Showing 150001 words to 153000 words out of 176868 words
Chapter 51 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
yayiwa Baba Bellon alamar cewa babu komai, nan suka shiga ɗan taɓa hira da Baba Bellon, inda Baba Bellon ya nuna jin daɗin zuwan Saifuddeen ɗin, domin kuwa tun ranan da suka dawo daga zuwa dubasa da sukayi, lokacin dawowarsa basu sake haɗuwa ba sai yau ɗin, hira sukeyi tsakanin magana da kuma body language, inda sosai Baba Bello ke gane yaren Saifuddeen, wato body language, cikin girmamawa haɗi da kulawa Saifuddeen ya labartawa Baba Bello maganan aurensa, kama daga farkon tura masa tambaya har kawo yanzu, cikin hikima yanemi shawarar Baba Bello agame da bikin.
Cikin jin daɗin yanda Saifuddeen ɗin ya karramasa, yakuma maidashi uba, yasanya Baba Bello gyara zama, nan yashiga bawa Saifuddeen ɗin shawarwari masu kyau, sosai kuwa Saifuddeen ya aminta da shawaran, inda ya yanke cewa jibi jibinna za akai masa lefe da kuma sadaki, sun ɗan jima suna hira daga bisani yayi wa Baba Bello sallama, kuɗi yaciro ƴan bandir ɗin ɗari biyar biyar sabbi ƙal ya ajewa Baba Bello agabansa, cikin dattako da halin kamala Baba Bello yace.
"Dan Allah Saifuddeen kada kasa kanka awahala, bayan ɗaukemin nauyin gidana da kayi gaba ɗaya kuma saika ƙara da sakanka a wata wahalan? kabar kuɗinka Saifuddeen nagode sosai bani da abinda zance maka sai dai addu'a, domin kuwa koda baka da lfy baka ƙasarma baka daina kulawa damu ba."
Fuska Saifuddeen ya kwaɓe cikin rashin jin daɗin dawo masa da kyautar tasa da Baba Bello yayi.
fuska ya marairaice, cikin body language ɗinsa yace.
"Dan Allah Baba Bello ka karɓa, kaifa matsayin Uba kake agareni, kamar yanda zanyiwa mahaifina kaima haka zanyi maka.!"
Jikin Baba Bello ne yayi sanyi, haƙiƙa Saifuddeen yaron ƙwarai ne, samun irinsa na da matuƙar wahala, tabbas Ummi tayi sa'ar haihuwa, domin samun Saifuddeen amatsayin ɗa babban nasara ce ga rayuwa, haka Baba Bello ya amshi kuɗin nan batare daya soba saidai sanin halin Saifuddeen yasanyashi karɓan kuɗin dole, nan ya rako Saifuddeen ɗin har bakin motarsa, saida Baba Bello yaga tashin motar tasu Saifuddeen kafun ya juya yakoma cikin gida.
Daga gidan Baba Bello kuwa kaitsaye ƙaramar kasuwa suka nufa, abakin kasuwan sule driver yayi parking motar, shida kansa ya buɗewa Saifuddeen murfin motar tare da gyara masa zaman kekensa, haka Saifuddeen da Sule driver suka kutsa cikin kasuwa, cikin nutsuwa Saifuddeen ke sarrafa kekensa, duk inda suka wuce ido ne ke binsu, yayinda mutane da yawa ke yaba tsantsar kyau irin na Saifuddeen, saidai ganinsa akan keken guragu shine abun dake ɗaure musu kai, kowa kallon cikakken balarabe yake yi masa, sam koda wasa babu wanda ya shaida kamannin Saifuddeen, duk acikin mutanen dake kallonsa babu wanda yakawo aransa cewa shine wannan matashin saurayin dake gararanban yawon raba leda, yake kuma yawon raba omo, kana harma da tallan fiyo wata (pure water), babu wanda zai gansa ayanzu yace shine wannan yaron da yasha gwagwarmayar rayuwa, yayi ta zagaye kasuwa koro-koro luggu da saƙo.
