Showing 9001 words to 12000 words out of 129558 words

Chapter 4 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

na iso wajen nan ku rabu da mutanan nan. Ku wasu irin yara ne kamar dabbobi. Kai ko dabba baza tayi abunda kuke yi ba. Babu wawuya mara hankali a cikin su kamar ke Lami. Wallahi kuka yi kisa a cikin gidan nan, nine nan zan bada shaida duk a tafi a rataye ku." D'agowa Lami tayi tana haki tare da fad'in, "To sai me idan mun kashe sun? Ai dama ni na jima da sanin ba k'aunar mu kake ba ni da y'ay'ana. Kana d'aka kana jin duk maganganun da matan nan suke fad'a min, amma baka iya fitowa ba, sai da kaji muna d'aukar mataki tukun zaka fito kana wani maganar banza da wofi, yara, ku cigaba da d'umamun su!" Ko rufe baki bata yi ba, su Nuratu suka cigaba da dukansu aunty Halima. Tsabar azaba aunty Luba kuka take yi tana basu hak'ura amma basu saurara ba. Baba kuwa dogaro sandar shi yayi tare da isowa inda suke ya d'aga sandar ya makawa Lami, sannan ya kuma d'agawa ya bugawa Nuratu da Aina'u, ya d'aga zai bugawa Na'ima, tayi caraf ta rike sandar tare da tura shi baya sai da ya kai k'asa k'afarsa ta markwad'e, Aina'u kuwa d'aga k'afa tayi dagangan ta take yatsun k'afarsa har da murzawa. Wani irin salati Baba ya saki tare da fashewa da kuka yana mai kai hannu kan k'afarsa da Aina'un ta mitstsike. Nuratu kuwa hannu ta saka ta dungure masa kai tare da fad'in, "Wallahi kar ka kuma ka kai hannunka jikina." Da mugun gudu Sarah ta iso wajen ta d'auke Aina'u da gigitaccen mari, sannan ta kuma d'aga hannu ta zabgawa Nuratu da Na'ima mari, sannan ta kuma d'auke Aina'u da mari don a idanunta ta mitstsike k'afar mahaifinsun. "Dan uwarki ni kika mara?" Fad'in Na'ima tana mai nuna kanta, Nuratu kuwa muciyar dake k'asa ta d'auka ta bari Sarah dashi a fuska, nan da nan fuskan ya tashi, bakinta kuma ya kumbura ya soma fidda jini don har ta wajen bakinta dukan ya samu. "Allah ya isa shegiya y'ar iska! Kuma wallahi nima sai na rama!" Fad'in Aina'u tare da yin hanyar pamfo da gudu ta d'auko bokitin da aka cika ruwa aka ajiye tayo kan Sarah wacce ke tsugunne dafe da kuncinta da Nuratu ta buga mata muciya. Sai ji tayi shaaaaa an antayo mata ruwan sanyi tun daga tsakar kanta har cikin pant d'inta. Saurin kallon gefenta tayi inda Baba yake saboda jin wani ajiyar zuciya da ya sauke, sai tayi arba dashi a jik'e shataf, don ba ita kad'ai Aina'un ta jik'a ba har da baban. Baba kuwa kallon Aina'u da Na'ima yayi yana fad'in, "Ni! Ni ko? Ina mahaifinku zaku saka hannu ku ture ni har sai da ba kai k'asa ko? Aina'u ni kika kwarawa ruwan sanyi a jiki har mitstsike min k'afa ko!" Sai kuma ya kalli Nuratu ya ce, "Nuratu ni kike saka hannu kina dungurewa kai kamar d'anki ko?" Ya fad'i hakan yana nuna kansa wasu zafafan hawaye na biyo kuncinsa. "Kuje! Duniya zata koya maku hankali." Ya fad'i yana mai fashewa da kuka tare da k'ok'arin mik'ewa. Sarah kuka take yi sosai ganin yanda jikin mahaifinsu ke wani irin rawa kuma yana kuka sosai. "Lami dan ubanki kizo ki bani abinci yunwa nake ji!" Fad'in Safwan d'an Na'ima. Saurin kallon Lami Na'imar tayi tare da fad'in, "Yanzu Lami dama yaran nan basu karya ba? Haba Lami! Haba!! Wannan wani irin wulak'anci ne. Nafa bar komai na abincin yaran nan." Marairaicewa Lami tayi tare da fad'in, "Yi hak'ura Na'ima, dama fitowa ta kenan domin in