Showing 153001 words to 156000 words out of 176868 words

Chapter 52 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

katafi kabarni? yazanyi? shin tayaya kake tunanin zan iya jure rashinka? nazautu akan sonka, nakai ƙololuwa,  nazama kurma, makauniya,  har wasu suna mini kallon zautacciya duk akan sonka,  Ina sonka! Ina sonka! Ina tsananin sonka!!!."  Taƙare maganar tana me rushewa da kuka, sosai Zaleeha tayi kuka awannan dare har da shiɗewa,  daƙyar ta iya jan jikinta ta wuce toilet, wanke fuskarta tayi kana ta ɗauro alwala, sosai wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon kai suka rufeta asakamakon kukan da tayi, wata zumbuleliyar hijab ta sanya ajikinta, inda ta hau kan shunfuɗaɗɗen dardumanta, cikin tsananin ciwon da kanta keyi mata tagabatar da sallan Nafila raka'a huɗu,  zama tayi akan praymad  tare da jingina bayanta da jikin bango, idanunta ta lumshe, ahankali wasu zafafan hawaye suka shiga kwaranyowa daga cikin idanun nata, ji take kamar zuciarta zata fashe saboda soyayyarsa, ashe dama haka so yake? ada taɗauki batun so wasa sai gashi kuma yanzu yana shirin yi mata ɓarin kwan makauniya, haƙiƙa gangar jiki da zuciyarta na azabtuwa, Inama da ace yin so baizama ɗaya daga cikin Ƙaddarorinta ba,  kuka tacigaba dayi sannu ahankali wani wahalallen bacci ya samu nasaran ɗaukarta..

Kamar yanda ya ƙudurta aransa hakance ta kasance, zuwa yanzu yasanar dasu Baffa Ali gaba ɗaya abun dake faruwa.

5 million ya ware daga cikin ribarsa,  ayau yau yake da buƙatar haɗa kayan lefe, inda Baffa Ali yace ya ɗauke masa nauyin biyan sadaki.
Aunty  Kubra matar yayan Abokinsa Jabeer dakuma Adda Rahama sune suka shiga cikin babban kantin nan na San Hussain Super Market don haɗo masa kayan aure nagani na faɗa,  dayake Aunty Kubra cikakkiyar ƴar kasuwace kuma sana'anta kenan saida kayan mata, hakan yasanya sosai ta darje wajen zaɓo zafafan lesuka, atamfofi, shaddodi, materials,  dakuma tsadaddun yadukan boyels na mata, kaya sosai suka saya masu tsananin tsada don kuwa kaf cikin kayan nasu babu wanda kuɗinsa yayi ƙasa da dubu Hashirin talatin dai arba'in dai kana hamsin, ɓangaren jakakkuna da takalma kuwa ba acewa komai domin kuwa kaya suka saya masu kyau da inganci.
sashin yan kunnaye da awarwaro haɗi da saraƙa kuwa komai na gwal suka saya,   ɓangaren takalma da jaka kuwa ko wani takalmi da mayafinsa, kana kuma da kalan kayansa, materials, lace, atamfa ko boyel,   sashin ƙananan kaya kuwa abun ba'acewa komai, ɓangaren dogin riguna kuwa saida suka cika akwatuna biyu tam da dogin riguna masu kyau da tsada, domin kaf cikin rigunan babu ta ƙasa da 30k, kaya kam dai sun haɗu sosai, musamman ɓangaren kayan meckup sun kashe kuɗi sosai, musamman suka sayi meckup kit har guda uku,   masha Allah kaya ya haɗu sosai inda aka shirya kayan cikin akwatuna, tsab kayan suka ɗauke gaba ɗaya akwatuna 24 dozin biyu kenan sai guda shida da akasa kayan uwa da uba a akwati sauran ukun kuma akasa na dangi shine ya bada akwati 30 da suka saya.   Koda suka dawo gida kowa saida ya yaba kayan domin anyi abu wanda sam babu ƙaranta aciki, ko ƴar Gwomna aka kaiwa ba laifi. ya ware Million uku da rabi ya bawa Salisu, tare da cewa ya kawo mishi dan ƙareriyar mota mai kyau ta mata irin wacce ake yayi.

