Showing 48001 words to 51000 words out of 129558 words

Chapter 17 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

irin makeken gado haka!" Ta fad'i hakan tare da hawa kan gadon tana shafawa. "It's a long story Munee, naji dad'i da Baba yaje yayiwa babanku magana don wallahi ke kad'ai ce k'awata a duniya gashi kuma d'azu muka gama waya dashi akan zai zo ya sallami k'awayen amarya." Saukowa Munee tayi tare da fad'in, "K'awata wa kika kamo haka? Kwanaki nake ta jin rumours wai kin yi cikin Shege Farouq ya fasa auranki. Ni ina jin maganar ta shiga kunnan hagu ta fita ta dama. Kuma kin san wake fad'awa mutane? Aina'u fa!" Tab'e baki Sarah tayi tare da fad'in, "Uhm, kyaleta. Kin san su suna goyon bayan Lami ne, basu son inyi aure. Ni kuwa zaman mai zan yi a gidan. Ai gwara na tafi nawa gidan nayi bautar ubangiji." Hannu Munee ta bawa Sarah suka kashe sannan tace, "K'awata kenan! To shi angon naki a ina yake." Gyara zama Sarah tayi ta d'an bata labarin in brief saboda ciki ba don abinci kawai aka yisa ba, duk da kuwa ta yarda da Muneeban. "K'awata na taya ki murna wallahi. Allah ubangiji ya sa mijinki ne ya kuma baku zaman lafiya mai d'orewa." "Ameen k'awar arziki." Daga nan suka fad'a hirar yaushe gamo har har lokacin da _Khalil_ yayi kiran Sarah a waya ya shaida mata yana waje. Tare suka fita da Muneeba zuwa wajen _Khalil_ d'in. Lokacin da Muneeba tayi arba da _Khalil_ rud'ewa tayi don b'ata tab'a hasaso haka yake ba. "Wannan itace k'awar tamu?" Fad'in _Khalil_ yana murmushi don tsabar rud'ewa Muneeba ta kasa gaishe shi har sai da Sarah ta d'an tsunguleta a cinya sannan ta dawo hayyacinta. "Kamar mai asibitin _Khalilullah specialist hospital_ ko? Ka tab'a duba ni sau d'aya a asibitin ka." Dariya yayi tare da fad'in, "K'aninsa ne, ba shi bane." Ya k'arisa maganar yana mai kashewa Sarah idanu. Dariya Sarah tayi tana kallon Muneeba dake masa anya kuwa. "Gaskiya kamannin sun b'aci. Kai ne mijin k'awar tawa kenan?" "In Sha Allah!" _Khalil_ yayi saurin fad'in. "Ma sha Allah! To bud'e kunnuwanka da kyau zan baka amana." Hannu biyu _Khalil_ ya saka ya rik'e kunnuwan nasa tare da fad'in, "Ina jinki k'anwarmu." Dariya Sarah ta kwashe dashi ganin yanda yayi tare da bada full attention d'insa wa Muneeba. "Wannan k'awata ce kuma aminiyata. A yau karo ba farko ina mai damk'a amanarta a hannunka, kar inji ko a cikin mafarkina tana kuka, idan ma za tayi, to ya kasance na farin ciki. Sannan a rik'a lallab'ata kamar kwai. Baka da matsala in dai aka zo fannin biyayya, don k'awata akwai biyayya kuma na tabbata za tayi maka biyayya. Yi, nayi, bari, na bari. Duk zata kiyaye su. Kai ne babba, key na controlling gidanka yana hannunka, Sarah kamar motarka ce, duk inda ka nufa da ita, nan zata bi. Saboda haka, dan girman Allah, kar inji Sarah tayi kuka da kai." Sosai _Khalil_ yaji Munee ta kwanta masa a rai. Murmushi yayi tare da fad'in, "An gama aunty Muneeba. Hud'ubarki ta shiga sosai." Juyawa tayi ta kalli Sarah