Showing 54001 words to 57000 words out of 129558 words

Chapter 19 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

tsaya fuska babu rahama ko kad'an har k'arshe layin. Su Hajiya Lami kuwa cewa tayi, "Yanzu haka saboda d'aurin auren da za ayi gobe ne aka turo so domin su bamu tsaro." Na'ima tace, "Babu shakka kam!" Baba dake d'aki kuwa hakanan yaji hankalinsa bai kwanta ba. Aina'u kuwa gaba d'aya ta kasa sukuni sai lek'e take yi tana kiraye-kirayen waya. Muneeba kuwa sai kuka take yi a gaban _Khalil_ tana mashi rantsuwar ba da ita aka had'a baki ba kuma wallahi bata san inda Sarah take ba, bata san ko wa ya sace ta ba. Shikuwa _Khalil_ kwakkwarar motsi ya hanata don cewa yayi bai yarda da ita ba. K'aran jiniyar motocin sojoji da y'an sandan da suka iso inda suke ne ya k'ara hargitsa mata tunani ta saki wani marayan kuka tana k'an'k'ame jikinta. "Ke!" Wani soja ya buga mata uban tsawa sai gata a zube a k'asa ta sume dai-dai lokacin da ya Abdul-Hakeem ya iso wajen. Shi da kansa ya zira hannu ta cikin motar _Khalil_ ya d'auko ruwa tare da yayyafawa Muneeba. A firgice ta farfad'o tana fad'in, "Wallahi bani bace, ban sa wanda ya sace ta ba, kuma wallahi bani na kirata a waya ba." Hannu ya Abdul-Hakeem ya saka a baki tare da fad'in, "Shssh! Kwantar da hankalinki babu abunda za ayi maki a nan wajen. Yi min bayani mai ya faru." Ajiyar zuciya Muneeba ta sauke tare da fad'in, "Sarah tu a gidan mu take kwana tun saura kwana biyar bakinta. Kuma mama ta hana mu fita kuma ta cewa _Khalil_ ya hak'ura da zuwa tad'i har sai an kawo masa ita gida sabida ana mata gyaran jiki. To kullum sai suyi ta damuna su biyu suna cewa suna kewar juna. Shine jiya muka yi waya da shi _Khalil_ akan in taimaka masa in fito masa da Sarah suga juna ko mintuna biyar ne, shine na fito da ita ba tare da sanin mama ba na kawo ta wajensa sai na koma gida domin basu waje suyi magana. To K'anwar Sarah tazo gidan mu tana neman ita Sarah har mama taji shine ta tambaye ni ina Sarah, sai nayi mata karyar tana ban d'aki shine nayi sauri na fito domin in kira ta mu koma gida. To da nazo nan d'in sai naga babu motar _Khalil_ sai nayi ta kiran number d'in Sarah amma ba'a d'agawa, daga k'arshe ma aka kashe. Shine na kira shi _Khalil_ d'in ina tambayarsa Saratu, sai ya fara min ihu wai ai nice na kira ta har ta tsora tace wata k'ila an gane bata gidan ne sai suka yi sallama ta tafi. Kuma ni wallahi, tallahi ban kira ta ba." Haushi ne ya kama _Khalil_ jin rantsuwar da tayi akan bata kira Sarah ba, bai san lokacin da ya d'aga hannu zai wanke fuskanta da mari ba, da sauri Abdul-Hakeem ya tare hannunsa tare da fad'in, "Baka da hankali ne? Ko in barka kayi binciken ne da kanka? Ashe babu amfanin kiran mu da kayi kenan?" Matsawa baya _Khalil_ yayi tare da fad'in "I'm sorry." Kallon Muneeba yaya Abdul-Hakeem d'in yayi tare da fad'in, "Ina wayarki?" Da sauri ta mik'a masa wayar hannunta na rawa shi kuma ya mik'a wani dake gefensa. Cike da ladabi ya amshi wayar sannan ya sara masa tare da koma cikin mota ya kunna computer ya soma danne-danne cikin sauri da kwarewa. Muneeba kuwa da mararta ke cike da fitsari, ihu d'aya za'a kuma buga mata ta saki fitsari. Mintuna biyar sai ga wannan da aka ba waya ya dawo tare da fad'in, "An kira number d'in sau bakwai