Shima Salisu nan yayi tasa bajintar, inda ya kawo haɗaɗɗiyar mota har ta million huɗu.

Can cikin gida kuwa tuni su Adda Rahama, Aunty Mina, Aunty Kubra, matar yayan Jabeer, da Goggo Dada, da  Hajia Rabi matar Alhaji kabiru duk suna cike a parlour Ummi, musamman sukazo don kai lefen Saifuddeen.

Hayatuddeen da abokanshi Imran da Sulaiman ne suka shigo da kayayyakin.
Wanda Ahmad yake matuk'ar jin takaici da bak'in cikin yawan kuɗaɗen da aka ɓatar akan yarinyar da ba mutunci ne da itaba.

Gaba ɗaya sun cika da mamakin irin Yanda Saifuddeen ya narka kuɗi wajen ƙawata kayan,
Hajia Rabi ce tace.
Sam baza'a kai kayan nan duka ba dole a rabashi biyu, ai wanna almobazzaranci ne.
Ita dai Ummi shiru tayi tare da danne ainihin abinda ke ranta wanda babu mahaluk'in da zai gane meke cikin ranta.
Aunty Kubra ce tace a a banda dai a raba biyu kam,
dan ita bata son harkan ƙaranta,
ita da tasoma a Dubai zasu haɗo lefen dan dai kawai abin yazo a ƙurarren lokaci ne, ta nace dole saida aka rarrage wasu abubuwan wasu kuma tama hana fir.

A gidan Baba malam kuwa tun jiya da yamma da Dirankadi ya shaida mishi gobe fa za'a kawo komai da komai kama daga gishiri goro da lefe da kayan rufi da sadaki,
duk zasu kawo a tare sai ya gayawa Mamy.
dan Mama yanzu ko Magana bata mishi, shiyasa shi kuma ya shareta dan ya bata iya matsayinta na uwa so yanzu dole ya nuna mata koda ita ko ba ita dole nefa zai aurar da yarsa ga wanda takeso, ya ga kuma ya dace da ita.

Daga nan ya ƙira ƙanwarshi Goggo Maryama ta kwarar Maryam yayar Zaleeha kenan.
Kana ya sanar da ita Maryam ɗin.
sannan matar abokinshi Malam Adam itama tazo,
sai Maman Ya Aminu matar yayanshi kenan,
ga Lubna matar Ahmad nan fa Lubna da Maryam suka shiga kitchen tunda safe
suka fara shirya abin tarban baƙi, waƴanda za abawa ƴan kawo lefe da kuma abinda za'a basu su tafi dashi gida, kamar yanda al'adar Gombawa take.
Mommy matar malam Adam ƙawar Mamy mace mai sauƙin kai gata ta iya girki da kala-kala kasancewar shuwa arab ce. Tana matuƙar son Zaleeha haka itama Zaleeha duk cikin matan abokan Baba malam  da suke ƙawayen Mamy tafi sonta.

Sosai suka shirya komai cikin manya-manyan food flask masu azabar kyau,
yayinda tuni sun cika fridge da ƙawatattun drinks.

Mama kuwa dama yau tunda sanyin safiya ta tafi Doho gidan yayarta Ruda da takebi wacce itama arniya ce dan duk zuriyar Mama ita kaɗaice ta musulunta sai ƙanwarta mai binta,
wacce ta sauya suna daga Rebeka ta dawo Aisha.
tana nan cikin Gombe da mijinta da yaranta Aisha macece mai nitsuwa da kamala sau da dama tana dakatar da yayar tata daga aikata wasu mugayen ɗabi'u da sukafi dacewa da masu aljihun baya.
Yayinda Ruda kuwa ke ingizata.

