Showing 42001 words to 45000 words out of 176868 words

Chapter 15 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

Saifuddeen ribar kwana biyar d'in yake had'awa yayi sayayyan abincin gidansu to zai yi mako biyu kuma yana saka ribanshi a asusu,
riban omonshi kuwa da pure water daya ya koma sai yake ajiyesu dan hidiman yau da kullum.

Ya Adnan kuwa tuni ya fara aikinshi gadan-gadan shida Dukku sai dai ziyara.
Tuni Mudassir ma yaci gaba da karatunshi a G.S.U inda a gidan Adnan d'in yake zama,
Ishaq ma tuni yaci gaba da karatunshi.
Hakama Saminu shima yayi nisa a karatunshi.

Salisu ma yanzu ya ci gaba da kanshi sabida Saifuddeen ya rege mishi kud'in balance sosai to sai in bashida darasi yake fita aiki dan ya samu damar yin hidimomin karatunshi da kula da kakarshi.


Hayatuddeen kuwa tuni ya fara koyan d'inki a wurin Ahmad da shima yanzu yanata cuku-cukun ci gaba da karatunshi inda yake son kafin ya koma cikin gombe Hayatuddeen ya gware a d'inkin,
shi kuma sai ya tafi da kekenshi zaije yaci gaba da karatu,
duk cikinsu Saifudddeen ne da Warisu sune basu samu daman ci gaba da karatun suba.

Sai dai shi Saifuddeen tuni ya samu ya gamawa Raihana da Raliya cuku-cukun karatunsu tuni ma Raihana kam ta k'are secondary school.

Yanzu hankalin Ummi ya fara konciya,

Tuni Ya Adnan kuma ya baiyana soyayyarshi da Rahma amman biki yace sai next year kowa yayi farin ciki da haka.

Koda Ahmad ya koma gombe gidan ya Adnan d'in shima ya zauna.


Kasuwa tayi al'barka kullum Saifuddeen baya fashin zuwa shida Salisunshi,
yana zuwa zai rarraba leda sai ya d'auko omonshi bisa kai sannan ya rik'o botikin pure waternshi dasu Coca-Cola yayi ta yawatawa kuma Alhamdulillahi sosai yake ciniki Allah ya sawa kasuwancin nashi al'barka.

Kota ina yanzu an sanshi a kasuwar gombe.

Yanzu duk kostomominshi suna da number shi yanada number su,
duk mai buk'atan kaya zai kirashi ya kai mishi misali in ledodin su ya kare suna son k'ari ko in suna son abin sha mai sanyi ko omo to kawai sai su mishi text.
Zuwa yanzu duk abo kanshi suna da woyoyinsu.

Yau jumma'a tunda sanyin safiya da suka shigo ya gama reba lododinshi har ya d'auko omonshi da da kayan sanyinshi yanata zagayawa.

K'arfe d'aya dai-dai na rana ya shiga bakin shagonsu Jabeer ya d'an zauna dan abin sanyinshi ya k'are kuma ya gaji shiyasa ya zauna dan ya d'an huta kafin ya d'auko wani,
sunata d'an tab'a hira da Jabeer
bai jima da zamanshi yaji wayarshi na babureshin cikin al'jihunshi na k'irjinshi alamun sak'o ya shiga, a hankali yasa hannunshi ya zaro wayar,
yana dubawa yaga Alhaji Kabiru ne mai shagonsu Mai, Manja, Maggi, kafi, da dai sauranshi.
Bud'e sak'on kana ya karanta sak'on.
"Saifuddeen kawo mana ruwa mai sanyi da molt guda hud'u sai fanta d'aya."
amsa ya maida mishi cewa.
"To gani nan zuwa."
daga nan ya mik'e tare da zaran botikin,
cikin sabo Jabeer yace.
"Allah ko Balarabe wlh ka rink'a hutawa fa."
kai ya jinjina mishi tare da mishi alamun ai.
"Me nema baya gajiya in dai yana samun d'an na kashewa a sama."
daga nan ya juya ya tafi.

Koda yaje ya ciko botikinshi da kayan sanyin kai tsaye ya nufi shagon Alhaji Kabiru.
Yana zuwa sai ya samu suna can cikin shagon bisa dukkan alamu bak'i yayi kuma manyane masu cikar haiba.

