Showing 42001 words to 45000 words out of 129558 words

Chapter 15 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

da sanin Aina'u ba k'aramar muguwar yarinya za ayi ba. Sai tace Lami bata yi komai ba a duniya. Amma abunda har yanzu ke bawa Baba mamaki shine, don me za tayi hakan? "Ya ubangijin sammai da k'assai, ga Baiwar ka nan ka jib'anci lamuranta. Allah ka bata lafiya." A bayyane yayi maganar yana mai d'aga hannu sama. A can asibiti kuwa, gudun laifi, tun kafun ya k'arisa ya fiddo baya tare da danna kiran number Hajiya domin shaida mata abunda ke faruwa. Don babu abunda gabansa ke yi sai fad'uwa ganin jiya-jiya suka gama kankara masa warning akan kar ya kuskura yace zai cire cikin dake jikin Saran. Ringing uku Hajiya ta d'aga tare da fad'in, "Assalamu alaikum." "Amin wa'alaikissalam, Hajiya dan Allah ki saka driver ya kawo ki asibitina yanzu. Saratu ce ba lafiya gamu tare da y'an uwanta zuwa asibiti. Fad'uwa tayi kuma jini ya b'alle mata." Da sauri Hajiya ta soma fad'in, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ai babu wani driver da zai kawo ni, tunda ga Muhammad Kabir a gida, bari na kira na fad'a masa abunda ke faruwa sai ya kawo ni." "To Hajiya nagode." Yana fad'in haka ya katse wayar tare da cigaba da driving da gudu yana yi yana juyowa yana kallon Sarah da ta jima da fita cikin hayyacinta sabida irin jinin da take zubarwa. Suna isa asibitin ya fito da sauri tare da bud'e gidan ya kuma ciccib'ota gaba d'aya jinin jikinta ya gama b'ata jikinsa amma ko a jikinsa. Cikin asibitin ya nufa da ita don ko tsayawa nurses su gunguro gadon marasa lafiya bai yi ba. Doctor Hayat, Doctor Nurain da doctor Kamal sune suka amshi Sarah tare da shiga da ita emergency kuma suka hana _Khalil_ shiga sabida ganin yanda ya rud'e, koma ya shigan ba wani abu zai iya yi ba. Mintuna goma tsakani sai ga Hajiya ita da aunty Maryam, aunty Khairat matar ya Barrister da shi kansa Barrister d'in. "Ina uwata take?" Fad'in Hajiya lokacin da ta k'ariso. Waro idanu tayi ganin gaba d'aya jikin _Khalilullah_ ya b'aci da jini. "Subhanallah!" Hajiya suka fad'i a tare ita da au aunty Maryam. Yaya Barrister kuwa cewa yayi, "Garin yaya haka ta faru?" _Khalil_ kuwa sai danne hawayen dake taho masa yake yi tare da fad'in, "Baban ne yace tayo masa kira na yana son magana dani, to naje ko zama ban kai ga yi ba, sai kawai jin talatin ta muka yi. Gaba d'aya muka fito muka taras da ita kwance a k'asa jini na zubar mata." Fuska cike da damuwa hajiya tace, "Kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Fad'uwa tayi kenan? Allah ya bata lafiya alfarmar ubangiji. Kai jama'a ni Mai gado!" Fad'in Hajiya tana da zabga tagumi. Can kuma ta kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Ka d'auke kaje gida ka canzo kaya sai ka dawo. Gaba d'aya jikinka ya b'aci da jini." " _Hajiya_ dan Allah kiyi hak'uri wallahi bazan iya yin ko taku d'aya ba har sai naga halin da baiwar Allah nan take ciki." Kallon Hajiya Barrister yayi tare da fad'in, "No, Hajiya kyale shi bari naje gidan na d'auko masa wasu kayan sai ya canza a cikin office d'insa." "Yauwa Allah yayi maka albarka. Maza je ka d'auko masa." Fad'in Hajiya. Aunty Maryam da aunty Khairat so suke su tambayi wacece babu lafiya, amma babu fuska wajen kowa don kowa cike yake da tashin hankali kar ma ace _Khalil_. Har