Showing 45001 words to 48000 words out of 176868 words
Chapter 16 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
yin wani mafarki ma kamacin wanda yayi ranan,
sosai abin ya d'aure mishi kai al'wala yayi sannan yayi ta karatun Qur'an washe gari, ana fitowa sallan asuba yaga Sabir k'anin Saminu yazo gaban Bappa Ali inda ya shaida mishi wai babanshine ya aikeshi kan yazo ya gaya mishi yana son ganinshi anjima shida Saifuddeen.
jin haka bai wani damu Bappa Ali ba dan akwai alak'ar zumunci a tsaka ninsu in abi ya shafi na addini to ana nemanshi.
Sai dai da yaji yace shida Saifuddeen shiyasa ya hana Saifuddeen tafiya cikin gombe yace Salisu yaje kawai shi Saifuddeen yau bazai jeba sai gobe in Allah ya kaimu da haka Salisu ya tafi.
K'arfe tare dai-dai na safe Saifudddeen da Bappa Ali suka isa fadan masarautan Dukku.
Bayan anyi musu iso suka isa har cikin masauk'in bak'i.
Cikin mutuntaka suka gaisa da mai martaba da Wazirinshi da sauran wad'anda ke wurin,
daga bisani Sarkin ya gyara zama tareda murza rawanin kanshi cikin salon mgnar sarakuna yace.
Malam Ali kunga na aika a kira minku da sanyin safi ko?."
kai Bappa Alin ya gyad'a tare da cewa.
"Eh shine ma dalilin zuwanmu domin amsa kiranka."
kai ya jinjina cikin salon adalcin sarauta yaci gaba da cewa.
"To batun dai filin nan naku na Dugge ne da filin yayanka na nan bakin kasuwa shine dai dililin kiran naku yau ma,
in baka mantaba kwanaki nayi maka mgnar cewar akwai masu son filin walau saya walau haya shi filinku na Dugge d'in sunce su ko haya ne a basu, to da nayima mgna kace min baka da hurumin saida filin domin filin nakune kai da d'an uwanka ne Bello mahaifinsu Saifuddeen ka shaida min cewa yanzu filin na magada ne yaran shi kenan da kai.
To kuma company layin waya na mtn suna tayi mana zirya a gari sabida sun tabbatar mana da cewa, sun samu igiyoyin services a cikin filin naku koda na sanar musu bani da hurumin saida musu filin sabida na magadane to sun kuma dawowa kan cewa ko hayane a basu filin duk shekara zasu rink'a biya,
nanma na kuma jaddada musu bani da hurimin filin, to sunci gaba da duddubawa cikin garin dukku amman Allah baisa sun samu wani wurinba da zasu samu su kafa na'u'rarsu ta services,
to shiyasa suka kuma dawowa gareni da neman al'farman a basu hayan filin zasu rink'a biyan kud'i mai tsoko cikin ko wanne shekara,
to ganin sun dameni nace bari in kuma kiranka kaida Saifuddeen d'in in sanar muku sannan kuyi shawara da juna."
ya k'arishe mgnar cikin son jin ta bakinsu,
shi kuwa Saifuddeen numfashi ya d'an fesar a hankali kana ya zubawa bappa Ali idanu cikin alamun nuna mishi duk hukuncin da ya yanke yayi dai-dai.
gane hakan yasa bappa Ali yin mgna cikin mutuntaka yace.
"To ba matsala in sha Allah zamuje gida muyi shawara da mahaifiyarsu Saifuddeen d'in da kuma yayarshi Rahma da k'anneneshi dan jin ta bakinsu tunda suma sunada hak'k'i a ciki."
cikin mutuntaka yace.
"To ba laifi, sai naji shawarar da kuka yanke,
amman nace musu su dawo jibi suji yadda mukayi daku."
Sai ya kuma yi gyaran murya tare da cewa.
"Yauwa to sai batun filinku na nan bakin kasuwa,
wanda kace min filin Bello ne mahaifinsu Saifuddeen ka shaida min cewa baka da ko sulai d'aya a kud'in sayan filin,
to kuma kasan tun last year hukumar bankin nan na GT bank sukayi ta zirya kan suna son sayan filin dan suna son su bud'a cibiyar bankin nasu a nan dukku,
to rashin amincewarka yasa suka hak'ura duk da sunyi ta nacin filin,
a cewarsu wai rigima kuke musu,
to kaga bayan nan kuma A. A Rano ya buk'aci sayan filin dan bud'e gidan mai nanma kak'i bada fuska,
dole ya hak'ura yaje ya nema a mashigan hari."
sai ya kuma d'an tsagaita tare da kallon yadda suke zaune cikin kamala da cikar haiba,
kanshi ya juya ga wazirinshi da Garkuwanshi kana sai sauran tsirarun mutane,
cikin tattausan lafazi yaci gaba da cewa.