Amir ne d'aya daga cikin yan gidan shagon Alhaji Kabirunne ya kalli Saifuddeen tare da cewa.
"Yauwa Balarabe tsallaka ka shiga can ciki yana tare da manyan bak'i ne su zaka kaiwa ruwan sanyin.
jin haka sai ya tsallaka ya shiga,
kai tsaye gefen da suke ya nufa,
yana isa Alhaji Kabirun yayi murmushi tare da cewa.
"Yauwa Saifuddeen balarabe, bamu ruwan sanyi Faro roba hud'u da molt roba hud'u sai ka mik'o min fanta d'aya kasan ni nafi son fanta."
cikin girmamawa fuska k'unshe da murmushi ya matso ya mik'a mishi fantan kana ya rusuna gabansu ya fara zaro gorunan Faro dana molt.
Yayinda tuni idanunshi yana kan d'aya daga cikin bak'in inda yake cewa.
"Gsky Alhaji Kabiru in dai kanada daman saran wannan kaya to wlh ka zuba jarinka domin kamfaninne ya kawo mana talla har gida,
sun bamu tabbacin tabbas akwai riba mai tarin yawa,
to ni kuma naga bazan iya yin harkallan ni d'aya ba."
ci gaba yayi da kallon bakin mutun tare da mik'a mishi roban Faro,
still yana kallon bakin mutum inda yake cewa.
"Koda bashi ne kaci muyi sarin nan in sha Allah zamuji dad'in hark'allan."
sai kuma ya juyo ya kalli d'aya daga ciki wanda ke cewa.
"Ni kaina last week nayi sari yanzu hakama bani da kud'i kuma wlh bashi zanci dan nasan in sha Allah zamu samu riba."
d'aya daga cikin sune yace.
"Kai bani ruwan nan zansha ka tsaya kana kallon bakin mutane."
Alhaji Kabirun ne yayi d'an murmushi tare da cewa.
"Alhaji Sani ai wannan yaron irin Isma'il nane kurmane baya ji."
jin haka yasa wanda aka kira da Alhaji Sani ya d'an tab'a Saifuddeen tare da mishi alamun ya bashi ruwan, juyowar da zaiyi ne yayi dai-dai da lokacin da Alhaji Sani yayi wata mgnar da ta sa Saifuddeen t...!






By
*GARKUWAR FULANI*


*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 9*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



_Ga masu buΖ™atar sayan littafin Nakasa ba kasawa bace, turo katin mtn na 300 kacal ta wannan number 09097853276. Ko kuma ka/kiyi min transfer ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ka/ki turo screenshort na shaidar ka/kin biya_


~Wannan shafi nakune mutanen Group Ι—in Nakasa ba kasawa bace fans two ina al'fahari daku~

Free page



Tsurawa fuskokinsu ido cikin hikima yake nazartan zantukan da sukeyi,
wanda ya rasa madosar zancen,
mik'ewa yayi a hankali ya fara nad'e gammon da yake sawa a kanshi kafin ya aza kwalin omon,
yana mai ci gaba da nazartan kalaman wanda aka kira da Alhaji Sani yana cewa.
"Nan da wata biyu zasu rufe sararwan,
dan haka muyi k'ok'ari mu samu mu sari koda kad'an-kad'an ne,
Company ya talla ta mana ne dan sanin mune manyan costumes d'insu na nan jihar Gombe,
sun kuma bani tabbacin tabbas nanda wata hud'u Maggi zaiyi tsada sosai kusan ninka kud'inshi zaiyi,
domin ya bani misalai da dama,
sun kuma ce wannan damace da aka bawa kuduncin Nigeria, to shiyasa suma musulmanmu suka nemi da a bawa arewacin Nigeria samun wannan garab'asar dan sanin arzik'in musulmi yanada fa'idoji da dama."
d'aya daga cikin sunne ya kuma cewa.
"Ni kam in sha Allah zan k'ok'arta in samu koda kad'an ne."
gyara zama Alhaji Kabiru yayi tare da zaro kud'i yana mik'awa Saifuddeen yayinda hankalinshi ke kan abo kan nashi,
cikin nitsuwarsa yace.
"To zanyi k'ok'ari inga ko zan samu wasu 'yan kud'ad'e na da nike bin bashi sai in sa hannu a ciki."
cikin farin ciki sukace.
"Alhamdulillahi to Allah yasa ka samesu."
Amin Amin yace tare da kallon Saifuddeen da ya juya ya fita zuciyarshi cike da sak'e-sak'e haka kawai yake son yaji tushen zancen.

Su kuwa bayan sun gama tattauna yadda abin zai wakana.
Nan suka sallami Alhaji Kabiru suka tafi.