yaya Barrister ya dawo daga gida ya kawo wa _Khalil_ kaya babu labarin Sarah. Sai da Hajiya tayi jan idanu sannan ya karb'i kayan ya nufi office domin canzawa. Sauri-sauri ya wanke jikinsa sannan ya saka kaya tare da fitowa. Duk k'aunarsa da turare yau ya manta anan saka wani abu wai shi turare a jiki. Nufa k'ofar emergency d'in _Khalil_ yayi gadan-gadan don ya gaji da tsayuwar gawon shanu. "kai! Maza dawo nan ka barsu suyi aikinsu. Idan ma ka shiga, mai za kayi." Fad'in Hajiya. Dawowa _Khalil_ yayi dai-dai lokacin da doctor Kamal shi da doctor Hayat. Da sauri ya nufeso tare da fad'in, "Ina Matata? How is she?" Da mamaki gaba d'aya suke kallonsa sabida Kalmar wife da ya kira don sun san bai da wata mata. Amma sai suka shanye mamakin. Doctor Kamal bai yi magana ba, doctor Hayat ne yace, "She's conscious now, amma tana buk'atar jini sabida ta zubar da jini da yawa. Sannan kuma I'm sorry to say, "She loose the baby. Babu cikin!" Zamewa _Khalil_ yayi ya duk'a a wajen tare da rik'e kansa yana nanata Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! "Kai, dakta mai ke faruwa?" Fad'in Hajiya ganin yanda _Khalil_ ya duk'e tare da kama kai yana salati. Barrister ya soma yi mata bayani don yaji komai, "Hajiya ita uwar ta farfad'o, sai dai tana buk'atar jini sabida ta zubar da jini da yawa, sannan kuma an rasa cikin jikinta." "La haula wala quwata illah billahi. To Allah yasa hakan shine alkhairi. Sai ayi gaggawa bata jinin ko. Amma kai dakta, ka tabbatar ba wani abu tasha ba cikin ya zube?" Fad'in hajiya tana kallon doctor Hayat. Girgiza kai doctor yayi tare da fad'in, "Gaskiya Hajiya babu wani abun da tasha wanda yayi sanadin fitar ciki. Mahaifar dama bata yi wani kwari ba. So sanadin mummunar fad'uwar da tayi ne ya jawo hakan." Dogon ajiye zuciya Hajiya ta sauke, don ta riga ta raya a zuciyarta in dai har zubar da cikin nan aka yi, to fa har abada d'anta ba zai auri Sarah ba ko da kuwa _Khalil_ d'in ne ya zubar da cikin. Mik'ewa _Khalil_ yayi tare da shiga cikin emergency d'in don har a lokacin ba'a fitar da ita zuwa ward ba. Kallonta ya dunga yi ganin lokaci k'ank'ani har tayi wani irin mugun rama tayi haske. Da sauri ya juya ya fita tare da nufa lab domin a d'ibi jininsa don jininsa irin wanda zai iya bawa kowa ne idan aka cire O-negetive. Leda biyu aka d'iba a jikinsa. Tuni har an maida Sarah d'akin hutu an kuma d'aura mata jinin _Khalil_. Lami kuwa da y'ay'anta sai tararrabi akan hukunci da za su yanke ganin cikin jikin Sarah ya zube. Lami kwata-kwata damuwarta ba rashin lafiyar Sarah bane. Damuwarta d'aya kada jin dad'in nan da suka soma samu a jikin _Khalil_ ya yanke sakamakon zubewar cikin jikin Sarah d'in. Sam basu gane yanayin Hajiyar ba, don fuskanta babu yabo kuma babu fallasa. Hajiya bata bar asibitin nan ba, sai da Sarah ta farfad'o sosai har tana ina gane kowa da kowa lokacin har anyi sallar magriba. Amma su Aunty Maryam tuni ya Barrister ya maida su gida sabida girkin da za'a kawo nan asibitin. Ya Abdul-Hakeem ne ya kawo abincin a cikin manya-manyan kula masu matuk'ar tsada sannan ya d'auki Hajiya ya mayar da ta gida. _Khalil_ kuwa sallar magriba ce ta fitar dashi, don tun tuni yana gefen Sarah tana yin motsi yake soma tambayarta ko wani wajen nayi mata ciwo. Sarah kuwa tun da ta samu labarin cikin dake jikinta ya zube, wani irin