"To fili dai na yaran d'an uwanka ne kamar yadda kasha jaddada min na kuma fahimceka baka son shiga hakk'insu ne ko ince kana gudun kar ka zama sanadin rabuwansu da kadarar mahaifinsu,
to nima bana son takuraku ko in saku yin abunda bakuyi niyaba,
to amman ba yadda zamuyi domin wannan filin ya kasance fili mafi girma da daraja gashi a bakin hanya gashi a bakin kasuwa gashi babban filine to wannan dalili yasa idanun manyan masu hannu da shuni ke kan filin dan duk abinda akeso za'a iya yi a wurin,
hakan yasa tun makon daya gabata hukumar ACCESS BANK suketa yi mana zirya,
na gaya musu duk yadda akayi a baya to sai sukayi ta k'ara farashin yadda zasu sayeshi sama da yadda sauran suka sayeshi a baya, har ta kai da sun ninka kud'in,
to shiyasa nace bari dai in sanar muku in kun amince la basa in kuma kunk'i amincewa bani da abin cewa,
sai dai kuma dole ku dage kuyi koda shaguna ne a wurin domin kauda idanun mutane."
jin yayi shiru alamun ya dasa aya ne yasa Waziri cewa.
"Wannan gsky ne babu dole cikin cinikin, amman kuyi k'ok'arin gine wurin in har bazaku saidaba."
cikin kamala Bappa Ali yace.
"To ba matsala ai Alhamdulillahi tunda zuwa yanzu Saifudddeen ya girma ya kuma mallaki hankalin kanshi,
ya kuma ji komai dan haka zamuje gida zamu tattauna duk abinda ya dace,
kana in mun yanke hukunci zamu zo mu sanar muku,
amman yanzu sai munje mun sanar da mahaifiyashi da k'annenshi dama yayarshi."
gyaran murya Garkuwa yayi tare da cewa.
"To ba matsala muna jiranku sai munji shawarar da kuka tsaidan."
Shi kuwa Saifuddeen wani kekyawan murmushi yayi wanda ya k'ara baiyana asalin kyanshi kai ya jinjina musu alamun sai kun jimun.
To da haka dai sukayi sallama suka tafi gida.
Koda suka koma gida kai tsaye sashin Ummi suka nufa inda suka shige har cikin d'aki kana Saifuddeen ya kira Rahma,
nan Bappa Ali ya musu bayanin duk yadda sukayi da sarki,
to ita Ummi cewa tayi ba matsala a kamfanin Mtn d'in hayan filin ko ba komai ai zasu rink'a samu ribar filin,
shima Bappa Ali ya amince da hakan hakama Saifuddeen da Rahma, to duk dai sun amince bayan sun gama mgnar wannan filin sai kuma Bappa Ali ya kalli Ummi cikin mutuntaka da tausayinta a matsayinta na yar goggonshi kuma matar yayanshi murya a tausashe yace.
"To sai kuma batun filin su Saifuddeen d'in na bakin kasuwa ya kuka gani,
kun ga dai tsawon shekara ake bibiyar filin wanne hukuncin kuka yanke?."
shiru Ummi tayi ta nisa cikin nazari tana tuno mafarkin da tayi kwana biyu da suka gabata inda taga Abbansu Saifuddeen tamkar a zahiri yana ce mata.
"Kada ki hanashi saida filin, a saida ki kuma bawa Saifuddeen kud'in kada ki damu d'anki zai kula da komai."
to a ranar wuni tayi tana nazarin wanne filin ne zata bari su saida sai yau ta samu amsar dan haka cikin nitsuwa tace.
"Ni dai a karan kaina na amince a saida filin,
dan banga amfanin zaman nashiba tunda ba komai muka gina a wurinba."
sai ta kuma kalli Saifuddeen cikin kula da yanayinshi tace.
"Babana ko kana da kud'in da zaka gina mana shaguna ne a wurin?."
da sauri ya girgiza mata kai dan shi Allah-Allah yake su amince a saida filin,
murmushi tayi tare da cewa.
"To ya ka gani ka amince a saida ne?."
murmushi yayi tare da lumshe mata ido kana ya bud'esu a hankali sannan ya zaro woyarshi tare da rubuta mata.
