Showing 9001 words to 12000 words out of 176868 words

Chapter 4 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

ya bar musu mara amfani,
ko su da kansu ai zasuce da mutuwar ta had'a uban nasu dashi wannan kurman ta yashe su ta bar musu Nuruddeen."
cikin tsananin b'acin rai Malam Ashiru yace.
"Kai tafi daga nan gaisuwa kazo ko cin zarafi?."
Bappa Ali kuwa ya gaza cewa komai sai idanu ya zubawa Saifuddeen wanda ya rumtse idanunshi da tsananin k'arfi dan azabar b'acin ran kalaman da Mala Bala ya mishi gashi abokin mahaifinshi ne ba daman ya mishi wani abun.
Sauran abokansu biyun da suka zo tare da Mala balanne suka mik'e cikin jin haushin kalamanshi suka sallami su bappa Ali tare da basu hak'uri sannan suka tafi.

A daran wannan ranar Saifuddeen yayi kukanda bai tab'a yiba,
inda yake ganin inama shi mutuwar ta d'auke ta bar Ya Nuruddeen d'inshi a ranar mutuwar ta dawo mishi sabuwa a ranshi,
tausayinsu Rahma da Ummi ya hanashi sukuni ya zaiyi ya kula da rayuwarsu? haka dai kwanaki sukayi ta tafiya


Randa akayi sadakan bakyai duk yan uwa suka watse gida ya rage su kadai.
Hakan yasa suka zauna sukayi ta kuka.