mintuna goma sha bakwai baya amma ba'a d'aga ba kuma daga baya aka kashe wayar. Lokacin da ake kiran wayar ba'a d'aga ba, nabi diddigin layin, makwamusan suna dai-dai round about d'in stadium, kuma an kashe wayar ne a dai-dai wajen tare da jefar da waya. Don har yanzu diddigin layin na wajen. Sannan kuma an kira wayar k'arfe bakwai da mintuna arba'in da uku, sai dai har ya gama ringing ba'a d'auka ba." Da sauri _Khalil_ yace "Lokacin muna tare, kuma a wannan ne Sarah hankalinta ya tashi ta wuce gida." Abdul-Hakeem ya kalli Muneeba tare da fad'in, "Kin ce baki kira Sarah ba, kuma gashi bincike ya nuna kin kira da misalin 7:43." Kuka Munee ta saka tare da soma rantsuwa tana fad'in, "Na rantse da ubangijin da ya halicceni ban kira taba, bani na kira ta ba." "To idan baki kira taba, waye ya kira ta? Kin ba wata wayar ne a wannan lokacin?" Shuru Muneeba tayi tana tunanin wa ta ba wayar a wannan lokacin? Kallon Abdul-Hakeem tayi tare da girgiza kai tace, "Ban ba kowa wayata ba a wannan lokacin. Kuma wallahi ban kira ba." "Oga wannan yarinyar fa baza tayi magana ba har sai mun tafi da ita." Fad'in wani police. Tuni Muneeba ta soma sakin fitsarin da ya dad'e da cika mata mara tare da durk'usawa a k'asa tace, "Na rantse da girman Ubangiji da ya halicceni ban sace Saratu ba. Wallahi bani bace. Dan Allah kar ku tafi dani." Yaya Abdul-Hakeem tun kallon farko da yayi wa Muneeba ya san cewar bata da hannu a cikin sace Sarah da aka yi, sai dai tabbas duk wanda yayi hakan yana tare da ita amma ita bata san hakan ba. "Wa kika ce tazo neman Sarah har mamanki taso ta fahimci bata gidan?" Da sauri Muneeba tace, "Aina'u!" Wani harara _Khalil_ ya watsawa Muneeba tare da fad'in, "Aina'un ce za ta sace Sarah?" Girgiza kai Muneeba tayi tare da fad'in, "Ba haka nake nufi ba." yaya Abdul-Hakeem kuwa cewa yayi "Aina'u tayi amfani da wayarki ne lokacin da tazo?" Da sauri Muneeba ta girgiza kai tare da fad'in, "Bata yi ba. Cewa kawai tayi ina Sarah. Ni kuma nayi saurin janta gefe nace tayi shuru kar mama taji don ta hana mu fita ni kuma na saci hanya na kai Sarah wajen _Khalil_. Ita kuma sai ta mik'o min kayan Sarah tace in bata baza ta iya jiran Sara ta dawo ba, don itama jiranta ake yi saurayinta yazo." "Wani irin kaya ta kawo mata, kuma dama Sarah ce tace ta kawo mata kayan?" Fad'in ya Abdul-Hakeem. "Eh ita ce tace ta kawo mata doguwar rigar baccinta da kuma hula." Jinjina kai Ya Abdul-Hakeem tare da fad'in "Jeki gida, zan neme ki idan buk'atar hakan ta taso." Da sauri Muneeba ta juya har da had'awa da gudu ta bar wajen. Shi kuma _Khalil_ a fusace ya kalli ya Abdul-Hakeem tare da fad'in, "Ya ka barta ta tafi? Ita ce suspect d'in fa." Ko kallonsa ya Abdul-Hakeem bai yi ba, sai daga ma d'aga kiran da aka yi masa yayi tare da sakawa a kunne. "Ok kar ku tab'a komai gamu nan zuwa." Yana gama fad'in haka ya yanke wayar tare da kallon _Khalil_ yace, "Shiga mota ka biyo bayan mu." Shi kuma ya nufi motar da ya shigo bayan ya bawa sauran y'an sandan umarni akan kar ku yarda su bar wajen har zuwa gobe shi kuma ya shiga motar da ta kawo sa suka nufi Barnawa inda wanda ya kira yanzu ya fad'a masa. Kasancewar gudu suke yi kuma ga shi dare ne babu mototi akan titi sosai, cikin k'ank'anin lokaci suka isa. Wasu cincirundo y'an sanda ne a