Showing 36001 words to 39000 words out of 129558 words

Chapter 13 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

yana hanya zuwa anjima zai biyo jirgi shi da Aysha. Kuma nima Hajiya ta saka na kira mijin Nafeesa akan ha kawo ta gobe. Wani irin meeting kuma za ayi yau a gidan nan? Allah yasa ba dai akan rigimar gado bane. Nifa wallahi abunda Papa ya tafi ya bari bai tab'a d'ad'ani da k'asa ba, abun na tara da gumina ma ya ishe ni zaman duniya." Tun da ya fara maganar _Khalil_ jinsa kawai yake yi amma kwakwalwarsa da tunaninsa sun yi nisa tun lokacin da yace masa yaya Abdullah na hanya. Wannan masifaffan mai bak'ar zuciya kamar da taurin kai. Don shine ya d'auko Papa sak. Shi kaifi d'aya ne, idan yace yes, to ko duniya zata tashi yes d'in ne, idan kuma yace no, tofa ko ana ha maza ha mata babu mai canza shi. Kuma duk gidan tsoransa ake ji. Shine babba kuma zai iya kaiwa shekaru hamsin da biyar a duniya. Daga shi sai yaya Barrister (Muhammad Kabir) kenan, shi yana da sanyi hali. Ba k'aramin abu ke b'ata masa rai ba. Idan kaga yana zafi da magana sosai, to fa a kotu ne musamman idan Shari'a ake yi akan fyad'e. Shi yaci gajiyar Papa don tun yana k'aramin yake fad'in "Papa idan na girma irin aikinka zan yi in rik'a Yankewa mugaye hukunci. Daga Barrister sai Abdul-Hakeem wanda shi kuma SSS ne, (D'an sandar farin kaya). Daga shi sai _Doctor Khalilullah_, sai Aysha, sai auta Nafeesa. "_Khalil_ kana jina kuwa." Fad'in ya Abdul yana tab'a hannunsa ganin yayi zurfi a tunani. "No, babu komai ina zuwa." Fad'in _Khalil_ tare da nufa part d'in Hajiya. Kai tsaye d'akinsa ya shige yana safa da marwa. Kwankwasa k'ofar d'akinsa aka yi, da sauri ya juya yana kallon k'ofar. Hannu ya kai ya danna wani switch sai ga Laure ta bayyana akan screen d'in dake saman k'ofarsa. Ajiyar zuciya yayi tare da nufa k'ofar d'akin ya bud'e, "Yaya _Khalif_ ina kwana?" Saude ta fad'i a sanyaye don tun jiya take jinta wani iri ganin uwar d'akinta babu lafiya. "Lafiya k'alau ya aka yi?" Ya amsa tare da jefa mata tambaya. "Hajiya ce tace in fad'a maka yau kar ka bar gidan nan akwai bak'in da zasu zo anjima." Shuru yayi yana kallon Laure kamar ita ce Hajiyar, can kuma ya nisa tare da fad'in, "Ok, to jeki." Yana gama fad'in haka ya rufo k'ofar tare da zama a bakin gado ya rik'e kai. Gaba d'aya natsuwa ta bar jikinsa. Gabansa sai dukan tara-tara take yi. Bai isa sakawa cikinsa ko ruwan Lipton ba har k'arshe sha d'aya yana nan zaune a d'aki yana sak'awa da warwarewa. Su aunty Maryam da Laure kuwa, sai kaiwa da komowa suke yi a kitchen suna had'awa bak'i abinci. Nafeesa ta riga kowa zuwa kasancewar ita mazauniyar Kaduna ce. Ana tayi aure a kabala shooting range. Hankalinta sosai ya tashi ganin halin da mahaifiyarsu take ciki. Don har a wannan lokacin jiri hajiye take gani, kuma idanunta sunyi luhu-luhu alamar taci kuka. "Hajiya dan girman Allah mai ke faruwa? Idan dai akan su uncle ne, dan Allah ki fitar da damuwarsu a zuciyarki. Har kuka gama zaman ku da Papa bai saka maki ciwo ba, sai y'an uwansa ne zasu buwayeki. Dan Allah Hajiya ki bari." Girgiza kai Hajiya tayi tare da fad'in, "Uhm, baza ki gane ba Nafeesa, bari dai sauran y'an uwanki su iso. Ni ba akan y'an uwan mahaifinku bane. Da sune ne abun da sauk'i." Shuru Nafeesa tayi tana tunani a zuciyarta