Showing 57001 words to 60000 words out of 176868 words
Chapter 20 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
Saifuddeen zasu k'auro zasu dawo gombe,
yanzu Hayatuddeen yake gaya min."
sai ya kuma manna wayar a kunne tare da cewa.
"Hello Ba dukke kace wannan shekarar tamu ce lokacinmu ne kace birnin gombe zai amsa da rayuwar zafafan samari."
tsalle yayi tare da cilla woyar tashi jin Ishaq ya kama mishi kunne cikin yarfa hannu yake cewa.
"Wayyo Ya ishaq na tuba."
"K'arya kake baka tuba ba nasan ina sakeka zankaci gaba."
cewar Ishaq kenan Mama kuwa cikin farin cikin k'aurowar dasu Hayatuddeen zasuyi tacewa ishaq.
"Kai maza sakarmin kunnen d'an autana,
barshi yayi farin ciki,
nasan kaima d'in zakayi naka tsallen a side d'inka."
dariya sukayi baki d'aya kana suka zauna a parlour sukaci gaba da hirar,
mik'ewa Imran yayi ya d'auki wayarshi dake gefen Mama,
Suleiman ya kira wani abokinshi da suke yawan mgnar Hayatuddeen dashi ana d'aga woyar Sulaiman d'in yace.
"Hello Sulaiman."
da Sauri d'aya abokinsu mai suna Zakariyya wanda shine ya d'aga woyar Sulaiman d'in yace.
"Hege to ba Sulaiman bane Zakine."
dariya suka kece dashi baki d'ayansu sannan imran yace musu.
"Ba dukkenmu fa zasu k'auro zuwa nan cikin Gombe."
Sulaiman dake gefene yana jinsu yace.
"Yanzu Isma'il yamin text yake gaya min wai yaga Hayatuddeen ya fad'a a cikin what's app group d'inmu wai zasu dawo cikin gombe."
nanfa sukayi ta murnar dawowar da Hayatuddeen zai a kusa dasu dan sun saba sosai a media kuma duk sanda Hayatuddeen yazo gidan Adda Rahma to ranar dai su duka a gidanta suke wuni,
Imran, Hayatuddeen, Sulaiman, dan alhaji Sani, sai Isma'il d'an Alhaji Kabiru,
Sai Zakariyya wanda d'ane ga wani babban malamin da k'asarmu baki d'aya ke ji dashi,
kani kuma ga wani babban Pilot,
k'ani kuma ga wata shaharartiyar 'yar jaridar da taurarinta ke haska tutatar yayinda iska ke kad'a igiyar budurcinta kenta ya zama tamkar manuniya a gareta, *Zaleeha* sai kuma wasu sauran 'yan uwanshi...!
*****
Wata uku akayi anayiwa gidan duk kan gyare-gyaren daya kamata duk da dama gidan bashi da wani makusa yau aka gama komai na gyaran gidan.
Washe gari kuwa da Saifuddeen yazo shida Salisu a wata zazzafar motar da ys sarota a wannan satin.
kai tsaye gidan Adda Rahma suka nufa,
nan suka had'u baki d'aya,
Saifuddeen, Ishaq Salisu Ahmad, Warisu, Mudassir,
suka nufi federal law cos sukaje ganin gidan.
Suna isa gidan duk suka shagala da ganin kyau da girman gidan uwa uba da tsaruwarshi.
