayi mata alaman cewa. "Koda ma bacci nake indai kece kika tsaya akusa dani dole za farka."
murmushi Ummi tayi dan tana tsananin gane body language , dai-dai lokacin Ishaq ya ƙaraso jikin gadon, tamkar wanda yake gani haka ya ɗaura hannayensa adai dai saitin zuciyar Saifuddeen cikin kulawa yace "Ko wani bai faɗamin ba yanda naji zuciyarka na harbawa nasan kana samun sauƙi".
murmushi Saifudden yayi tare da sakin hannun Ummi ya kamo na Ishaq ya riƙe cike da ƙaunar abokin nasa, mahaifiyar Ishaq ne taƙaraso tare da duban Saifuddeen cike da kulawa tace "Saifuddeen ya jikin naka?"  dayake yana kallon fuskarta ne hakan yasanyashi gane me take nufi,  kansa ya kaɗa mata tare da ɗan motsa laɓɓansa alaman da sauƙi,   sosai su UMMI da Ishaq suka jima awajen Saifuddeen har dare kafun Hayatuddeen yayi musu rakiya inda zasu kama hotel, anan hotel ɗin Sahar International Mumbai suka sauƙa inda Ummi da Ummun Ishaq suka kama ɗaki ɗaya, shikuwa Ishaq nan ɗakin Hayatuddeen ya sauk'a, ganin sun samu masauƙi ne sun ci abinci yasanya Hayatuddeen komawa asibiti wajen Hamman sa...

***
A Nigeria kuwa Yanzu Adda Rahama ta shiga watan haihuwanta, yanzu ma zaune take akan kujera yayinda ƙaton cikinta ya cika mata gaba, aje kofin tea ɗin dake hannunta tayi tare da kai dubanta ga Dr Adnan wanda ke gefenta yana me aiki a laptop ɗinsa, cikin kwantar da murya tace.
"Dan Allah Ya Adnan yaushe ne zanje naga Saifuddeen? koda yaushe idan nayi maka magana sai kace nayi haƙuri ba yanzu ba!".
taƙare maganar tana me langwaɓar da kanta gefe. Murmushi Dr Adnan yayi tare da dubanta cikin son kwantar mata da hankali yace.
"Kiyi haƙuri ba na hanaki zuwa bane, kinsan dai halin da kike ciki yanzuma haka kinsan kinshiga watan haihuwan ki haihuwa yau ko gobe, kiyi haƙuri idan kin haihu zamuje tare dukanmu!".
Sake shagwaɓe fuska tayi tare da cewa.
"Shikenan ai dai kullum haka kake cewa, Allah yasa na haihu lafiya ko sati bazan ƙara ba zanje na gansa!".
Dariya me kama da murmushi Dr Adnan yayi tare da kama hannunta ya shiga murzawa, cike da ƙaunar matar tashi yace.
"Karki damu zamuje ki ga ɗan ƙaninki".
Murmushi tayi tare da ɗaukan cup ɗin tea ɗinta tacigaba da sha kaɗan kaɗan.
Koda dare ya d'anyi nisa misalin ƙarfe 9 naƙuda ta tasowa Adda Rahama gadan gadan wanda har saida yakaisu ga zuwa asibiti, ƙarfe 10 dai-dai ta haifo kyakkyawan ɗanta na miji,me kama da ita sak,  farin ciki awajen Dr Adnan ba a magana, nantake yashiga ƙiran mutane yana sanar musu, koda ya sanarwa mahaifiyarsa baƙaramin murna tayi ba, nan ya bugawa mutanen India yasanar dasu, daɗin dasu Ummi sukaji baya faɗuwa nan yabata waya suka gaisa, inda Saifuddeen kuwa ya ɗauki wayarsa ya tura mata saƙon murnar haihuwar da tayi lafiya tare dayin kyakkyawan addu'a ga yaron data haifa, koda takaranta saƙon sosai taji daɗi inda ta mayar masa da amsa tare da tambayar jikinsa.

Alhamdulillah kulawa ta musamman Adda Rahama ke samu daga wajen mijinta da mahaifiyarshi Dr Adnan inda yaɗau soyayya da tarairaya ya ɗaura ga yaronsu da suka haifa.