numfashin rahama da natsuwa ta sauke tana mai godewa ubangiji don ita kad'ai ta san halin da take ciki. Sam bata son shiga cikin sahun y'an uwanta na ajiye d'a ko y'ar shege. "Allah na gode maka da ka cire cikin ta hanyar mafi sauk'i. Allah na gode maka." Duk a cikin zuciya tayi maganar. Baba kuwa na can hankalinsa a tashe jin babu wani feedback game da Sarah. Sai da yayi kamar zai yiwa Aina'u kuka sannan ta kira masa Lami kasancewar shi bai da waya. Shi d'in ma sai da ya bata dubu d'aya sannan ta kira. Bayan sun gama waya da Lami ta fad'a masa halin da ake ciki, sai ya mik'awa Aina'u wayar dake tsaye tana jin matsanaicin farin ciki jin ciki ya zube. "Shegiya! Ai nayi wa kaina alk'awarin sai na raba ki da _Ibrahim_. Wallahi ba zan bari ki shiga gidan na ba. Mayya kawai!" Tana gama fad'in haka ta juya ta fice daga d'akin tare da komawa nasu d'akin ta kwanta a kan gado tare da jawo ledar tsire mai kulin da ta siya ta hau jefawa a baki tana tauna tana lumshe idanu. A can asibiti kuwa, wajajen k'arfe tara da rabi, bayan su Lami sun gana hani'an da abincin da Hajiya ta saka su aunty Maryam suka yi, sai _Khalil_ yace masu ya kamata su tashi ya kai su gida, don mutum d'aya aka amince ya kwana da majinyaci. "Lami tunda ga yara a gida, ku tafi kawai ke da Nuratu, ni zan kwana anan da ita." Lami ji tayi kamar ta shak'o Na'ima, amma jin abunda _Khalil_ yace sai tayi shuru. "Eh hakane. Mama ke ki koma gida, ita sai ta kwana da itan. Idan yaso gobe sai ku dawo da safe. Dare nayi. Muje na sauke ku a gida." Fita Lami tayi ba tare da ta k'ara cewa komai ba. Don gani take kamar wani abun dad'in Na'ima zata ci idan ta tafi. Ko kuma _Khalil_ d'in yayi mata wani kyauta. Har gida ya sauke su tare da shiga wajen Baba ya kwantar masa da hankali tare da shaida masa in Sha Allah nan da wasu y'an kwanaki Sarah zata warware. Hajiya tana isa gida ta d'aga waya ta kiran number d'in ya Abdullah. Kamar kullum ya yanke kiran tare da kiranta. "Assalamu alaikum, marmari sai kaji abunda ya faru ko?" Fad'in Hajiya. "Wa'alaikissalam, Muhammad Kabir ya kira ni ya fad'a min komai, amma Hajiya an tabbatar da a asibitin ba wani abu tasha ba? Don jiya kamun na bar Kaduna sai da na wakilta wad'anda zasu min bincike yarinyar. Kuma binciken ya iske ni tun a jiyan. Hajiya maganar dai babu dad'in ji, don sai da nayi dana sanin amincewa da wannan maganar auren. Don fisabilillahi gaba gidan tun daga kan uwarsu babu tarbiya. Dama-dama ita yarinyar ma, an samu mutane hud'u zuwa biyar da suka yabi halinta." Shuru hajiya tayi tana sauraran ya Abdullah kamun tace, "To marmari ya za muyi, _Khali_ dai ya riga ya jawo mana magana. Tunda har yaji ya gani, kuma ita yarinyar ta samu shaida ko yaya ne, hakanan za muyi hak'uri ayi auren kawai don nan gaba bamu san wani irin magana zai je ya d'auko mana ba. Kuma maganar ciki, dagaske b'ari tayi amma ba ta hanyar shan magani ba. Allah ne ya kawo hakan ta sanadin fad'uwa da tayi." Ajiyar zuciya ya Abdullah yayi tare da fad'in, "To shikenan Hajiya. Tun da har hakan ya kasance, ba sai an d'au wani dogon lokaci ba, da zarar Yarinyar taji sauk'i, zan zo Kaduna sai muyi magana dasu uncle Ridwan sai aje a kai kud'in auren." "Kaga inda matsalar take kenan. Allah yasa dai kar su tada k'ananun maganganu dai!" Fad'in Hajiya, "Ki kwantar da hankalinki, in Sha Allah baza a