Washe gari da safe duk suna tsakiyar gidan time to time in Ummi ta kallesu sai tayi ta zubda hawaye.
ganin haka duk sai jikinsu yayi sanyi,
Rahma kam tuni kuka takeyi dan ita kam rayuwa ta mata zafi ba miji ba uba ba yayansu jigonsu, wanda suke ganin zai zama gatan nasu kuma gashi kurmane.
jin kukan Rahma yasa Ummi tsananta kukanta,
shi kuwa Saifuddeen idanu ya rumtse sabida ba abinda yafi tsana a duniya kamar yaga hawayen Umminshi,
Raihana kuwa ruggume Hayatuddeen tayi tana kuka Raliyya kuwa su Faruq ta ruggume.
Suna cikin haka sukaji sallama,
cikin sauri Ummi ta d'ago kanta jin muryar Bappanta k'anin babanta da Goggonta, sai matar Bappan nata iya bukku muguwar mace, shiyasa Ummi take rayuwa tamkar bata da dangin Uba.
da sauri ta taso ta nufi Goggonta,
kan taburma suka zube nan raunin Ummi ya tashi ganin danginta kife kanta tayi kan cinyar Goggo Rabinta d'in ta saki wani marayan kuka.
itama Goggo Rabi kukan takeyi dan tausayawa d'iyar yayanta.
hakama Bappa idintan shima kukan yakeyi dan tausayawa rayuwar Ummi da yaranta,
ita kuwa Iya Bukku sai wani mugun kallo na rashin imani take bin su Rahma dashi.
Yayinda shi kuwa Saifuddeen ita ya zubawa idanu ganin mugun kallom data juyo tana yiwa Ummimshi.
cikin tausayawa Goggo Rabi ta d'ago Ummi cikin sanyin murya tace.
"Kiyi hak'uri Bisije dukkan tsanani yana tare da sauk'i, ki dena musu kuka Allah yana sane dake da marayunki."
murya a disashe Ummi tace.
"Goggo Rabi ya zanyi ina zan shiga a duniyar nan inji dad'i wa zai rik'e min yarayuna wazai tallafawa maraicina dana yarana da marayun jikokina?".
sai ta kuma juyowa ta kalli Bappa idin nata cikin rawan murya tace.
"Bappa ya zanyi wa zai zama gatanmu wa zai zama garkuwarmu, tunda shima bappan su Rahma ba wadata yakeda shiba, sana'ar me zanyi in rik'e yarana?."
kafin Bappa idin yayi mgna tuni iya bukku ta cab'e mgnar da cewa.
"Wannan kurman d'an naki mai kama da dutse shi baida amfanin komai ne?."
sai ta kuma tsuke fuska dan bata son bappa idi yace zai d'aukesu su koma garinsu dasu,
da sauri ta kauda kanta lokacin da ta kalli Saifuddeen sabida wani irin mugun kallo daya watsa mata.
sai kuma ta tsuke fuska kana taci gaba da cewa.
"In dai bazai amfanekiba ai sai ku jefar dashi ku huta da ciyar da mai zubin mutanen b'oye yaro tun yana k'arami ni tsoro yake bani dan wannan kyawun nashi ya zarta na mutanen mu.
in kuma bazaki iyaba, tunda ke jakar 'ya'yace akan yaranki zaki mutu,
to sai ki shiga cikin gari kije gidajen masu kud'i kina musu share-share da wanke-wanke da girki, suna baki dubu 6 a wata kullum kuma kina kwatsawa zugan yaran naki tuwo, nasan harda k'anzo zasuke baki."
wani irin mugun kallo da tsana Saifuddeen yake cilla mata,
domin tunda yake a duniya bai tab'a jin mgnar da tai mishi zafi kamar wannarba, kana bai taba jin mutun mai munanan kalamaiba kamar iya Bukku ba.
Goggo Rabi kuwa kai ta rink'a jujjuyawa alamar batajin dad'in kalaman da matar yayan nata takewa d'iyar yayanta marigayi.
Bappa idi kuwa sunkuyar da kanshi yayi dan yasan motsi kad'an zaiyi iya Bukku zata solleshi.
Raihana ce ta share hawayenta tare da murgud'a mata baki kana tace.
"Allah ya kiyaye Umminmu tayi ai katau a gidajen wasu,
kuma Hamma Saifunmu ba k'aton banza bane kurwarshi kur sai dai kici kanki wlh yafi k'arfinki,
har zakice mishi baida amfani to in sha Allah aniyarki kanki zata kom...!"
da sauri tayi shiru dan bugun da taji Ummi ta kaimata a baki tare da cewa.
"Raihana ki kiyayeni fa, banfa miki irin wannan tarbiyarba maza tashi ki bar nan."
cikin sanyi ta mik'e tare watsawa iya Bukku harara kana tace.
"Kiyi hak'uri Umminmu bazan k'araba."
Goggo Rabi kuwa ji tayi kamar ta goya Raihana dan dad'in ta sulle iya Bukku.
shima bappa idin dad'i yaji.
shi kuwa Saifuddeen, Ummi ya zubawa ido yana karanto bac'in ranta,
sai ya kuma juyawa ya kalli Rahma da ta sunkuyar da kanta hawaye na zubo mata.
itako Iya Bukku cikin masifa da rashin mutunci tace.
"Kaji hegiyar yarinya mai kama da aljan kujiye min fitsarerriyar yariya da uwarta bata haifeta da bisimillaba,
ke har kin kai ki zageni?
to na fad'a bashi da amfani, ai da yana da amfanin da ya tsare muku maraicinku,
ya zauna kamar dutse ya wani zuba min shegun idanunshi ya had'e wannan fuska tashi mai kama data al'jamu."