d'aura masu abincin sai ga wad'annan fitinannun mutanan sun shigo." Kallon su Na'imar tayi tare da fad'in, "Zaku fita ku bar gidan nan ne ko kuwa sai kun sake ji a jikinku?" Babu wanda yayi magana cikinsu sai ma kama junansu da suka yi suka nufi k'ofar gida. "Sake ni Saratu kije ki bud'e masu kwar gidan ki basu hak'uri ki dawo." Fad'in Baba yana mai share hawayen da suka kasa tsayuwa a idanunsa. Sarah bata sake shi ba sai da ta kai shi wajen barandarsa sannan ta nufi k'ofar gida da gudu, nan tayi arba dasu suna ta kiciniyar bud'e gidan. Hannu Sarah ta kai bayan sun bata hanya ta bud'e masu gidan tare da saurin kai guiwowinta k'asa ta shiga fad'in, "Aunty dan girman Allah kuyi hak'uri da abunda y'an uwana suka yi maku. Ku......" Katseta aunty Bilkisu tayi tare da fad'in, "Matsa mana a hanya mu wuce tun kamun nayi ball dake a nan wajen." Aunty Luba kuwa saurin cewa tayi, "Mai ya kawo maganar Ball kuma! Ke jeki gida mun ji mun yi hak'uri. Bamu hanya mu wuce tun kamun shan ruwan mu a duniya ya k'are. Wannan da muka sha ma, ya ishe mu ishara!" Ta fad'i hakan tana mai bud'e gidan. Karaf gaba d'ayan su suka yi ido hud'u da Farouq dake k'ofar gidan. Da sauri Sarah ta mik'e tana kallonsa, kallon irin na bankwana. Najma kuwa tana arba dashi ta fashe da kuka tare da soma labarta masa abunda ya faru. Wani irin yunk'uri Farouq yayi zai fad'a cikin gidan ganin yanda jini ya b'ata gaba d'aya gaban rigar aunties d'insa da k'annan nasa. Saurin rik'osa aunty Luba tayi tare da fad'in, "Bada yawuna ba wallahi ka shiga cikin gidan na, yaran da har mahaifinsu duka suke yi, to uban waye baza su daka ba a cikin fad'in duniyar nan. Farouq dama inda kake nai man aure kenan? Wallahi, tallahi ko da ace yarinyar nan ba ciki bane a jikinta, kai da ita sai dai a lahira idan da rabon auren a can. Sam wannan gidan ba gidan had'a zuri'a dasu bane." Sarah kuwa da sauri ta fito daga cikin gidan ta zube a gaban Farouq, ko kamun ta bud'e baki ya d'aga hannu ya wanke fuskanta da gigitaccen mari tare da nuna ta da hannu yace............



_08128755583 WhatsApp only dan Allah. Ban
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: _K'ANWAR MATATA_*>؜?

_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_




&? *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*&?

Page 5

A gigice Sarah ta d'ago tare da dafe kuncinta tace, "Farouuuuq." sai da ta ja sunan cike da tausayi tana kallon fuskansa hawaye na shatata a idanunta. Bakin Farouq har rawa yake yi wajen fad'in, "Kar ki kuskura ki k'ara kiran sunana anan wajen idan ba haka ba karya ki zan yi billahil lazi. Wawuya shashasha mai fuska biyu. Ashe watsatsatsiya ce ke kamar sauran y'an uwanki. Kin cucuni Saratu da har kika saka ni na d'auki dakon sonki a cikin zuciyata har tsawon shekara. Allah ya isa tsakani na dake. Kuma ki sani, ko da ace daga ni sai ke muka rage a duniya, har sai dai na mutu babu aure. Banza budur-bazar." Kuka Sarah ta fashe dashi jin zafafan kalaman da Farouq ke fad'a mata. So take yi ta bud'e baki tace wani abu, amma rawar da bakinta yake yi ya hana ta iya furta ko kalma d'aya. Ji tayi an watso mata papers a fuska. Bin papers d'in tayi da idanu, sai kuma ta kai hannu ta dake rawa ta dauki paper d'in ta bud'e. Waro idanuwa tayi ganin papers d'in scanning d'inta ne har guda uku wanda tayi jiya. Bata