Showing 174001 words to 176868 words out of 176868 words

Chapter 59 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

yiwa Baban mu biyayya, Insha Allah aurenki da Saifuddeen al'khairi ne, sannan Baba Malam bazai taɓa kaiki inda za'a cutar dake ba!."
Sabon kuka Zaleeha tasanya wiwi kamar wanda aka faɗawa ranar muruwarta, sam kalaman Ya Ahmad basu shigeta ba, inama dazai gane cewa ayanzu idanunta sun rufe, bataji bata gani, inama dabai ɓata lokacin sa ya faɗi waƴannan maganganun ba, zuciyarta tajima dayin nisa wajen tsanan Saifuddeen, bata sonsa, ba kuma ta son aurensa. Haka Zaleeha ta dinga yi musu kuka wiwi, Ya Ahmad da Maryam kuwa sai nasiha sukeyi mata tare da ban baki, saidai kuma ko ɗaya bata ɗaukar nasiharsu, aduk ma sanda sukace da ita tayi haƙuri ta ɗauki Ƙaddara, takuma yiwa mahaifinsu biyayya, saitaji kamar wuƙa suke caka mata agadon bayanta, idan kuwa suka yaba Saifuddeen, suka kuma ce ta rungumi aurensa hannu bibbiyu sai taji kamar narkakken dalma suke watsa mata cikin kunnuwanta.
Haka dai tasha kukanta ta ƙoshi har saida idanunta suka kumbura, daga ƙarshe dai Ya Ahmad ne dayaji yanda jikinta ya ɗau zafi yasakata amotarsa suka dawo gida, yayinda tabar motar ta agidan Maryam ɗin.
Tunda ta dawo daga gidan Maryam tasa kanta aɗaki ta kulle, wani zazzafan zazzaɓi kuwa take yakawo mata ziyara, domin irin kukan da tayi yauɗin nadabanne.

Haka Zaleeha ta kwashe kwana d'ayan cur bata fitowa ko ina, banda kuka ba abun da ta sa agaba, washe garin nema da taji zaman kaɗaici naneman takurata yasanya ta shirya don zuwa aiki ko kewan da takeji zai ɗan ragu, ko wani wadataccen kwalliya yau ɗin batayi akan fuskarta ba, wata bubu gown red colour da red vail kawai ta yafa ajikinta, amma dayake itaɗin ce mai kyau bawai kwalliyan da takeyiwa kanta ba duk da haka saida tayi kyau, cikin ƙunci haka ta nufi gidan redion nasu na Vission FM.
Koda taje banda Rabeel da suka gaisa babu wanda ta kula, kai tsaye tatafi gabatar da shirinta na Mushaƙata.
A kasalance ta gyara zamanta tare dacewa.
"Barkanmu da war haka sannunmu da sake saduwa cikin shirinmu mai taken mu shak'ata.
sai kuma ta d'anyi shiru tare da sakin wak'ar,.
Tattausan lafazi mai dad'i jinshi ya ratsa raina, hadarin so yayi had'owa.
Sai ta kuma d'an rage volume tare da cewa.
"Taken na masoya ne, gareku masoya."
A hankali ta dinga sake zafafan waƙoƙi na soyayya masu taɓa zuciya, wani waƙan idan tasaka har ƙwalla ne ke bin ƙuncinta, domin sosai suke ratsa mata zuciya.
kai ta jinjina tare dacewa.
"Ganin lokaci na hararanmu a gurguje ga zazzafan sak'o na masoyo, wanda shine na kusa da k'arshe.
sai kuma ta saki wak'ar K'anina Hamisu Breaker tare da k'ara volume.
A hankali Wak'ar ke tashi.
Tun forkona duniya an dasa so bisa zuciyar mutun biyu.
kuma har abadan bazai yankeba dan yanada armashi.
sai ta kuma d'an rage volume d'in tare da d'aga muryarta tana bin wakar yadda sautin ke fitowa tare cikin rauni take bin baitukan.
"Soyyyy ruwan zuma inji wasu,
wasuko sukace ruwan gubane." haka tai tabin wak'ar har k'arshe kana tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
"Ganin lokacin da aka d'ibar mana ya k'are ga wak'armu ta k'arshe." wak'ar isa ayagi.
Duk masoyi zai jure karan tsan." sai kuma ta d'an k'ara sautin muryarta tare da bin mawak'in inda yake cewa.
"Zaya jure kai kawo ko ina, zai nufin masoyinsa da hassada. Ba'ason fushi sai dai dangana."
sai kuma ta dai-daita muryarta da mawak'in suka had'a baki wurin cewa.
"Yin fushi a so tono fittina, wanda ya fara so baishiga yak'i na kanganba."
sai kuma tayi maza ta katse wak'ar dan sai taji kamar Saifuddeen take bawa k'arfin guiwa,
tana ƙare shirin nata ta fito.
Balkeesu ce ta karɓa don itace zata gudanar da labaran duniya, bayan tagama gabatar da labaranne ta gyara zama, cikin isgilanci tace.
"Kanun Labaran duniya da ɗumi ɗuminsu.mun samu wani labarin mai cike da al'ajabi daga wata majiyarmu mai taken Babu nakasasshe sai rago, cewa soyayya ta ɓarke tsakanin masu lafiya da kuma nakasassu, inda shahararriyar matashiyar budurwa maiji da kyau, ilimi, wayewa, haɗi da aji tayi gamdakatar da wani nakasashshen kurma, kana gurgu, inda yazo ya bayyana mata soyayyarsa hartakai ga suna ƙoƙarin yin aure, mudai fatan mu anan shine Allah yaƙara danƙon ƙauna da soyayya, domin ai Nasaka ba kasawa bace, kuma babu nakasasshe sai kasasshe!." taƙare maganar tana me ƙoƙarin gimtse dariyarta.