to mai ya faru idan har ba su uncle bane. K'arfe sha d'aya da mintuna arba'in, yaya Barrister ya iso gidan shi da matarsa aunty Khairat da yayansu uku, Sam'an, Sahla da Nu'aima. Nan aka dunga oyoyo-oyoyo. Ko mintuna goma basu yi da zuwa ba, soja marmari daga nesa, LTG Abdullah ya iso shi da Aysha da kuma tawagar sojojin da suka yiwa unguwar k'awanya. Don gaba d'aya unguwar sai da suka shaida *_Lieutenant General Abdullah Nurudden Muhammad_* ya shigo unguwar. Tun da _Khalilullah_ ya lek'o ta window ta can saman d'akinsa yaga uban sojojin sun gewaye gate d'in gidan, wasu ma har ta cikin gidan yaji kamar an cire lakar dake jikinsa. Laure gaba d'aya ta rud'e don har wani zawo-zawo take ji sabida ba k'aramin tsoro da shakkar _LTG Abdullah_ take yi ba. Don shi fuskansa ma bata cika fara'a ba. Kai tsaye gaba d'aya suka wuce d'akin Hajiyar ban da _Khalil_ da ko lek'owa parlor bai yi ba. Har k'asa k'asa ya _LTG_ ya duk'a gaban gadon da take tare da fad'in, "Hajiya ina wuni, mun same ku lafiya? Ashe baki ji dad'i ba. To menene amfanin _Ibrahim_ a cikin gidan nan da ba zai iya kai ki asibiti ya duba ki ba. Wallahi wani irin iskanci ne. Ina yaje?" Hawaye Hajiya ta soma yi tare da fad'in, "Ni na hana a kai ni asibitin, don ciwon dake damuna, _Khalil_ d'in ne sanadiyarsa. Marmari, _Khalil_ ya b'ata mana sunan famili. Ya rusa duk wani tarbiyar da muka ginasa akai. So mu had'u mu duka a parlor, bayan anci abinci, sa muyi maganar." Kai a k'asa zuciyarsa na tafasa ganin mahaifiyarsa na hawaye yace, "Hajiya abinci ba zai ciwu ba, har sai naji abunda yake damunki nayi maki maganinsa tukun." Gaba d'aya su Barrister, Aysha da Nafeesa har da yaya Abdul suka ce, "Hajiya abinci tabbas ba zai ciwu ba har sai munji matsalarki." "Ku aika Laure ta kira _Mu'azzam_ a d'akinsa ya fito mu tafi can parlor ayi maganar a can." Mik'ewa Nafeesa tayi tare da nufa corridor d'in da zai sadata da d'akin yayan nata tana mamakin wani irin laifi ya aikata da har Hajiya take cewa ta b'ata masu sunan family. "To ko zubar da ciki yake yi a asibitinsa?" Fad'in Nafeesa cikin zuciyarta dai-dai lokacin da take knocking d'in k'ofar d'akina. Bud'ewa yayi, kallon fuskansa kawai za kayi ka tabbatar yana cikin tashin hankali. Kuma ba komai ke d'aga masa hankalin ba irin fushin Hajiya. "Nafeesa!" Ya fad'i a hankali yana kallonta. "Na'am yaya _Khalil_. Tun d'azu gaba d'aya muka zo amma babu kai a wajen. Hajiya tace kaje parlour duk muna can." Fitowa yayi gaba d'aya tare da kullo k'ofar yace, "Muje Nafeesa. Hankalina ne gaba d'aya a tashe. Har da ya Abdullah ko?" Gyad'a masa kai tayi suna tafiya a jere tare da fad'in, "Yaya _Khalil_ wai don Allah mai ke faruwa ne Hajiya ta kira mu gaba d'aya? Wani abun kayi ne?" Bai ce mata komai ba har suka k'ariso parlourn. Bai iya d'aga kai ya kalli kowa a cikinsu ba. Neman waje tayi daga gefe ya zauna kansa a k'asa tare da fad'in, "Ina wuni ya Abdullah? Sannu da zuwa ya Barrister. Kun zo lafiya?" Babu wanda ya amsa gaisuwarsa. Bai damu ba don dama ya san dole hakan zata kasance. Ya Abdullah kuwa duk ba sai ainahin abunda _Khalil_ d'in ya aikata ba, sai jifansa yake yi da wani irin mugun kallo. Su kad'ai ne a parlor, don ko Barrister da yazo da matarsa, tana can ita da Y'ay'anta a part d'in ya Abdul-Hakeem. Sune kawai isu-isu a