sai ta kuma ja tsaki kana ta mik'e tsaye tare da juyowa ta kalli Saifuddeen da zuciyarshi ke tafarfasa da sauri ta kauda idonta daga kanshi sabidah arararda yake watsa.
cikin k'arfin hali tace.
"Wannan da gani rabi mutum ne rabi aljan, mutun da aljan.
Dan duk zuriyar kakanunku babu kekyawa kamanshi wannan kyau bana Allah da annabi bane, hege mai jajen kunnuwa da labban baki."
sai ta kuma juyo ta fuskancesu baki d'aya kana tace.
"Bisije in kin yarda da shawarata wlh ki kaishi bakin kogi dan da gani wannan d'an ruwane,
in kuma kingi to ki bashi k'ok'on bara yaje yayi ta bara a cikin Gombe nasan wasu ko dan kyanshi zasu bashi sadaka, tunda nakasasshene bararce kawai aikinshi ai."
cikin zafin rai Rahma ta mik'e tare da tsuke fuska kana tace.
"Bamu jikiba! aniyar kura tabi daji!
k'anina ba nakassashe bane, domin nakasar zuciya itace sahihiyar nakasa ba nakasar gangan jikiba.
In sha Allah har abadan Saifuddeen bazaiyi bara ba, in Allah ya yarda hannunshi bazasu tab'a rik'e k'ok'on baraba.
Kuma acan zuriyarku ne ba kyawawa mu ki kallemu gaba d'ayanmu ba mummuna ki kuma bincika zuriyarmu kab kyawawane waya ce miki Baddukke yana muni bare bak'i,
to mu mune dukku jinin Dukku bamu da mutuwar zuciya,
bare muyi maula,
ki kama bakinki sai randa muka nemi al'farma a wurinki kafin ki gaya mana ba sugari,
in kyawun Saifuddeen ke baki tsoro to sai dai ki makance. Ke! da kin san k'uruciyar Abbanmu sanda yanada lfy da suma zakiyi in kin ganshi, dan haka mu kyau gadanshi mukayi ki dena cewa k'anina d'an ruwa eh!."
shiru Ummi tayi dan tasan Rahma nada hak'uri k'ureta akayi,
Raliyya kuwa sai harara taketa dokawa iya Bukku,
Goggo Rabi kuwa murmushin jin dad'i take.
Bappa idi kuwa tsorone ya rufeshi yasan in sun koma zaisha rashin mutunci dan sunfi kwana biyar da jin mutuwar tace bazasu zoba da yake can garin Hashidu suke.
shi yayi ta lallabata kan dole su zo, to yasan kanshi zata huce cewa zatayi da gayya yasata suka zo dan jikokinshi suci mata zarafi,
shiyasa duk sai ya tsure da yake dama mijin tacene.
Ita kuwa iya Bukku mari ta yarfawa Rahma,
wanda yasa suka mik'e gaba d'ayansu kana cikin masifa tace.
"To me amfanin kyan naku? Uban naku da yayi kyau d'in ina da aljani ya rayu a jikinsa ya zama mahaukaci tuburan.
To wane rana kyan naku ya muku,
tunda gaki ke bazawara baki auruba ga kuma kitika-kitikan yan mata har biyu suma basu auruba,
wata k'il basu da ko mashunshini,
gaya min me amfanin kyan naku, uwar rashin kunya?."
gaba d'aya jikin Saifuddeeem b'ari yakeyi sabida zafin zuciya irin na kurame,
ita kuwa Rahma rik'e hab'arta tayi tana kuka hakama Ummi.
Itako iya Bukku cikin iya bak'ar mgna taci gaba da cewa.
"To tunda baki san amfanin da kyan naku zai mukuba, ni bari in gaya miki,
kuje ku fara *KARUWANCI* nasan tabbas zakuyi kasuwa, kuyi karuwanci ku tara kudi dan nasan shima wannan Saifuddeen aljanin uban naku kanshi zasu dawo dan haka kuje kuyi karuwanc...?"
bata kai ga k'arishe mgnarba ta kurma wani irin razanenne ihu da ya cika unguwar baki d'aya.
bata ida dawowa haiyacintaba ta kuma kurma wani azabebben ihu,
sabida wasu zafafan maruka da Saifuddeen ya yarfa mata,
wanda a take sai ga hagwaranta a biyu a k'asa.
Ihu ta kumayi jin yasa k'afarshi ya tad'eta ta zube kasa rakacab ji kake d'im kamar an tila kayan wonki,
cikin rufewar ido da fita haiyaci Saifuddeen ya zaro ball inshi ya tsula mata d'aya zai kuma na biyu ne Ummi ta rik'o hannunshi tana kuka tana cewa.
"Saifuddeen ka rufa mana asiri muji da maraicinmu,
gaishemu fa sukazo yi."
Raliyya kuwa da Raihana sai murmushin jin dad'i suke yayinda Hayatuddeen yake tsalle yana cewa.
"Allah shi k'ara Ummi barshi ya dakata hegiya mai k'aton d'uwawu."
iya Bukku kuwa ai tana samun Ummi ta rike mata Saifuddeen cikin tsananin gigita da tsoro,
ta mike ta wawuri takalmanta a hannu gabas ta nufa a gigice sai ta kumayi kona tayi yamma kana ta juyo arewa, ganin har yanzu dai bata gane hanyar fitarba sai ta kuma yi kudu cikin tsananin gudu ta fita tare da cewa.
"Rabi, malam ku fito mugudu, aljanin sun motsa dama ba nace muku ruwa biyu bane shi ku fito mu gudu karya kashemu."
ita kam Goggo rabi niyarta zata tsaya, to ganin yayanta yabi matar tashi a guje shiyasa itama tabi bayansu a saba'in suka bar garim Dukku akan baburdin Bappa idin.

