Showing 84001 words to 87000 words out of 129558 words

Chapter 29 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

kanta kawai tayi akan hannun kujeran tana shashshekar kuka don kukan ya?i fitowa. Ajiye ledar yayi a kan gado tare da isa wajenta duk da uban warin da take yi ya cicciSeta ya kaita bayi ya ajiye a cikin bathroom tub sannan ya fita cikin sauri ya gyara inda ta Sata sannan ya dawo da ita kan gado bayan ya shimfiWa wani zani gudun kada tsutsotsin su sake Sata wajen. Wannan ledan ya Wauko tare da buWewa ya zaro pampas Win manya guda Waya ya saka mata........


_Kuyi ha?uri da wannan Please, in sha gobe zan yi mai yawa_


*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_MATAR SAYYADEE_*



>؜? *KANWAR MATATA*>؜?

*28*


"Mine, Nafeesa ta samu ?aruwa Wazu." Ya faWi maganar yana mai jan skirt Winta sama ya zage zip Win. Out of excitement tace, "Dan Allah! Alhamdulillah Allah ya raya, don Allah ka Wauko min picture Win babyn in ganta." Kallon fuskanta Khalil yayi, babu abunda yafi kyau da fuskanta irin fara'arta, sai yaji kamar kar ya faWa mata babyn ta koma. "Ya naga kayi shuru Happiness?" FaWin Sarah. Ajiyar zuciya Khalil ya sauke tare da kau da kansa daga kallonta yace, "Allah ya amshi abunsa, babyn ta koma." Zaro idanu Sarah tayi tare da faWin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ina Nafeesan yanzu? Wani hali take ciki?" Sarah ta faWi hawaye na zubar mata. Hannunta biyu ya kama tare da faWin, "Ta Wauki dangana, ta san cewar Allah da ya amshi rayuwarta ya fita son yarinyar, ta amshi ?addararta ta hanyar dangana da fauwalawa Allah komai." A hankali Sarah tace, "Allah ya ?ara mata ha?uri da dangana." Mi?ewa yayi tare da faWin, "Haka ake son duk musulmi da Waukar ?addara mai kyau da mara kyau idan har ya yarda shi Win cikakken musulmi ne, shiyasa nake so kema ki fauwalawa Allah komai ki daina koke-koken nan, in Sha Allah zaki samu lafiya. Bari naje zana'idar in dawo sai mu tafi asibitin, kina bu?atar wani abu?" Girgiza kai Sarah tayi tare da faWin, "Babu abunda nake bu?ata, kayi tafiyarka, Allah yasa mai ceto ce. Nima zan gwada mi?ewa inje can wajen Hajiya yanzu tunda ka saka min pampers tsutsotsin baza su zubo ma." Kallonta yayi tare da faWin, "Idan har kin ga baza ki iya ba, kiyi zamanki gaba Waya sun san baki da lafiya. Ki kular min da kanki, sai na dawo." Yana gama faWin haka ya fita ya bar Wakin. Hannu Sarah ta Waga tare da faWin, "Ya Ubangiji ga mijina nan, ka kare min shi daga dukkanin cutuwa, ka ?ara masa so da ?aunata a cikin zuciyarsa, ni kuma bani lafiya mai amfani ta yanda zan bauta masa wajen yi masa biyayya har in dawo gareka. Allah ka bani lafiya alfarmar annabi sallallahu alaihi Wasallam." Ta ?arisa maganar tare da fashewa da kuka. Can cikin gida kuwa, har mijin Nafeesa da danginsa sun ?ariso, mahaifiyarsa ita tayiwa babyn wanka tare da yi mata sutura, shi kuma Qasim mijin Nafeesa sai lallashinta yake yi yana bata ha?uri akan in Sha Allah zasu samu wani nan kusa. Kamun magrib har sun