tare da fad'in, "K'awata na dawo kanki, kin ga, wallahi kiyi masa biyayya domin aljannarki na k'ark'ashin k'afarsa. Idan ya take, sunanki sorry, don haka kema kar inji yayi kuka dake. Irin tarairayan duk ki rik'a masa. Kamar irinsu, Gwandi, zaka sha gwanda, honey zaka sha Honey, Sweety zaka sha swee....." Kamun ta k'arisa cewa sweet d'in daga _Khalil_ har Sarah suka fashe da dariya. Ita kanta Muneebar dariyar take yi. "Gaskiya k'awar mu naji dad'in wannan hud'uba naki. Mun gode Allah ya saka da alkhairi kuma mun d'auka." Murmushi a fuskanta tana mai taya k'awarta farin cikin samun miji kamar _Khalil_ tace, "To ma Sha Allah. Haka nake so ai." Gyara tsayuwa _Khalil_ yayi tare da fad'in, "To yanzu wani shirye-shirye kuka tsara ta wajenku?" Kallon Sarah Munee tayi sai kuma ta kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Gaskiya ta wajen mu, walima kawai za muyi da k'awayen mu na makaranta da kuma mutanan anguwa. Ko ya kika ce k'awata?" Ta k'arisa maganar tana kallon Sarah. Gyad'a mata kai Sarah tayi tare da fad'in, "Eh hakane." "To ustazai. Ni dai abokaina sun had'a min dinner. Don haka bayan an d'aura aure akwai dinner sai ku kasance cikin shiri. Allah yasa k'awar tamu tana da account?" Ya k'arisa maganar yana kallon Munee. "Eh ina da shi." Fad'in Munee. Fiddo wayarsa yayi tare da fad'in, "Fad'a min account number d'in." Bayan ta fad'a masa da sunan bank d'in, a take yayi mata transfer d'in 500k. Waro idanu Munee tayi lokacin da tayi arba da kud'in da ya turo don har sai da ta murza idanu. Tun da take kud'i dubu ashirin ma basu tab'a zama cikin account d'inta ba ko da mistake, sai ga dubu d'ari biyar sun shigo yau. "Wad'annan kud'in fa? Wallahi sun yi yawa. Duk na minene haka." "Duk na walimar ce." Ya fad'a kai tsaye. "Dan Allah sunyi yawa wallahi." With serious face yace, "Basu yi ba. Kuma kar ki sake magana. Kuje kuyi duk wani hidimar da za kuyi dasu. And in Sha Allah two days before the wedding za'a kawo maku raguna guda uku da drinks. Yanzu haka ma idan kun koma gida kuyi list d'in duk wani abubuwan da zaku buk'ata sai ku turo min." Gaba d'aya Muneeba is speechless. Sai gyad'a kai kawai take yi. B'ata tab'a yin y'an matan amare ba, amma ta sha gani da ji, wani lokacin ma da fad'a ake k'arewa da abokan angon domin wasu dakyar suke fitar goma zuwa sha biyar. "Bari na baku waje, sai kin shigo k'awata." Fad'in Muneeba. "To k'awarmu, mun gode sai ta shigo tunda ni baza amin sallamar ba." Dariya Muneeba tayi tare da fad'in, "Sai da safe asha soyayya lafiya." Tana gama fad'in haka ta shige gida tana dariya. Sun jima a waje suna hirar su ta soyayya, sai da zai wuce yake fad'a mata ta fad'a a gida gobe za'a kawo akwati. Tana shigowa gida ta nufi d'akin Baba kai tsaye ta fad'a masa sak'on _Khalil_ shi kuma ya cire dubu hamsin a cikin kud'in da _Khalil_ ke basa idan yazo gaishe sa yace taje gidan su Muneeba ta kaiwa mahaifiyarta ayi y'an soye-soyen fulawa da kuma kaji. Sannan ya ware wasu