"A tambayi Adda Rahma dasu Raihana in sun amince dai to ni na amince na kuma amincewa Hayatuddeen tunda shi har yanzu k'ara mine."
yana gamawa ya mik'awa Ummi bayan ta karanta ta mik'awa bappa Ali shima yana karan tawa ya mik'awa Rahma, koda ta karanta murmushi tayi tare da zubawa k'anin nata idanu cikin sanyin muryarta tace.
"Ni na amince Raihana da Raliyya kuwa amincewar Ummi itace tasu, tunda suma har yanzu yarane gwara Raihana za'ace ta kai matakin balaga."
murmushi yayi tare da mata alamun ta kira Raihana.
Koda ta kira wota da akayi mata bayani sai ida nunta suka cika da hawaye cikin rawan murya tace.
"Bappa Ali ka cewa Hamma Saifuddeen yayi duk abinda ya dace a kan duk abun da mahaifinmu ya bar mana ba sai an nemi shawararmu ba."
itama Rahma sai cewa tayi.
"Damu da kadararmu ai duk kaine Garkuwarmu."
to nanfa suka tsaida mgna akan za'a saida filin.
Cikin ikon Allah a kwana biyar aka gama duk mgnar filin da za'a kafa services d'in da kuma filin da za'a gine Access bank.
Jin kud'in hayan filin services d'inma ya matuk'ar bawa Ummi Mamaki inda sukace duk shekara zasu biya one million,
sannan filin bakin kasuwar kashi uku suka rabashi in duka ce kashi biyu zasu saida d'aya kuma zasu ajiye kasan cewar filin k'atone eka-eka ne bila adadin,
to bankin sun amince dan kashi biyun zai ishesu suyi gininsu mu samman in sunce bene zasuyi har filin zai zarta zatonsu, million biyu da dubu d'ari uku da hamsin aka karkare cinikin a cikin fadar masarautan dukku, ranar ma Saifuddeen bai je kasuwaba.
Sai washe gari tun da sanyin safiya suka tafi shida Salisunshi,
koda yaje sauri-sauri ya raba ledodinshi kana ya wuce shagon Alhaji Kabiru inda yayi kicibis dashi yana shirin fita zaije gidan Alhaji Sani,
koda Saifuddeen yace mishi zai sari magin ya samu kud'in da ake buk'ata sosai Alhaji Kabiru yayi mmki,
dan haka sai ya d'aukeshi suka tafi gidan Alhaji Sani,
shima kanshi Alhaji Sanin yayi mmki sai sukaji tsoron sharrin zamani dan haka sukace dole sai yazo da manyanshi an gaya musu ina ya samu kud'in,
bai damuba ya basu tabbacin zai kawo manyan nashi.
Koda suka dawo kasuwa ranan bai saida pure water ba, gidansu Ishaq ya wuce,
ya kuma yi sa'a ya sameshi a gida nan ya tad'a mishi komai nan take kuma Ishaqn ma ya bashi k'arfin guiwa ya k'ara da cewa.
"Alhamdulillahi dama jibi Ya Rabi'u zai shigo Gombe kaga zai zauna maka matsayin lawyernka mai kare dukiyarka da kadarorinka sannan yasa hannu a lamarin dan gudun kada su cutar da kai ko su damfareka zan kuma sanarwa Babanmu ma dan ya kasance da saninshi."
ruggumeshi Saifuddeen yayi tare rubuta mishi sak'on
godiya.
daga nan ya koma kasuwa ya d'an zazzagaya da ruwan.
Shi kuwa Ishaq Saifuddeen yana tafiya ya sanarwa babansu tare da neman shawararshi ya amince ya kuma basu k'arfin guiwa sannan ya kira barrister Rabi'u ya sanarmishi komai yace ba matsala sai ya shigo Gomben.
Shi kuwa Saifuddeen koda ya koma gida,
cikin nitsuwa yayiwa bappa Ali bayanin komai.
Cikin nisan nazari da zurfin tunani Ummi da Bappa Ali da Rahma suke karanta duk bayanin da ya musu,
tun randa ya fara kai kaya shagon Alhaji Kabiru da yadda yake sonshi da yadda ya samu su Alhaji Sani suna tattauna batun tallan sirri da company maggi ta kawo musu,
da yadda yaje ya sameshi da mgnar da yadda ya gaya mishi batun yawan kud'in sarin da ake buk'ata, ya kara musu da cewa ya gayawa Ishaq shi kuma zai gayawa Babansu, da Babban yayansu Barrister Rabi'u dan yasa mishi hannu a cikin lamarin ya tsaya mishi a matsayin lawyer inshi.