Gidane mai girma wanda yakeda zagaye da dogayen bishiyoyin nan na gidajen 'yan gayu ga kuma gajerun fulawi da yayiwa k'asan dogayen bishiyoyin nan k'awanya, sai daga cikin gidan wanda yake da wadaceccen parking lot ta gefen dama,
wanda zai iya d'aukan motoci bakwai zuwa takwas,
sai d'an wani d'aki mai girma wanda yakeda bathroom a ciki,
sai yar barandarshi ta gefen barandar kuwa akayi wani d'an rumfa mai girma in ka ganshi kamar d'aki wanda shima
yakeda bathroom a ciki,
can gefen hagu kuwa BQ ne mai d'an girma wanda yakeda d'an madaidaicin parlour sai two bedroom ko wanne da bathroom a ci sai d'an k'aramin kitchen da dinning area,
kana fitowa harabar gidan zaka fuskanci wani tsarerren gini mai tsananin kyau da d'aukar hankali,
daga harabar gidan wani babban corridor ne wanda ko motace zata iya ratsawa ta nan ta wuce, gefe da gefen corridor d'in duk fulawowine a shuke kansu dai-dai sunyi cib-cib dasu sunyi kore shar,
sai kuma fitilun dake biye da layin d'an dakalin da abakinshi aka zagaye fulawin
tafiya mai d'an nisa zakayi zaka ratsa ta wani dank'areren side mai girma wanda yake d'auke da wasu plat masu azabar kyau,
plat d'in guda biyune wanda suna gab da gab da juna,
daga tsakiyarsu anyi wani rawun da fulawowi masu d'an karen kyau da d'aukan hankali colors d'insi green and yellow sai ratsin pink suna da d'an tsayi sai hamyoyin shiga cikin zagayen fulawowin aka bari guda biyu,
bima'ana ko wanne part akwai kofar shiga ta gaban barandar.
cikin rawun d'in kuwa wata yar madaidaciyar bishiyar mangoroce wacce bata da tsawo sosai dan wasu ganyayenta har suna tab'a fulawowin sai 'yan k'ananun fulawowin da akayi musu zubin zanen heart daga nan tsakiyar heart d'in kuwa sai tattausan ciyawar grass carpet koro shar dashi,
sai wasu tim-tim d'in fulawowin da in ka gansu zakace kujerun zamane dan suna zagaye da heart d'in,
sai wani dogon k'arfe da kwan fitala guda buyi a jikin k'arfen,
sai kuma wani d'an pompo dake nan gefen wurin kusan dashi akeyiwa fulawin wurin ban ruwa.
Sai bakin barand'ar mashigar Part d'in duk suma suna zagaye da fulawowi,
barandar irin mai fad'in nanne,
marfin k'ofar parlour kanshi abin kallone,
kana shiga daga ciki wani tamfatsetsen parlour ne mai girma,
wanda daga gefen dama akwai wata k'ofar wanda kana shiga cikin zaka ratsa wani parlour mai girma wanda yake d'an madaidaicin dinning area,
sai bedroom mai girma wanda yakeda babban bathroom,
sai kuma gefen hagun asalin banban parlour da aka fara shiga,
wani tamfatsetsen dinning area ne mai girma wanda sai ka taka wasu step guda uku kafin ka hau wurin dinning d'in,
daga nan cikin dinning d'in gefenshi k'ad'an wani d'an corridor ne wanda gab da mashigar corridor akayi wani d'an wuri kamar na ajiye firij sai wata babbar k'ofa dake ciki wanda yake d'auke da tam fatsetsen bedroom mai girma sai bathroom shima k'ato,
sai d'aya gefen na cikin wurin dinning area d'in,
wanda yakeda kofofi uku d'aya kofar wani d'an madaidaicin d'akine wanda yakeda d'an ma daidaicin bathroom,
sai d'aya kofar shi kuma d'an k'aramin d'akine babu bathroom bisa dukkan alamu sito ne,
sai kofar dake gaba dashi shi kuma wani tamfatsetsen kitchen ne wanda yake,
daga cikin kitchen d'in kuma akwai wata kofar da kana bud'ewa bakiyat nasune sai dai bakin kofar anyi wani k'aton baranda irin na asalin mashigar babban parlour,
sai dogon luggu da yayiwa part d'in kawanya sai manyan igiyoyin shanya da ke d'aure guda uku sai pompo a dake wurin,
sannan sai jerin fulawowi da futilun dake mammane jikin ginin.
