Showing 108001 words to 111000 words out of 129558 words

Chapter 37 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

uban wanene kuwa!" Da sauri Khalil ya ce, "Aina'u......" "Don as I said!" Ta katse shi da ?arfi. Juyawa yayi ya kalli Sarah tare da nuna mata ?ofa yace, "Get out of this house right now, and don't forget to go with your kids!" Hawaye kawai Sarah keyi tana kallonsa, irin kallon kar kayi min haka. Juya baya yayi yana hawaye gabansa na wani irin faWuwa. Sarah kuwa wani irin kuka ne ya kufce mata, da sauri ta ?arisa kusa dashi ta Wuka tare da ri?e ?afafunsa ta shiga faWin, "Happiness, Kar Kayi min haka, ka manta al?awarin da kayi min? Ka manta kace min zamu kasance tare, for better for worse, ka mance kace baza ka taSa bari nayi hawayen ba?in ciki ba, ka manta kace an halicceni ne domin ka, kai ma Kuma an halicce ka ne domin ni? Ka dubi girman Allah ko don Sam'an da Sauban ka barni a Wakin mijina." Da ?arfi Aina'u tace, "Capital NO! You're more welcome. Park your things and get lost!" "Da mijina nake magana ba dake ba Aina'u!" Sarah ta faWi da ?arfi. Wani shu'umin murmushi Aina'u tayi tare da faWin, "To ai shi kansa mijin da umarnina yake amfani. Ko baki san ni nace ya kore ki ba?" Sarah bata bata amsa ba ta cigaba da yiwa Khalil magiya. Tureta Khalil yayi tare da faWin, "Please Sarah, don't make things worse, just do as I said." Yana gama faWin haka ya tashi ya fita. Aina'u sai da tayi mata gwalo sannan ta fice daga Wakin, "Sarah ki tashi kawai ki tafi kar ?ar iskan nan ta saka Khalil ya yanke igiyoyin aurenki dake kansa." Wata zuciyar ta faWa mata haka. Da sauri ta tattare kayan ta zuba a akwati ta zuge zip tare da saka hijjab sannan ta jawo akwatin zuwa parlour ta Wauki Sam'an ta ri?e Sauban kuma ta goya shi, sai da ta ?arewa parlourn kallo sannan ta murWa handle ta fita tana kuka, tana zuwan wajen gate, kamar ance ta juyo, sai ta ganshi a bayanta yana hawaye, buWe hannunta yayi tare da saka mata Atm card Winsa tare da faWin, "Current account, date of birth Winki ne pin Win. Ki kular min da kanki da yaranmu." Caraf Sarah ta rike hannun tana kuka tana girgiza masa kai, shima hawayen yake yi tare da ?o?arin kwatar hannunsa, da kyar ya zame hannun tare da yiwa Sam'an kiss a goshi yace, "I'm going to miss you son, ku tayani neman gafarar mummynku." Yana gama faWin haka ya juya da sauri. Kuka sosai Sarah tayi ta rusawa kamun ta juya tare da jan akwatin suka fice daga gidan..........


( _Wannan scene Win ya taSa min Heart =?-? da gaskiyar Sarah da tace Aina'u ?ar wuta ce_)

*Kuyi ha?uri da rashin ganin update jiya, transformer Win mu ce ta buga*



*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*





*_MATAR SAYYADEE_*

*Paid book 08128755583*
>؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*34*