kai gawan makwancinta sun rufe sun dawo, sai gidan yayi wani irin tsit kowa da irin jimamin da yake yi, yayin da Laure ke wani irin zabura da firgita idan ta kasance ita kaWai a waje, don babu fuskan da take gani sai na Aina'u da _Hell Ofulafu_ suna tsoratata gashi kuma babu bakin magana. Sarah ta iya fita har side Win Hajiya, kallon Waya Hajiya tayi mata gabanta ya faWi ganin wani mahaukacin rama da tayi, don ko Wazu da safe sun haWu kamun faruwar komai, "Wannan wani irin cuta ce kamar ta iska?" Hajiya ta faWi a zuciyarta. Sarah kuwa da bata san halin da Hajiyar ta shiga ba, waro idanu tayi ganin halittarta gaba Waya ya canza, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Hajiya haka kika koma?" Aunty Maryam ce tayi saurin tarota ganin zata zube a ?asa, ta zaunar da ita. Rarrafawa tayi ta ?arisa wajen Hajiya tare da Waura kanta akan ?afafun Hajiya ta hau rera kuka, hajiya bata iya cewa komai ba sai shafa bayanta da ta shiga yi tana danne nata hawayen. "Oh Allah! Abu kamar jifa, daga wanda halittarsa ta canza, sai kuma wacce maganarta ya Wauke gaba Waya, da kuma mai aman tsutsotsi! Gaskiya wannan abun dubawa ne. Duk mai bin mu da sharri in Sha Allah sai ya koma masa." FaWin Nafeesa wacce taci kuka ta ?oshi, idanun nan sun yi jazur." Wani wawan kallon gefen idanu Aina'u tayiwa Nafeesan a zuciyarta tana faWin, "Ashe kema zaki bi ?arki kenan!" Sarah kuwa Wagowa tayi ta kalli Nafeesa tare da faWin, "Nafeesa wacece kuma maganarta ya Wauke?" "Laure!" Nafeesa ta bata amsa hawaye na zubowa. Hajiya ta kalli Waya daga cikin yaran dake Wakin tace, "Namrah kunna rediyon can ki kunna mana karatu zuciyar kowa tayi sanyi." Da jin haka wuff Aina'u ta mi?e ta fita daga Wakin ta baya gudun a ganta, don yi nayi kamar zata shiga toilet Win dake parlourn, Aunty Maryam kuwa tunda ta mi?e take lure da ita, don haka nan taji tana mugun zargin Aina'un, sam tun ranar farko data fara ganinta bata kwanta mata a rai ba. Da sauri ta zaga ta baya ta tsaya bayan flowers, sai da ta kalli gefe da gefe sannan ta fiddo hannunta tare danna tsakiyar tafin hannun, cikin second biyar sai ga _Hell Ofulafu_ ya bayyana cikin suffarsa ta tsoro, gefensa kuma wani gajeren halitta abun tsoro ne mummunan gaske, shi ya daka mata tsawa tare da faWin, "Menene bu?atarki ta gaba?" "Nafeesa! Ita nake so tabi jaririyar, ba bada jininta matsayin ruwan da Hell zai WanWana, sannan ina so a saka mummunar warin da yafi wanda Sarah keyi a jikin mijinta ta yanda zata ri?a kyamatarsa har hakan ya fusata shi yayi mata wula?anci, don na san tabbas idan aka yi haka Khalil zai ji haushinta tunda shi ya jure bai kyamaceta ba duk da tsutsotsin dake fita a jikinta da kuma warin da take yi. Sannan na uku, ina so a Satar da kokwanto da shakkun da ke zuciyoyin mata da mijin gidan nan a kai na, ina nufin SS Abdul-Hakeem da matarsa Maryam, sannan Barrister Muhammad Kabir da LTG Abdullah ka mantar dasu suna da family ka Kaduna, ina so su manta da kowa nasu dake Kaduna, ko da wasa kar su waiwayi