Fuskarsa ɗauke da annuri ya ƙarasa gaban wawakeken shagon wanda yake mallakinsu, Mudassir da Warisu naganinsa suka taso cikin tsananin farinciki suka tarbeshi, sam basu tsammaci ganinsa ba don ya matuƙar shammace su, yaɗan jima kaɗan ashagon nasu Warisu inda suka ɗan taɓa hira kaɗan, duban Mudassir da Wareesu yayi cikin body language ɗinsa yace.
"Kufara shiri tun yanzu don nanda ƴan sati kaɗan zakusha biki."
Mamakine ya bayyana akan fuskar Wareesu, daɗan ƙarfi yace.
"Biki kuma na waye?."
Murmushi Saifuddeen yayi tare da nuna kansa.
Cikin alamun ban mamaki Wareesu yace.
"Wow Surprise kenan! Kai amma naji daɗi sosai Allah yasa ayi damu, koya Mudassir, yakamata ne ma ai mufara gagarumin shiri."
Wareesu yafaɗa cike da farinciki.
Shiru Ahmad da ya shigo yanzu yayi tare da kafe Saifuddeen da idanu, kallonshi shima Saifuddeen ɗin yayi, yanayin yanda yaga fuskar Ahmad kaɗai yasayashi gane abun dake cikin zuciyarsa, murmushin daya bayyana kyawawan dimples ɗinsa yayi, cikin son ganar da Ahmad irin yanayin dayake ciki ya lumshe idanunsa, hannunsa yaɗaura adai-dai saitin zuciyarsa wacce ke beating.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ahmad ya sauƙe, tabbas ya gane hakan da Saufuddeen ɗin yayi me yake nufi, alamace dake nuna cewa Saifuddeen ɗin nasonta da duka zuciyarsa, tabbas yana matuƙar jin tausayin Saifuddeen domin kuwa shi tuni yajima da gano cewa Zaleeha ba matar aure bace, ba irinta Saifuddeen ke buƙata ba, Saifuddeen yana buƙatar kamilalliyar mace, nutsatstsiya, wacce ta yarda da ƙaddara tayi imani mai kyau ko akasinsa daga Allah Ne, amma ya zaiyi dolensa zai haƙura da ƙin Zaleeha da yake, sahoda yaga gaba ɗaya soyayyarta ta rufe idanun Saifudeen, ya fahimci cewa Saifuddeen Zaleeha kawai yake gani aciki da wajen idanunsa, saboda haka zaiyi ƙoƙari wajen manta abun da tayi musu, zai taya Saifuddeen ɗin ƙaunarta, nan yayiwa Saifuddeen ɗin Allah yasanya al'khairi, daga shagon nasu Warisu kaitsaye Saifuddeen shagonsa ya nufa, shida Ahmad masha Allah koda yaje yasamu nutane maƙil sun cika shagon, sayan kaya kawai suketayi, yayinda cikin shagon ke shaƙe da kaya tam na yara irin new designer ɗinnan masu kyau, Manyan Hajiyoyine keta business ɗinsu, wasu sayan dayawa sukazo wasu kuwa sayan ɗaɗɗaya , kasancewar shagon cike yake da mutane yasanya Saifuddeen baiwani zauna acikin shagon sosai ba ya tafi, Kaitsaye shagon Ba mishkila ya nufa, nan ya iske Ba mishkila yau shida kansa ne acikin shagon, ba ƙaramin farin ciki ba mishkila ya yiba dayaga Saifuddeen, nan yashiga tambayarsa jikinsa, inda ya amsa masa cewa "Dasauƙi sosai"
Daga shagon ba mishkila shagon Alhaji Ishaq baban abokinsa wato Ibrahim ya nufa, sosai Alhaji Ishaq yaji daɗin ganin Saifuddeen, shima sun ɗan taɓa hira inda yayi masa ƙarin ya jiki, daga shagon Alhaji Ishaq shagon Alhaji Kabiru Saifuddeen ya nufa, nan fa shima Alhaji Kabirun yacika da murnar ganin Saifuddeen, kasancewar hakan alamace dake nuna cewa sauƙi ya samu ga Saifuddeen ɗin. Sosai Saifuddeen yaɗan jima acikin kasuwan yayinda ya tsaya yagabatar da sallan Magriba cikin masallacin dake gefen kasuwan, yana idarwa suka kama hanyar dawowa gida.