Sai da ta juyo ta kuma ?arewa gidan kallo sannan ta soma tafiya tana hawaye, kasancewar gidan babu nisa da bakin titi nan da nan ta iso bakin titin tana nishi don ba ?aramin kaya bane a cikin akwatin har da atamfofinta na lefe kusan kala ashirin a ciki wanda ba'a Winka ba, don ta kwashe wasu ta saka cikin wardrobe da kuma wasu akwatinan don da ma?il yake da kaya, yanzu kuma ga kayanta dana su Sauban a ciki sannan kuma ga goyo ga kuma Sam'an dake hannu. Tsaye tayi a bakin titin tana tunanin inda zata, don ji tayi gaba Waya bata ?aunar komawa gidansu, gashi kuma babu wani wajen da take dashi da zata je. "Lafiya state!" Ta faWi a bayyane tare da saurin nufa wani shagon pos dake bakin titin ta ciri dubu hamsin tana yin hamdala a zuciya saboda taimakonta da Allah yayi wajen sa Khalil Win ya kawo mata ATMcard Winsa da yanzu bata san yanda za tayi ba don ita bata samu sararin da ta Wauko nata ATM Win ba da kuma kuWinta da take ajiye a Wakin duk lokacin da Khalil Win yayi mata kyauta. Napep ta tsayar tace masa tashar kawo ze kaita, shi dakansa ya fito ya saka mata akwatin a ciki sannan ta shiga, har cikin tashar ya kaita tare da fiddo mata da kayanta sannan ta biya shi hakkinsa ta ja akwatin ta soma tafiya, nan da nan aka soma tambayarta inda zata, "Nasarawa zani!" Da sauri wani tsoho a ciki yace, "Taho nan muje dama ke kawai muke jira motar ta cika." Hamdala tayi cikin zuciyarta jin saura mutun Waya, don ta bala'in ?osawa ta bar kaduna. Bayan kowa ya bada kuWin mota tare da rubuta address da number waya da suna sannan driver yaja motar suka Wau hanya. Sai da suka hau hanya sosai sannan gabanta ya hau faWuwa kasancewar bata taSa zuwa ba, sunan garin da unguwan kawai take ji a bakin baba, ga kuma ?an biyu da suke ta yi mata kuka a cikin motar, sai wajajen ?arfe biyar suka isa, daga nan ta ro?i mai motar akan y taimaka mata wanba zata kuma bata san garin ba, nan ya sakata a motar wamba, ko da suka isa wamba, da tambaya aka kawota layin abakwa da take ji baba Nuhu na yawan ambata matsayin layinsu. Kalle-kalle kawai take yi ta rasa inda zata nufa, gashi isha'i ake neman yi don garin ya soma duhu, wajen wani gindin bishiya ta nufa inda ta hango dattijai su bakwai a zaune a kan tabarma, da kyar take tafiya, Sauban yayi bacci a bayanta, Sam'an shima haka sagale a kafaWanta, ga kuma ?atuwar akwati tana ja. Har ?asa ta Wuka bayan tayi sallama sun amsa mata, sai duk suka zuba mata idanu suna kallonta da mamaki, gashi dai bata yi kama da mabaraciya ba balle suyi tunanin bara tazo yi. "Sannunku da hutawa baba, Ina wuni?" FaWin Sarah, sai gaba Waya suka amsa mata da "Lafiya ?alau." Cikin gurSatacciyar hausarsu. "Baba dan Allah tambaya nake yi, ina neman gidan wani ana ce masa Nuhu, amma ya jima da barin garin nan." Kallo-kallo suka shiga yi, can kuma Waya daga ciki yayi wa na kusa dashi magana a kunne, sai wanda aka yiwa maganar a kunne yace, "Nuhu? Shekarunsa nawa da barin nan, kuma kin tabbata Wan nan Win ne?" Shuru Sarah tayi na ?an wasu da?i?u kamun tace, "Eh to, a yanda dai yake bamu labari ya tabbatar mana dashi haifaffan nan ne, kuma yace sunan unguwarmu layin abakwa, sunan mahaifinsa Murtala, mahaifiyarsa kuma Zainabu! Sannan kuma ya bar garin nan shekaru talatin da huWu kenan, ya bar garin ne saboda ?an uwansa basu so ya auri budurwar da yake so kasancewar ta kirista mai suna Elizabeth ana yi mata inkiya da (Lami)." Gaba Waya wajen suka Wauka da faWin, "La'ilaha