zagaye da wata mota k'irar golf, sai wasu matasa su shidda an fito dasu sun yi kneeling a k'asa fuskokinsu a kumbure. Abdul-Hakeem na isowa wajen ya fiddo pistol tare da kicking ya d'aura akan goshin d'aya daga cikin su, zawo ne ya soma zubowa daga jikinsa na tsoro tare da fad'in, "Kar ka kashe ni dan Allah. Wallahi ba muyi mata komai ba. Tana cikin buhu a bayan mota." Da jin haka haka ya Abdul-Hakeem nufi bayan motar bayan ya saka hand gloves sannan ya bud'e tare da warware saman buhun. Da mugun gudu _Khalil_ ya iso wajen zai kai hannu ya d'auko Sarah da bata da maraba da gawa amma ya Abdul-Hakeem ya tare sa tare da fad'in, "Wait a minute!" _Khalil_ bai saurari ya Abdul-Hakeem ba ya ciccib'o buhun ya fito dashi tare da fiddo Sarah da gaba d'aya jikinta a sake yake ya nufi motarsa da ita ya bud'e back seat da d'ayan hannunsa ya shimfid'ar da ita tare da soma ceto ranta don ya duba pulse d'inta yaga akwai rai a jikinta. Tsabar wahala kawai tasha da kuma abunda suka shak'a mata. Numfashi ya soma bata ta bakinsa yana hura mata. Sai da ta d'au tsayin lokaci kamun ta ja wani irin dogon numfashi tare da rirrik'e damatsen _Khalil_ d'in da k'arfi. Wani irin ajiyar zuciya ya saki tare da d'agota ya had'a da jikinsa ya rungume k'am-k'am. Yana jin yanda bugun zuciyarta ke tafiya da k'arfi. A can waje kuwa, wani irin mahaukacin duka sojoji hud'u suka rufe su dashi. Sai da suka karya k'afafun su da hannaye sannan suka jefa su cikin mota. Yaya Abdul-Hakeem kuma k'arisowa yayi ya kwankwasa motar _Khalil_ sai a sannan ya saki Sarah dake kuka a hankali ya fito daga motar. "Ka mayar da yarinyar gidan iyayenta. Sojoji da y'an sanda zasu cigaba da bata tsaro har sai an d'aura aure gobe an kawo ta gida tukun zasu bar layin." _Khalil_ yace, "To yaya. Amma ya akai aka gano su?" Murmushi ya Abdul-Hakeem yayi tare da fad'in, "Tun da muka gama waya da kai na kira wani daga wajen aikinmu, kwararren masanin na'ura na tura masa number d'inka. Na number d'inka yabi diddigin layin Sarah. Ko da nake wa yarinyar nan tambayoyi, wasu na can tuntuni sun bi bayansu har Allah yasa suka damk'o su. Sai dai kuma koma wanene wanda ya saka aka sace Sarah, ba k'aramin wayau gare shi ba, don bai yarda ya bar wani makama ba, ko su wanda muka kwamushe yanzu, basu san ko wanene ya basu aikin ba. Kuma da boyayyiyar number ake basu umarni. Kuma sun ce muryan namiji ne ke basu umarnin." Da mamaki _Khalil_ yace, "To wanene wannan yake son ganin baya na ta hanyar raba ni da Sarah?" Kai tsaye ya Abdul-Hakeem yace "Makiyi!" "Allah ya shiga tsakanin mu da koma wanene. Kuma in Sha Allah aure babu fashi. Gobe za'a d'aura aure." Fad'in _Khalil_. "In Sha Allah. Ma mai masu yarinya gida dare nayi." "To yaya sai na dawo gidan. Don Allah kar ka fad'awa Hajiya ka santa nan da nan hankalinta ke tashi" Sai da ya hararesa sannan yace, "To yaya _Khalil_, ai ka san dama bani da hankali." Dariya _Khalil_ yayi tare da bud'e gidan baya inda Sarah take ciki ya shiga. "Stop crying my baby. Gani a kusa dake. Bazan k'ara bari haka ya faru dake ba. I'll always protect you my wife. Kiyi hak'uri laifina ne. Da ban zo ba, hakan ba zai faru ba." Share hawaye Saratu tayi tare da fad'in, "Ko kazo, ko baka zo ba, haka sai ya faru tunda rubutaccen al'amari ne." Hannu ya kai ya share