iya cewa komai ba don ta san babu abunda zata fad'i wanda zai saka Farouq ya yarda da ita. Tsirtar da miyau Farouq yayi tare da kama hannu aunty Luba yace, "Aunty mu wuce anan kada amai ya kama ni dan Allah. Don ganin fuskan yarinyar nan kawai yana saka ni tashin zuciya." Rintss idanu Sarah tayi tana jin bugun zuciyarta na k'aruwa tamkar yanda jirgin k'asa ke malala gudu akan titinsa. Bata iya tashi a wajen ba sai da ta kwashi mintuna kamun ta mik'e, shima sabida mutanan da suke wucewa suna zund'enta ne ya saka tayi k'arfin halin tashi ta tura k'ofar gida ta shiga. Kai tsaye d'akin mahaifinsu ta wuce duk da maganar da Lami take mata a tsakar gida tana yiwa yaran Na'ima wanka, amma bata kula ta ba. Tana shiga dakin ta zube a k'asa sai da guiwowinta suka bugu da k'asa, amma bata damu da zafin da taji ba. Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe dashi tare da fad'in, "Wallahi, tallahi, billahil azim Baba ban tab'a sanin wani d'a namiji a rayuwata ba. Baba namiji da na tab'a bawa kaina. Ban san ta yanda akayi ciki ya shiga jikina ba. Na shiga uku na lalace Baba. Shikenan nima ba zanyi aure ba?" Sunkuyar da kai Baba yayi yana mai zubar da hawayen tausayin Sarah. Dakyar ya iya d'ago kai ya kalleta tare da fad'in, "Saratu da badin manzon Allah SAW yayi hani da d'auke mace a burni a kaita k'auye ba, da nace ki tattara kayanki ki koma _Wamba_ kiyi auren ki acan. Amma kuma Saratu babu ta yanda za ayi ki samu ciki ba tare da d'a namiji ba. Kin tabbata baki tab'a zuwa wani waje ba an baki abun sha kin sha ba? Watak'ila ta nan aka yaudare ki." Girgiza kai Sarah tayi tare da fad'in, "Baba ban tab'a zuwa party ba. Ko k'awaye bani da balle su gayyace ni." Shuru Baba yayi na kayan tsawon mintuna biyar sannan ya nisa tare da d'agowa ya kalleta yace, "Jeki d'akin ki Saratu. Allah shi yasan abunda ke b'oye. Duk wanda yake k'ok'arin cutar dake, in Sha Allah, Allah ba zai bashi dama ba. Kina gani da idanunki Saratu, kina ganin irin wulak'ancin da mahaifiyarku da sauran y'an uwan ki suke min a cikin gidan nan. Kina tunanin ko ban bud'e baki nayi masu baki ba, Allah ba zai tsine masu ba. Ni dai Sam ban yi sa'ar mace ba. Haka zan koma ga Allah da bak'in cikin Lami da y'ay'anta. Sai da y'an uwana suka yi min gargad'i, amma kuma nayi kunnar uwar shegu dasu. Gashi yanzu ina girbe abunda na shuka." Baba ya k'arisa yana mai fashewa da kuka. Itama Saratu kukan ta fashe dashi tare da fad'in, "Kayi hak'uri Baba. Dan Allah ka cigaba da hak'uri dasu kamar yanda ka saba." Bai d'ago ba ya ce, "Saratu y'ay'an ciki na suke duka na! Wallahi tallahi har mahaifina ya koma ga ubangiji, bai tab'a fad'i na fad'a ba balle har in d'aga in kallesa inyi masa k'unk'unai. Wannan jarabta ce kawai daga Allah!" Shuru Saratu tayi tana mai jin k'una sosai a cikin ranta. "Na'ima y'ay'anta uku babu aure, dan ma Allah yayi wa d'ayan cikawa da yanzu y'ay'anta hud'u duk babu uba. Nuratu biyu, Marfu'a nada d'aya, Hassana kuma tayi y'an biyu, ko wata uku ba'ayi ba da d'aya daga cikin y'an biyun ya koma. Wannan bak'in cikin kawai ya isa ya kashe ni Saratu. Gashi itama autar taku Aina'u tana so ta fad'a cikin halakar da y'an uwanta suke ciki. Yanda idanunta suke a tsatstsaye, wallahi ni sai nake ganin ma kamar sai tace duk abunda y'an uwanta suke yi basu yi komai ba akan wanda zata yi ita." "A'a