A cikin gidan kuwa Raihana da Raliyya da Hayatuddeen sai su kalli juna kana suyi yar dariya.
Cikin fad'a Ummi ta watsa musu harara, kana ta fuskancesu da kyau dan duk sun tsaya sunyi cirko-cirko sun tasa a gaba cikin nuna b'acin ranta tace.
"Dariyar me kukayi? dan baku da wayo baku san halin da muke cikiba, wani farin cike muke dashi da har zai saku dariya?
kema Rahma da nake miki kallon mai hak'uri ashe ba haka bane."
sai ta kuma nuna Raihana tare da cewa.
"Duk kece kika jawo abinnan da baki tanka mataba da tayi ta bari,
amman sai kika tsafe ido zaki zageta bayan kunsan ba hak'urine da itaba."
sai ta kuma juyawa ta kalli Saifuddeen nan take sai zuciyarta ta raunata cikin zubda hawaye da rawan murya tace.
"Babana meyasa kayi haka? ka mance yanzu bamu da kowa a duniya dole muna buk'atar taimakonsu."
cikin tsananin kunar zuciya ya tsuguna k'asa ya fara rubutu da sauri yayinda hannunshi har rawa yakeyi dan bac'in rai.
"Dan Allah Ummi karki sake cewa bamu da kowa,
kin mance munada Allahn daya haliccemu shine mai rayawa mai kashewa mai badawa mai hanawa shine wanda ya mana gida biyu duniya da lahira,
shine mai azirta bayinshi a duk sanda yaso shine yake ciyar da dukkan abin halitta, kuma muma shine zai cidamu,
shine gatan kowa kuma muma zai zama gatanmu baifa mance da muba.
Ummi koke da kike yarsu dame suka amfaneki a rayuwarki? bare mu jikokin d'an uwansu da ya rasu shekaru da dama.
Ummi ki kalleni nayi al'k'awari in sha Allah zan nema da k'arfina da lfyta zan kula daku iya iyawata, karki sake kaiwa kowa kukanki ki kaiwa Allah shi zai biya miki buk'atunki ba gajiyawa bare gori.
Ummi kiyi min addu'a ki sanya min al'barla in sha Allah ni d'innan zan cidaku in kuaa shayardaku in jinyaceku in suturtaku."
ita kam Ummi ta kasa cewa komai sai ido ta zuba mishi domin yana tsugune sai rubutu yakeyi in inda yake ya cika kana sai yaja baya yanayi jikinshi na rawa cikin zubda hawaye taci gaba da bin rubutun da yakeyi tana karantawa.
"Ummi rabuwarmu dasu shiyafi al'khairi domin muddin tana zuwa tana fad'i mana mugayen kalamai wata rana zan karya mata wuya,
Ummi na karkiji tsoro in sha Allah k'annena bazasuyi karuwanciba ni kuma bazanyi baraba bare maula, kema bazakiyi aikatauba, ki kalleni ki gaya min dukkan matsalarki kiyi shawara dani ko k'annena kada ki gayawa kowa matsalarki ki sirranta matsalarki damu yaranki.
Insha Allah zan fara neman sana'ar yi dan rik'eku ke dai ki samin al'barka."
Rahma kam sai hawayenta take shartewa,
su Raihana kuwa sai binshi suke suna karanta abinda yake rubutawan.
Ita kuwa Ummi da sauri ta isa inda yake hannunta tasa tsakiyar kanshi cikin k'arfin hali tace.
"Ya Allah kayiwa wannan bawa naka Saifuddeen al'barka ya Allah ka yalwata mishi samunshi hagu da dama rabbi ka al'barkaci duk abinda ya tab'a ya wahidun k'ahhar ka bud'a mishi k'ofofin samu gabas da yamma kudu da arewa.
Ya Allah ka kauda asara da gafala da tab'ewa daga gareshi dashi dama dukkan yan uwa musulmai, ya rabbil izzati ka al'barkaci rayuwar Saifuddeen ka raya minshi ka shirya minshi ka bashi arzik'i mai al'barka wanda musulmai da musulunci zasu al'fahari dashi ya ka bud'a mishi k'ofofin samu ka yalwata arzik'inshi."
kasan cewar tunda ta dafa kanshi ya d'ago kai ya kalleta shiyasa yake gane abinda take cewa,
yana kallonta still yatsarshi na k'asa yana.
Rubuta "Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati".
daga nan suka zauna tayi ta musu nasiha mai ratsa jiki.