kud'i ya ajiye wanda idan y'an kawo kaya sunzo a basu tukwuici. Da Muneeba zata wuce gida tare suka tafi wajen mahaifiyarta tayi mata bayanin sak'on da Baba ya turo ta ta fad'i. Hannu biyu Mama ta karb'a har ta bada sautu saboda a sayo komai da wuri kasancewar gobe bak'in za suzo. Anan ne kuma Sarah da Muneeba suka fad'a mata yanda suka yi da _Khalil_ game da walimar da za suyi da kuma kud'in da ya turo. Ita kanta mama tayi mamakin kud'in, amma da taji anan mahaifin _Khalil_, sai mamakin ya sake ta don ta san irin kud'in da suke dashi. Mama tambayar Sarah tayi shin akwai wani gyara ne da ake mata na jiki a gida, sai Sarah ta fad'a mata babu abunda ake mata. A take mama ta kira waya aka turo mata number d'in wata kwararriyar mai gyaran jiki da yake tana home service. Cikin awa d'aya ta iso da duka kayan gyaran jiki. A cikin kud'in _Khalil_ da ya turo aka tura mata 200k domin soma fara yiwa Sarah gyaran jiki daga yau da daddare. Ai kuwa na dare d'aya tal sai da Sarah ta tabbatar an soma gyara jikinta. Baba da kansa yaje har d'akin Lami ya shaida mata y'an kawo akwati za su zo, sai da tayi masa kallon sama da k'asa tukun sannan tace, "To wata uwar zan yi masu da kazo ka tsaya min a kai?" Murmushi kawai baba yayi tare da juyawa ya koma d'aki don dama yaji a jikinsa babu wani abu da Lami za tayi shi yasa ma ya tura Sarah can gidan su Muneeba. Na'ima ce ta kalli Lami tare da fad'in, "Gaskiya Lami ba haka ake yi ba. Idan fa za'a kawo akwati, dangin amaryar sha tara na arziki suke yiwa dangin ango kamar irin su soye-soyen kaji, su meatpie, samosa, spring rolls da sauraransu har da tukwuicin kud'i. Kuma ni ina ji a jikina ba k'aramin kaya za'a kawo wa Sarah ba." Harara Aina'u ta makawa Na'ima tare da fad'in, "Munafuki annamimiya!" A cikin zuciyarta. Amma a zahiri sai cewa tayi, "Wallahi Lami kar kiyi komai. Kin san halin masu kud'in nan da shegen raini da d'aga kai kamar dan su Allah yayi duniyar." Da sauri Na'ima tace "Ke dai Aina'u annamimiya ce. Idan baza ki kashe wuta ba, to kar ma ki soma hurawa. Shegiya gwara dai ki fito da naki nashinshinin bar yiwa wata hassada. Ko sau d'aya bam tab'a jin wani yazo yana sallama dake ba." A fusace Lami tace, "Wannan wani irin maganar banza ce haka Na'ima? Ban so! Kar ki kuma yi mata irin wannan maganar. Ni kaf y'ay'ana babu wanda bai da farin jini. Farin jini a nono na kuka tsotsa." A fusace Aina'u tace, "Ni ko mai zan yiwa Hassana a jikin wannan banzan da zata aure! Allah ya kiyaye in auri wanda zan zama baiwarsa. Ai duk wata shegiyar da tayi aure ta san inda ta kai kanta. Daga wanke min kayana, dafa min abinci sai goge min takalmi. Sannan idan dare yayi ya kwashi romon albarkan jikin banza a banza ya tashi ya kakkab'e jikinsa kuma ba shi zai hana gobe yayi maki muzurai ba. Watak'ila ma naira d'ari biyu sai kinyi kamar za kiyi kuka ka mun ya cire ya baki. Allah ya sawake nayi aure! Ita ma da kuka ga ina nuna kamar ina jin haushi, sabida y'ar uwata ce ina hango