samu matsala ba." "To Allah yasa!" Fad'in Hajiya. A can asibiti kuwa, sai da gaba d'aya nurses suka fahimci Sarah budurwar _Khalil_ ce sabida yanda yake nan-nan da ita. Kwanan Sarah uku a asibiti, amma ko sau d'aya Aina'u bata tab'a zuwa dubata ba. A asibitin nan kuwa, wani irin soyayya ce da shak'uwa mai zafi ta shiga tsakanin Sarah da _Khalil_ ta yanda har idan bata ganshi ba, ta dunga kallo agogo tana kuma duban hanya. Da taji motsin bud'e k'ofa take saurin kai idanunta wajen. Satinta biyu aka sallameta, baza ka tab'a cewa daga ciwo ta tashi ba sabida wani irin haske da kyau har da d'an k'iba da ta k'ara. Cike da murya da farin ciki ta isa d'akin Baba tana mai jin kewarsa. Abunda ya bata mamaki ganin Baba a tsaye babu sandar da yake dogarawa. Da mamaki take kallon Baba har da zagaya shi. Dariya yayi tare da fad'in, "Bar mamaki Sarah, mahaifinkin ne dai a tsaye gabanki. Kin ga ikon ubangiji ko? Allah dai ya yiwa _Ibrahim_ albarka domin shi ya zo ya d'auke ni ya kai nj asibitinsa na k'ashi aka duba k'afata. Kuma har gida kullum ake zuwa ana min gashi. Kuma Alhamdulillah k'afar ta soma warkewa don yanzu haka zan iya zagaye tsakar gidan nan babu sanda." Da matsanaicin farin ciki Sarah ta soma fad'in, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!!, Allah mun gode maka. Baba Ashe zaka samu lafiya? Kai Alhamdulillah." Baba yace, "Ki godewa ubangiji sannan ki godewa _Ibrahim_ Saratu. Domin sanadinsa ne kika ganni a haka yau a gabanki. Saratu don girman Allah, kiyiwa yaron nan biyayya, babu abunda za kiyi ki b'ata min rai Sarah kamar ki k'i yin zaman lafiya dashi. Hakan zai b'ata min rai kuma zan rik'e ki a zuciya domin yaron nan ya gama yi mana dukkan alkhairi shi da iyayensa." Sarah wani irin matsanaicin soyayyar _Khalil_ ne taji yana hud'a ko wani sak'o da lungu na zuciyarta. D'ukawa tayi tare da fad'in, "Baba nayi maka wannan alk'awarin na zama da _Khalil_ da zuciya d'aya, kuma ko da sab'ani ya shiga tsakanin mu wata rana, ba zan tab'a juya masa baya ba. Kuma ba zan tab'a rabuwa dashi ba har sai idan shine ga gaji da zama dani." "Allah yayi maki albarka Saratu. Allah yasa auren da za kuyi mutuwa ce zata raba shi." Sai da Sarah ta saka gyale ta rufe fuskanta sannan tace, "Ameen" tare da mik'ewa ta fita daga d'akin ta koma nasu d'akinsu ta d'auko wannan turaren da _Khalil_ ya bata tare da fesawa sosai sannan ta canza hijjab ta saka wani don a waje suka bar _Khalil_ d'in. Sarah tayi alk'awarin yau zata bayyanawa _Khalil_ baki da baki cewar tana sonsa. A tsaye a k'ofar gidan ta same sa yayi folding hannunsa yana kallon k'ofar gidan. Tana fitowa ya saki ajiyar zuciya tare da fad'in, "Har na k'agu ki fito." Murmushi tayi tare da fad'in, "To ba yanzu muka rabu ba." "To ba kece kika ce kar na wuce na jira ki ba. Na k'agu inji mai zaki fad'a min." Murmushi ta k'ara yi karo na biyu tare da fad'in, "Wai sanyi kake ji?" Harararta yayi tare da fad'in, "K'arshen sanyi, a Atlanta nake." Dariya ta saki wanda ya k'ara bayyanar da bayyannar kyawunta, gaba d'aya kumatunta sai da suka lob'a. "Ban da Allahn musuru, amma ina ji a jikina da d'a ko y'ata ya fito duniya, da dake zai yi kama sak. Ke kyakkwa ce." Rufe fuska tayi da hijjab d'inta tare da fad'in, "Har na kai ka kyau? Kai fa kama kake min da wannan matashin kudancin indian _Ram Charan_" waro idanu _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Haba dai! Ke kuma kin san dawa kike kama, _Aishwarya Rai_, wallahi kin ma fita kyau." Rufe baki Sarah tayi tare da fad'in, "Kar ka yarda Na'ima taji, don ita ce aka cewa suna kama da Aishwarya." "Wa, to ai kin fita kyau wallahi." Dariya tayi tare da fad'in, "Beauty is in the eyes of the beholder." "Eh d'in naji, ko ma dai menene, ke d'in kyakkyawa ce kuma ta musamman. Wani albishir za'a fad'a min ne aka hana ni tafiya gida." Sai da Sarah tayi farr da idanu sannan tace, "Abunda kake muradin ji kullum daga baki na kuma fuska da fuska." Gyara tsayuwa yayi tare da fiddo wayarshi ya danna recording ba tare da ta san me yayi ba. "Gwara in gyara tsayuwa da kyau kar inzo in fad'i in suma don dad'i." Dariya tayi tare da fad'in, "Ba zan bari ka kai k'asa ba zan taro ka. Idan har ina waje, baza ka tab'a fad'uwa ba in Sha Allah!" Da mamaki yake kallonta don bai tab'a tsammani zata iya magana haka ba. "Yanzu kina da k'arfi taro ni?" Ya tambaya yana mata gwalo. "Ba da k'arfin cin tuwo zan rik'o ka ba, zuciyata ce zata rik'o ka. Ka manta kai da kanka ka fad'a an halicceni ne domin kai, kuma kai ma an halicceka ne domin ni? To ai zuciyoyinsu a had'e suke kuma tare suke bugawa kuma gangan jikinmu a tare suke sarrafuwa, sabida haka d'aya ba zai tab'a barin d'aya ya fad'i ba. Ka saka hakan a ranka." Mutuwar tsaye _Khalil_ yayi yana jin maganganunta na shiga ko wani sak'o da lungu na jikinsa har sai da tsikar jikinsa ya tashi. Wani irin kallon k'auna ya dunga binta dashi kamar zai had'iyeta. "Ina sonka _Khalilullah_, Ina k'aunarka har cikin zuciyata." Dum yaji wani abu kamar guduma ya bugi dodon kunnensa, wani irin shauk'i na mamaye ilahirin jikinsa. Ji yake dama yana da dama da jawota zai yi jikinsa ya rungume sosai. Aina'u dake lab'e jikin k'ofa tana sauraransu, don tun lokacin da Sarah ta fita ta biyota a baya. Wasu irin ruwan hawaye ne ke gudu a fuskanta. Ji take kamar ta koma cikin gida da gudu ta d'auko kaifaffiyar wuk'a ta soki zuciyar Sarah dashi ta tafi ta bar duniyar. "Sarah, nagode ba wannan alfarma da kika min na sanya ni cikin zuciyarki da kuma bani damar kasancewa dake har mutuwa. Ina so ki sani, zan killaceki a nan, (yayi nuni da zuciyarsa), ba zan tab'a bari kiyi hawayen bak'in ciki ba, idan har za kiyi hawaye, to na farin cikine, nayi maki wannan alk'awarin. Zamu dunk'ule mu zama d'aya Sarah. Zan tarairayeki ta yanda ko bugun zuciya mai k'arfi bazan bari kiyi ba. Zan kula dake fiye da yanda ake ririta kwai. Zan mayar dake sarauniya, sannan in kasance bawanki. Sarah baki ba zai iya musulta yanda zanji dake ba. Allah ya nuna min ranar da zan mallakeki matsayin mata. Wannan ranar kawai nake jira. Zan gwada maki practically abunda ake nufi da k'auna. In Sha ni da ke, _couples for eternity_ ne. Rayuwar aurena dake, babu condition Sarah, unconditional love nake maki Sarah. Ko da zaki zama mara k'afa da hannu, soyayyarki baza ta tab'a canzawa ba a gare ni. Allah yayi mana jagora." Hawayen farin ciki kawai Sarah take yi, bata tab'a tunani ko cikin mafarki akwai wanda zai iya fad'a mata wad'annan kalaman ba. Ashe dai ita ma za tayi farin ciki a rayuwa. "Wallahi idan har ina da rai, ni Aina'u ba zan tab'a bari alk'awarin daka d'auka ya zama cikakke ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login