Bappa Ali kuwa da matarshi suna side d'insu sam basu san meya faruba.


A daren ranar Saifuddeen yaje ya samu Bappa Ali da fefanshi da biro,
nan yake neman izinin bappan nashi da kuma shawarshi cewa.
A d'auki machine d'in Nuruddeen a bawa wani d'an mak'ocinsu Salisu wanda shima d'an acaba ne to dama na haya yake karba, to kuma an karb'e machine d'in wai mai ita zai saidata ya cikata ya sai sabuwa,
ba musu bappa Ali ya yarda dan yasan ko ba komai balance d'in zai taimakesu,
shi kuwa Saifudden gyara zamanshi yayi kana ya rubutawa bappan nashi cewa.
Kullum da safe in Salisu zai tafi zai bishi su tafi tare,
in yaje zai shiga cikin kasuwan Gombe zai nemi sa'ar da zaiyi."
da fari Bappa Ali yak'i kasan cewar yanaga Saifuddeen d'in kurma ne,
to amman da suka dunguzuma sukaje wurin Ummi sai ta kauda kai yadda Saifuddeen d'in bazai ga bakintaba tace.
"Ba matsala Ali barshi yaje, in mun hanashi zaiga ko dan yanada nakasane, mukuma bamu son hakan to amman ai kasuwa saida jari,
amman tunda yace a barshi yaje,to mu barshin in yaje yaga ba abinda zai ai zai bar zuwa, mu kuma bishi da addu'a Allah ya taimaka mishi."
cikin sanyi bappa Ali yace.
"To shake nan ba matsala Allah ya bashi sa'a."
"Amin Amin." sukace baki d'aya.

