Showing 105001 words to 108000 words out of 176868 words

Chapter 36 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

yasanya key ya buɗe ƙofar ɗakin, Hayatuddeen na biye dashi abaya haka suka shiga cikin ɗakin, amatuƙar gajiye hayatudden ya faɗa kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin, wanda ke ɗauke da wata luntsumemiyar katifa me laushin gaske, lumshe idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kallonsa Ahmad yayi tare da girgiza kai aransa yana me cewa .
"Allah Ya shirya mana kai Auntan Ummi".
  kasancewar agajiye suke su dukansu, yasanya Ahmad soma ɗan rage kayan jikinsa kana ya wuce bathroom,  wanka yayi tare da ɗauro alwala don gabatar da sallan magriba wanda daf ake da cikar lokacinta, yana fitowa daga cikin bathroom ɗin yaci karo da wandon Hayatudden daya cire yayi wurgi dashi atsakiyan ɗakin, gefe kaɗan ma rigarsa ce wanda ya cire a yashe, cike da takaicin halin Hayatuddeen Ahmad ya girgiza kansa tare da ƙarasawa gaban mirror, don yasan idan yace da Hayatudden ya ɗauke kayan nasa daga ƙasan ma, wani sabon sakalci ne zai tashi, hakan yasa ya ƙyaleshi yashiga fito da kayansa dake cikin jaka don zaɓan wanda zai saka.
  Haka dai cike da sangarta Hayatuddeen ya wuce bathroom shima yayi wanka tare da ɗauro alwala,  koda ya fito awankan kamar yanda ya saba haka ya zazzage kayansu dake cikin jakan kaf akan gado, shidai Ahmad yana kallonsa bai kulasa ba, don yasan me hali baya taɓa fasa halinsa,  riga da wando na jeans Hayatuddeen yasanya cike da sakalci ya dubi Ahmad dake ƙoƙarin rufe kwalban turaren dake hannunsa, ɗan ɓata fuska yayi tare da shafa cikinsa cikin murya me ɗauke da gajiya yace.
"Yaya Ahmad nifa gaskiya yunwa nakeji, gashi bamu sayawa su Hamma Saifuddeen abinci ba!"

