Showing 27001 words to 30000 words out of 129558 words

Chapter 10 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

auri Saratu ne?" Sai da _Khalil_ ya d'ago suka had'a idanu da Baba sannan ya sunkuyar da kai yace, "Baba mahaifiyata sam bata da matsala. Mace ce mai fahimta sosai. In Sha Allah baza'a samu matsala da family na ba. Amincewar ka shine kawai nake buk'ata Baba." Fad'in _Khalil_ amma deep down ga san k'arya yake yi, ya san tabbas za'a sha daga da Hajiya, duk da yana da yak'inin zata amince musamman idan ta samu labarin yayiwa Sarah ciki, amma y'an uwan mahaifinsa ne yasan za'a mugu-mugun kai ruwa rana dasu. "To shikenan, Ubangiji Allah ya shige mana gaba yasa muna da tsawancin kwana." Da "Ameen" _Khalil_ ya amsa yana mai jin farin ciki a zuciyarsa. "Baka shaida min sunanka ba." Fad'in Baba. "Sunana Ibrahim Baba." Jinjina kai Baba yayi tare da fad'in, "Ma sha Allah!" _Khalil_ kallon k'afar Baba yayi tare da fad'in, "Baba ka dad'e kana ciwon k'afar nan ne?" Kallon k'afar Baba yayi tare da fad'in, "Shekaru talatin da biyu kenan ina fama da ciwon nan, tun Na'ima na da shakara d'aya a duniya" da mamaki _Khalil_ ya kalli Baba tare da fad'in, "Kuma baka je asibiti ba?" Murmushin Baba yayi tare da fad'in, "A kan ciwon k'afar nan sai da na rasa komai nawa. Da wannan gidan kawai na tsira. Ai da abun yafi muni ma. A hankali Allah ke ta kawo sauk'in." K'urawa k'afar idanu yayi kamun yace, "Allah ya baka lafiya Baba. Zan rik'a zuwa lokacin bayan lokacin. Sannan in Sha Allah zan zo na d'auke zuwa asibitina a duba k'afar sosai." Ya fad'i hakane tare da saka hannu a aljihu ya fiddo rafar kud'i y'an dubu-dubu guda biyu ya ajiye a kan yaloluwar katifar Baba. "Zo-zo-zo, d'auke kud'inka dan girman Allah. Wanda ka bawa Lami ma ya isa haka." D'ukawa _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Baba dan girman ubangijin kada ka k'i karb'an kud'in nan. Ka d'auke ni matsayin dank'a na cikinka. Nasan baza ka k'i karb'an kud'in hannun dank'a ba. Kayi min wannan alfarmar Baba." Ajiyar zuciya Baba yayi tare da fad'in, "To d'auke daya ka bar d'aya dan Allah Ibrahim." Hannu _Khalil_ ya kai ya d'auka tare da fad'in, "Nagode da karamcin ka Baba. Allah ya saka da alkhairi. Sai na sake zuwa." D'aga masa hannu Baba yayi tare da fad'in, "To d'ana nagode nima. Allah yayi albarka." Da ameen ya amsa tare da fitowa daga d'akin. Gaba d'ayansu suna tsatstsaye a tsakar gidan suna kallon k'ofar d'akin Baban, sun k'osa ya fito ya basu nasu rabon don Lami tace kwandala baza ta basu ba. Yana fitowa suka saki murmushi tare da fad'in, "K'aninmu har an fito." Babu yabo babu fallasa yace "Eh" tare da mik'a masu kud'i da Baba ya sashi ya d'auki d'aya tare da fad'in, "Ku raba!" Yana fad'in haka ya fita. Da sauri Lami ta bishi a baya, sai da ya kai k'ofa sannan ya tsaya tare da juyowa, sam baya ganin girmanta matsayinta na surukarsa. Fuska ya tsuke sosai tare da fad'in, "Lafiya?" Murmushin tayi tare da kwance zanintata sake d'aurawa sannan tace, "Dama maganar abincin Sarah ne. Dama na fad'a maka tun farko, ni ban ciyar da y'ay'ana kuma in ciyar da nasu Y'ay'an. Kaga ai yanzu Saratu tana d'auke ne da cikinka, dole ne duk wani abincin da zata ci da duk wani abu da zata nema kai zaka kawo kud'i a sayo. Ko baka duba list d'in da na baka bane?" Fuskan nan a tsuke _Khalil_ yace, "Ban duba ba, amma zuwa anjima za'a kawo komai. Sannan a kula da ita sosai. Duk abunda take buk'ata a kira ni a waya a sanar min. Kar a bari ta sha wani magani idan ba wanda na kawo ba. Idan wani waje nayi mata ciwo, immediately a kira ni a sanar min. Sannan abu na gaba, idan wani abu ya samu ciki na, ba zan kyale kowa ba. Ki turo min ita idan kin koma." Fad'in _Khalil_ tare da bud'e gidan ya fita. Don wani irin haushi da tsanar Lamin yake ji. Sam bata cancanci zama surukarsa ba. Lami kuwa tab'e baki tayi tare bud'e gidan ta kallesa tsaye jikin k'arfen gidan