parlourn. Don maganar tasu tana buk'atar privacy. "Abdul-Hakeem bud'e mana taro da addu'a." Fad'in Hajiya wacce ke hakimce a kan kujera tana girgiza k'afa. Sai bayan yaya Abdul-Hakeem d'in ya gama addu'ar sannan Hajiya tace, "Na kira ku ne anan wajen ba don komai ba, sai don saboda _Ibrahim_. Na san dukkan ku kun san bak'ak'en maganganu da kuma zagi da nake jurewa daga wajen dangin ubanku. Tun yana da rai suka kafa min k'ahon zuk'a har ila yau da ya kasance babu shi a raye. Kuma kun san cewa iyayenku suna son had'a _Khalil_ aure da Nina wanda shi kuma yak'i bada fad'in kai a cewarsa bata da kamun kai ita mazinaciya ce." Da sauri yaya Barrister yace, "Hajiya idan dai a kan wannan maganar ce ta Nina, to ba wai bane. Don ni da kaina na tab'a ganinta a wani babban hotel a Kano ita da wani sa'an mahaifinta." Da k'arfi Hajiya tace, "Kayi min shuru! Ai ita da _Khalil_ d'in zani ce ta tadda muje." Da sauri _Ya LTG_ yace, "Hajiya ban fahimta ba." Gyara zama tayi tare da fad'in, "Yanzu kuwa zaka fahimta. Kai _Khalil_ yi masu bayani abunda ka aikata." Kansa a k'asa gabansa na fad'uwa ya d'ago ya kalli Ya Abdullah, wata uwar hararar da ya watsa masa ya saka yayi saurin sunkuyar da kai k'asa." Wani mahaukacin tsawar da yayi, ba _Ibrahim_ kad'ai ba, hatta ita kanta hajiyar sai da ta tsorata. "Za kayi magana anan wajen ko sai na taso na taka cinyarka tayi dagwa-dagwa!" A razane _Khalil_ yace, "Hajiya wallahi, tallahi wa billahil azim ba halina bane. Tsautsayine ya saka nayi mata fyad'e har ta samu ciki." A mugun mamakance da bak'in ciki ya Barrister da ya Abdullah suka ce "Fyad'e!" Wani mik'ewa _Lieutenant Abdullah Nurudden Muhammad_ yayi tare da isa inda _Khalilullah_ yake tare da............




*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*

*_MATAR SAYYADEE_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*PAGE 14*


Here are the list of my books:
=?G?
1. Anya uba nane?
2. Auren cikin gida (paid)
3. Ni da shi abu d'aya ne
4. Zina babbar bala'i ce
5. Bani da gata (paid)
6. Garwashi
7. Sai a lahira (paid)
8. D'an Faari (First born) (paid)



Wani irin murmushi mugunta ta saki bayan ta kalli goron fantar. Bud'ewa tayi tare da jefa duka kwayoyin sannan rufe da k'arfi ta girgiza tare da saka shi cikin aljihun doguwar rigar dake jikinta ta nufi hanyar gida cike da jin dad'i. Ko da ta shiga d'akin, bata samu Sarah a ciki ba lokacin Baba yayi kiranta tana d'akinsa domin tattauna da ita game da batun aurenta da iyayen _Khalil_ suka yi. Sai ta ajiye fantar a dai-dai inda ta san Sarah na shigowa zata gani sannan ta bar d'akin ta koma d'akin Lami inda ta same su duka a d'akin suna tattauna game da zancen aure da iyayen _Khalil_ suka yi. "Kuma ke Lami sai ki yarda? Tabd'ijam! Bayan kin hana d'aya daga cikin yin soyayya mai zurfi balle har hakan ya saka mu bujire maki wata ran muce aure muke so. Ai kamar yanda muke zaune a gida har wannan lokacin, haka ita ma zata zauna babu wani zancen aure." Fad'in Aina'u wacce ta tsinci maganar daga sama kawai ta tsumbula baki. "Kuji min shegiyar yarinya! Ke da Naima wanene babba da har zaki bud'e baki kiyi wannan maganar. Ke da ko b'ari baki tab'a yi ba cikin gidan nan har kyayi wannan maganar. Wai ma Lami tana da samari ne masu fita da ita?" Fad'in Nuratu. "Ina fa!" Lami ta bada amsa