wanda koda da dare ne zakaga kamar da ranane.
to shima d'aya part d'in haka yake,
wannan ciki da parlour da dinning area ne kawai ke tsakaninsu.
daga nan kuma sai can cikin gidan wanda gidan samane mai girma.
kana shiga asalin wannan corridor direct har bakin k'ofar shiga cikin part d'in dake k'asan gidan saman ne inda gefen shi kad'an akwai bishiyar dabino wacce take 'yar d'ugus da ita sai yawan haihuwa.
wanni k'aton parlour ne mai d'auke da wani babban dinning area, sai wani dogon corridor wanda yakeda kofofi biyu suna fuskantar juna bedroom ne da bathroom nasu masu girma,
sai kuma can gefen hagun parlour kuwa wani d'an matakalane mai hawa d'aya wanda kofar kitchen ne a wurin sai sito dake manne da kitchen d'in.
Sai kuma wata k'ofar da takeda girma kana bud'ewa zaka ratsa cikin wani d'an parlour mai d'auke da bedroom.
Sai shimfidaddan steps d'in dake tsakar parlour wanda zaka hau ya sadaka da asalin saman.
Wanda kana hawa saman zaka ratsa wani tamfatsetsen parlour mai girma wanda yakeda two bedroom sai dining area da kitchen sai kofa d'aya rak wanda zata sadaka da wata 'yar baranda mai kyau wanda aka zagayeta da k'arafun silver masu shek'i wanda in kana daga cikin barandar zaka ke hango asalin tsakiyar wannan part mai plat guda biyun nan.
Kana daga windows d'in parlour ma zaka kalli duk abinda ke guda a tsakiyar wad'annan part d'in da asalin harabar gidan.
Sai kuma can bayan gidan saman wanda yake d'auke da wani babban garden mai tsananin sanyi wanda yake zagaye da fulawowi da itatuwa kamarsu Ayaba, goiba, dabino, mangoro, tsada, d'inya, gwanda, sai bishiyar giginya,
sai babban sweeming pull wanda yake zagaye da kujerun silver sosai wurin yakeda d'an duhu dan duhun itatuwan daga d'an gefe kad'an kuwa rufumfa ce guda d'aya rak sai dai tanada matuk'ar girma,
daga can gefe kuwa akwai fili mai girma wanda za'a iya tada wani part d'in.
Fentin gidan white and purple ne mai tsananin kyau sai shek'i yakeyi kasancewar fentin mai maine.
Gida kam dai masha Allah mak'i gani ya kauda idanu maso gani yayi son barka.
Sosai tsarin gidan yayi matuk'ar burgosu,
Addu'a sosai sukayi tare sanya al'barka,
sunata yiwa Saifuddeen tsiya wai saura a shiga babin batun aure tunda ya tara.
Nan Bappa Ali yasa musu ranar k'auran saura wata d'aya nan gaba.
Yayinda Hayatuddeen kuwa yaketa mita wai anja lokacin yayi yawa,
waishi wallahi ya gaji dan haka zai k'aura in yaso su biyoshi daga baya shi dai ya gaji da zaman Dukku.
Yau saura sati uku su k'auro sosai hidimomi sukayiwa Saifuddeen caa a kanshi,
danma Ahmad dasu Salisu suna samun lokacin tayashi hidima,
Yau tunda da Saifuddeen ya gama abinda yakeyi a kasuwa,
ya wuce shagonsu yana isa ya samu bakin shagunan na cike mak'il da mutane maza da mata yara da manya masu sari da masu sayan kad'an-kad'an,
ratsawa gefe yayi ya shiga cikin shagon inda Ahmad ke zaune yanata had'a kan kudad'en cinikin da sukeyi,
Warisu, Mudassir, kuwa sunata aunarwa masu sayan kad'an-kad'an Bello kuwa yana fama da masu sari
a d'aya sashin kuwa masu barone cike sai yara masu zuwa sarin pure water a kattin girijin da Saifuddeen ya ajiye a bakin shagon,
wanda yawanci Ahmad ke kula da cinikin,
matsowa yayi kusa da Ahmad suka ci gaba da harhad'a kan kudad'en,
tare da lissafi da ware na gegen magi da ban da ware na gefen kayan masarufi da ban dan su jarin Saifuddeen ne halal d'inshi sai kuma gefen kayan abinci.