Ahankali yake tuk'a kekensa haryakawo cikin falon na ummi inda ya iske Raliya, Hayatuddeen, da kuma Ummi wacce ke zaune akan kujera, Hayatuddeen na zaune aɗan gefe da ita yana latsa wayarsa, Raliya kuwa tsugune take agaban Ummin tana mammatsa mata ƙafa, murmushin dake kan fukar Ummi ne ya faɗaɗa sakamakon ganin yanda fuskar ɗan nata ke ɗauke da farin ciki, cikin kulawa tace.
"Saifuddeen kadawo?"
Kansa ya jinjina mata tare dayi mata alama, cikin body language ya sanar mata cewa daga kasuwa yake.
Murmushin jin daɗi Ummi tayi tare da cewa.
"Allah ya taimaka."
Duban Raliya tayi cikin kulawa tace.
"Bar matsamin ƙafannan haka jeki kawowa hamman naku ruwa mai ɗan sanyi yasha."
"To."
Raliya tace tare da miƙewa tsaye ta nufi hanyar kitchine ɗin dake cikin falon.
Hayatuddeen ne ya ɗago kansa, inda ya kalli Hamman nasa, cikin tausasawa yace.
"Hamma barka da dawo, dama kamar kasan naƙosa ka dawo wallahi."
Murmushi Saifuddeen yayi tare dayi masa alaman meke faruwa?
Gyara zama Hayatuddeen yayi cikin zumuɗin labarin dake cinsa yace.
"Ina wannan kyakkyawar mawaƙiyan da muka haɗu da ita a jirgi, lokacin da zamu dawo Nigeria, Hamma ka tuna ta Asma'u Ahmad Matawalle?."
Yaƙare maganan yana me tsatstsare Hamman nasa da ido.
Ɗan jim Saifuddeen yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, in few second ya hasasho fuskarta, duban Hayatuddeen yayi tare da gyaɗa masa kai alamar eh ya tunota.
Gyara zama Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Yauwa Hamma, wai kasan mene? tun ranan da takarb'i phone number na, kullum sai munyi chart, bata da wani labari sai naka, kullum maganarka take, shine yau tace nafaɗa maka wai tanasonka, zaka aureta?."
Baki Ummi ta buɗe tana kallon Hayatuddeen, shikuwa Saifuddeen fuska ya yamutsa tare da tab'e baki, wai harshi wata y'ar jagaliya mace mai rawa da wak'a data gama nunawa duniya sirrin jikinta babu hijabi zatace tanaso, bama wannan ba shi ayanda yakejinsa, ayanzu babu wata mace da zaiso, So d'ayane tak kuma Zaleeha yakeyiwa shi, sam bayajin cewa wata mace zata samu matsuguni ko muhallin zama, koda ko abaki-bakin zuciyarsa ne, d'an madaidaicin glass cup ɗin da cikinsa ke d'auke da lemon exotic, wanda Raihana ke mik'o masa ya amsa, da kad'an-kad'an yake sipping exotic juice d'in, saida yasha kusan rabin cup d'in kafun ya ajiye, ahankali yatuƙa kekensa inda ya k'arasa har gaban Ummi, hannayensa ya d'aura akan nata tare da langwab'ar dakai.
Murmushi Ummi tayi don hakan da yayi yasa ta fahimci cewa magana me mahimmanci yakeso suyi.
Cikin sakin fuska Ummi tace.
"Faɗi duk abun dake ranka Saifuddeen ni me mara maka baya ce akoda yaushe."
Murmushin jin daɗi yayi inda ya ciro wayarsa daga cikin al'jihun rigarsa, duk wani abun dake cikin rai da zuciyarsa haɗi da duk wani ƙudirinsa saida ya rubuce shi cikin text message, miƙawa Ummi wayar yayi inda ya sunkuyar da kansa ƙasa, karɓan wayar Ummi tayi cikin nutsuwa ta shiga karanta abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta, wata irin sassanyar ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe alokacin da ta gama karanta saƙon nasa, murmushine ya bayyana akan fuskarta take kuma sai ga hawaye sun cika idanunta, sosai rauninta ke ƙoƙarin fallasa sirrin zuciyarta, hannayenta tasanya ta ɗago haɓarsa, cikin son ƙarfafa masa guiwa ta shafi gefen fuskarsa, cikin yanayi na tausasa murya tace.