Zaleeha dake zaune aɗakin watsa shirye shirye tanajin abun da Balkeesun ta faɗa, taji ranta yayi wani irin ƙuna, take ɓacin rai ya cika mata zuciya, sam bata tsammaci haka daga Balkeesu ba abinda taketa boye shine take son sanarwa duniya.
Jakarta ta ɗauka tare da miƙewa tsaye batajin zata iya jure zama awajen aikin, saboda haka tafiyarta gida shine kawai zaifi.
Tana fitowa, tayi kiciɓus da Balkeesu, tare da wani Hamza wanda yake shima abokin aikinsu ne, Hamza irin mutanen nanne masu gulman tsiya da kuma shishshigi, gason shiga abun dabai shafesa ba, shiyasa ma sam basa shiri da Zaleeha.
Yana ganin Zaleehan yasaki dariya tare da dubanta da kyau, cikin son ƙarin jin gulma don wanda Balkeesu ta gulmata masa bai ishesa ba yace.
"Zalees fashion amaryar nakasasu, anguji masu lafiya an ƙare a nakasassu."
Cak ta tsaya da tafiyan da takeyi tare da juyowa ta watsa masa wata uwar harara, bata da lokacin tanka masa hakan yasa ta juya taci gaba da tafiyarta.
Dariya suka ci gaba dayi shida Balkeesu, ita kuwa ko sake waiwayosu batayi ba.
Kaitsaye wajen motarta ta nufa, tana shiga ta murza wa motar key tare da cillata kan titi, kanta ne ke mata ciwo sosai, gaba ɗaya damuwa ya cika zuciyarta, har wani ɗaci takeji aranta.

Baba malam ne zaune a falonshi bayan tafiyan iyayen Abdussalam wai sun kawo sadakinsu wa Zaleeha kuma wai masu kawo kayan aurenma suna kan hanya,
Malam Adam ne ke tausarsa da cewa.
"Malam Bashir ka kwantar da hankalinka domin al'amarin yaran yanzu sai du'a'i." cikin tsananin b'acin rai da tarin bak'in ciki murya a hargitee Baba Malam yace.
"Me Zaleeha take son maidani da zatayi ta turomin manyan mutane masu daraja a kanta ita d'aya, da kaifa muka amshi sadakin Saifuddeen a hannun mutane masu kima da daraja, sannan yanzu ta kuma turo min wasu, biyu za'a rabata ne? ga uwarta ita ma sai tayar min da hankali takeyi."
cikin tausasawa Malam Adam yace.
"Kada ka damu tunda su iyayen Abdussalam mun basu hak'uri mun kuma ce musu kada su bari a kawo kayan lefensu ai inaga sun fahimcemu."
kai ya jujjuya tare da cewa.
"Banga alamun hakaba a fuskokinsu, bakaji cewa suke ai dai da fari nine na bawa d'ansu damar zuwa zance wurinta, kanaji har cewa sukeyi wai in dai daure inyi dottaku kaji fa abinda Zaleeha ta jaza min zubewar mutunci da kima da dottaku a idanun mutane."
"Ba komai in sha Allah, bari inje gida anjima zan dawo inyi mgna da ita Zaleeha ka kwantar da hankalinka."
Da haka Malam Adam ya sallami Baba Malam ya tafi ya barshi cikin tarin bak'in cikin abinda Zaleeha da Mama keyi mishi...