Ya kuma sanar musu cewar suma su Alhaji Kaburu sunce sai sunga iyayenshi sunji inda ya samu kud'in kafin su amince da batunshi.
Gyara zama Bappa Ali yayi tare da fuskarshi kana cikin sauk'e numfashi yace.
"To inaga dai mu barshi ya gwada mu gani, domin bahaushe yace matsoraci bashi zama gwani ko shi wanene,
mu bada yak'ini a kanshi tunda munada makama kuma ba da ka za'ayi abinba kamar yadda abokinshi ishaq ya bada shawara hakan za'ayi,
dan su kansu sun tsorita da batun yadda yace yanada kud'in shiyasa sukace sai sunga iyayenshi kinga alamun gsky kenan domin da 'yan damfarane ce mishi zasuyi kada ya gayawa kowa har uwa da uba in yana dasu kada ya gaya musu,
in kin amince ni dai na amince na kuma gamsu da kasuwancin."
Ya k'arishe mgnar yana kallon Ummi da Rahma jinjina kai Ummi tayi tare da cewa.
"Ba matsala Allah ya bashi sa'a ya sanya al'khairi da al'barka a cikin lamarin ni na amince."
sosai Saifuddeen yaji dad'in amincewarsu domin suna bada dukkan yardansu a kanshi tamkar bashida nakasar komai,
shi kuwa Bappa Ali cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
"Zan je in samu Malam Ashiru abokin ya Bello, in mishi bayanin komai sannan muje gomben mu samu Babansu Ishaq da shi barrister Rabi'un sannan muje wurinsu Alhaji Kabirun sai mu tattauna duk abinda ya dace."
cikin nitsuwa Rahma tace.
"Hakan yayi Allah ya shige mana gaba."
Amin Amin sukace baki d'aya sannan suka tashi daga taron nasu.
Washe gari tun da asuba bayan an fito masallaci Bappa Ali yasa Salisu ya kaishi gidan Malam Ashiru bayan sun gaisa ya mishi bayanin abinda ke tafe dashi kan batun Saifuddeen,
sosai suka tattauna a kai nan suka tsaida cewar gobe zasuje su samu su Alhaji Kabirun.
Salisu na dawowa suka d'auki hanyar gombe suna isa Saifuddeen ya rarraba ledanshi kana yaje shagonsu Alhaji Kabiru ya shaida mishi cewa gobe iyayenshi zasu zo cikin mutuntaka alhaji Kabirun yace to sai sun zo d'in.
Daga nan Saifuddeen ya wuce gidansu Ishaq yana shiga yayi kicibis dashi da a tsakar gidan,
a tare suka shiga parlour Babansu nan ya samu Ya Rabi'u ya iso, bayan sun gaisane suka tattauna lamarin nan ya sanar musu gobe ma su Bappa Ali zasu zo sundai ajiye zance sai goben.
Washe gari kuwa koda su Bappa Ali da Baba Ashiru suka taho da babban yayansu Samisu yariman Dukku kenan kai tsaye gidansu ishaq suka wuce.
sosai suka samu tarba ta mutuntaka,
suka gaggaisa sannan sukayiwa juna k'arin bayani,
daga bisani suka sa ishaq yayiwa Saifuddeen text cewa sun isofa a ina zasu had'u dasu Alhaji Kabirun.
Yana ganin text d'in ya wuce shagon Alhaji Kabiru d'in ya gaya mishi cewar sun isofa,
cikin kula ya mik'e tare da cewa.
"To muje can gidansu abokin naka sai muyi musu jagora zuwa can gidan Alhaji Sanin."
cikin jin dad'in haka Saifuddeen ya gyad'a mishi kai sannan ya juya yabi bayan Alhaji Kabirun,
motarshi suka shiga kai tsaye suka isa gidansu ishaq sosai Alhaji Kabiru yayi mamaki ganin manyan mutane dan barrister Rabi'u sanannene hakama mahaifinshi baraden Gombe, ga kuma Yariman dukku ga kuma Malam Ashiru da Bappa Ali wanda da ka gansu kaga kamala irin ta malaman addinin musulumci.
bayan sun gaggaisa ne kuma suka mimmk'e suka nufi gidan Alhaji Sani wanda tuni Alhaji Kabiru ya mishi bayanin zuwansu a waya.