"To acici kai-dai baka da wani zance saina ci, yanzun idan mukayi sallah sai munemi waje mafi kusa musai abinci mukai musu, don tabbas nasan zuwa yanzu dole zasuji yunwa".
 Ahmad yafaɗa yana me ƙoƙarin saka takalmi aƙafarsa.
Shi kuwa Hayatuddeen bai sake cewa komai ba har Ahmad yagama kimtsa kansa suka fice daga cikin ɗakin, cikin harshen turanci Ahmad ya tambayi ma'aikatan dake aiki a hotel ɗin inda zai samu abinci,  dayake babu wani nisa tsakanin hotel ɗin da kuma inda ake sai da abincin hakan yasa ɗaya daga cikin ma aikatan yayi musu kwatance,  saida suka fara zuwa wani masallaci da ke nan kusa suka gabatar da sallan Magriba, daga Hayatudden har Ahmad babu wanda daya kafa goshinsa aƙasa ba tare da yayiwa Saifuddeen addu'ar samun lafiya ba, 
suna idar da addu'o'insu suka nufi inda zai sadasu da inda ake saida abinci. 
Koda suka ƙarisa wajen cin abincin, waje ne me kyau da tsabta sannan babu irin abincin da babu awajen,  cimar Nigeria sukaci, inda Ahmad yaci Fish roll and gas meat, shikuwa Hayatuddeen yaci roasted fish da kuma damammiyar madara me kaurin gaske, daganan takeaway sukayiwa su Dr.Adnan da Saifuddeen, kasancewar tsakanin hotel ɗin da asibitin babu wani nisa sosai hakan yasa da ƙafansu suka shiga takawa har zuwa privet hospital ɗin.
Kaitsaye inda su Hamma Saifuddeen din suke suka nufa,  abakin ƙofar ɗakin da Saifudden ɗin yake suka hango Dr.Adnan tare da Dr.Acash prasat, da alama magana suke mai mahimmanci, tsayawa sukayi daga gefe har saida suka kammala maganan kafun suka ƙaraso, kallon fuskan Dr. Adnan sukayi su duka, cikin yanayi naɗan damuwa Ahmad yace.
"Akwai matsala ne?"
Kai Dr.Adnan yagirgiza tare da cewa.
"No babu wata matsala, sai-dai bayanzu zamu samu ganin doctors ɗinba aƙalla sai munshare kwana biyu kafun mugansu,
  Dr.Anan Mehta, ƙwararren  likitane a ɓangaren  Orthopeadic surgeon, sai kuma  Dr.Mahesh Khurana, wanda shima ƙwararrene afannin neurosurgeon, muna da buƙatan ganin wad'annan likitotin don kuwa sune masu kula da irin lalurar Saifuddeen, fatanmu akullum dai shine Allah yabashi lafiya".
Da.
"Amin Amin". suka amsa su dukansu, ko wanne zuciyarsa cike da tausayin Saifuddeen. 
Ganin rauni nashirin bayyana akan fuskokinsu ne yasanya Dr.Adnan karɓan takeaway din hannunsu kana yace su koma masauƙinsu su huta sai kuma zuwa da safe idan Allah yakai rai,  bazasu musa masa ba domin dama agajiye suke, hakan yasa sukayi masa saida safe, koda Hayatuddeen ya buƙaci ganin Hamman nashi cewa dashi Dr.Adnan yayi yayi bacci sannan ba aso atasheshi, dole haka Hayatuddeen ya haƙura yabi Ahmad suka koma masauƙinsu.

Koda Dr.Adnan ya koma cikin ɗakin nan ya iske Saifuddeen kamar yanda yafita ya barshi wato idanunsa alumshe tamkar wanda yake bacci, shi kuwa Saifuddeen ba bacci yake ba, yayi nisa ne akan tunanin Zaliha, kyakkyawar fuskarta ne keyi masa gizo acikin ƙwayan idanunsa da zuciyarshi, tuno da yanda ta rungumesa ta baya tana me jansa akan su gudu alokacin da yaran Dalla suka kusa cimmasa  yasanya tsikar jikinsa tashi, lokaci guda ya tuno da taushin hannuwanta da kuma yanda daddaɗan ƙamshin turarenta ya zautar dashi,  yanayin da yakejin kansa aciki, ya sanya shi jin tamkar alokacin abun ke faruwa, sake lumshe idanunsa yayi alokacin da ya tuna da yanda bakinta ke motsawa alokacin da take cewa yazo su gudu kada su cutar dashi, wani irin yawu ya haɗiya wanda tuntuni ya tsaya masa amaƙoshi, gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi wani iri, yayinda yakejin wani irin sassanyan yanayi shauƙin sha'awa na musamman suka rufeshi dangane da ita.     "Saifuddeen!".
Dr Adnan yaƙira sunanshi yana me kamo hannunshi, tayanda zaiji ya buɗe ido, jin sauƙan hannu akan nasa hannun yasanyashi buɗe idanunsa ahankali, murmushi Dr Adnan yayi masa tare da cewa.
"Tashi kaci abinci, danajika shiru na ɗauka ma ai bacci kakeyi".
Ɗan murmusawa kawai Saifuddeen yayi, inda shi kuma Dr Adnan yaɗan ɗago saman gadon da Saifuddeen ɗin yake yayi sama, shida kansa ya gyara masa kwanciya inda yayi kamar azaune yake saidai kuma bayansa yana jingine ne da gadon, abinci Dr Adnan ya miƙo masa kana ya koma gefe shima ya soma cin nasa,   cikin nutsuwa haka Saifuddeen ya shiga cin abincin ahankali yake ɗan lumshe kyawawan idanunsa masu matuƙar ɗaukar hankali, haryanzu tunaninta ne kwance aƙasan zuciyarsa, ahaka dai har ya ɗanci abincin kaɗan ya ture sauran gefe, don shi ba mutum bane me yawan cin abinci sosai...