Ranan da ta cika kwana huɗu da haihuwa Raihana tazo daga Kaduna, sosai taji son yaron yana ratsata kyawun yaron ba, don idan ma idanunta ba ƙarya sukai mata ba har kamannin Hamma Saifuddeen ɗinsu ta hango akan fuskar yaron. 

Ranan da tacika kwana 7 da haihuwa arananne aka sha shagalin suna wanda yasamu halartar ƴan uwa da abokan arziki, inda yaro yaci sunan SAIFUDDEEN. sosai bikin sunan ya ƙawatar don kuwa Dr Adnan ya buɗe bakin al'jihunsa inda ya gwadawa mai jego da ɗanta gata, anyi taron suna an watse lafiya sai- dai muce masha Allah, koda su Ummi sukaji sunan yaron Saifuddeen baƙaramin murna sukayi ba musamman Ummin nan tace ake kiranshi da Deen.

India.
Yau su Ummi suka cika sati a India kuma yau ne suketa shirye shiryen dawowa Nigeria, sosai kuma suka aminta da sauƙin da Saifuddeen ke samu don ayanzu su kansu sun samu nutsuwa a zuciyoyinsu,  tsab suka gama shirya kayansu, inda suka wuce asibiti don yiwa Saifuddeen ban kwana,  sam Saifuddeen baiso tafiyansu ba saboda zuwansu sosai ya ɗebe masa kewa musamman daya kasance kullum suna tare da abokinsa Ishaq, haka su Ummi sukayiwa Saifuddeen sallama bayan Ishaq ya basa maƙudan kuɗaɗen da Ƙungiyansu ta *Joint National Association Of Persons With Desabilities. (Jonapwd) Gombe state chapter. All the best!👍🏻* suka bada abasa kamar yanda suke bawa kowani member ɗinsu wanda ke cikin hali na rashin lafiya, sam Saifuddeen ƙin karɓa yayi shikuwa Ishaq rufe idanunsa yayi ya dage dole saida Saifuddeen ya amsa bisa sanya bakin Ummi.
Hayatuddeen ne ya rakasu airport inda suka hau jirgi daganan sai Nigeria.

Koda suka dawo agidan Adda Rahama suka sauƙa inda suka duba yaro, daganan Ummi ta wuce gidanta Ummun Ishaq ma ta wuce nata gidan...

Yau Jummu'a ta kasance ranar da Zaleeha ke gabatar da program nata mai taken babu nakasasshe sai rago.
Bayan ta gama gabatar da shirin natane ta shigo wurin masauk'i bakisu,
a hankali ta zauna akan wata baƙar kujera dake cikin office ɗinsu wanda ke cikin gidan radion vission FM.
Sanye take da wata haɗaɗɗiyar doguwar rige me walwali yayinda tayi rollin kanta da mayafin rigar, sosai rigan ta bayyana tsananin kyawunta, wayarta ƙiran iphone 11 pro max ne riƙe ahannunta tana latsawa. Manager da shigowarsa offie ɗin kenan cak ya tsaya yana kallonta, sosai take burgesa komai nata abun so ne ga ɗa Namiji, haƙiƙa yasan Zaleeha dabance acikin mata.
Ahankali yatako zuwa inda take, Zaleeha da hankalinta gaba ɗaya ke kan wayarta ta ɗan ɗago kanta tare da dubansa, ganin Manager da kansa acikin office ɗin nasu yasanya ta sakin murmushin da ya sake bayyana kyawun fuskarta, cikin zazzaƙar muryarta tace.
"Barka da shigowa Manager!"

Murmushi Manager yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, dan sosai yakejin wani abu na musamman a dangane da ita.

"Barkanki dai Sarauniya" Manager yafaɗa yana murmushi.

Aɗan mamakance ta kalleshi jin yaƙirata da sunan sarauniya.

"Sarauniya kuma manager?" tafaɗa tana me ƙoƙarin rataya hand bag ɗinta don dama lokacin tashinta yayi.