mata wahala musamman da zata shiga gidan masu arziki. Kun ga sun samu y'ar aiki a sama wacce bata da salary." "Nace ba, da kike wannan hak'ik'icewar, ina naki tsayayyan kwarton?" Fad'in Na'ima tana harararta. Aina'u za tayi magana kenan Luckyboy ya fad'o d'akin tare da fad'in, "Ke Aina'u, gasu can a waje suna jiranki." Kwafa Aina'u tayi tare da mik'ewa babu ko gyale ta fice daga d'akin. "Kina ji ko Lami, dan Allah kar kibi shawarar Aina'u, kiyi amfani da kud'inki kiyi masu sha tara ta arziki, sannan gayya fa ake yi. Dole sai kin kira k'awayenki domin su zasu karb'i kayan ba ke ba." Fad'in Na'ima. "Wai maganar me kuke yi haka? Ni sallame ni kawai Lami in ware. Kuma eh, naga anyi eh ya ne a cikin gidan nan, amma ba'a bani rabona ba. Ke nan ni ba d'an gidan bane?" "Ungo wannan, tafi ni ka ishe ni." Fad'in Lami tare da mik'a masa dubu talatin. Da idanu Na'ima tabi kud'in sannan ta juyo ta kalli Lami bayan fitar Luckyboy tare da fad'in, "Lallai ma Lami! Dama duk uban kud'in da muke baki, da wanda _Khalil_ yake baki Lucky kike tattarawa kike ba yana tafiya shi da abokai suna shaye-shaye." Lami ko taro bata yi ba sai zurawa plasma TV tayi tana kallon arewa kamar bata san mai Na'imar ke cewa ba. Washa gari wajajen k'arfe biyu sai ga dirar motoci masu kawo lefe sun zo. Dama kuma Munee na gidan, da sauri ta fiddo waya ta kira mahaifiyarta ta shaida mata sun zo don ita ce tace su fad'a mata a waya idan sun k'ariso. Cikin k'ank'anin lokaci sai ga mama da tawagarta su k'ariso gidan hannunsu nik'i-nik'i da manyan kuloli. A nan tsakar gidan aka shimfid'a masu k'atoton tabarma. Su suka yi insisting sabida d'akin ba d'aukar su zai yi musamman da irin kayan da suka zo dashi. Aunty Maryam, aunty Khairat, kanwar Hajiya, matan uncles da matar ya Abdullah ne suka kawo kayan. Su suka fara shigowa, sai da suka gama gaisawa da mahaifiyar Munee da mutananta da ta gayyato. Na'ima kuwa hana Lami fitowa tayi don cewa tayi sai tayiwa Baba da mahaifiyar Munee tujara akan abunda suka yi mata. Sai zage-zage take tana fad'in akwai wani banzan alak'a tsakanin Baba da mahaifiyar Munee. Allah yaso babu wanda yaji abunda take fad'i sai Na'ima da take ta faman bata baki a d'aki. Kuma ta kulle d'akin ta ciki duk da kuwa tana so ita ma taje taga kayan da ta hanga ta window driver na wucewa dasu yana ajiyewa a nan tsakar gidan. Sai da ya kawo duka sannan aka soma bubbud'ewa. Babu abunda ke tashi sai kabbara da gud'an mata. Tun mata na irge har suka hak'ura don b'ata lissafi suke yi. Mata sai uban santi suke yi da gud'a. Gaba d'aya gidan ya cika da mutanen dake ganin kayan Sarah. Aina'u kuwa zawonta uku a cikin wando ganin mahaukatan kayan da aka zubawa Saran. Bayan an gama gani, mama ta ware na Baba, Lami da kuma wanda aka ce na k'annai da yayyin amarya ne ta ajiye a gefe, sauran kuma aka bar su nan tsakar gida. Dubu d'ari uku Baba ya bada matsayin tukwuicin duk da kuwa bai san adadin kayan da zasu kawo ba. Y'an kawo akwati sun mik'e