baba, addu'a zaka yi mata. In Sha Allah hakan ma ba zai faru ba. In Sha Allah Aina'u baza tayi halin su Na'ima ba." Girgiza kai Baba yayi tare da fad'in, "Uhm! To Allah yasa. Amma da kamar wuya. Hatta shi kansa namijin da Allah ya bani tilo, sakarai ne. Tunda shima shaye-shaye babu wanda bai yi da kuma d'aukar kayan mutane. Jiya da daddare, ina jin lokacin da wannan yaron wa yake da suna?" " *_Naliliyo_*" Fad'in Sarah. "Yauwa eh shi! Ina jinsa yana karta adda a k'asa yana zage-zage. Kuma uwar na d'aure masa gindi. Ya Allah idan wani laifi nayi maka kake min wannan jarabawar, Allah na tuba ka yafe min dan tsarkin mulkinka." Da "Ameen." Sarah ta amsa tana mai jin tausayin kansu ita da mahaifin nata. "Tashi kije Sarah. Kije kiyi ta addu'a. In Sha Allah, Allah zai kawo maki mafita. Ki k'addara dama can Umaru ba mijinki bane. Idan kuma mijinki ne, wallahi duk wannan abun da ya faro, babu makawa sai anyi wannan auren." Share hawaye Saratu tayi tare da fad'in, "Nagode Baba. Amma dan Allah idan ka yi min izini, zan koma asibiti domin ganin likita." Sai da ya gyara k'afarsa sannan yace, "Saratu ki bari gobe kyaje. Yanzu ki koma d'akinki ki huta." Mik'ewa Saratu tayi tare da fad'in, "To Baba, nagode Allah ya baka lafiya." Da Ameen ya amsa, ita kuma ta fice daga d'akin. Sanye yake cikin jeans d'in _Secret Circus_ da shirt na kamfanin _Saint Laurent_, sannan ya sanya takalmin _Stuart Weitzman_. Babu abunda ke tashi a jikinsa sai turaren _Imperial Majesty_, kallon kansa yayi a cikin k'aton madubin dake d'akinsa ya saki lallausar murmushi ganin irin kyawu da yayi. Juyawa yayi ya nufi wani katoton showglass wanda ba komai bane a ciki sai mahaukantan expensive sunglasses, wani waje ya danna sai ga glass d'in ya zuge, rabi yayi sama, rabi yayi k'asa. Sai da ya k'arewa glasses d'in idanu sannan ya kai hannu ya d'auko _Bulgari Flora_ wanda duk cikin sunglasses d'insa yana matuk'ar k'aunar wannan. Madannin ya kuma dannawa glass d'in ya rufe sannan ya juya ya koma wajen madubi ya d'auki Microfiber cloth ya goge glasses d'in sannan ya saka a fuskansa. Yanda yayi matuk'ar yi masa kyau, zaka d'auka dan shi kawai aka yi glasses d'in. Sai da ya k'ara kallon kansa from head to toes yaga he's perfectly dress sannan ya d'auki iPhone d'insa a kan bed ya nufi k'ofa ya murd'a ya fito. "Barka da fitowa ranka ya dad'e" Shi gaba d'aya tsorata yayi don bai tsammaci ganinta a k'ofar d'akinsa ba. "Laure! Kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Wai ni Ibrahim ya zanyi dake ne wai dan Allah? Sau nawa zan fad'a maki ki daina zuwa kina tsayuwa a k'ofar d'akina kamar wata security. Dan Allah, dan Allah Laure ki daina firgita ni. Ni wallahi babu abunda ke tada min hankali da tsoro kamar wad'annan kacakoren hakwaran na...." Tun kamun ya kai k'arshen zancen ta fashe da dariya wanda ya bayyanar da manya-manyan hakwaranta na sama guda hud'u da suka turo suka yi curko-curko a waje. Sam bata iya rufe bakinta ruf saboda hakwaran. "Precious Lord in heaven! Laure bar nan wajen tun kamun na zubar da wad'annan kacakoren hakwaran wallahi." Ja da baya tayi tare da fad'in, "Ni hwa tsaya kaji Ya Khalif (Khalil), Hajiya ce tace nazo nayi kiranka tana can parlor kai take jira. Kuma ni kayi mani wanin (warning) akan kar ba kuskura na kuma shigar maka d'aki kai tsaye. Kuma nayi k'ok'arin