Saifuddeen kuwa yana fita yaci gaba da zageyenshi na tallan omo da kayan sanyin nashi,
bai fito kasuwarba har k'arfe shida na yamma dan tunda azumi ya wuce suka dawo kamar da sai bayan sallan isha suke komawa.

Yana fitowa yayi al'wala yayi sallan magrib yana fitowa ya samu Salisu na jiranshi,
daga nan bakin Al'kasim suka tsaya nan suka d'anci abinda ya sauwak'a sannan suka wuce Dukku.

Bayan kwana uku da zuwan su Alhaji Sani wurin Alhaji kabiru suka kuma zuwa,
kan su jaddada da mishi batun kadafa ya d'auki abun a shirme ya dai ce musu yana nan yana tabin wad'anda yake bin kud'in.

Iya bukku kuwa ,tun randa suka koma ko mai sunan Saifuddeen taji an kira sai gabanta ya faΙ—i.
A cewarta ba ita ba dukku har gaban abadan, dannan wannan kurman matashin daya zubda mata haΖ™ora biyu a karonsu na forko. Tofa tabbas in antayi artabu dashi a karo na biyu kanta zai sare ya bata a tafin hannunta, Goggo Ummi kuwa da Bappan ta sunji daΙ—in hakan a ransu, kuma sunada niyar sake ziyartarsu.

Yau tunda Saifuddeen ya gama raba ledanshi kana ya yawata da tallanshi har la'asar bayan anyi salla ne ya nufi gidansu Ishaq dan sunyi dashi zaije su Ahmad da Saminu da Mudassir ma duk sunyi dasu zasuje dan sun kwana biyu basu had'uba,

Hud'u dai-dai duk suna had'e a d'akin Ishaq yayinda gari yayi duhu sabida tasowan hadari,
Mama kuwa tuni tai ta musu hidima dan dama sun ce mata danbun zogale sukeso,
nan suka zube suna hira sunaci,
Ahmad ne ya kalli Saifuddeen da yayi shiru alamun nazari had'iye abincin bakinshi yayi sannan ya kalli Saifuddeen tare da cewa.
"Saifuddeen kaci dambun mana."
Kai ya jujjuya mishi alamun bazai cima,
cikin kula yace mishi.
"Meyasa bazaka ciba?."
Mudassir ne ya d'auki ledan pure water ya b'ula kana yashanye fiye da rabi sannan ya kalli Ahmad tare da cewa.
"Ka manna Saifuddeen da zab'en abinci ai baicin dambu."
jin haka yasa Ishaq mik'ewa tare da cewa.
"Yes haka nefa kaga ni nama mance bari inje in gayawa Mama tayi mishi d'anwake dan na lura yana son abincin mata."
dariya sukayi baki d'aya sannan ya fita,
Saminu kuwa gyatsa ya d'anyi tare da cewa.
"Au ashe dama d'an wake cimar matane?."
kai Saifuddeen ya jujjuya mishi alamun a a kam.
fitan Ishaq ba jimawa sai gashi ya dawo nan sukaci gaba da hira.
Bayan kamar awa d'aya da rabi sai ga Imran ya shigo da tire,
kai tsaye gaban Saifuddeen ya ajiye,
sannan ya juya ya fita,
shi kuwa Saifuddeen tiren ya jawo wanda aka cika d'an madaidaicin pilet da d"anwake sai dafaffan kwai guda uku a sama sai mai da magi da yaji,
nan ya fara ci sosai yaji dad'in d'anwaken,
Mudassir ne ya kalleshi tare da cewa.
"Oga ba tayine?."
hararanshi ya d'anyi tare da nuna mishi kulan dambun cikin mishi alamun kunci nabanku.
Ahmad kuma tab'e baki yayi tare da cewa.
"Ahab barshi da d'anwake ko rabi nai bazai ciba zaice ya k'oshi, sai dai ka ganshi yana ture pilet d'in."
ana cikin haka Allah ya sako iska mai sanyi wanda yake nuni da hadarin ya watse lokaci d'aya gari ya washe.

Shi kuwa Saifuddeen baici rabinba ya ture pilet d'in kana ya mik'e ya shiga bathroom,
nan sukayi ta mishi tsiya wai yana nan kamar kifi,
wonka yayi yana fitowa ya bud'e durowan Ishaq ya canza kaya sannan ya kallesu tare da musu alamun shi zai tafi,
sai ya kuma kamo hannun ishaq tare da mishi alamun ya tafi,
nan suka mik'e duk suka fita daga nan duk suka salami juna.