Daga part d'in Ummi woje suka fita,
sukako yi sa'an samun Salisu a harabar matsallacin k'ofar gidan nasu.
Nan bappa Ali ya mishi bayanin yadda sukayi, aiko dad'i kamar ya kashe Salisu,
ya kuma yarda da shared'in zaike zuwa da Saifuddeen su kuma dawo tare.
A take bappa Ali ya bashi Key d'in machine d'in.
sannan ya wuce cikin sangayarsu ya fara ratsa tsakiyar d'aliban nasu.
shi kuwa Saifuddeen gida ya koma ya sanarwa Ummi yadda sukayi, ita ko Ummi sai addu'a da samishi al'barka takeyi.
A daren ranar Ummi da Rahma da Raihana da Bappa Ali kusan kwana sukayi sunayi mishi addu'ar samun madafa da sa'a.
Shi kam Saifuddeen baiyi bacci a ranar bare ya rumtsa,
Kwana yayi yana neman yardar Allah da sanya al'barkanshi ya bashi sa'a a cikin k'udurin da yayi.

Washe gari da sanyin safiya Saifuddeen ya shirya bayan ya karya Salisu ya shigo yace su tafi.
gaban Ummi ya tsuguna kanshi ta dafa tare da sa mishi al'barka.
sannan su Rahma suka mishi addu'a baki d'ayansu kana suka fita suka tafi.


Suna shiga Gombe Salisu ya wuce dashi k'aramar kasuwa,
gab da San Hussen mall ya ajiyeshi,
kamar yadda sukayi tun jiya da dare,
bayan ya sauk'ane Salisu ya kalleshi tare da cewa.
"Ana yin sallan magrib kazo ka tsaya a nan, dan zanzo in d'aukeka mu tafi in munyi sa'a bayan isha mun isa Dukku."
cikin nuna alamar ya gane ya gyad'a mishi kai alamar toh.
Salisu na ganin haka yaja machine inshi gaban wata yar budurwa data tsaidashi,
lokaci d'aya suka shirya kud'in da zata bashi kana ta hau yaja ya tafi.

Shi kuwa Saifuddeen juyowa yayi ya zubawa makeken wurin San Hussain d'in idanu a lokacin tun forkon-forkon bud'eshi kana wurin ba'a wani gyarashi sosaiba kamar yanzu ba,
ajiyan zuciya yayi lokacin daya karanta sunan wurin,
sai kuma ya k'auda kai kana yayi tafiya kad'an yazo dai-dai mashigar kasuwan,
inda zai bulla ta babban layin na k'aramar kasuwan.
ida nunshi ya lumshe kana ya bud'esu a hankali hannunshi ya had'e wuri d'aya kana ya fara karanto addu'o'i yayi kusan 16 minutes yana addu'o'in kana ya shafa a fuskarshi kasan cewar da d'an sanyin safiya ne wurin bai cika jama sosaiba kuma kowa sauri yake ya wuce ya isa wurin sana'arshi ya bud'e.
bayan ya shafa addu'ar ne yayi bisimillah tare da d'ago k'afarshi ta dama ya shiga cikin kasuwan.
Sannan ya mik'e gabanshi samb'et, yana tafiya a hankali.
har yazo dai-dai wani babban shagon seye da sayarwa inda mata keta shiga da fita irin masu zuwar sassafen nan shagon kuma cike yake mak'il da atampopi, shadda, laces, material, voyels, su wagbari, gyalulluka. da dai sauransu,
ido ya zubawa yaran shagon kowa na hidiman gabanshi.
a hankali ya kalli saman shagon inda yaga an rubuta.
Alhj Ishaq,
murmushi yayi dan sunan mai shagon ya tuno mishi sunan abokinshi wanda kusan sau biyu kenan yana zuwa Dukku bayan Abba ya rasu.
juyawa yayi d'aya sashin inda yaga wani k'aton shagon mai cike da gyalulluka da dogayen riguna,
kana ya kalli d'aya sashin inda yaga k'aton shagon saida takalma,
sai kuma kusa da inda yake shagon masu saida yadin hijabai ne da masu d'in kasu.
shiru yayi sai ya kuma ci gaba da tafiya ganin ya b'ata kusan 30 minutes a wurin.
A hankali yake taku har ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login