"Dama nasani ɗana bazai taɓa zama rago ba, haƙiƙa kai ɗin jarumine, haka kuma babu wata ƴa mace da zata so yin asararka."
Ɗan numfasawa tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya akaro na barkatai.
"Nayi matuƙar farin ciki Saifuddeen, haƙiƙa ganin aurenka yana ɗaya daga cikin burukan rayuwata, Allah Ubangiji yasanyawa tarayyarku albarka!."
Ummi tafaɗi haka cikin tsananin farin ciki, sosai takeson abun da Saifuddeen ɗin ke so, saboda farin cikinsa itama shine nata.
Cikin samun nutsuwar zuciya Saifuddeen ya ɗaura kansa bisa kafaɗan mahaifiyar tasa, cike da ƙaunarta yayi mata alaman godiya, ahankali tashiga shafa kansa, tana mejin farin ciki aranta, lallai dole ta-tayashi wajen ganin ta ƙawata bikin ɗan nata.
Hayatuddeen da Raihana kuwa idanu kawai suka zuba musu, aƙalla Saifududdeen yaɗauki kusan 4 minute kansa na bisa kafaɗan Ummi, kafun daga bisani ya janye, cikin nuna alamun gajiya ajikinsa yace da Ummin nasa zaije yaɗan watsa ruwa.
"To." Ummi ta amsa inda tace dashi Hayatuddeen zai kawo masa abinci.
Hayatuddeen naganin wucewar Hamman nasa ɗaki ya zaburo, cikin tsananin gulman dake cinsa yace.
"Ummi wani abu ya farune naga kunata farin ciki keda Hamma?".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Banason gulma fa Hayatuddeen."
Baki Hayatuddeen ya turo gaba.
Raliya ce ta gyara zama tare da cewa.
"Ummi ai ba Hayatuddeen kaɗai bama nima ina son ji, dan Allah Ummi menene, ko akan maganan aurensa ne?"
Dariyan yaran nata ne ya kamata, cikin kulawa tace.
"Yarinyar da Hammanku yakeso ta amince dashi, harma ta bashi daman turo magabatansa don atsaida maganan aure, yanzu haka mahaifinta ya amince, mu kawai ake jira mukai lefe da sadaki asaka ranar aure!."
Wani irin ihun daɗi Hayatuddeen yayi tare da miƙewa tsaye, cikin tsananin farinciki yace. "Yessss!! Lokacin yazo!."
Raliya ma tashi tsaye tayi cike da murna tabawa Hayatuddeen hannu suka tafa, cikin jin daɗi da farin ciki tace.
"Masha Allah, ae kuwa za ayi biki irin wanda ba'a taɓa yiban zaton mai nakasa zai yishiba acikin garin Gombe."
Sake tafawa da Hayatuddeen sukayi cikin jin daɗi Hayatuddeen yace.
"Yanzune jama'ar cikin garin Gombe zasu san cewa akwai manyan yara masu tasowa, na rantse Adda Raihana saina baku mamaki, saina nunawa Hammana cewa idan yana dani bashida damuwa a duniya!."
Yaƙare maganar yana me jujjuyawa, tare da soma yin rawar shaku-shaku.
Dariya Ummi da Raihana suka saka, don abun na Hayatuddeen ya wuce tunaninsu, ganin hayaniyan su Hayatuddeen ɗin na ƙoƙarin damunta yasanya ta miƙewa ta koma ɗaki bayan tace da Hayatuddeen ya kaiwa Saifuddeen ɗin abincinsa, tana shiga ɗaki ta dannawa number'n Adda Rahama ƙira, bugu biyu Adda Rahama dake kwance jikin Dr Adnan suna shan love ɗinsu ta ɗaga wayar, cikin son dai-dai-ta nutsuwarta tace.
"Ummi barka da dare."
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Barkanki dai, fatan kuna lafiya baki ɗayanku."
Da "Lafiya ƙalau." Adda Rahama ta amsa mata.