Bayan sun gamane Ahmad ya d'ago kai ya kalleshi cikin fidda numfashi yace.
"Har ka gama ne yau?."
kai ya gyad'a mishi tare da mishi alamu da body language yace.
"Na gama so nake kazo muje wurin kafin tannan ya gama aikin kayan."
kai Ahmad ya jinjina tare da mik'ewa yaje gaban firijin nan ya rink'a d'aukan katon d'in juice da ledodin pure water yana sawa cikin firijin saida ya ciccikasu baki d'aya sannan ya dawo cikin shagon mik'a yayi tare da cewa.
"Wach Allah na."
sai ya kuma juyo ya d'an harari Saifuddeen tare da had'e fuska sannan yace.
"Kai yaseen na gaji bazan iya wahalar nanba."
sai ya kuma kalli Saifuddeen dake hararanshi da alamun kai dai ragone.
bud'e marfin robar faron daya d'auko yayi saida ya sha rabinshi sannan yace.
"Hege kai kuma waya kaika tsoron wahala,
gsky aiyukan shagunan nan suna mana yawa,
dole za'a nemi sabbin ma'aikata koda mutun biyu ne,
sam bamu da hutu wuni muke sunkuyawa da tashi,
shiyasa in dare yayi sai mu zama kamar tsoffi masu 70 years,
wannan a haka mutun yace zayi aure ai matar taga ta kanta."
mik'ewa Saifuddeen yayi tare kallon Ahmad da yaci gaba da cewa.
"Bari in d'auki jakar kud'in nan inzo mu tafi,
amman sai mun biya ta GT bank na ajiye kud'in sai mu wuce ko?."
kai ya gyad'a mishi alamar to.
A tare suka foto bakin shagon inda kasiyar Ahmad take,
shi ya fara hawa kafin Saifuddeen ya hau kana yaja suka tafi,
kai tsaye GT Bank suka nufa,
tare suka shiga bayan sun gama hidimarsu suka fito nan suka kama layin bello sabon kud'i inda jerin kafintocin jihar gombe suke cike birjic,
suna isa wurin kafintan suka samu an gama komai an kimtsasu an lik'esu cikin leda,
suna isa Babban kafintan ya kira biyu daga cikin direbobin motocinsu na kwasar kaya ih zuwa gidanjen costumes d'insu,
sukazo suka kwashi kayan aka loda a motocin,
sannan matasa uku suka shiga wanda su zasuyi jeren,
suna gaba motocin na binsu a baya,
suna isa Ahmad ya sauk'a ya karb'i key d'in gidan a hannun Saifuddeen sannan ya bud'e musu gate d'in yazo ya shiga suma sukabi bayansu.
Daga nan suka fara shisshigar da kayan suna shigarwa cikin can asalin cikin gidan.
Ahmad ke musu bayanin yadda zasu sassaka kayan dan su basa gane body language d'in da Saifuddeen zai musu,
Bedroom guda biyu dake cikin parlour dake k'asan suka fara kimtsawa suka kafa gadajen tare da durowowin da mirrors d'in,
sannan suka sassaka katifun,
sai kuma suka dawo cikin parlour suka kimtsa lumtsuma-lumtsuman kujerun masu kama da kiran royal sai dinning table mai azabar kyau da suka shiryashi a dinning area,
sai da suka gama kimtsa parlour sannan suka shiga d'aya kofar da zata sadasu da d'an karamin parlour da bedroom nan gado durowar suka kafa,
parlour kuma suka barshi ba komai,
sai kuma suka haura sama can suna shiga parlour bedroom d'in dake hannun dama suka shiga nan suka kafa gado da durowa da duk sauran kayan gado sannan
suka dawo falon nan suka samu Ahmad ya firfito musu da sauran kayayyakin da suka saya suka tara a d'aya bedroom d'in kamarsu cainis carpet da labulaye sai zannuwan gadaye da TV, Firij da dai sauran kayan wuta.