gida! Abdul-Hakeem ma ayi masa abunda zai jawo a koresa daga aiki, don na tsani ?an sanda musamman na farin kaya!" Wannan mummunar halittar ya fashe da dariya tare da faWin, "Aikin ya kammala, sai dai jinin ?anwar Mijin yayarki yayi kaWan, dole sai kin ?ara da jinin yaro ?aramin kuma namiji." Shuru Aina'u tayi tana tunanin ta inda zat dea samu jinin yaro ?aramin, "Rabo Wan wajen Na'ima!" FaWin Aina'u a bayyane tana mai sakin murmushi tare da ?ara faWin, "Na rage maki wahala Na'ima, a sauka lafiya Rabo!" ?at _Hell Ofulafu_ da wannan halittar suka Sace daga tafin hannunta don sun gama sauraran abunda zasu saurara, tun ambaton sunan Rabo da tayi na farko, har _Hell Ofulafu_ ya janyo kurwarsa tare da haWiyewa. Aina'u na juyawa suka yi idanu huWu da Aunty Maryam da ta biyo ta a baya, har fitsarin tsoro ya gama wanke jikinta, gaba Waya jikinta sai kakkarwa yake yi. Aina'u kuwa wani murmushi ta saki ba tare da ko War ba don Aunty Maryam Win taji komai da take tattaunawa da _Hell Ofulafu_. Zagaye Aina'u ta shiga yi tare da faWin, "Makanta, kurmanta, rashin yin magana, mutuwa Sarin jiki, mutuwar gangar jiki gaba Waya, ?ona ki da ranki, wanne kika zaSa?" Kuka Aunty Maryam ta soma yi tare da faWin, "Dan girman Allah Aina'u kiyi ha?uri kar kiyi min ko Waya daga cikin abunda kika lissafo, na zaSi da nayi shuru da baki na, babu wanda zai ji wannan maganar nan daga ni sai ke!" Wani dariya Aina'u ta kwashe dashi tare da faWin, "Kin ga nayi maki kama da wawuya? Ko da yake, ni nayi maki zaSi, shine barin gidan nan, kuma kin san wani abu, duk lokacin da bakinki yayi kuskuren buWewa ya faWawa wani wannan abun da kika ji, baza ki iya faWin komai ba, kuma daga ranar baza ki kuma magana ko kiji ba har ki mutu! Wuce kije ki fara haWa kayanki kamun takardar sakinki ya biyo ki!!" Ta ?arisa maganar a tsawace tana mai nuna mata hanya. Da sauri Aunty Maryam ta ri?o ?afafuwanta tare da faWin, "Na ro?e?i da girman Allah kar ki raba ni da aurena, wallahi nayi maki al?awarin babu mai jin wannan maganar har sai idan Allah ne yayi ikonsa, ina son mijina da aurena don Allah kar ki raba ni dasu." Wani mugun tsaki ta ja tare da faWin, "Sai ki zaSa, rayuwarki, lafiyar jikinki, ko kuma aurenki?" Shuru Aunty Maryam tayi tana wani irin kukan ba?in ciki. Aina'u ta taSe baki tare da faWin, "Gidan na kowa sai yaji a jikinsa, na rantse da Yesu Almasihu mai ceto!" Da saurin Aunty Maryam ta kalleta jin abunda ta furta tare da faWin, "Babu shakka, ashe shiyasa babu Wigon imani a zuciyarki, in Sha Allah sai kin girbe abunda kika shuka azzaluma kafurar banza!" A cikin zuciyarta. "Ki wuce kije ki soma haWa kaya, don yau gidan mai dattin hula da Wan kwali za'a kwana!" Tana gama faWin haka ta wuce ta bar wajen tana wa?ar zumunta. Aunty Maryam kuwa kuka ta dunga rusawa tana tunanin makomarta, ita da babu uwa, babu uba, rayuwa take yi a wahale a wajen dangin ubanta kamun Allah ya kawo mata Abdul-Hakeem har suka yi aure, idan ka ganta gidansu gaisuwa taje ko kai masu abun arziki don suna ba wasu masu arzikin bane, talla tayi su kala-kala irin su kunun gyaWa da alale, da daddare kuma burabusko da miyan taushe, kuka da kuSewa! Har zunWenta ake yi wai don ta auri Wan masu kuWi sai fankama take yi tana ?o?arin manta asalinta. "Shinekan wahalata ta dawo sabuwa fil, masu fatan irin haka ta faru dani sun samu dama. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allahumma arji'ini fi musibati wa aklifni khairan minha!!" Haka aunty Maryam tayi ta nanatawa har ta isa Sangarenta. Cak ta tsaya a parlour tana kallon tan?ameman hotunsu su uku, ita da Abdul-Hakeem da kuma ?arsu Maimoon. Can gidansu Lami kuwa, Rabo na zaune kusa da ita da roban abinci a hannunsa yana ci, gaba Waya suna tsakar gida suna shan iska kasancewar garin akwai zafi, kawai sai suka ga Rabo ya fara wani irin jijjiga idanunsa na sama, hatta robar abincin dake hannunsa jijjiga yake yi, kumfa ba?i??irin ya soma kwaranyowa daga bakinsa, gaba Waya da gudu sukai kansa suna kiran sunansa, Lami kuwa wani tsalle ta buga tare da fasa ?ara ta shiga faWin, "Yesu! Yesu!! Yesu gamu gareka mun bar zunubi, duk wani dodo ko maye ko mugun dake son tafiya da granson Wina ka tsine masa, a cikin mu'ujizozinka ka cire shaitan Win dake kusa da jikana yaaaa Yesu Almasihu mai ceto!" Tana faWin maganar ne tana wani irin tuma a ?asa tare da fasa ihu. Da sauri baba dake Waki ya fito, tuni Na'ima dake ri?e da Rabo tana kuka ta nufi wajen baba tare da mi?a masa shi tana mai Waura hannu a kai tana kuka. Baba kuwa yana amsar Rabo ya fahimci rai yayi halinsa saboda yanda jikinsa ya sake. ShimfiWar da shi yayi akan tabarma tare da mi?ar masa da hannu sannan ya mi?a hannu ya janyo zanin dake kan igiya ya lulluSesa har kai. Wani irin baya Na'ima tayi ta tafi luuuuuu ta faWi ?asa sumamma! Da gudu su Marfu'a suka yi kanta tare da cicciSanta suka kai ta Waki suka shinfiWe. Lami kuwa sai kururuwa take yi, hakan ya jawo hankalin ma?ota suka cika gidan tam. Baba kuma waya ya Waga ya kira abokansa su baba Sama'ila, har aka gamawa Rabo wanka Na'ima bata farfaWo ba, sai can har ana tunanin kaisa kawai sai ta farfaWo, har Waki baba ya shigo yayi mata nasiha tare da ce masa taje tayi masa addu'a, da kyar ta isa zuwa ta zube guiwowinta a ?asa kusa da gawar, "Ka yafe min, ka yafe min!" Shine abunda Na'ima tayi ta maimaitawa tana kuka. "Ba'a kuka gaban gawa Na'ima, haramun ne!" FaWin baba Sama'ila. Hassana ce ta kama hannunta suka fita daga Wakin don har an kawo makara za ayi masa sallah, Gaba Wayan su babu mai hijab ko Waya, a wajan ma?ota suka ara sannan suka iya fita aka yi sallar dasu. Na'ima bata kusa haukacewa ba, sai da aka saka Rabo cikin mota za'a wuce, sai da aka turata cikin gida aka kullo ?ofar saboda yanda take wani irin mahaukacin kukan tashin hankali. Baba kuwa babu abunda dake zuwa bakinsa sai Allah yasa mutuwar nan ta zama sanadin shiryuwar ?a?an nasa. Bayan an dawo daga ma?abarta baba yayi ta kiran layin Khalil domin ya shaida masa mutuwar amma bai samunsa, layin Sarah kuma har ta gama ringin ba'a Wauka ba. Can gidansu Khalil kuwa, Aunty Maryam zaune a ?asa wayarta a hannunta tayi masa ?uri tana jiran message daga Abdul-Hakeem akan ya saketa, Wiririn sa?o ya shigo wayar, gabanta ne ya buga da ?arfi don har sai da ta rintse idanu tana addu'a, dakyar ta iya duba sa?on, sai taga ashe daga bank Winta ne suna tayata murnar zagayowar ranar haihuwarta. Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tare da hamdala a bayyane, daidai nan ya Abdul-Hakeem Win ya murWa handle Win ?ofar ya shigo, da wani irin sauri ta mi?e tana kallonsa gabanta na wani bugawa kamar zai faso ?irjinta ya faWo. A hankali ya ri?a takowa ita kuma tana matsawa har suka dangana ga jikin bago. Goshinsa ya haWe da nata tare da faWin, "Maryama, tun da na aureki tsayin shekaru biyar kenan, baki taSa yi min wani abun da naji kamar in rabu dake ba, ko wani aiki nake yi na wahala a wajen aiki, idan na tuna da ke, sai inji farin ciki ya mamaye zuciyata tare da fuskantar abunda nake yi domin inyi in gama in dawo gida na ganki, ki sani shi aure rai gare shi, idan lokacinsa yayi, da daWi da babu daWi sai an rabu! Kiyi ha?uri Maryam, zan ?ara maimaita maki, baki yi min komai ba sai alkhairi, kiyi ha?uri da abunda zai fito daga bakina yanzu," sai dai ya Wan yi jim yana kallonta sannan ya haWe hannunta biyu tare da faWin, "Ki yafe min, na sake ki saki Waya Mary......" Bata bari ya kai ?arshe ba ta fashe da wani irin kuka tare da gittashi da sauri ta haura sama tare da banko ?ofa, shi kansa Abdul-Hakeem Win wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo masa daga idanunsa, ya rasa wani irin wutane yake ta ruruwa a zuciyarsa, haka nan ya dunga jin zafi da raWaWi, can kuma ya soma jin shi kawai aure ne ya ha?ura dashi, kamar ana ingizashi yaji domin yazo ya saki matarsa da a kullum burinta ta kyautata masa. Aina'u bata koma Wakin Hajiya ba saboda ?ira'ar dake tashi, sai ta koma can baya ta inda baza taji sautin karatun ba ta zauna tana mai jin zafin furucin Nafeesa, "Sai na WanWana maki azababbiyar mutuwa in dai ni ?ar Elizabeth da Nuhu ce!" Ta faWi maganar tana sakin kwafa. A Wakin Hajiya kuwa, Sarah tayi kuka kamar zata mutu, bata soma jin salama a ranta ba sai da aka kunna ?ira'ar nan. Zuwa anjima can sai ga Khalil ya shigo Wakin, shi bai ma Wauka ta iya zuwa ba nan Win ba, sai da ya shiga Wakinta ya taras bata nan sannan ya dawo nan, "Ya ?arin ha?uri Nafeesa?" Luhu-luhun idanunta ta Wago tare da faWin, "Alhamdulillah!" Kallon Sarah Khalil yayi tare da faWin, "Mine taso mu tafi yamma nayi." "Ina zaku?" Hajiya ta tambaya, "Asibiti nake so muje na dubata." GyaWa kai Hajiya tayi tare da faWin, "Allah ya ?ara sau?i, sai kun dawo." Da ameen Khalil ya amsa, ita kuma Sarah ta mi?e ta fito ya biyo bayanta, abunda ya matu?ar bashi mamaki shine, lokacin da take cikin Wakin Hajiya, babu wannan warin da take yi ko kaWan, amma tana fitowa warin ya dawo. Bai ce komai ba har suka isa Waki, kalonta yayi tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login