mak'otansu, mik'a masa wayarta tayi kirar Itel tace, "Saka min number d'inka don ban da shi." Karb'an wayar yayi tare da danna digits d'insa ya mik'a mata. Ita kuma ta amsa tare da juyawa ta koma cikin gidan. D'akin su Sarah ta shiga, zaune ta same ta a k'asa hannunta rik'e da kwalbar fantan da Aina'u ta sayo mata d'azu kamun su tafi asibiti. Da fantan ta iya shan maganin da _Khalil_ d'in ya bata. Don ruwa bai wuce mak'ogoronta. "Sai ki tashi ki fita yana jiranki a waje." Fad'in Lami tana kallon Sarah dake maida numfashi. "Waye?" Fad'in Sarah tana kallon Lami. "Ubanki ne. Idan kin fita zaki gansa." Lami ta fad'i tare da juyawa ta bar d'akin. Sarah kuwa turo baki tayi tare da mik'ewa ta saka hijab d'inta da ta cire ta fita. Yana nan inda Lami ta barsa. Tana bud'e k'ofar suka yi ido biyu dashi. Kwafa yayi tare da fad'in, "Na d'auka ai baza ki fito ba." A shagwab'e tace, "To wai ni mai zanyi maka ne? Dan Allah ka fita daga harkata." Gyara tsayuwa yayi tare da fad'in, "Zaki fara shagwab'an naki ko? Ki dai kiyayi kan ki, tom! Dama zan fad'a miki Baba ya riga ya damk'a min ke. Don haka ke tawa ce. Kuma sannan ki kular min da kanki da kuma babyn mu. Mai kike so in kawo miki a idan zan zo gobe?" Kuka ta saki tare da fad'in, "Wallahi kar ka k'ara zuwa mana gida. Ni bana son ganinka. Kuma babu abunda zai saka na aure ka. Ina haihuwa zan baka abunda na haifa maka, shikenan mun rabu!" D'age gira yayi tare da fad'in, "Za dai ki haifa min ko? In dai zaki haifa min baby d'in ai shikenan. Sai muyi deal ni dake. Idan kin amince, kamar yanda kika ce d'in, kina haihuwa zan karb'i d'an nawa shikenan kowa sai ya kama gabansa." Da sauri Sarah tace, "Eh na amince!" Waro idanu _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Tun kamun ma kiji deal d'in har kin amince. Ok, to shikenan. Na farko, duk lokacin da nazo, zaki fito, kar fa kiyi tunanin don in ganki zan zo, sam baby na nazo gani. Sannan idan na kira ki a waya, dole ki d'auka, shima ba don inji muryanki bane, lafiya babyna zan ji. Sannan duk abunda kike son ci zaki fad'a min, shima fa kar kiyi tunanin ke zan sayo mawa, a'a sam baby na na sayo mawa don nasan shi ke saka ki kwad'ayin. And dole ki rik'a shan magani tare da kiyaye duk wani abun da zai damu cikin jikin ki, sannan idan lokacin zuwa asibiti yayi, zaki je dole domin a duba min baby na. Idan kin amince da wannan sharad'in, bayan kin haihu ni da kaina zan shaidawa Baba na janye maganar auren ki, amma kuma idan baki harda ba, duk wad'annan abunda na lissafo dole ayi su, kuma a k'arshe sai na aure ki dole." Zaro idanu Sarah tayi tare da fad'in, "Kuma duka wad'annan sharad'in sai na cika?" D'aga k'afada tare da tab'e baki _Khalil_ yayi tare da fad'in, "If you wish, ki karya d'aya daga ciki. Amma ki sani, karya d'aya daga ciki yana nufin rushe deal d'in gaba d'aya. Kuma kin san dai abunda zai faru." Marairaicewa tayi tare da fad'in, "To ta yaya zaka gane idan ina son wani abu, kuma nak'i in kira in fad'a maka? Kuma misali idan ka kira wayar bana kusa fa?" Dariya ne ya kama _Khalil_, amma sai yayi murmushi kawai tare da fad'in, "Zan yi connecting CCTV camera ta inda zai r'ika hasko min duk wani motsin ki, idan ma bakya kusa na kira waya, zan sani, idan kuma da gangan ne, shima zan sani." Turo baki tayi tare da fad'in, "To amma baza a rik'a dad'ewa ba ko idan ka kira wayar?" D'aga kai sama yayi tare da fad'in, "Eh to, sai yanda babyn cikin ko yayi suggesting." Shuru tayi tana tunani, can kuma tace, "To amma kayi alk'awari idan na haihun zaka amshi babynka ka tafi baza ka sake dawowa ba?" B'ata rai yayi tare da fad'in, "Ohh wato baki ma yarda dani ba ko? Wato ga k'atoton mak'aryaci ko? To na ma fasa deal d'in. Zan yi duk abunda nace da k'arfi da yaji." Da sauri har da d'aga hannu Sarah tace, "A'a dan Allah kayi hak'uri ba haka nake nufi ba. Na amince da deal d'in." Wani mugun dariya ne ya kama shi cikin