a gajarce. "Har wani fad'i take kamar yanzu har yanzu bamu yi aure. Dudu-dudu fa bata wuce sha bakwai sha takwas ba amma har take wannan maganar. To Na'ima tace me ita da take da shekaru talatin da d'aya a duniya?" Dogon tsaki Na'ima taja tare da fad'in, "Bar y'ar iska. Lami dube ni nan in baki shawara idan zaki amsa. Kin ga, kar ki sake kice zaki ja game da batun auren Sarah da _Khalil_. Kin ga dai uban sojojin da suka zo gidan na d'azu, kuma da bakinki kike bamu labari Y'ay'anta gaba d'aya hukumomine, daga soja, sai d'an sandar farin kaya da kuma lauya. Kuma kin san akwai dukiya babu k'arya a wajen su. Wallahi Lami sai kin fi jin dad'i idan Sarah ta shiga gidan matsayin mata ba dadiro ba. Kuma kince mana dagaske fyad'e yayiwa Sarah ba kanta ta kai ba. Yanzu idan kika k'i amincewa, da zarar ta haihu karb'e y'ar ko d'an kawai za suyi, shikenan ku da k'ara ganinsu sai Allah. Amma idan auranta yayi, arziki har mu sai mun ture don Sarah ba marowaciya bace kowa ya sani. Maganar gaskiya idan ta fito a fad'eta ko yaya take." Shuru Lami tayi tana auna maganganun Na'ima. Aina'u kuwa wani dogon tsaki taja tare da fad'in, "Wallahi idan har tsautsayi yasa aka yi wannan auren, sai na zame wa Sarah bala'i daga ita har su dangin mijin nata." A zuciya tayi maganar. "Ke Na'ima, Saratu fa tana da mugun hali. Ina tsoron kar ta shiga gidan arziki ta manta cewar nice wacce tayi sanadiyar zuwanta duniya. Da ace zata iya shawo kanta kawai yayi ta d'ura mata ciki a waje yana kashe mata kud'i ni kuma ina kula da yaran ina kame y'an currencyn zai fi min. Amma zuwan gidan matsayin matarsa sai inga kamar akwai matsala. Don a irin kallon rainin da yaron yake min, sai inga kamar zai iya hana ni zuwa gidan ko kuma ita ya hana ta zuwa nan d'in. Kuma tsaf ubanku zai goya masa baya." Marfu'a tayi karaf tace, "Kuma wallahi Lami zai iya hakan. Don ko mu baki ga irin kallon da yake mana ba matsayin yayyin budurwarsa." Gyara zama Lami tayi tare da fad'in, "To ya kuke ganin za ayi kenan?" Karaf Aina'u tace, "Lami, zubar da cikin kawai za ayi!" Da sauri gaba d'aya suka kalleta tare da fad'in, "Baki da hankali ne Aina'u? Ai idan aka zubar da cikin kamar rabasu aka yi. Halan baki san abunda baban wansu yace ba ko?" Fad'in Hassana. Yamutsa fuska Aina'u tayi irin ban san komai d'in nan ba tare da fad'in, "Mai yace shi babban wan nasu?" "To cewa yayi idan har aka zubar da cikin to babu aure tsakaninsu." Fad'in Lami. Tsaki Aina'u tayi tare da fad'in, "To dama ba auren ake so a samu hanyar fasuwarsa ba?" "Ke dak'ik'iya ce wai? Idan har haka ta faru ai fita za suyi daga harkan mu gaba d'aya kuma su hana shi _Khalil_ d'in zuwa gidan nan. Kin ga kenan anyi two-zero babu ciki, babu auren." Murmushi Aina'u tayi tare da fad'in, "To ku saurare ni da kyau. Shin ke Lami baki lura da irin son da shi _Khalil_ d'in yake wa Sarah ba? Idan da ace ba sonta yake yi ba, babu abunda zai saka ya nemi gidansu har yazo ya samu mahaifinta suyi magana, kuma sannan ba zai tab'a d'auko iyayensa ya kawo su gidan nan ba. Sannan da baya sonta ba zai tab'a yarda shine uban cikin jikinta ba. Kar ki manta shi likitane. Da zai iya duk dabaru ya cire cikin ya kuma koreta. Idan ta nemi tona mata asiri yayi amfani da dukiyarsa ya kulle ba ita kad'ai ba har damu y'an uwanta ko kuma ya kai mu