Ita kuwa Zaleeha kaitsaye ta fara zuwa Makay ice cream and chocolate ta saya, daganan ta ɗauki hanyar komawa gida.
Tun daga shawo kwananta ta hango wata ƙatuwar mota tirela fake aƙofar gidansu sai ya Habu dake kusa da masu motar alamun suna mgna dashi kamar dai umarni yake basu kan su dena fidda kayan bisa dukkan alamu jagoranci ko kwatancen wani wuri yake musu inda zasu kai kayan.

Abakin tangamemen gate ɗin gidannasu tayi parking, buɗe murfin motar nata tayi ta fito nan tashiga bin kayayyakin furnitures ɗin da ake shigarwa cikin gidannasu da kallo, mamakine bayyane akan fuskarta haka ta wuce zuwa cikin gidan.
Kai tsaye ɓangaren Mamy ta nufa, nan ta iske su Zahira da Ziyada zaune gefensu kuwa Mamyne hannunta riƙe da littafin hisnul muslim.
Wurga jakanta tayi kan kujera cikin gajiya ta dubi Mamy ashagwaɓe tace.
"Barka da gida Mamy."
Dubanta Mamy tayi tare da cewa.
"Yauwa Zaleeha ya aikin."
"Alhamdulillah".
tafaɗa tana me ƙoƙarin buɗe ledar ice cream ɗinta,
zaro roban ice cream ɗin tayi tare da buɗewa, harta sanya ɗan ƙaramin cokali cikin ice cream ɗin sai kuma ta ɗago kanta duban Mamy tayi cikin son ƙarin bayani tace.
"Mamy naga anata shigo da kayan furnitures gidannan, Baba ne zai sanja kayan part ɗinsa ko?"
ta k'arishe maganar tare da cika bakinta da daddad'an sassanyan ice cream d'in
Kafun Mamy tayi magana tuni Zahira tayi carab ta cabke maganan inda tace.
"Kayan furnitures ɗinki ne na aure wanda Ya Ahmad yayi miki order daga Dubai shine suka iso."
Tuni ta ƙware da ice cream ɗin dake cikin bakinta, wani irin tari me ƙarfi ne ya sarƙafemata wuya da numfashi, take idanunta sukayi jajur, tari take sosai, har saida su Mamy suka tsorata, Ziyada ne tatafi kitchine da gudu inda ta dawo hannunta ɗauke da bootle water, Mamy ne ta karɓi ruwan tare da ɓalle murfin goran ta kai bakin Zaleehan, sosai tasha ruwan, saida taji ta rin nata ya tsaya sannan ta kawar da goran daga bakinta, zamowa ƙasa tayi daga kan kujeran tare da fashewa da wani irin kuka, kuka take sosai kamar wacce aka faɗawa ranan mutuwarta,
Mamy da su Zahira baki kawai suka sake suna kallonta.
Cikin kuka ta mirgino tare da kama ƙafafun Mamy, cikin matsanancin kuka tace.
"Mamy dan Allah Kifaɗawa Baba Malam cewa banason wannan auren, wallahi na tsaneshi, matuƙar aka aura mini shi kashe kaina zanyi, wallahi dana aureshi na gwammace mutuwata!"
Ajiyar zuciya Mamy ta sauƙe tare da kamo kafaɗun Zaleehan cikin son bata baki tace.
"Ki kwantar da hankalinki Zaleeha, babu wani bawa da ya isa kaucewa ƙaddaransa, ki amshi auren nan amatsayin ƙaddaranki..."
Ihun da Zaleeha tasanya ne yasanya Mamy yin shiru ta zuba mata ido, kuka sosai Zaleeha takeyi, afujajan ta nufi hanyar fita daga cikin falon sambatu kawai takeyi tana cewa.
"Wallahi Bazan aureshi ba, na tsaneshi saina kashesa sannan kuma nakashe kaina!."
Da kallo suka bita su dukansu harta fice.

Kaitsaye part ɗin Mama ta nufa, da kuka sosai ta shiga cikin falon, kaitsaye ɗakinta ta wuce, Mama da Yayarta dake zaune afalon suka bita da kallo.
Tana shiga cikin ɗakinta ta murzawa kofar key, nanfa tashiga buge 'uge da fashe fashe, tanayi tana ihu da kururwawa akan cewa ita lallai batason Saifuddeen.