mata hawayen da suka gangaro tare da fad'in, "Gobe, by this hours, kina kwance a k'irjina, ba zan bari ko sauro ya hau kan jikinki ba bare kuma d'an Adam." Hannu sara ta saka ta rufe fuskanta tare da fad'in, "Ni dai ka bari. Mu tafi gida dare nayi." Dariya yayi tare da fita daga motar ya koma mazaunin drive ya kunna tare da barin wajen ya hau hanya. Sarah ganin basu yi hanyar gidansu Muneeba ba, sai tace, "Gidan su Muneeba zaka kai ni fa." Sai da ya juyo sannan yace, "Babu gidan wata Muneeba da zaki k'ara kwana. Gida zan kai ki. Ni ban yarda da Muneeba d'in nan ba. Ina zargin har da saka hannunta a sace kin da aka yi. Don tana ta rantsuwa wai ita bata kira ki ba lokacin da muna tare dake." Waro idanu Sarah tayi tare da fad'in, "Dan Allah kar kace haka. Wallahi Muneeba baza ta tab'a cutar dani ba. Babu hannunta wallahi." Kallon titi yayi tare da fad'in, "love, mugu bashi da kama. Ki bar wannan maganar. Gida zaki kwana." Kuka Sarah ta saka tana fad'in, "Wallahi Muneeba ba muguwa bace." Banza yayi da ita har yayi parking a k'ofar gidansu. Uban dandazon sojojin da ya ta gani a k'ofar gidansu sai da ta tsorata. Ganin da sauri sojoji kusan hud'u sun nufo su tare da bud'e gidan baya ina take, baya san lokacin da ta kwala ihu ba sai da _Khalil_ ya tsorata tare da fitowa da sauri ya ture wani soja yana fad'in, "Baby lafiya?" Da hannu tayi masa nuni da, sojan dake tsaye k'ik'am kamar an dasa shi. "Malam matsa mana. Baka ganin tsoranka take ji." Da sauri sojan ya matsa, shi kuma ga kamo hannunta ya fito da ita. Har tsakar gidansu ya raka ta dai-dai lokacin da Baba ya fito daga d'aki yana fad'in, "Wanene nan wajen?" Amma ganin _Khalil_ da Sarah tsaye sai hakan ya bashi mamaki don ga san Sarah a gidan Liman Muhammadu take kwana. "Ibrahim lafiya? Wani abun ya faru ne? Shiyasa naji jiniyan sojoji ko ta ina kenan d'azu?" Baba ya jero tambayoyi gabansa na fad'uwa. Jin muryan baba sai gaba d'aya mutanan gidan suka fito. Aina'u kuwa har da cin tuntub'e tana waro idanu ganin Sarah a tsaye. "Baba wani tsautsayine ya d'an afku, amma Alhamdulillah yanzu." Daga nan ya kwashe komai ya sanar da baban. Salati Baba da su Na'ima suka d'auka. Lami kuwa wani uwar yare mai tsawo ta dire tare da fad'in, "Yesu almasihu kana ganin komai. Mak'iya sun fara bina don sun ga y'ata zata auri babban mutun d'an gidan manyan mutane." _Khalil_ kuwa kunnansa ne suka yi masa wani duum jin Lami tace _Yesu almasihu_. Bai gama dawowa daga duniyar mamaki ba, Lami ta kuma cewa, "Ya Uba mai-iko duka, mai-yawan jinkai, mun rantse, mun bache daga tafarkokinka kaman batattun tumaki. Mun cika bin dabarun zukatanmu da muradinsu. Mun sab'a dokokinka masu-tsarki. Abin da ya wajabba garemu, mun bari: Abin da ya wajaba mu bari, shi muke yi; Babu lafiya garemu. Amma, Ya Ubangiji, ka yi mana jinkai, mu masu-sab'o abin tausai. Ya Allah ka yafi masu fad'in laifinsu, Masu tuba kwa ka amshe su: bissa alkawalin da ka furta ma yan Adam. Almasihu Isa Ubangijinmu, Uba kuma mai-yawan jinkai, ka sa duk mai neman mu da sharri ya koma masa, kada kayi duba da laifinmu a gare ka. Ya Almasihu mai-tsarki ka amsa addu'armu Amin." Ba _Khalil_ kad'ai hatta su Nuratu sun firgita da jin maganganun mahaifiyarsu. Marfu'a kuwa kallon Lami tayi tare da fad'in, "Lami dama ki koma addinin kiristancinki? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Gaskiya Lami baki kyauta ba. Shikenan baki da rabo a lahira." Aina'u tayi caraf tace, "Tunda kece da aljannar sai ki hanata ai. Ai gwara ita an san cewa kirista ce, ke kuma fa? Kina amsa sunan musulma amma ban tab'a ganin kin aje goshinki a k'asa ba. To Menene marabarku kenan? Kowa dai yasan bambamcin musulmi da kirista shine Sallah." A fusace Marfu'a tace, "Dan uwarki dake nake magana? Alhamdulillah tunda da na furta kalma La'ilaha illallah Muhammadur Rasulillah. Kuma dai ai ance duk wanda ya furta Kalmar bai dauwama a wuta." _Khalil_ gaba d'aya ji yayi kamar ana zare nasa wani abu a jiki, yayi dana sanin shigowa cikin gidan. Sai yaji dama a k'ofar gida ya tsaya har Sarah ta shige ciki. "Ke, ba kowa bane yake da rabon shiga addinin kiristancin. Addini na shine addinin gaskiya. Kuma ni tun farko ban tab'a yin wani addini bayan addinina ba. Addinin ku ya cika tsauri da yawa, mutum yayi da dungure sau biyar a rana, wata d'aya ana azumi, ba'a sata, ba'a k'arya ba'a saduwa, ba'a shan burkutu. Abubuwa da yawa addininku sun hana. Addininku addinin takura ne." Sai a lokacin Baba ya bud'e baki tare da fad'in, "Ke Lami! Ki kiyaye harshenki. Addinin Musulmi addinine na gaskiya kuma addini ne mai bawa kowa y'anci. Duk abunda kika lissafo addinin da kike ik'irararin shi kike yi, shima yayi hani akai. Babu wani Bible d'in da ya halasta duk abunda kika lissafo. Idan kinga dama ki zama mara addini gaba d'aya, wannan ruwanki ne. A gaban sirikinki kike wad'annan maganganun sabida baki da hankali da tunani." Da sauri _Khalil_ yace "Baba sai da safe, sai da safe Sarah." Yana fad'in haka ya juya. Aina'u kuwa wani farin ciki taji ya ziyarci zuciyarta ganin reaction d'in _Khalil_. Tana ji a jikinta auren Sarah dashi ba zai yuwu ba gobe. Baba juyawa yayi tare da shiga d'aki Sarah ta bishi a baya. Su Nuratu ma suka shige d'aki. Aina'u kuwa, hanyar toilet ta nufa. Tana shiga ta rufo k'ofar tare da kiran wata number bayan ta shiga magic voice ta mayar dashi na tsofaffi sannan ta b'oye number. Ringing uku aka d'aga wayar tare da fad'in, "Zance ya b'aci, su Arowa suna state CID yanzu haka. Sai dai sunana bai fito ba, don kamar yanda ake b'oye number ana canza muryoyi ana kirana, nima haka nake musu. Ni dai koma wanene nake magana dashi yanzu haka, bamu da matsala domin babu wanda ya san mu." Aina'u wani murmushin jin dad'i tayi duk da tasan ko ta fashe babu wanda zai kamata don bata bada k'ofar da za'a ganeta ba. "Yayi kyau! Zan kira ka idan wani aikin ya kuma b'ullowa." Tana gama fad'in haka ta yanke kiran ta fito daga bayin ta koma d'aki." "Baba wallahi ban san ko su wanene suka min haka ba. Amma ga dukkan alamu anso ayi garkuwa dani domin kud'i. Tunda kaga da zan ba'a yi hakan ba sai da aure na ya kusa kuma da d'an Chief Justice Nurudden Muhammad." Ajiyar zuciya Baba yayi tare da fad'in, "Ubangiji Allah ya kare ki daga sharrin mutum da aljan. Wannan aure kuma, idan ma anyi hakan ne domin a fasa,in sha Allah an riga an d'aura a sama, shaidar duniya kawai ake jira. Tashi kije ki kwanta, in Sha Allah da safe zan je can gidan liman Muhammadu inyi masa bayani komai. Ni kai na ban ji a jikina Muneeba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login