Ƙarfe uku da rabi  na yammaci dai-dai,
Salisu yazo da Matarsa Sadiya da zazzafar motarsa,
Kana Ahmad ya d'auki motar Saifuddeen,
sai kuma Aunty Kubra da Jabeer yazo ya amshi tuk'in haɗaɗɗiyar motarta ƙiran babbar vibe,
sai kuma Motar Ishaq da direbanshi. sai Motar ya Adnan. Sai dalleliyar mota kirar kia samfurin bugun 2019, wacce take baƙa mai Shek'i dan har an kawo fara Saifuddeen yace,
ai ita farar macece dan haka baƙa za'a kawo mata, don haka dole aka canzo aka kawo mata kalar da yake so ɗin.
Nan duk suka kwashi kayan suka shirgeshi cikin motar kana aka bawa Muddasir Key ɗinta yaja.

A jere-a Jere suke tafiya yayinda,
Hayatuddeen ke cikin motar Aunty Kubra,
yana gaba gefen Ya Jabeer. Ita kuwa Aunty Kubra ita da Aunty Mina suna baya.
Imran kuwa motar ya Adnan ya shiga yana gaba kusa dashi baya kuma Adda Rahma ce da Goggo Dada.
Sai motar Saifudddeen da Ahmad ne  aciki,Raliyanshi na gefenshi,
tana ta son sama mishi farin ciki dan ta lura sam shi baya wani farin ciki da abun.

Sai Hajia Rabi dage gefenshi wacce itama sam bata farin ciki da abin sabida Hayatuddeen yana gaya mata komai.
sai motar ishaq wacce ba komai a ciki shiyasa shida Saifuddeen suka shiga baya direbanshi yaja,
suka nufi can k'ungiyar tasu.

Shima Ahmad sam baiso zuwaba to ya zaiyi dole yaje.

Su kuwa masu kai lefen.
Suna isa bakin Gate ɗin gidan mai gadi ya wangale musu gate inda suka kutsa cikin gidan cikin nutsuwa,
bayan sun gama yin parking ne.
Ahmad ya fito ya nufi wurin mai gadin,
hannu ya bashi suka gaisa sannan yace mishi ya shiga cikin gida yace bak'in sun iso.
Cikin mutuntawa mai gadin yace to tare da juyawa ya shiga cikin gidan.

Jim kaɗan ya fito yace.
Ance su isa.

Nan duk matan suka shiga su kuma mazan duk suka zauna cikin motocin.

Suna shiga cikin gidan Maryam tayi musu jagora har babban parlour Mama duk da bata nan dole a bata matsayinta na uwa.
Bayan sun zazzauna, an gaisa cikin mutun taka, an kawo musu drinks da snacks, sun ɗan taɓa abin sha.
Hajia Rabi ce ta gyara zama tare da cewa.
"Raliya je kice Imran Suleiman da Hayatudeen su shigo da kayan."
A hankali ta mik'e tare da cewa.
"To."