Gyara zama Ummi tayi, take tashiga labartawa Adda Rahama maganan auren Saifuddeen ɗin da ta taso lokaci ɗaya.
Hmmm faɗar irin tsananin farin cikin da Adda Rahama tasamu kanta aciki ma ɓata lokaci ne, sosai taji daɗin labarin nan tace zata tambayi Dr Adnan gobe idan yabarta zatazo gidan, da haka sukayi sallama ita da Ummin nata, cikin ɗoki haɗi da marari ta rugume mijin nata ƙam-ƙam, fuskarta ɗauke da farin ciki tace.
"Yaya Adnan Saifuddeen zaiyi aure, ina cikin tsananin farin ciki wallahi, nasan shima zai samu salihar mace wacce zata kawar masa da duk wata damuwarsa!."
Cikin jin daɗin labarin Dr. Adnan yasake hugging ɗinta, dogon gashin kanta ya shafa, tare da sanya hannuwansa ya ɗago haɓanta, ido cikin ido suke kallon juna cikin nuna jin daɗinsa yace.
"Alhamdulillah lallai zamusha biki, masha Allah mun kusa zama surukai!."
Murmushi Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Farin cikina bazai faɗu ba Ya Adnan, akullum da tausayin Saifuddeen nake kwana nake tashi, raunin Saifuddeen raunina ne, naji daɗi matuƙa saboda nasan shima ayanzu zai samu gamsuwa irinta aure!."
Murmushi Dr Adnan yayi tare da jan dogon hancinta cikin salon tsokana yace.
"Hmmm irin wato ke kinsan gamsuwar aure ɗinnan ko?"
Dariya suka sanya atare, cikin yanayi najin kunya ta ɓoye kanta acikin ƙirjinsa, sake matseta yayi cikin raɗa yace.
"Dama kuma nima gashi yau inada buƙatar wata gamsuwar, ke ma kinsani bana taɓa gajiya dake!." yafaɗi maganar yana me haɗe bakinsu waje ɗaya.
***
Fitowarsa daga wanka kenan, wata brown jallabiya yasanya ajikinsa, tattausan darduman sallansa ya shumfuɗa inda ya gabatar da sallan Isha, kana kuma ya gabatar da sallan shafa'i da wuturi, yajima zaune akan sallayan yana addu'o'i har Hayatuddeen yakawo masa abinci ya fita, bai idar ba, cikin nutsuwa yajawo kekensa, cikin yanayi na ɗan dabara daya saba ya zauna akan lafiyayyar keken nasa, food flask d'in da Hayatuddeen yakawo yashiga bubbud'ewa, kulan farko daya bud'e yam balls ne aciki wanda yaji kayan ƙamshi da kuma ƙwai, sai kuma sauce ɗin egg and onion da akayi musamman don cin yam balls ɗin dashi, ɗayar kulan kuwa pepper chicken ne aciki wanda yaji curry da kayan ƙamshi, gaba ɗaya ƙamshin abincin ya cika ɗakin, pepper chicken ɗin yaɗan ɗiba kaɗan a plate, wani ɗan madaidaicin flask ya jawo wanda ke ɗauke da tafashashshen coffee, ruwan coffee ɗin wanda yaji kayan ƙamshi ya zuba acikin wani ɗan madaidaicin cup, bawani sosai yaci naman ba saidai ace ba laifi, coffee ɗin nema yasha sosai, minti 10 da gamawa Hayatuddeen yazo ya kwashe kwanukan yafita dasu, kekensa ya tura inda ya nufi bathroom, kaitsaye gaban ɗan madaidaicin sink ɗin dake cikin toilet ɗin wanda yake dai-dai tsawonsa ya nufa, yana daga zaune akan keken nasa yayi brush, yayinda ya sake ɗaura sabuwar al'wala ajikinsa, don sam hakanan yake baya wasa indai wajen zama da alwala ne shi gwanine awannan fannin, domin yawan zama da alwala ma wata babban kariyace ga bawa.