zuciyarsa. K'are mata kallo yayi ya tabbatar da yarinya ce ita. "Shekarunki nawa?" Ya tambayeta. Kanta a k'asa tace, "I'm 21years old." Sai da ya kuma kallonta daga sama har k'asa sannan yace, "I see. Yanzu to ki shiga gida. Deal d'in mu zai fara daga yau. Bye ki kular min da kanki." Sarah bata san lokacin da tace, "Bye" ba har da d'aga masa hannu. Sai bayan ta shiga cikin gida sai haushin kanta ya kamata. _Khalil_ kai tsaye gida ya nufa, cikin mota sai sak'e-sak'e yake yi na yanda zai tari Hajiya da maganar Sarah. Ya san dai akwai k'ura. Shi yafi jin nata ma akan nasu Uncles d'insa. Don idan har ta amince, to shafawa idanunsa toka zai yi. Ai ba wani zai zauna masa da matar ba. Beside shi ya lalata masu yarinya don haka shi zai d'auki abunsa. Horn yayi mai gadi ya wangale masa gate ya shigo. Sai da tayi parking mai kyau sannan ya fito daga motar. Gani Honda anyi parking d'insa daga gefen motarsa, ya saki siririn tsaki don ya shaida ko su wanene suka zo gidan. Kamar ba zai shiga ba, sai kuma ya doshi hanyar cikin gida amma ta baya ta yanda babu wanda zai fahimci ya dawo gidan. Sai dai abunda bai sani ba, tun shigowarsa Uncle Ameeru ya gansa, don shi ya fito harabar gidan domin amsa waya. Kuma yana kallonsa lokacin da yabi ta baya ya shige cikin gidan zuwa d'akinsa. A fusace Uncle Ameeru ya shiga ciki tare da Fad'in, "Bilkisu! Bilkisu!! Wallahi babu abunda za muce maki sai Allah ya isa! Yanzu tsabar yanda baki nunawa _Ibrahim_ mahimmancin mu ba matsayinmu na k'annai da yayyin mahaifinsa, shine zai dawo cikin gidan na don bai son ya ganmu sai ya zagaya ta baya ya shige ciki. Na san ma kece zaki kira sa a waya ki fad'a masa mun zo don ya doje mana. Wallahi Bilkisu ki kiyayi kanki damu. Kuma yanzu-yanzu ki tashi ki wuce ki kira mana shi dan ubansa." Hajiya da ranta yayi mugun b'aci da abunda _Khalil_ yayi, mik'ewa tayi tare da fad'in, "Kuyi hak'uri dan Allah. Bari na kira sa." Tana gama fad'in haka ta nufi wani corridor da zai sadata da matattakar da zai kai ta d'akin _Khalil_ d'in. _Khalil_ na shiga d'aki ya zauna bakin gado tare da kai hannu ya jawo side drawer ya d'auko *_MASTIKA GUM_* ya jefa a baki ya hau tauna yana mai kwanciya rigingine tare da saka hannayensa biyu ya tallabo kansa yana tunanin hanyar da zai bi yayiwa Hajiya bayanin Sarah da kuma cikin dake jikinta. Ya san Hajiya sai ta kusa kashesa da masifa. Don da ana aro baki, sai ta aro tabbas. Da ace mahaifinsa nada rai ne, to da worse kenan, don ko da ace zai amince ayi auren, to sai ya kullesa a prison ko da na sati biyu ne tukun. He's father *_Nurudden Muhammad Ibrahim_* was the chief justice of Nigeria (CJN) before he died. Yana da mahaukatan kud'i wanda kwakwalwa ba zai d'auka ba. Sam baya d'aukar raini da rashin adalci. He raised all his children very well. "I really miss you papa. I miss everything about you daddy. Allah ya jik'anka da rahama ya gafarta maka." Yana fad'in haka ya lumshe idanu siraran hawaye na zubowa daga idanunsa. Dai-dai nan jai ana danna doorbell da k'arfi. Da sauri ya tashi zaune yana kallon k'ofar. Wani abu ya danna daga gefen gadonsa, sai ga hoton Hajiya b'aro-b'aro ajikin wani screen dake saman k'ofarsa. Kai baza ka tab'a ganin screen d'in ba sai idan shi ya danna wannan madannin. Da sauri ya sauka daga kan gadon tare da isa wajen k'ofar ya bud'e. Ido hud'u suka yi da Hajiya ranta a mugun b'ace. "Ai sai ka fito tun da kai a rayuwarwa kafi so kaga raina yana ta b'aci." Tana gama fad'in haka ta juya tabi corridor d'in da ta biyo. Shima bayanta yabi don yasan dama tatsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i. Fuska babu yabo babu fallasa ya isa parlor. A zazzaune ya taras da gaba dayansu su biyar k'annai da yayyin mahaifinsa. Zama yayi a kan carpet tare da fad'in, "Barkan ku da zuwa Uncles." Uncle Ameeru ya kallesa tare da fad'in, "Kalle ni, ungo nan!" Ya fad'i haka tare da yi masa dak'uwa............