A tare suka shigo duk suna riƙe da akwatuna harda ma'aikatan gidan,
haka suka dinga shigowa da haɗaɗɗun akwatunan cikin falon, saida suka ƙare
sannan suka juya suka fiti suna haki,  dan sosai akwatunan suke da nauyi kasancewar kowanne ashaƙe yake da kaya.
Aunty Kubra ce ta kalli Raliya dake riƙe da ɗan Maryam tana mishi wasa,
tace.
"Ke ƙanwar ango ai bakici ta zama tashi ki nuna musu kayan."
murmushi tayi tare da cewa.
"To Aunty Kubra amman dai a tayani."
Murmushi sukayi baki ɗaya ganin yadda taketa kiciniyar bubbude akwatunan,
tare da cewa.
"Wannan turamene a ciki wannan laces, wannan shadda wanna boyel."
sai kuma ta fara jawo na ƙananun kaya dana kayan shafa wanda ta buɗe akwatuna biyu wanda suke cike maƙil da ababen shafawa na kwalliyar jiki irin na mata.
Da sauri Mommy matar Malam Adam tace.
"Masha Allah. Gsky ki huta kawai, wannan ai yafi ƙarfinki muma masu gani har mun gaji,
wani abun ai bazai ganuba,
sai dai muce Allah ya sanya al'khairi yasa al'barka a ciki."
Aunty Lubna kuwa kai kawai take jinjinawa domin idonta ya raina fata,
nakasasshen da ake zatawa riƙe ƙoƙon bara da bin kwararo lungu da saƙo yana allazi wahidin,
shine da wannan kayan lefe wanda ita dai a iya ganinta lefen Zahra buhari ne kawai ta taɓa gani wanda zatace yafi wannan, a dai gani da idonta.
Goggo Maryama kuwa tausayi suka bata ganin irin ruwan dukiya da suka binne a kan yarinyar da ta sani tabbas uwarta bazata barta ta zauna a gidan Saifuddeen ba.
Mamy ma tabbas tausayinsu taji ganin yadda sukayi ɓarin naira.
Maryam kuwa sai addu'a takeyi a ranta tana cewa.
"Ya Allah ka rufa mana asiri,
ka hana mahaifinmu jin kunya da tozarta,  ya Allah ka tausasa mana zuciyar wannan baiwar taka Zaleeha kasa tayiwa mahaifinmu biyayya ta zauna lfy da mijinta da yan uwanshi."
sosai Maryam ke jin tsoron abinda zai zubarwa mahaifinsu darajarsa da mutuncinsa.
Adda Rahamace ta ɗanyi dariya kana ta jawo ɗan kit ɗin  da saraƙuna suke ciki, ta buɗe  babban gwal ɗin da Saifuddeen ya saya  a India ta zaro ta miƙawa Mommy dake kusa da ita cikin sanyi tace.
"To ga wannan ko za'a adanashi da ban, duk da cewa sauran ma gwala gwalaine amma shi tsadansa dabanne."
sosai Mommy ta girgiza da girma da darajan gwal ɗin, mai surki da ruwan farin zinari.
amsa tayi tare da miƙawa Mamy,
mamakinsu ya ƙaru ne lokacin da Aunty Kubra ta miƙawa Aunty Lubna car key ɗin kia d'innan tare da cewa.
"Ga wannan Key d'in motar amaryarmun ce,
motar tana nan waje.
zuwa yanzu fa Mamy abin ya fara zarta zatonta cikin dattaku da nitsuwarta da iliminta tace.
"Anya kuwa, gsky Malam zaiyi faɗa in muka karɓi abubuwan nan, ko lefen ma in ya gani zaiyi faɗa."
Da sauri Goggo Dada da Aunty Kubra sukace.
"Dan Allah da manzonsa kar muyi haka daku,
Saifuddeen bazaiji daɗiba tunda shi ya gani zai iya yiwa matarsa komai,
kuma abinda nanda wani ɗan lokaci ta zama matarsa."
Murmushi Aunty Lubna tayi tare da cewa.
"Kuma shi za'ayiwa kolliyar ba."
Ta ƙarishe mgnar tana kallon Aunty Kubra wacce bazata wuce sa'arta ba.
da sauri Aunty Kubra tace.
"Ato kunga ai kanshi yayiwa tanadi, mutun da matarsa."
Goggo Maryama ne tace.
"To mu dai tunda kunce dan Allah da manzonsa to zamu amshi kayan,
saura mgna kuma tana wurin Yaya Malam."
Hajia Rabi ce tace.
"Shima anjima da dare za'a kawo sadaki fatanmu Allah yasa,
a saka bikin nanda mako ɗaya."
Amin Amin sukace baki ɗaya.
Maryam ce tace.
"ai kam naga alaman Saifuddeen ya zaƙu yana son matarsa nan kusa tunda gashi harda kayan rufi kuka kawo."
Cikin sakin fuska Adda Rahma tace.
"Sosai makuwa ,ai shi ko yau ya sameta yana so."
Daga nan suka ɗan taɓa hira sannan suma miƙe tare da cewa.
"To mu zamu tafi sai kuma in munzo ɗaukan amaryarmu."
Da sauri Mommy ta kalli Maryam da Lubna ta musu alamun su ɗauko food flasks ɗin dake cike da ababen mƙulashe.