Gombe Nigeria

Dawowarta daga wajen aiki kenan,
aɗan gajiye ta shigo cikin  haɗaɗɗen ɗakin nata, jakar dake hannunta ta aje gefe tare da soma rage kayan jikinta, saida ta cire komai na jikinta sannan ta sanya wata kekyawar rigan wanka baby pink colour, dogon gashinta ta ɗaure da ribbom sannan ta wuce kai tsaye zuwa toilet, wanka tayi da sabulunta me daɗin ƙamshi kana ta ɗauro alwala, kasancewar ankusa ƙiran sallan Magriba, zama tayi agaban tangamemen dressing mirror'n ta wanda gabansa ke cike maƙil da kayan shafa masu kyau da tsada, body lotion ɗinta tashafa wanda gaba ɗaya sanyin ƙamshinsa ya game ɗakin, yanayin yanda takejin kanta agajiye yasanyata miƙewa tsaye, ahankali ta ƙarasa gaban drawer ɗinta wanda cikinsa ke shaƙe tam da kayan sawanta masu kyau da tsada, wanda ita kanta batasan iyaka yawan suturun sawanta ba, wata ƴar doguwar riga marar nauyi ta zaro wanda yake daga ɓangaren kayanta marassa nauyi, rigar irin mai taushin nanne wanda takebin jikin mutum ta lafe, da fararen stones aka ƙawata wuya da hannayen rigan, wanda hakan kuma ba ƙaramin ƙarawa rigan kyau yayi ba, sosai rigan ta amshi jikinta ta lafe, hakan yasa kyakkyawan body structure ɗinta bayyana, wanda da ace lafiyayyen Namiji zai gani to fa tabbas dasai ya rasa nutsuwarsa, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasanyata zura wani dogon hijab ajikinta tare da shumfuɗa sallaya, koda ta idar da sallan magriba bata tashi akan sallayan ba har saida ta sallame sallan Isha, bayan ta tarin addu'ointa wanda mafi yawansu akan Saifuddeen ne, cikin sanyin jiki ta tashi daga kan sallayan tare da cire hijab ɗin ta ninkesa, kana tayi taku uku zuwa biyar ta isa bakin gadonta kwanciya tayi akan lallausan gadonda tare da jawo pillow ta matse a ƙirjinta, rumtse idanunta tayi da tsananin k'arfi tare da fesar da wani zazzafan numfashi me ɗan karen zafi yayinda takejin wasu zazzafan hawaye sun tsastsafo mata cikin jijiyoyin idanunta, cusa kanta tayi cikin hannayenta tanajin akowani bugu na zuciyarta da tunaninsa yake wanzuwa, ina yake!? a ina zan ganshi? wani hali yake ciki? sun kasheshi ko yana da rai? tana da buƙatar sanin waƴannan amsan fiye da komai ayanzu, gyara kwanciyarta tayi tare da buɗe idanunta, kan zanen pop'n dake mamaye saman ɗakin ta tsaida idanunta sun kad'a sunyi jazir cikin raunin murya take cewa.
"Ya Allah kasa ako ina yake yana cikin ƙoshin lafiya, in kuwa sun mishi rauni ya Allah ka bashi lfy!".
tafaɗi haka aɗan raunane, ahankali hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa suka biyo ta gefen kumatunta, haƙiƙa zuciyarta cike take da son jin wani abu daga garesa, yayinda idanuwanta kuwa ke ɗokin sake ganinsa, tunaninsa ya matuƙar tsaya mata azuciya babu dare ba rana ko yaushe bata da sukuni bata fahimtar komai domin duk nazarinta da tunaninta a kanshi yake k'arewa,
sake muskutawa tayi ta gyara kwanciyarta akaro na biyu, kana ta lumshe idanunta da har yanzu suke ɗigan hawaye, da sauri ta buɗe idanunta tare da dafe ƙirjinta dake wani irin bugawa sakamakon tunowa datayi yanda
Yaran Dalla suka caka masa wuƙa abayansa, da ƙarfi ta rumtse idanunta tare da sakin kuka me cin zuciya cikin yanayi mai kama da sambatu tace.
"Ya Allah Kasa ba mutuwa yayi ba, Ya Allah ko sau ɗayane ka ƙara nunamin shi, ya taimakeni alokacin danafi kowa buƙatar taimako, Ya Allah kasa yana cikin halin nutsuwa aduk inda yake ya Allah ka kaddara saduwa ta dashi koda godiya in mishi!!".
Da sauri ta d'ago kanta jin k'anwarta Zahira na cewa.
"Dan Allah Anty Zaleeha, ki bar irin wannan kukan, kici gaba da yimishi addu'a insha Allah addu'arki zata riskeshi."
cikin kuka ta kife kanta bisa cinyar k'anwar tata wacce ita kad'aine tasan da batun. Cikin kukan take cewa.
"Bai sanniba, bai tab'a ganinaba cikin taron maza dake wurin kab babu wanda ya kula da ni bare ya taimaka min dan tsoron Dalla da sukeyi,
sai shi d'aya ya zame min Garkuwata, kuma sun mishi illa gashi ban san ina zan sake ganinshi ba."
shafa kanta Zahira tayi tayi tare da kwantar mata da hankalin.
A haka tacigaba dayin kuka ƙasa-ƙasa tana me fidda shashsheƙa da haka har bacci ɓarawo ya ɗauketa.