daga parlour saman suka fara saka labulayen masu azabar kyau da shek'i kalarsu pink and white, hakama kujerun da carpet d'in.
bedroom d'in da suka kafa gado suka shiga nanma suka sa labulayen masu kalar ja da fari,
zanin gado ma red and white sai carpet shima red and white,
suka gama kimtsa komai sannan suka dawo parlour suka ajiye d'an madaidaicin firij a cikin dinning area wanda shi bai samu damar samun dinnin table ba,
sai katon TV da suka manna a parlour,
daga nan suka sauk'o k'asa suka gama shirya koma inda kalan labule da carpet suke white and people.
sai tv da firij da suka ajiye komai a mazauninshi,
sai kuma suka shiga d'an k'aramin parlour nan suka malale tattausan carpet a tsakiyar parlour sannan suka lik'a tv a jikin bongo,
daga nan suka ajiye d'an k'ank'anin firij a parlour.
Daga nan kuma suka shiga cikin kitchen d'in suka shirya durowowin kitchen d'in na sama da k'asa sannan suka ciccibo kwalin gas suka zo suka sashi a mazauninshi sannan suka had'a ma sank'alin sink da bakin pompo sosai kitchen din yayi kyau.
Sosai gidan yayi kyau komai yayi ras,
daga nan Saifuddeen ya biyasu kud'in aikinsu kana ya sallamesu,
sannan suka dawo parlour suka zauna shida Ahmad bisa kujerun suka zube suna shak'ar k'amshin sabon fenti da k'amshin sabbin kayan d'aki inda ya had'e ya zama daddad'an k'amshi, Ahmad ne yayi mik'a tare da cewa.
"Masha Allah gida yayi kyau sosai,
sai dai nasan Hayatuddeen zaiyi mitar an sa mishi k'aramin tv a d'an k'aramin parlour shi."
murmushi Saifudddeen yayi tare yin alamun.
"Ai zaiyi fushi kam dan zaice ban sa mishi kujeru a parlournba."
dariya Ahmad yayi tare da zaro wayarshi daketa ringing da sauri ya d'aga ganin Salisu ke kiranshi.
"Hello Salisu ya kake."
"Lfy lau Ahmad ya kasuwa?."
"Alhamdulillahi ya naka kasuwan?."
"Lfy lau wlh, ina kake ne nazo shagonku ban sameka ba."
gyara konciyarshi yayi tare da cewa.
"Muna gidan Saifuddeen d'azu nai ta kiranka baka picking call."
Numfashi Salisu ya fesar tare da cewa.
"To gani nan zuwa ku jirani."
"To sai ka zo." cewar Ahmad har zai katse kiran sai kuma yace.
"Kana inane yanzun?."
"Ina nan cikin shagonku."
"Yauwa to d'an taho mana da abin sanyi,
sannan ka d'an biya ta tashan dukku ka biya Abba bekery ka sama mana abinda zamuci dan wlh ni yunwa nakeji."
Dariya Salisu yayi sannan yace.
"To ba matsala a cici,
ci ba k'iba asaran gaya kawai."
yana fad'in haka ya katse kiran,
sannan ya juya ya kalli Mudassir dake dariya dan yana jiyo mgnar Ahmad kad'an-kad'an ,
sai ya kuma nuna Warisu da idanu yace.
"Nida Ahmad ci kamar gara, amman bama k'iba, ga oga Warisu kuwa yanata yiwa kanshi k'aidar ci amman a banza sai zuba k'iba yakeyi."
hararanshi Warisu yayi tare da cewa.