*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*



*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*PAGE 12*


Sai da ya isa k'ofar gidan sannan ya d'auko wayarsa dake gefensa ya lalubo number Sarah da yayi saving da *_My endless bliss_* yayi dialing, ringing uku ya amsa kiran tare da fad'in, "Hello, Assalamu alaikum." Tab'e baki yayi kamar tana kallonsa tare da amsawa da, "Hi, wa'alaikissalam." Da sauri Sarah ta cire wayar daga kunne tana k'arewa special number d'insa kallo wanda ya k'are da 3 guda shidda a k'arshe. Turo baki tayi don sarai ta gane muryansa, gashi kuma tana tsoran yanke kiran don bata manta da deal d'in su na d'azu ba. "Wake magana!" "Bugun zuciyarki!" Kai tsaye ya bata amsa yana mai sakin murmushi. Sarah kuwa yana fad'in hakan zuciyar nata ta soma bugawa. Shuru tayi bata k'ara cewa komai ba. Sun d'au lokaci har na tsawon mintuna biyar babu wanda ya sake yin magana. _Khalil_ ya ciro wayar daga kunne, kamar yanda itama Sarah ta fiddo nata domin ganin is he still their. Sai taga yana reading kamar yanda shima ya gani daga can, mayar da wayar yayi kan kunnansa tare da fad'in, "Tun ba'a je ko ina ba, har kin fara karya dokar ko?" K'ara turo baki Sarah tayi daga can tare da fad'in, "To ni ai kai ne baka yi magana ba, kuma ni ban san mai zan ce ba." Gyara zama yayi cikin motar tare da fad'in, "Ki fito ina waje." Waro idanu Sarah tayi tare da fad'in, "Waje kuma? Ni dai......." Sai kuma tayi shuru bata k'arisa ba. "K'arisa maganarki mana, ke dai baza ki fito ba ko?" Kwanciya tayi rigingine tare da fad'in, "Ni dai Allahna yana sama yana kallo ba haka nayi niyyar cewa ba." D'age gira yayi kamar tana kallonsa tare da fad'in, "Au Allah d'in naki ne ke d'aya mai son kai. To idan ba tsoro ba ki fad'i abunda kika yi niyyar fad'i daga farko mana." Sai da ta juya idanuta sannan tace, "Ni dai so nake in ce maka, ni dai gaskiya.... Gaskiya, ummm-ummm...." Dariya ya saki tare da fad'in, "Kin ga k'aryar ma ta kasa fitowa. To bari na juya kawai kin ga kenan deal d'in mu ya rushe." Waro idanu Sarah tayi tare da mik'ewa da sauri tana fad'in, "Wallahi a'a, wallahi ni dai a'a ba haka nake nufi ba. Gani nan zuwa yanzu." Sosai ya saki dariyarsa tare da fad'in, "Matsoraciya, ana so ana kaiwa kasuwa." "To mai ake so d'in." Ta tambaya tana hararar wayar. " _Khalilullah_ mana." "Khalilo." Ta fad'i cikin zuciya har da Allah ya kiyaye. Bata san ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????cewar a zahiri tayi maganar ba sai da taji yace, "Ni ne _Khalilo_ d'in?" "Na shiga uku na!" Ta fad'i jin ashe a bayyane tayi maganar. "Ki fito maman twins kar ki b'ata min lokacina." "Mene? Ni wallahi ba maman Twins bane. D'aya kawai zan haifa maka. Shima don babu yarda zanyi ne. Ai don dai zubar da ciki haramun ne, kuma tamkar kisan kai mutun yayi, da zubarwa zanyi wallahi." Fad'in Sarah. "Don Allah ki gwada! Da na baki tsan-tsan mamaki don kin san Allah sai na kuma yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login