illalah Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama! Wannan ai Nuhu na wajen mu take magana a kai!" ?aya daga cikinsu ya ?arisa maganar da faWin haka. "Ke yarinya ya kuke dashi?" Tun kamun tayi magana wanda ke Wan gab da ita yace, "Tun da yarinyar ta Wuka anan nake kallon fuskanta, babu hoton wanda na gani a kwance a fuskanta sai na Wan uwana Nuhu." Ya ?arisa maganar yana share guntun hawaye. "?arsa ce ni!" Sarah ta faWi muryanta na cracking. Su uku dake wajen suka mi?e a tare tare da faWin, "Taso yarinya, gida kika zo, duk nan iyayenki ne." Wani irin sanyi da salama Sarah taji yana shiga jikinta. Mi?ewa tayi ta soma bin bayansu kasancewar Wayan ya Wauki akwatin yayi gaba, sai ya kasance yaran ne kawai a hannunta da ?aramin handbag Win da ta saya a lokacin da suka sauka. ?atoton gidane irin na da Win nan wanda aka yi sa da ginin ?asa, sai dai yasha gyara da abubuwan zamani, kuma akwai wasu gina-gine guda biyu a tsakiyar gidan da aka yi su da cement blocks. ?aya daga cikin ginin bulo suka nufa mai kyau dashi, Sarah sai kalle-kalle take yi hannunta dafe da bayan Sam'an dake kwance a kafaWanta. Hannu ya saka ya murWa handle Win ?ofar tare da yin sallama sannan ya shiga. Babu kowa a parlourn sai fankar sama dake gudu sosai. "Zauna mana, suna cikine, bari na kira su." Ya faWi hakan yana mai nuna mata kujera sannan ya bi wani Wan dogon hanya a parlourn. Sarah kuwa kamun ta zauna sai da ta gama ?arewa tsaftaccen parlourn mai Wauke da set Win kujeru da kuma Tv bango 32 inches da idanu sannan ta shimfiWar da Sam'an a kan 3sitter tare da kwanto Sauban sannan ta zauna ta rungumesa tana cigaba da ?arewa parlourn kallo har idanunta suka sauka akan wani ?atoton hoto a jikin bangon Waki ta bangon arewa, ?urawa hoton idanun tayi duk da kuwa irin Black and White Win nan ne, su huWu ne reras a jikin hoton, waro idanu tayi sosai tana ?ara kallon hoton da kyau, baba Nuhu ne zaune a kan wata farar kujeran ?arfe shigen irin ta sarauta, sai wani ta gefen hagunsa mai irin kamanninsa babu bambanci yana murmushi sannan ya dafa mai kama dashi sak Win nan dake zaune a kan kujera, sai wannan mutumin da ya kawota cikin Wakin da take yanzu a ta gefen wanda ya dafa baba Nuhu ya Wan le?o shima yana murmushi, sai shima mai kama dashi sak ta hannun damar wanda ke zaune a kan kujera ya turo hulan kansa gaba tulun gashin da ya tara ya fito ta baya da kuma gefe-gefe kansa stil shima yana murmushi, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, kaii! Kenan da baba da wannan mai kama dashi Win ?an biyu ne, shima kuma wannan da ya kawo ni nan shima Win ?an biyune kenan? Kenan anan nayi gadon ?an biyu, ikon Allah!" Cike da tsantsan mamaki tayi maganar a bayyane. Daga ?arshe sai ta tashi ta isa wajen hoton tana kallo daga tsaye. Da wani irin ihuu da murna taji an rungumeta ta baya, da sauri ta waigo tana mai cin karo da fuskan wata kyakkyawar yarinya mai kama da ita, gaba Wayansu waro idanu suka yi suna mai shafa fuskansu suna kuma dariya at the same time, "Sunana Suhana, yarinyar wannan dake zaune a hotonan!" Suhana ta faWi tana mai nuna hoton wanda ke zaune, don ita Sarah a tunaninta ma shine baba Nuhu, sai Suhana ta nuna shi matsayin mahaifinta, sai ta fahimci baba Nuhu shine na tsayan. "Abbana da Abbanki are twins!" Suhana ta kuma faWi tana dariya tare da kamo hannun Sarah wacce ke ta kallon fuskar Suhana kuma murmushi ya?i barin fuskanta. "Uwar surutu, kin tsareta da surutun