K'arfe 11:15 pm Saifuddeen ya mik'e tsaye tare da ninke sallayan da yayi sallan shafa'i da wutiri, a kanshi
bakin katifarshi ya zauna tare da yin addu'a ya shafa a jikinshi sannan ya kwanta ta b'arin dama.
Can misalin k'arfe biyu dai-dai ya farka bakinshi d'auke da addu'a,
a hankali ya bud'e idanunshi yana mai tuno mafarkin da yayi,
salati ya kumayi ya sanarwa mahaliccinshi,
jingina yayi da jikin pillow sai ya kuma lumshe idanunshi tare da son nazartan mafarkin nashi,
sai ya kumayi saurin bud'e idanun nashi dan ganin abin ya dawo mishi tamkar yana ganinshi a majigi,
a hankali ya mik'e ya fito tsakar gidan nasu inda ya samu ashe anyi musu ruwan sama kamar da bakin gwarya,
cikin nitsuwa ya wuce bandaki fitsarin da ya matseshi yayi sannan ya fito bakin barandan k'ofan d'akinshi ya tsuguna yayi al'wala sannan ya mik'e ya shiga d'akin kana yayi ta nafilfilinshi.

Washe garin da rana irin rana tayi fed'e-fed'e d'innan lokacin gari ya d'anyi zafi sai inuwan gajimare kad'an-kad'an,
sosai ya saida kayan sanyin koda ya gama kafa na uku, sai ya wuce shagon su Jabeer nan sukayi ta hira har aka kira salla bayan sunyi salla kuma sai ya wuce shagon Alhaji Kabiru yana isa ya samu yaran shagon duk sunata hidiman jera kayayyakinsu bisa dukkan alamu sarin da sukayi ne ya iso,
shi kuwa Alhaji Kabiru yana cikin shagon bisa alamu lissafi yakeyi,
ganin haka sai Saifuddeen ya tsallaka ya shiga ciki can kusa da shi ya zauna cikin body language ya gaida Alhaji Kabiru da tuni ya gama lissafin ya had'a takardun wuri d'aya,
cikin mutuntaka da dattaku ya amsa gaisuwar Saifuddeen,
sai ya kuma kalleshi ganin yana mishi alamun tambyar ina woyarshi,
murmushi yayi tare da cewa.
"Wayata gata a aljihuna."
kai ya jinjina mishi kana ya mishi alamun ya fitar da ita zasuyi mgna,
gane hakan ya sashi zaro woyar,
daga nan ya suka fara mgna ta inbox nasu suna musanyan text messages,
sosai Alhaji Kabiru ya nitsu yana kallon text d'in da Saifuddeen ya tura mishi inda yake cewa.
"Assalamu alaikum, Alhaji ya gida ya kasuwa,
Allah ya taimaka."
sai ya rubuta mishi amsa da.
"Wa alaikassalam lfy lau Saifuddeen, Amin Amin. Naga kamar muhimmiyar mgna kakeson muyi, kada ka damu ka d'aukeni kamar mahaifinka ni ina ina jinka tamkar Isma'il d'ina."
Sosai Saifuddeen yaji dad'i mgnar hakan ya sashi murmusawa tare da rubuta mishi.
"Ngd matuk'a Alhaji." sai ya kuma yi shiru bai kuma rubuta komaiba ya rasa ta ina zai faro zancen gane haka yasa Alhaji Kabiru dafa kafad'unshi cikin bashi k'arfin guiwa yace.
"Ina jinka."
shi kuwa rusunar da kai yayi tare da rubuta mishi.
"Kayi hak'uri Alhaji ka gafarceni ranan asabar d'in da ya gabata, ka kirani na kawo maka ruwan sanyi, inda nazo na sameka da bak'i to nayi laifin fahimtar maganganunku, sai dai kuma naji ina sha'awar sanin kasuwancin da suke tallata maka,
in akwai damar da nima zan iya sa hannuna a ciki nima zanyi."
yana tura text d'in sai ya sunkuyar da kanshi,
shi kuwa Alhaji Kabiru murmushi yayi bayan ya gama karantawa cikin kekyawan fahimta ya dafa kafad'un Saifuddeen wanda ya sashi d'ago kai ya zuba mishi ido alamun jin na bakinshi.
Gyara zama yayi tare da zuba mishi idanu cikin sanyin sauti alamun yana son su sirranta zancen yace.
"Me zai hana zaka iya mana, ai duk abinda mai ji zai iya na kasuwanci in sha Allah zaka iya,
sai dai kuma fa wannan al'amarin da kamar wuya."