Ganin sunata cika musu kulolin a gabansu yasa,
Goggo Dada cewa.
"wannan abu yayi yawa ku barshi."
da Saudi Goggo Maryama tace.
"A a ai yaba kyauta tukuici, ku barmu muma muyi iya iyawarmu."
Hajia Rabi ce ta kalli Mommy matar Malam Adam dake miƙa mata damin kuɗin tukuicinsu rafa guda shida yan dubu daddaya.
A hankali tace.
"Hajia wannan kuɗin kuma na menene duka?."
Cikin salon girma ba batun ƙaramta Mommy tace.
"Yaba kyauta tukuici, ba ku muka bawa ba yaran da suka shigo da kayan muka bawa."
Akan dole su,suka karɓa, nan Aunty Lubna taƙira biyu daga cikin masu aikin gidan Baba Malam ɗin suka shiga jidan food flask ɗin suna kaiwa cikin motocin da su Adda Rahama suka zo dashi.

Har bakin gate suka rakosu baki d'ayan su,
aka rabu cikin mutunci da jin dadi.

Bayan sun koma cikin gida ne,
Aunty Lubna ta kalli Maryam tare da cewa.
"Ke zo muga kayannan da kyau,".
Dariya Maryam tayi kana ta matso ta fara bubbud'e akwatunan, Mommy, Mamy, goggo Dada kuwa suma zama sukayi suna kallon kayan d'aya bayan d'aya.
yayinda tuni Aunty Lubna keta viewing tana d'aukan komai a zazzafar wayarta.

Sune basu gama ba har aka kira sallan magrib, dole suka hak'ura suka k'arisa kallon a gaggauce kana suka rufe komai,
suka shirgeshi a cikin d'akin Mama,
kana duk sukayi al'wala dan gabatar da salla.

Bayan sunyi sallah harda na isha,
sukaci abinci,
sukaci gaba da hira,
dan Maryam jira take mijinta ne zaizo ya d'auketa hakama Mommy Malam Adam ne zaizo ya d'auketa,
Goggo Maryama kuwa Ya Ahmad ne zai maidata gida.

Baba Malam kuwa, tunda yamma yake gidan Malam  Adam,
dan amaryarshi bata zoba.
Ya Ahmad kuwa da Ya Aminu tunda safe suka tafi dukku kai ziyara dan Ya Ahmad ya kusa komawa Abuja.

Saida akayi sallan magriba suka dawo,
Kai tsaye parlour'n Baba Malam suka nufa,
nan Maryam ta kawo musu abinci,
bayan sun gama cine sukayi al'wala suka nufi masallaci a nan suka samu Baba malam da Malam Adam.
Koda aka idar da salla tare suka shigo cikin gida.

Suna shiga bada dad'ewa ba,
Dirankadi da Bappa Ali da Malam Ashiru suka iso harabar gidan.
Dirankadi ne ya kira Baba malam ya shaida masa isowarsu,
jin haka ya kalli Ahmad tare da cewa.
"Ahmad tashi kaje ka shigo da iyayen Saifuddeen."
Cikin tsananin girmamawa da sanin darajar mahaifa Ahmad yace.
"To." sannan ya miƙe tsaye ya fita.
Yana zuwa yayi musu jagora har zuwa parlour'n Baba Malam ɗin, sunyi farin cikin ganin juna sosai.