danna wanna madannin amma na kasa. Kasan ni d'in ce kamar a duk'e aka haifo ni sabida rashin tsaho." Harara ya maka mata tare da fad'in, "To naji bar nan wajen." Washa bakin ta kuma yi sai da ya matsa baya don da gaske shi hakoran nata tsoro suke bashi. Gaba tayi kad'an, sai kuma ta juyo tare da fad'in, "Nace dan Allah yaya khalif ko zaka d'an sammun wannan turaren naka mai shegen k'amshi anan, ko baka cika min ba wallahi nagode." Ta k'arisa maganar tana mai ciro wata k'aramar kwalba irinta fiya-fiya a k'ark'ashin zaninta. Yunk'urowa yayi kamar zai kai mata duka ta juya a guje ta nufi dogon corridor d'in da zai fitar da kai katoton parlorn gidan. Tsaki yayi sannan ya jawo k'ofar d'akina nasa ya murza key tare da saka key d'in cikin aljihun wandonsa ya soma tafiya majestically har ya iso parlor. Tsaye yaga Laure da mopa a hannunta, maimakon tayi abunda za tayi, sai ta b'ige da kallon katoton tv na bango dake manne a jikin bango. Wani film d'in India mai suna *_Sultan_* ake haskawa d'ai-d'ai inda yake gudu domin kamo jirgin leda. Babu abunda Laure kayi sai kyalkyalewa da dariya. Khalil na k'arisowa ya d'auki remote dake hannun kujera ta jefi Laure dashi a goshi, don Hajiya tayi kiran sunanta har sau hud'u amma film ya d'auke mata hankali. Kuma ita ta zubar da juice d'in da Hajiya ke sha sabida rawar kanta. Saurin susa goshin Laure tayi tare da fad'in, "Laa! Wallahi kuma naji kamshin turaren ka, wata zuciyar tana ce min kai ne ka k'ariso, amma wanna gayen ya tafi da imani na. Dan Allah Hajiya zaki biya min kud'in jirgin inje indiya mu gaisa tare da d'aukar hoto dashi? Na san wallahi zai ji dad'i idan ya ganni. Na san har fim sai mun yi tare in fito a budurwarsa." Harararta Khalil yayi tare da fad'in, "To dan gidan ku matsayin saka ki a cikin keji ana zuwa ana ganin ki ba zaki samu ba, shashasha kaiwa. Za kiyi abunda ke gabanki ko sai na isko ki nan wajen." Marairaicewa tayi tare da fad'in, "Allah sarki yaya khalif. To na rantse maka fad'in k'asar indiya samu mai kyawuna abune mai matuk'ar wuya. Ko kai d'innan da kad'an ka fini kyawu." Zama yayi kuwa da Hajiya yana mai fad'in, "Tabbas, babu shakka. Dama ai samun irin ki a indiya ai sai an tona. Don ko namun dajinsu sun fiki kyawun gani." Turo baki tayi tare da fad'in, "Kina dai jin sa ko Hajiya!" "Kar ma ku soma saka ni cikin shirmen ku. Ke da Khalil dai kamar kuna ganin hanjin juna." Fad'in Hajiya dai-dai lokacin da Maryam matar wan Khalil tayi sallama ta shigo d'akin hannunta rik'e da wani kyakkwar kula. Dai-dai inda Hajiya take ta ajiye kulan tare da fad'in, "Tom and Jerry! Kun soma fad'an naku ko." Kallon kukan da aunty Maryam ta ajiye a gaban Hajiya yayi sannan ya kalli aunty Maryam d'in tare da fad'in, "Ai kin san Allah, sai na kori yarinyar daga gidan nan.???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Ni da gidanmu amma bani da sakewa. Babu ranar duniya da wannan yarinyar bata tsora tai da muggan hakwaran nan nata." murgud'a baki Laure tayi tare da fad'in, "Halittar Allah kake zagi. Idan ka isa halicci kiyashi anan wajen mu gani. Sai rowar tsiya, d'an turaren da mutum zai baka kad'an cikin kwalba amma ya kiya sabida rowar tsiya. Wallahi Hajiya dai kowa ya san ita d'in hannunta a bud'e yake kamar kasuwar kwari ta Kanon mu. Ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login