da sauri Saifuddeen ya gyara zama tare da fuskantarshi yana mai kallon motsin bakinshi ta yadda zai fahimceshi da kyau shi kuwa Alhaji Kabiru cikin tsarkakan zuciya ya fara mishi bayanin kasuwancin.
"Company Maggi ne suka kawo mana tallan Maggi a sirrance a matsayinmu na manyan dilolin maggi,
sun tallatama mana ne dan suna mana sha'awar ci gaba,
sun bamu sirrin company cewa nanda wata biyar magi zaiyi tsadan da bai tab'a yiba,
sun k'ara da ce mana mu fito da kud'ad'enmu mu sari maggin mu ajiye sun sanar damu cikin wata biyar zuwa bakwai company zai k'ara tsadan magi sun bamu tabbacin in sha Allah babu batun fad'uwa sai dai cin riba,
in dai bamuci riba ba toko bazamuyi asaraba."
sai ya kuma d'an tsagaita tare da kallon kekyawan fuskar Saifuddeen kana cikin tausayawa yace.
"Tabbas nasan akwai riba dan yar daddunmu ne suka sanar mana dan son ci gaban junanmu,
to matsalar uku daga cikinmu duk last week mukayi sari bamu da kud'i a k'asa asalima kaga sai yau kayan ya isomu,
sannan masu zuwa sari su zo su sara wanda yawanci bayan wata d'aya suke dawo da kud'in.
To da fari company wata biyu suka bada k'a'idar rufe sarin dan kamar bonanza ne zasuyi mana to sai kuma suka maida k'a'idar wata d'aya.
to shi kanshi uban gidanmu Alhaji Sani wata uku da suka gabata ne ya gama ginin sabon gidanshi inda ya k'aura ya koma yanzu,
to bashi da kud'i sosai a k'asa da zai ranta mana."
ganin yayi shirune yasa Saifuddeen gyara zamanshi tare rubuta mishi.
"To magin kuma kamar na k'asa da nawa zasu bada sarin?."
Numfashi Alhaji Kabiru ya furzar tare da cewa.
"To ai anan gizo ke sak'a domin sun san in sukace kad'an-kad'anne da yawa zasu iya sara,
so sai suka d'an saka hikimar da suma zasu samu wani abu,
sun bada tabbacin cewa mafi k'arancin sarin da zasu bada shine na 2 million,
tofa shisa duk jikinmu yayi sanyi da abun."
cikin d'imuwa Saifuddeen ya maimaita 2 million to shi tunda aka haifeshi yazo duniya baima tab'a ganin dubu dari biyar cikakku bama,
kai ya rink'a jujjuyawa da a zatonshi ko irin d'an sarin 100k ne zuwa 200k nan zai iya zaton zai samesu in ya fasa asusunshi,
tab'ashi da Alhaji Kabiru yayine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi kai ya rink'a jujjuyawa jin tambayar da Alhaji Kabirun ya masa cewa.
"Kanada kud'in sari ne?."
ganin yanata jujjuya mishi kaine yace.
"Shiyasa nace abin da wuya ni du'du du yanzu dubu d'ari biyar nake dashi,
in samu wanda zamu had'a hannu muyi sarinma abin ya gagara ya rigada yanzu cinikaiya ta d'anyi k'asa, amman kaje kayi shawara in kanada yadda zaka samu 500k d'in kamar nawa sai mu had'a in sha Allah zan samu su Alhaji Sani sai mu had'a da wasu in an samu."
Cikin rauni da sanyi Saifuddeen ya jujjuya mishi kai tare rubuta mishi.
"Kud'in sunfi k'arfina bani da hanyarsu ko dalilinsu.
Ngd matuk'a da bani kulawa da shawara naji dad'in yadda kamin kekyawar fahimta."
Cikin kula ya kalleshi ganin yana shirin aza kwalin omonshi a kai alamun zai tafi murya a tausashe yace.
"Ba komai Saifuddeen wlh ni ina jinka tamkar d'ana na cikina,
na kuma yarda da amincinka,
muyi ta Addu'a Allah ya bamu sa'a."
A saman labb'anshi ya amsa da Amin Amin kana ya juya ya fita shagon.

Daga nan yaci gaba da tallanci yanayi cikin nasara,
randa yayi kwana biyu da zuwa wurin Alhaji Kabiru, da dare ya sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login