Motocine jere reras kusan guda goma ke shigowa cikin gidan a dai-dai lokacin da tuni Habu yayiwa tirelar nan jagora sun tafi bayan yasa sun kwaso kayan yaje ya gayawa Baba Malam uzurinshi,
suna gama dai'dai-ta parking, wasu mata suka soma fitowa daga cikin motacin nan aka soma fito da wasu haɗaɗɗun akwatuna kai tsaye matannan ɓangaren Mama suka nufa, koda suka ƙarasa falon na Mama cike da farinciki Mama da Yayarta suka karɓesu, nan fa matan suka baje waƴannan akwatunan nan guda 35 agaban su Mama, haka suka dinga fito da tsadaddun kayayyaki suna nunawa su Mama, Mama kuwa da Yayarta tuni zuciarsu sun cika da farinciki, Mama dai burinta na son ƴarta Zaleeha ta auri Abdussalam ya kusa cika, yanzu ma aka soma wasan tunda dai ga kayan aure nan dangin Abdussalam sun kawo, haka Mama suka cika dangin Abdussalam da kayan tarban baƙi, cikin girmama juna sukayi sallama inda suka rakasu har bakin motocinsu saida sukaga tafiyarsu kafun suka dawo cikin gida.

Afujanan Zaleeha tafito daga cikin ɗakinta aniyarta nason zuwa falon Baba Malam don sanar dashi cewa batason auren, fitowarta yayi dai-dai da shigowan Maryam cikin falon wanda yanzun zuwanta gidan.
Baki buɗe Zaleeha ke kallon tarin akwatunan dake zube gabansu Mama, kamar zatace dasu wani abu kuma saita fasa, hartakai ƙofar fita daga cikin ɗakin, Muryar Ruda ya daki dodon kunnenta inda take cewa.
"Kee! Zaleeha bakiga kayan aurenki da Abdussalam ya kawo bane?".
Dummmmm dammmmmm haka zuciyar Zaleeha ya buga, a firgice ta juyo cikin tsananin damuwa haɗe da tashin hankali murya can sama da k'arfi tace.
"Kayan aurena kuma again?".
Cikin son lallaɓata Mama tace.
"Eh mana Zaleeha ko bakyaso afasa aurenki da wancan bazan musakin ne?".

Wani irin tsalle ta daka tare da kururuwa haɗi da ihu Zaleeha tayi da k'arfi nan fa ta shiga kuka tare danufar kayan auren, cikin fitar hayyaci tashiga ɗiban kayan tana watsi dasu acikin falon, babu abun da take sai sambatu masu nuni da cewa bata cikin hankalinta sam.
Ganin watsi da kayan basu mata ba yasa ta shiga ɗaukan kayan tana watsawa can waje, cikin zaucewa take ihu kana tana buge-buge da ife-ife kamar wanda aljanu suka shafa,
Dai-dai lokacin Ya Ahmad da Mamy suka ƙaraso don tun daga part ɗin na Mamy sukejiyo ihu da kururwan Zaleeha.
Ganin Zaleeha na watsi da kaya yasa Ya Ahmad ƙarasowa da sauri ya nufi inda Zaleehan take, ƙoƙarin kamo ta yake da sauri taja da baya, wata ƴar knife ɗin da ke aje bisa wani table ta ɗauka, saita knife ɗin tayi akan cikinta, cikin zaucewa haɗi da fitar hayyaci ta zazzaro jajayen idanunta murya a hargitse tace.
"Zan kashe kaina, wallahi idan aka auramin ɗaya daga cikinsu saina kashe kaina, kada ka matsoni Ya Ahmad kana matsowa wallahi saina kashe kaina ayanzu nan!.." taƙare maganan tana sakin wani matsanancin kuka mai nuna tsantsar tashin hankali.

Iya tashin hankali babu wanda bai shigesaba acikinsu, tuni Maryam ta saki kuka mai taɓa zuciya, Ya Ahmad ma hawayene suka cika cikin idanunsa.