***

A gidansu Saifuddeen kuwa.
Ummi ce zaune afalo tayi jigum yayinda tunanin ɗanta kuma farin cikinta Saifuddeen ke kwance acikin ranta, dare da rana bata da wani addu'a sai na nema masa lafiya awajen mai duka, Raliya ce da Adda Rahma da tazo musu tunda safe,
sune suka tafito daga cikin kitchine, hannun Adda Rahma ɗauke da goran ruwa me ɗan sanyi, jingina bayanta tayi da jikin ƙofar kitchine ɗin tare da kafe Ummin nasu da ido, wani irin tausayin kansune ke ƙara ɗarsuwa acikin ranta a kullum, haƙiƙa SAIFUDDEEEN shine komai nasu, Allah Ne gatansu amma Saifuddeen babban jigone agaresu wanda kuma shine gaba ɗaya farin cikinsu.
Raliya kuwa da sauri ta k'araso gefen Ummi ta zauna, ita kuwa Adda Rahma cikin sanyin jiki ta fara d'aga k'afafunda da suka kumbura sabida tsufan cikin jikinta da kyar take tafiya bisa dukkan alamu cikin ya cika wata bakwai ya shiga na takwas a hankali ta ƙaraso cikin falon tare da sanya hannu taɗan taɓa Ummi wanda tayi nisa acikin duniyar tunani.
Ummi kuwa jin sauƙan hannu akan kafaɗanta ne yasanyata ɗagowa da sauri ta kalli wanda ya dafatan, da fuska Raliya tayi arba wacce ta marairaice tuni idanunta sun tara k'walla.
A hankali ta kuma juya ganinta zuwaga Rahma wacce ta fara mgna cike da sanyin murya haɗi da tausayawa tace.
"Dan Allah Ummi kidaina sa kanki adamuwa, Ummi idan kika kasance acikin damuwa akullum natabbata Saifuddeen idan yasani bazai taɓa yafewa kansa ba,
Ummi kinfi kowa sanin Saifuddeen sam bayason damuwarki, dan Allah Ummi kidaina sanya kanki adamuwa Saifuddeen addu'a yake nema daga gareki damu baki d'aya , sannan Ummi kada kimanta addu'an uwa yana da matuƙar tasiri akan ƴaƴa, please ki tausaya mana ki dage da yi mishi addu'a!"