kotu yace zamu b'ata masa suna da sharri. Duk k'auna ce mai zafi ya kawo haka. Kuma wallahi kinji na rantse maki Lami, da ace _Khalil_ bai son Sarah, babu abunda zai kawo shi, shi da iyayensa gidan nan a yau. Kuma a gaban idanunsu ya dunga kwarara godiya bayan Baba da y'an uwansa sun amince ya auri Saratu." Hannu Marfu'a ta bata suka tada tare da fad'in, "Shegiya k'anwata! Ina maki kallon k'aramar yarinya ashe kwakwalwarki na ja. Na yarda da maganar Aina'u yasin Lami. Ko ya kuke gani y'an uwana?" Ta k'arisa maganar tana kallon su Nuratu. Na'ima tace, "Ni dai maganar zubar da cikin nan har yanzu bai gama kwanta min ba. Duk da kuwa zuciyata tana rawa akan wata rana Sarah zata iya juya mana baya sabida mijinta. Babu wata shawara ce sai wannan Lami?" "Gaskiya ni dai babu a waje na." Fuska kumbure Aina'u tace, "Shikenan Lami tunda ni kun d'auke k'aramar yarinya wacce shawararta bai da wani amfani. Idan komai ya kwab'e maku nan gaba, zaku tuna wannan ranar wallahi." Tana gama fad'in haka ta tashi ta fice tana mai dana sanin yin maganar zubar da cikin kasancewar basu amince da shawararta ba. Sarah zaune gaban Baba tana hawaye, "Saratu, ba zan tilasta maki ki auri _Ibrahim_ ba, sai dai a matsayina na mahaifinki, ina mai baki shawara da ki bawa zuciyarki hak'uri ki amince da wannan yaro don Shi kad'ai ne rufin asirinki. Na yaba da hankalisa da kuma karamci irin na iyayensa. Kuma ina da kyakkyawar zato akan zasu rik'e ki bisa amana tamkar y'ar cikinsu ba suruka ba." Jan majina Sarah tayi tare da fad'in, "Baba ba kukan nake yi ba sabida ban son zab'in da kayi min, kukan farin ciki nake yi sabida zab'a min kai da Allah yayi matsayin mahaifi. Wallahi ko mahaukaci ka zab'a min matsayin mijin da zan zauna dashi, zan amshe shi hannu bibbiyu in kuma yi biyayya a gare shi. Nagode sosai Baba, Allah ya k'ara maka lafiya. Sannan nayi maka alk'awarin yiwa _Khalilullah_ biyayya har k'arshen numfashina idan har Allah ya rubuta ni matarsa ce. Bazan tab'a baka kunya ba Baba." Tausayi da k'aunar Sarah ya lullub'e Baba, "Allah ya maki albarka Saratu, Allah ya saka maki da alkhairi ya kuma zab'a maki abunda yafi zama alkhairi a rayuwarki ya shirya sauran y'an uwanki. Ubangiji ya jib'anci lamuranki. Je ki kwanta ki huta. Allah ya tashe mu lafiya." Da "Ameen" Sarah ta amsa bayan ta matso masa da duk wani abunda za zai buk'ata cikin dare sannan ta fice. Sai da tayi alwala a fanfo tukun ta nufi d'aki domin yin sallar shafa'i da wuturi. Tana shiga babu abunda idanunta suka fara gani sai wannan robar fanta mai sanyi da Aina'u ta ajiye sai naso yake yi. Hakanan Sarah taji bai wani burgeta ba. Sallaya ta shimfid'a tare da tada sallah. Tun bayan shigowarta d'akin Aina'u ta shigo ya kai sau biyar amma tana ganin robar fantar a inda ta ajiye. Ji take kamar ta shak'o wuyar Sarah da bacci ya kwashe bisa darduma ta d'ura mata wannan fantar. Da k'afa ta dunga shurin Sarah har sai da ta farka, "Ga Fanta nan mai sanyi idan zaki sha. Na sayo ne d'azu domin in sha, sai kuma ya fitar min a rai. Ki shanye ba sai kin biya. Tun d'azu dama ke na ajiyewa ganin duk gidan nan kece mai son Fanta." Bacci a idanun Sarah ta mik'e zaune tare da fad'in, "Bar mi shi a wajen. Sai zuwa anjima nasha yanzu cikina a cike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login