Cikin hikima ya hau kan gadonsa tare da rage gudun AC'n dake ɗakin, luf yayi akan gadon nasa tare da fidda wani irin numfashi, lumshe kyawawan idanunsa yayi yana me imagine kyakkyawar surarta acikin idanunsa, kyakkyawan murmushine ya bayyana akan fuskarsa, sakamakon tunawa da yayi da yanda ɗan ƙaramin bakinta ke motsawa, alokacin da take surfa masa ruwan masifa, komai nata me kyau ne, haka kuma komai nata gwanin burgewa ne, harshensa ya sanya yaɗan lashi laɓɓansa wanda suke cike da muradin jinsu akan nata laɓɓan, wani irin so yakewa Zaleeha wanda shikansa baisan iyakarsa ba, yanason Zaleeha fiye da duk yanda wani zaiyi tunani, sake gyara kwanciyarsa yayi tare da sakin wani killer smile, wani irin nishaɗine yakejin ya cika zuciyarsa, kalmar
"Maye." da ta ƙirasa dashi shine abun daya dawo cikin brain ɗinsa.
cikin ƙasan zuciyarsa yace.
"Am so sorry My Beautyful Wife, dama kin sani da bakicemin maye ba, don kuwa gashi yanzu kinjawo dole saina nunamiki cewa eh da gaske niɗin maye ne."
Cikin wani irin azababben shauƙin sonta haka bacci ɓarawo ya ɗaukeshi.
Gaba ɗaya ko ina dake cikin gidan nasu ya ɗauki shiru, a irin wannan lokacin mafi yawancin mutane kowa na kwance ne a makwancinsa, yayinda wasu ke gudanar da baccin nasu cikin yanayi mai daɗi, saɓanin wasu kuwa da sukeyinsa cikin rashin yanayi me daɗi, adai-dai wannan lokacin cikin waƴanda suke bacci cikin rashin jin daɗi hadda Zaleeha domin kuwa duk sanyin dake cikin ɗakin ita gumi ne ke fesowa daga jikinta.
Binsa takeyi cikin sauri ayayinda ko takalma babu aƙafanta, ƙoƙarin cimmasa take amma yana ƙara yi mata nisa, bayansa kawai take iya hangowa kasancewar ya bata baya, cikin ƙosawa haɗi da gajiyawa ta tsaya tare da sanya hannuwan ta duka biyu ta kama ƙugunta, cikin tsananin gajiys muryar dake bayyana rauninta tace.
"Dan Allah katsaya, katsaya atare dani, barinka cikin rayuwata tamkar rabani da numfashina ne, tayaya zaka gane irin sonda nake maka? shin tayaya zaka gane cewa ina buƙatarka cikin rayuwata, Dan Allah kazo, katsaya nazo gareka!!."
Cak ya tsaya daga tafiyan da yakeyi, amma saidai ko motsawa baiyi ba balle tasa ran cewa zai juyo ta kalli fuskarsa.
Ahankali tashiga takawa zuwa garesa, taku biyu kacal ya rage taƙarasa garesa, ahankali yaɗan juyo gareta, idanunta ne suka sauƙa akan kyawawan laɓɓansa wanda ke ɗauke da kalar red, yayinda wasu kwantattun gargasa sukayiwa bakinnasa ƙawanya, wani irin sheƙi da shinnig gashin dake kwance akan fuskar tasa keyi, idanunta taɗaga daniyar kallon full face ɗinsa, kafun ta sauƙe ganinta akansa wani irin haske wanda batasan daga ina yafito ba ya cika gaba ɗaya idanunta.
Azabure ta-tashi daga baccin da takeyi, cikin ƙaraji tace "Dan Allah kada katafi pleaseee help me!!!."
Buɗe idanunta wanda suka kaɗa sukai jajur tayi, lokaci guda wani irin gumi ya shiga keto mata, ƙirjinta ne yashiga bugawa da sauri sauri, aƙalla taɗauki kusan 3 minute kafun taɗan soma dawowa cikin hayyacinta gane cewa mafarki take yasanyata sakin kuka mai ciwo, jikinta ta takure waje ɗaya tare da cusa kanta tsakankanun cinyoyinta, kuka take rerawa sosai mai ɗauke da tsanin ciwon so, cikin rufewar ido haɗi da sambatu tace.
"Shikenan