Wani irin dogon Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da ɗan rausayar da kanta gefe tana mai son maida hawayenta amman ina ta gaza tuni sun zubo mata bisa k'unshinta, haƙiƙa shiga damuwa yazame mata dole, tunda ɗanta mafi soyuwa agareta yana cikin wani irin mawuyacin yanayi a hankali tace.
"Ina yimasa addu'a akullum akuma ko yaushe Rahma, sannan nakasa ɓoye damuwata akansa, ke uwace Rahma kinsan irin tsananin so da kuma ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa, wannan ƙaunar fiye da itace ke tsakanina da Saifuddeen, kuma kisani ko ban nuna damuwata afili ba to tana nan kwance acikin zuciyata tana cina!".
ta ƙare maganar murya araunane.

Hawaye ne suka cika idanun Raliya har suna kwaranyowa kan fuskarta yayinda itama Rahma ida nunta suka cicciko da hawaye,
tabbas idan harsu da suke ƙannansa suna tsananin jin ciwonsa ajikinsu, sannan kuma suna tsananin tausaya masa, basu da wani fata daya wuce samun sauƙinsa, to ya Ummi da take mahaifiyarsa zataji? ƙoƙarin maida hawayen da suka cika idanunta tasomayi tare da sadda kanta ƙasa murya asanyaye tace.
"Kiyi haƙuri Ummi In sha Allah Saifuddeen zai samu lafiya, zai warke yazama cikakken mai lafiya, Saifuddeen d'inmu shine jigo kuma farin cikin mu, In sha Allah ko dan wannan Allah zai dubemu ya bashi lafiya, don bamu kaɗai keda buƙatarsa ba mutane dayawa daga waje suna da buƙatarsa!".

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Allah Yasa!".

Da "Ameen".
Raliya ta amsa kana ta miƙe ta wuce ɗaki don duba Adam yaron Adda Rahma dake bacci koya tashi.



k'arfe biyar dai-dai na yamma Zaleeha ta shigo cikin gidan radio vision FM gombe. Driving takeyi cikin tsananin nitsuwa a hankali take tafiya,
yayinda take sa hannunta tana goge sirarun hawayen dake zubo mata time to time.
parking tayi kana ta fito kai tsaye d'akin watsa shirye-shiryen su ta nufa,
a bakin k'ofa tayi cikibis da Raveel wanda ya gama gabatar da shirinsa kenan ya fito da nufin zai kirata domin tazo ta gabatar da program d'inta.
Murmushi yayi tare cewa.
"Yar halas kink'i ambato yanzu nake kiranki a raina."
sam hankalinta da nitsuwarta basa jikinta bare ta kulashi ratsawa gefenshi tayi a bakin k'ofar shiga ta cire takalmanta masu d'an karen tsini,
kana ta zura silipas dake wurin sannan ta kutsa kai cikin d'akin.
Shi kuwa Raveel jingina yayi da jikin gini ya zuba mata idanu yana kallonta ko k'ebta idonshi bayayi koda ta shiga ta meda k'ofar ta rufe sai ya lik'a idanunshi kan takalmanta.