zasu wuce kenan sai ga tawagar matan zumunta sun shigo gidan da wani irin mahaukacin gud'a suna tafi tare da yin wak'ok'in coci. Gaba d'aya sai kallo ya koma sama. "Elizabeth kina ina? Ashe aurar da yarinyarki za kiyi amma shine baza ki gayyaci mutanan coch ba. Baki kyauta ba sam. Pasto William yayi fushi dake kuma yace idan baki kai Sera (Sarah) ya saka mata albarka ba, auren ba zai yi albarka ba. Yace ya baki kwana biyu ki kaita ayi mata wankan zunubi kamun ta shiga gidan miji. Da k'arfi aunty Rose Merry take maganar duk da kuwa bata ga Lami a tsakar gidan ba. Aunty Maryam da aunty Khairat da kanwar Hajiya, sai wannan ta kalli wancen, sai wancen ta kalli wannan. Da suka ga abun ba na k'arewa bane, sai suka yi salama suka tafi domin sosai dai aunty Rose Merry da tawagarta suka baje suna wak'ok'in suna kiran sunan yesu almasihu. Idan suka buga wani ihu har hanjin mutum sai ya kad'a. Baba dake d'aki kuka kawai ya fashe dashi. Don bai tab'a kawowa Lami zata iya yin wannan iskancin ba. Lami dake d'aki ita ma mamaki ne ya kamata don ko da wasa bata tab'a fad'awa mutanen coch d'insu zata aurar da y'a ba. Ko aunty Rose Merry da take k'awarta bata fad'a mata ba. "Na'ima wallahi bani na gayyace su ba, kuma ban san wanda ya kira su ba." Na'ima kuwa kallon mahaifiyarta take yi cike da tuhuma tare da fad'in, "Lami dama kina zuwa coch? Wa za ayiwa wankan zunubin?" Lami bata ba ta amsa ba, sai wucewa da tayi ta bud'e k'ofar ta fita ta samu ce aunty Rose Merry dake ta kwasar ihu da kiran yesu suna d'ad'd'aga kayan akwatin Sarah. "Hajiya kina bacci ne aka kwaso maki dangin arna matsayin surukarki?"




*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*

*_MATAR SAYYADEE_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜?*KANWAR MATATA*>؜?

*PAGE 17*


"Hajiya kina barci ne zaka kwaso maki dangin arna matsayin surukarki? D'iyar Elizabeth ce kuma Wallahi matan zumunta cike da gidan har da zancen zuwa wajen Pasto domin ayiwa ita matar _Khalil_ d'in wankan zunubi." "Wankan Zunubi?" Hajiya ta fad'i cike da mamaki tana kallon K'anwar tata Marwanatu. "Wallahi tallahi Hajiya kar ki yarda da wannan aure idan ba haka ba akwai mummunar matsala. Wannan wani irin bahagon gida ne haka." Fad'in Inna Marwanatu. Amma abunda ya matuk'ar d'aure mata kai da bata mamaki shine ganin hajiya tayi murmushi tare da cigaba da ware anko da take yi wanda ta sayawa y'an uwa da abokan arziki. "Hajiya dariya fa kika ki. Na fad'a maki irin wannan magana mai d'aga hankali shine kike murmushi mai makon ki fusata ki kira waya a fasa wannan aure." Ajiye kayan da ta d'auko tayi tare da kallon Marwa sannan tace, "To ai ni ban fahimceki bane Marwa. Shin laifin uwar ne zai shafi y'ar ko kuwa? Ba ita bace arniyar idan rrtkq a kina magana akan a fasa auren. Ko da kuwa itace, ai addininmu bai haramtana mana kawo su cikin mu, mu dai matsayin mata addini bai amince mana da mu zauna dasu ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login