ko? Ai sai ki wuce ki haWa mata ruwan zafi a bayi tayi wanka taji daWin jikinta sai taci abinci." FaWin wannan da ya kawo ta cikin gidan cikin yaren _Nindire_, bayansa kuma wata kyakkyawar mata ce mai fara'a sosai, ha?orinta guda Waya na gefen dama na Makka ne sai kyalli yake yi. "Wallahi ga kama nan, ai surprise zamu bawa su Ya Hassan da Nnanne, sai da safe tukun duk zasu ganta." FaWin matar tana kallon Suhana tare da faWin, "Saura kuma kije ki faWa masu, don na sanki da tsinannan surutu!" Turo baki Suhan tayi tare da faWin, "kaji ta ko Ba Lukman!" Da sauri Sarah ta kalli wanda Suhan Win ta kira da Ba Lukman tana murmushi gano ashe wanta Lukman sunan wannan Win baba ya saka masa. "Baki faWa mana sunanki ba yarinya!" FaWin Ba Lukman. Sunkuyar da kai Sarah tayi tare da faWin, "Sunana Saratu!" Da sauri ba Lukman yace, "Kai! Kai!! Kai!!! Suna mai girma da daraja Nuhu ya saka maki, ai sunan wacce ta ri?e mu duka kenan har shi bayan mutuwar mahaifiyarmu, kuma ita Win ?anwace ga mahaifiyarmu uwa Waya uba Waya." Murmushi Sarah tayi yayin da matar Ba Lukman ta nufi inda twins suke tana kallonsu, "Tubarkalla ma sha Allah! Kaga ?a?a kyawawa kamar su suka yi kansu, ni wannan ma ai sun fiku nuna kamanni, taS! Zan iya bambance su kuwa?" Ta faWi cikin yare, Sarah da bata jin ko zo in kashe ka, sai binsu da idanu take yi. Ba Lukman ma ?arisawa kusa dasu yayi yana kallonsu cike da ?aunarsu daidai lokacin da Sauban ya farka yana mai furta, "Mummyyyy, I want to piii." Ko kamun tayi wani motsi har Suhana ta isa wajen tare da sunkutoshi, shi kuwa bai mata ?iwa ba, don suna matukar kama da Sarah shiyasa bai gane ba Sarah bace ta Wauke shi, po ta Wauko wankakke tas kamar ba'a komai a ciki ta Waurasa a kai, tana kallon fuskansa, "Momma, har da pupu zan yi!" Dariya Suhana tayi tare da faWin, "To kayi!" Kallonta Sauban yayi ta yi kamar yana so ya gano ba mummynsa bace, sai da ya gama kashin ta wanke masa, wajen mayar masa da wando suka soma faWa don ya?i sam ya mayar da wandon, daga ?arshe sai ya lankwashe ?afar yana kuka, le?owa Suhana tayi tare da faWin, "Ya?i yarda in mayar masa da wando." Sarah nufar akwatinsu tayi ta kwantar tare da fiddo masa wani wandon ta mi?awa Suhan tana mai faWin, "Ai su haka suke, idan suka yi pupu basu taSa yarda su mayar da wandon jikinsu sai dai wani." "Yaran nawa ashe ?an gayu ne!" FaWin Suhana bayan ta karSi wandon. "Saratu ki shiga wancen bayin kiyi wanka sai kizo kici abinci." Kai sunkuye Sarah tace, "To Baba!" Ta ?arisa maganar tare da cire hijjab Win jikinta ta ninke ta ajiye a hannun kujera sannan ta nufi bayi. Suhana na dawowa parlourn Sam'an shima ya tashi, sai ta haWa su ta rungume duka a jikinta. Bayan Sarah ta fito daga wanka, sai Suhana ta nuna mata Wakin da zata shiga domin tayi shiri ita kuma ta nufi bayi da twins domin yi masu wanka. Sarah tana shiga Wakin, ko mai bata shafa ba, riga kawai ta zura tare shimfiWa dardumar da ta gani a gefen gado tare shimfiWawa ta saka hijjab ta tada sallah, sai da tayi na magrib da isha sannan ta kuma tada sallah tayi raka'a biyu, a sujadarta na ?arshe ta shiga kwararo bukatun tana kuka sosai. Ta jima a sujada tana kai kukanta ga mahaliccinta......



_Anticipate a long page tomorrow, wallahi har yanzu ban jin daWi, Wannan ma dakyar nayi_




*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*

_MATAR SAYYADEE_






>؜? *KANWAR MATATA*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login