Ita kuwa Zaleeha tana shiga cikin d'akin watsa shirye-shiryen nasu wani azabebben bege da shauk'in son ganin fuskar da ta tab'a gani sau d'aya ya d'arsun mata a rai.
A hankalin ta zauna kan kujerar zaman nasu,
Kana ta ɗauki wannan ɗan abu da suke sawa a kai ta saka wanda yake isa har zuwa kan kunnensu ta jawo ta sank'ala.
Ji tayi zuciyarta na sarrafa gangar jikinta,
madadin ta gabatar da program nata mai taken Babu nakasshe sai rago,
kawai sai ta tsinci kanta dafuskantar na'urar tasu da kyau tare da zab'o wak'ar da take jijjiga sirrin zuciyarta.
can cikin gidan Radio kuwa cikin mmki managernsu ya kasa kunne a na'urorinsu na tantance abinda suke watsa jin sautin sassanyar wak'ar da Zaleeha ta sake, dan ya hango shiganta, da sauri ya kalli agogon dake fuskar wayarshi ganin ai lokacin gabatar da shirinta har ya shiga da 3 minute.
Da sauri ya jingina jikin kujerar jin ta d'an rage sautin wak'ar.
Yayinda mutanen cikin garin gombe da kewaye ke jinta dan shirinta yanada matuk'ar farin jini,
musamman a wurin nakasassu, wanda yanzu hakama duk inda nakasasshe yake yana jinta sanin lokacin nasune.

A hankali take jin sautin wak'ar da tasa yana ratsa mata jiki da jini har zuwa cikin zuciyarta a hankali ta bud'e bakinta ta fara bin wak'ar.
Yayinda akejin muryarta na gaurayewa da muryar mawak'an dan ta rage sautin hakan yasa abin ya had'e yake bada wani sok'o mai armashi wanda da zaran kajita kasan wani takewa baitukan,
lumshe ido tayi tare da bin sautin waƙar a hankali take cewa.
"Soyayyar dake raina bazan sauya ra'ayi ba."
sai kuma ta bud'esu tare daci gaba da cewa.
"Nayi lullubi kamar na ango da amarya."
sai kuma ta d'an d'aga sautinta kad'an taci gaba da rere wak'ar.
"So yanada dad'eeeee maso dashen wani ya shiga haushi."
sai ta kuma d'an k'ara volume na radio kana taci gaba bin waƙar.
"Soyayya ta zahiri ba'ayi mata gudun barewa."
sai kuma wani sassanyan shesshek'a ya danne mata harshenta wanda kowa yaji salon yadda muryarta ke fita zai iya gane tana kuka da zubda hawaye take bin wak'ar cikin tsananin tausasa lafazi take cewa.
"In nayi rashin sautinka zan fad'a k'inshi ruwa.
Idan har na barka aban sona bani da kowa.
Dana ganka sai na wadatu da k'oshi bani yunwa.
Duba ka gani tsuntsun k'auna ya zana barewa.
Girgije samani tai lub-lub, lif tana zubar ruwa.
Ga itatuwa koraye d'orowa da sanwa."
sai kuma ta lumshe idanunta hayenta suka samu daman zubowa sannan taci gaba cewa.
"Munshiga ginin sha'awa ga iska tana kad'awa.
Da k'auna tabi jiki an komawa wa da k'anwa.
a hankali ta lumshe idanunta yayinda hawayenta sukaci gaba da kwaranyowa,
tana ganin wayarta nata kawo haske alamun ana kiranta amman bata da tunanin d'agawa,
murya na rawa taci gaba da bin baitukan wak'ar a hankali take cewa.
"Jikina yana jurar rab'ar wata soyayya.
sai kuma ta d'an d'aga murya da ɗan ƙarfi kana tace.
*"Nayi adanin soyayyata bani baiwa kowa!*
Barewa batayi gudu d'anta ya rarrafaba,
*Soyayyar dake raina bazan mata kishiya ba.*
sai kuma ta lumshe ida nunta kana ta buɗi baki a hankali ta taci gaba da raira wasu baitukan da yafi kama da amsa take bawa ƴan Nakasa ba kasawa bace fans 2, murya a tausashe take cewa.
*Mai sukar masoya bai san sirrin zuciya ba.*
_Idan na rasata jiki bazai daina bariba_
*baniwa masoyi rowar tattausan lafaziba.*
_K'auna ke gushe haushi so bazai canja wuriba
So in yayi kewar gani aso bazai tsayaba."_
Tana ganin ana danna mata danja alamun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login