"Kin ma wuce haka Zaleeha, ke tamkar zara kike acikin dubbanin taurari! ko ince zinariya"

Yanzu kam sosai maganganun Manager ɗin yabata mamaki don baitaɓa mata irin waƴannan maganganun ba.
Murmushi kawai tayi tare da dubansa kamar zatace wani abu sai kuma taɗan raɓa ta gefensa zata wuce. Da sauri yaƙira sunanta, inda yace.
"Zaleeha!"
Jin yaƙira sunanta yasanya taɗan tsaya tare da juyowa ta fuskance sa.
Gyara tsayuwa yayi tare da zura hannayensa cikin al'jihun wandonsa cikin tausasa murya yace.
"Zaliha Ina sonki! Inada buri da fatan ki zamo matata uwar yarana na".
idanunta ta zazzaro da sauri sai kuma ta fara jan baya-baya ganin yana takowa zuwa gabanta,
da sauri ta rumtse idanunta ganin ogan nata kuma babban mutun ya durk'usa gabanta da guiwowinshi duka biyu,
hankalin ta ya kuma tashi jin yana cewa.
"Na dad'e ina adana soyayyarki a zuciya ta, ina sonki irin so mai kauda nitsuwar mutun, kece fatana ki zame min matata ta biyu, shine cikar burina.
Ina matuk'ar jin tsoro da fargabar kada na rasaki."
Wani azabebben ajiyan zuciya Zaheela taje tare da yin mgnar zuciya.
"Meyasa? Meyasa ne? mutane sukayi mata caaa a kanta, meyasa tun da can basu baiyana kansu gareta ba sai yanzu da Allah ya jarab ceta da son wanin namijin.
ido ta rumtse tare da bud'esu sannan tayi k'asa dai-dai gaban manager d'insu ta durkusa kamar yadda yayi cikin son yakice soyayyarta a zuciyarshi murya na rawa tace.
"Kai matsayin yayane a gareni, koda zan boyewa kowa kai dai bazan boye maka ba Ya Abubakar.
Zuciyata ta cika ta batse tana zubda tururin zazzafar soyayyar da nake mishi, ina gab da rasa lfyar zuciyata muddin ban sameshi ba, ya shigemin zuciya a lokacin da ni kaina ban Sabina, shine fatana, bani da mosoyi samadashi shine kad'ai mahaluk'in da zan iya mallakawa kaina,
shine abinda zuciyata keso. Tabbas da ka gabatarmin da kanka kafin had'uwata da shi to da na aminta da kai."
Idanu ya zuba mata yayinda yake gano wutar so da gskyar mgnarta cikin kwayar idanunta,
cikin tsananin kad'uwa yace.
"Waye ne shi?."
cikin zubda hawaye tace.
"Oho shine abinda nima nake son in sani."
ido ya firfitar cikin azama yace.
"Baki sanshi bane?."
Kai ta gyad'a mishi tare da yunk'urawa ta fita da sassarfa dan kukan dake taho mata.
wani mayataccen murmushi yayi tare da cewa.
"Wannan ai shirmenki ne, dama kin sanshi ya sankine dole in hak'ura amman yanzu dole in nace."

Ita kuwa tana fita ta nufi parking lot nasu,
tana isa wurin tayi kicibus da Abokin aikinta Raveel, ganin yadda take saurine yasashi saurin sa hannunshi ya kamo nata cikin tsareta da ido yace.
"A haka zakiyi draving so kike ki kashe kanki ni ki illatamin rayuwa ne?."
fuzge hannunta tayi tare da cewa.
"Ka sake min hannu."
cikin tsawa yace.
"Ank'i a sake d'in, ni da kika rik'e min zuciyata bance ki sakemin itaba sai ke dana rik'ewa hannu.
Na gaji da ganinki cikin damuwa, yanzu tsawon wata hud'u kenan na fahimci kina cikin matsala ki gaya min make damunki? meke faruwa da rayuwarki?."
tattaro sauran k'arfinta tayi ta fizge hannunta tare da wucewa ta shiga motarta ta figi motar da gudu ta nufi gidansu Bilku k'awarta da tasan sirrin soyayyar da take boyewa a ranta.

Ahmad ne da kawunshi Bappa Ali dasu Warusu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login