Duk abun dake faruwa akan idanun Baba Malam, da ya taho tun ihun Zaleeha na forko wanda a zatonshi wani mugun abune ya farmata, jin kalamanta da ganin abinda takeyi ne yasashi bud'e labulen ƙarasowa cikin falon yayi tare da duban Zaleeha dake kuka harda shiɗewa still knife ɗin na hannnunta da alama ƙiris take jira ta cakawa kanta.
Cikin tsananin takaici haɗi da ɓacin rai da tsantsar tashin hankali da bak'in ciki ya bud'e bakinshi cikin tsananin cushewar sauti muryarsa cike da amon ɓacin rai yace.
"Kin nunamin ban isa dake ba, kin nunamin cewa baki ɗaukeni matsayin uba agareki ba, haƙiƙa kin nunamin cewa ke bakizama ƴa ta gari mai biyayya ba, shikenan zan barki keda mahaifiyarki kuyi duk abun da kukeso, zama daku sam bashida amfani awajena saboda haka yau zan tafi zanyi nesa daku, Zaleeha yau zanbar miki gidan idan yaso kiyi duk wani abun da kikeso, duniyace ae ta isheki riga harma da zanin ɗaurawa, zan tafi inyi nesa daku tun kafin ku kasheni da bak'in ciki." Yana kaiwa nan azance nasa ya juya yanufi ƙofar fita daga ɗakin.
Cikin tashin hankali da fargaba Ahmad da Maryam suka zube aƙasa tare da kamo ƙafan Baban nasu cikin matsanancin kuka suka shiga basa haƙuri.
Rumtse ido Baba Malam yayi har cikin ransa yanajin wani matsanancin ɓacin rai, saidai suyi haƙuri amma tabbas tafiya zaiyi zaiyi nesa dasu domin bazai iya jurar haɗiye baƙinciki da ɓacin ran da Zaleeha da kuma Mama ke ƙunsa masa ba.
Hawayene ke zuba a idanun Mamy yayinda zuciyarta tayi wani irin mummunan karyewa tabbas idan Baba Malam yatafi itama bazata zauna ba, saboda dama danshi kawai take zaune agidan.
idan babushi kuwa me zata zauna tayi agidan.

A kid'ime Maryam ta dawo kusa da Zaleeha cikin muryar kuka tace.
"Dan Allah Zaleeha kice kin amince kada kice a a, Baba fa tafiya zaiyi Zaleeha, kiji tausayinmu! Zaleeha kiji tausayinmu!! dan Allah kada ki bari bak'in cikinki yasa mahaifinmu yayi nesa damu." cikin matsanancin kuka Maryam takare maganan.
Kai Zaleeha ta girgiza cikin bushewar zuciya tace.
"Wallahi Bazan auresu ba, natsanesu dukansu biyu ba wanda nakeso, wlh xan kashe kaina matuƙar aka matsamin kan aurensu."
Cikin ƙaraji tace.
"Natsanesu Bana sonshi!"
Wani irin gigitaccen ihu tasa tare da sanya knife ta yanka wuya..............!



Alhamdulillah...

Mu had'u a kashi na biyu, dan jin yadda wasan zai kaya. K'ak'a-tsara-k'ak'a?." Shin Dalla me zai aikatawa Zaleeha? 1 towai ina Baba malam zai tafi? 2 Ya cire hannunshi cikin auren ne? 3 wa zai auri Zaleeha!? 4 Anya kuwa Saifuddeen zai iya ratsa budurcin budurwa?. 5 Wacece Amina me nufinta kan Saifuddeen? 6 Shin Asma'u zata hak'ura da wannan zazzafan matashi mai suran laraban kuwa? 7 Ummi dai tace dolefa a fasa wannan auren na Zaleeha da kekyawan d'anta! 8 Me nufin Ishaq akan Bilkeesu? 9 Me gskyar zuciyar bilkeesu akan Zaleeha? 10 Shin Saifuddeen kuwa zai iya yin sex kamar ko wanne lafiyayyan namiji? 11 ina Habu zaisa akai kayan da akace na Zaleeha ne? 12 Me Raveel zai iya yi a rayuwar Zaleeha?. 13. Me nufin Mama me zata aikata? 14 Ya Aminu da Ya Habu me zasu aikatawa Zaleeha shalelen Ya Ahmad in sunji tasa Baba malam Kuka? 15 Amsoshin tambayoyin nan duk suna cikin littafin Nakasa ba kasawa bace part two kada ku sake a barku a baya, dan yanzu muka shiga cikin ainihin gundarin labarin. Zazzafar soyayya mai kashe jiki da ratsa zuk'ata, al'ajabi, tausayi, mamaki, dariya, Shauk'i mai girgiza zuk'atan makaranta duk abubuwan suna cikin part two. Saifuddeen zaiyi abunda babu jarumin da ya tabayi cikin jaruman books na, zai shayar daku mmki zai saku Shauk'i mai tunzuro k'uruciyar amarci...!





*BY*
*GARKUWAR FULANI*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login