G.R.A suka nufa inda nanne anguwar gidan Alhaji Sanin yake,
suna isa mai gadi ya bud'e musu gate ganin tsaleliyar motar ya Rabi'u a gaba wanda Saifuddeen da Ishaq ke ciki a baya Yariman Dukku kuma yana gaba kusa da Barrister Rabi'un,
sai kuma motar Alhaji Kabiru wacce Malam Ashiru da Babba Ali ke ciki Babansu Ishaq kuma na gaba kusa da Alhaji Kabirun,
suna shiga harabar gidan sukayi parking,
suna firfitowa wanni d'an matashi wanda zai kai sa'an su Hayatuddeen ya iso gabansu cikin nitsuwa ya gaidasu,
kana ya kalli Alhaji Kabiru tare da cewa.
"Abba ku shigo ciki inji Daddy na."
shafa kanshi yayi tare da cewa.
"To Sulaiman." sai ya kuma juyawa ya kalli su Babba Ali tare da cewa.
"Bisimillanku mu shiga ciki."
to sukace kana suka biyo bayan yaron da aka kira da Sulaiman ,wanda yake rik'e da hannun Alhaji Kabiru yana cewa.
"Abba ina Isma'il baka zo min da shiba."
dai-dai lokacin kuma suka shiga cikin tamfatsetsen parlour yayinda Alhaji Kabiru yayi sallama tare da cewa Sulaiman.
"Isma'il baya nan ai sun tafi Yola shida Maminshi."
sai kuma yayi murmushi ganin Alhaji Sani ya nufi gaban Babansu Ishaq cikin mamaki yace.
"A a yau inada manyan bak'i kenan kaida kanka Baraden Gombe ai da kayi aike ka kiranima zan amsa kiran."
Sai ya kuma kalli su Bappa Ali dake cikin shiga ta kamala cikin sakin fuska yace.
"Marhabikun ku iso ku iso."
cikin kamala suka zazzauna shi kuwa Alhaji Sani cewa Sulaiman yayi.
"Sulaiman maza je ka kawo musu abin sha."
da sauri yaron ya juya ya fita ba jimawa ya dawo da wani babban tire cike da ababen sha mai sanyi,
sai ya kuma juya da sauri ya fita,
yayinda tuni su kuma suna gaggaisawa,
cikin nitsuwa Sulaiman ya kuma shigowa tare da tire cike da fruits ya ajiye bisa stol dake tsakiyansu,
sannan ya fara ajiye musu gorunan ruwan dana juice sai cup d'ad'd'aya a gabansu.
yayinda tuni su kuma suna tattauna abinda ya kawosu,
sosai Alhaji Sani ya d'auki abin da mahimmanci dan ganin manyan mutane suna cikin lamarin,
nan take yayi musu k'arin bayamin sannan suka bashi kud'in da dama sun taho dasu nan shaidu suka sa hannu,
Barrister Rabi'u da Barrister Salman yayan Saminu kenan Yariman dukku suka rattaba hannu ga manyan shaidu.
A nan take kuma sukayi mgnar hayan shagon da in kayan sun iso zai ajiyeshi.
ba tare da b'ata lokaci ba Alhaji Kabiru ya shaida musu akwai wani shago can k'arshan layinsu amman a luggune,
murmushi Babba Ali yayi tare da cemishi.
"Ba matsala nawane kud'in hayan."
Alhaji Sani ne ya d'an gyara zama tare da cewa.
"Shagunanshi ne ai, in kunaso ku biya kud'in wata shida in kuma kunga ba matsala ku biya kud'in shekara d'aya yadda dai kasuwa ta kama."
Barrister Rabi'u ne ya kalli Bappa da Saifuddeen tare da cewa.
"In dai da hali ku biya kud'in shekara d'aya."
da wannan shawarar bappa Ali ya biya kud'in shekara d'aya,
sannan Saifuddeen yasa hannu a cikin dukkan takardun da ya kamata na company maggi daga nan suka gama komai sannan suka sallami juna a mutunce suka tafi.
Koda suka koma gida kuma Bappa Ali ya fito da sauran kud'insu na hayan filinsu da za'a kafa services ya nunawa Ummi dasu Saifuddeen dan cikinsune ya biya hayan shago,
nan kuma suka tsaida shawarar bappa Alin ya sari kayan abinci tunda dama sana'arsa ce aune-aune.
nan bappa Ali ya fara sari a duk kasuwannin da yake zuwa kamarsu.
Ngalda, bajoga, Nafad'a, Hashidu, dogon ruwa, kiri, Malam Sidi, Kurugu, kumo, Dad'in kowa D'ukul togo. Da dai sauransu.
kasan cewar lokacin Kaka'ace amfanin gona ya nuna so kayan abinci yana araha inda tuni masu kud'i keta sara suna boyewa da nufin