Bayan sun gaisa ne tare da ɗan taɓa hira,
sai Bappa Ali ya ɗan gyara zamanshi tare da yin gyaran murya kana ya fito da damin kuɗi kimanin dubu ɗari cas,
daga cikin aljihun babbar rigarshi,
miƙa kuɗin yayi wa Malam Adam tare da cewa.
"To ga aiken ɗana Saifuddeen ga sadakinshi."
cikin sakin fuska Malam Adam ya karɓa tare da cewa.
"Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi. Yasa ayi damu."
"Amin Amin." suka amsa baki ɗaya,
sai kuma suka kalli Dirankadi da yace.
"Tofa ɗalibin naka yace yanzu sauran a saka masa rana kawai."
Murmushi mai kama da dariya sukayi baki ɗayansu, sannan
Malam Adam ya kalli amininshi Baba malam da yaketa murmushin jin daɗi yace.
"To Malam Bashir me kace kan batun saka ranan?."
Kanshi ya ɗan rausayar ya kalli babban ɗanshi mafi soyuwa a zuciyarshi, kana kuma ɗansa mai tsananin biyayya da kare mutuncinsa,
sannan ya kalli ɗan ɗan uwanshi kuma surkinshi mai kare daraja da martabar ahalinshi wato Ameenu kenan, yace.
"To ga yayun Zaleeha nan mu basu dama muga irin dattakunsu mana."
da sauri Ahmad ya ɗago kanshi ya kalli mahaifin nashi sai kuma yayi sauri yayi ƙasa da kannasa tare da cewa.
"Baba malam in dai kuna raye ai mu bamu da bakin mgn, sai abunda kukace."
sosai Ahmad ke burge su Bappa Ali yanayin biyayyarsa tamkar Saifuddeen.
malam Adam ne ya ɗan kishin giɗa kana ya kalli Ahmad da Aminu yace.
"To Ahmad mu ɗin tabbata zamuyi ne?."
A hankali ya jujjuya kanshi yana mai jin tsoron randa zai rasa iyayenshi.
Shikuwa Malam Adam cigaba yayi da cewa.
"To kaga shiyasa muke jawoku a jiki dan mu nuna muku yadda ake aiwatar da komai na jagoranci,
a matsayinku na manya wanda dole wata rana kune a madadinmu,
yanzu dole zamu so muga yanayin dattakunku,  tunda dai kusan komai kuma kunga an kawo ko wani abu na al'ada kama daga gishiri da goro da lefe da kayan rufi, kana yanzu kuma kunga sun gabatar da abinda shariya ta zantar sun kuma buƙaci a saka ranar biki,
to yanzu dattakunku muke son gani,
kai Aminu kaine Babba kan Ahmad yaushe nene kakega za'ayi bikin?."
A hankali Ya Aminu ya ɗan rusunar da kanshi sai kuma ya kalli Ahmad,
kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa.
"Ashirin da bakwai ga wata mai kamawa. Yayi ko?."
A hankali Baba malam ya fidda sassauƙan numfashi tare da cewa.
"Yayi kyau,  to Amman meyasa har wata ɗaya, baku shirya bane?."
Cikin nitsuwa Ahmad ya kalli mahaifin nashi tare da cewa.
"Eh to Baba malam mun shirya amman bamu gama shirin ba.
Nanda kwana biyar zan koma Abuja,
sannan inada zirga-zirga tsakanin ƙasashe da dama Dubai, India, US, Korea, Egypt. Yanzu dai in na fita zan ɗan kwana biyu kafin in karkato Nigeria, kuma inaso inyiwa Zaleeha kayan ɗaki mai kyau zan bata zabi kayan ƙasar da takeso,
zan gama saya mata komai a online sannan nasan cikin sati biyu jirgi zai iso dasu nan,
to shiyasa nake son ya kai wata ɗaya."
murmushi Dirankadi yayi tare da cewa.
"Yaran zamani ku dai kunfi yarda da kayayyakin ƙasashen turawa, sam kun Kasa tsayuwa ku inganta mana na ƙasarmu yadda zamuci gaba muma, yanzu jihar gombe wanne irin kayane babu?.
Duk fa arewacin ƙasarnan babu jihar da ta kai jihar Gombawa yawan kafintoci da ci gaban kafintoci. Babu irin samfurin kayan ƙasar waje da basa iya sarrafawa,yanzu konan cikin Sahaja Ventures kuka shiga ae akwai kaya masu kyau da inganci, wasu ma harsun ɗarawa kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login