"Kada ka damu yaro nima zan sace."
dariya sukayi baki d'aya,
sannan Salisu yace.
"Yauwa ina son shinkafa buhu biyu d'anya da gumi sai buhun semo, da katon d'in spaghetti and macaroni indomi. d'ad'd'aya
Sai kuma mai manja magi sugar fulawa.
Bello ne dake tsaye ta woje yace.
"To an gama Warisu had'a mishi lissafin kud'in da zai bada."
to Warisu yace kana ya jawo Calculator dake gabanshi ya fara had'a lissafin,
yayinda tuni shi kuwa Bello ya had'a kayan duka,
sannan Warisu ya fad'i lissafin nan take ya biya kud'in sannan ya kira 'yan baro guda biyu suka kwashi kayan suka fita Salisu na biye dasu a baya.
Suna zuwa inda yayi parking motarshi ya bud'e but d'in motar kana ya loda kayan daga nan ya sallami yaran suka tafi shi kuma ya shiga mota yaja ya tafi direct Abba Bakery ya nufa ya sai musu abinda zasuci kana ya shiga cikin federal law cos,
Yana isa ya kira Ahmad yazo ya bud'e mishi gate sanan ya shiga da motar,
daga nan ya bud'e but d'in motar suka fara jidan kayayyakin sukayi ta shigarwa cikin sito d'in parlour da aka gyara.
Sosai Ahmad yaji dad'in kawaicin da Salisu yayiwa Saifuddeen,
shima kanshi Saifuddeen mutuncin Salisu ya k'aru a ida nunshi duk da bashi da matsalar kayan abinci amman yaji dad'in kyautar.
Nan sukaci suka sha sai bayan sallan la'asar suka fito,
suna fitowa gidan Alhaji Kabiru suka shiga nan sukayi sa'an samunshi a harabar gidanshi yana shirin fita,
bayan sun gaisane yacewa Saifuddeen.
"Ya kamata ka samu mai gad'in da zai zauna a gidan dan barin gidan haka ba mai gadi baiyiba."
kai Saifuddeen ya gyad'a mishi alamun za'ayi hakan.
shi kuwa Alhaji Kabiru buzayen dake zaune can harabar gidanshi ya nuna musu wani d'an ma daidaicin dottijo dake tsakaninsu kana yace.
"Ga wannan dottijon yanada kirki dama shine a gidan kauran masu gidan ne yasa nace ya dawo nan kafin a samu mai d'aukanshi aiki."
cikin gamsuwa Ahmad yace.
"To shike nan ba matsala kawai ya koma can yaci gaba da aikinshi."
cikin jin dad'in nitsuwar yaran Alhaji Kabiru yayi musu bayanin kud'in da ake biyanshi sun amince da za'a biyashi hakan,
nan take ya kwashi kayanshi ya koma gidan akan za'a rink'a bashi abinci daga gidan Alhaji Kabiru kafin su Ummi su k'auro.
Shirye-shiryen k'aurafa ya kankama Bappa Ali ya kwashi d'alibanshi sukaje sukayi kwana uku a gidan suna sauk'an karatun Qur'an da sadaka maganin masifa,
bayan sun gama suka dawo gida,
sannan Adda Rahma kuwa ta fara shirya musu waliman k'aura.
Raihana ma da Saminunta sun baro Kd zuwa gombe dan ayi k'auran a idansu,
Imran kuwa shida kanshi yaje gidajen abokanshi ya gaggayacesu suzo tarban abokinsu ba dukke,
Saifuddeen kuwa ya sanarwa abokanshi Jabeer, Hisham, Ibrahim da dai sauransu.
A dukku kuwa Aunty Nina sai kuka takeyi dan tasan zatayi kad'aici dan rabuwa da Ummi da yaranta zai shiga jikinta,
hakama goggo Dada maman Ahmad sai kukan k'auran sukeyi.
Ranar k'auransu ya kama