Showing 105001 words to 108000 words out of 129558 words

Chapter 36 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

ta ?arisa maganar hawaye na zubo mata. Gaba Waya sai jikin Sarah yayi mugun sanyi ganin tsohuwa na hawaye. Hannunta Sarah ta dafa tare da faWin, "Hajiya kiyi ha?uri, amma ni a tunanina ba hakannan ba su ya Abdallah zasu ?aurace maki har na tsawon shekara Waya da watanni! Hajiya addu'a da ro?on Allah har da sadaka zaki fara daga yau akan Allah ya karkato maki da dukkan hankalinsu a kanki, in Sha idan muka mi?awa Allah lamuranmu da kyakkyawar ya?ini, in Sha Allah zai yaye mana damuwarmu, Hajiya gaba Waya mun mance da Allah shiyasa shima ya mance damu, kuma na tabbata idan muka koma garesa zai amshi bu?atunmu da hannu bibbiyu. Hajiya ban san cewar duk tsawon shekarun nan aikin banza nake yi ba wajen raya darena da kuka ba sai yau da na shigo Sangaren nan na tarar da Laure na ganawa da ubangijinta tare da ?as?antar da kanta tana kuka. Hajiya muyi koyi da Laure in Sha Allah duk matsalolinmu zasu gushe!" Shuru Hajiya tayi tana sauraren Sarah cike da jin kunya da kuma dana sani akan rashin kai kukanta tuntuni zuwa ga mahalicci, sai hakan ya tuno mata da marigayi (Nuruddeen Muhammad) mahaifinsu Khalil, da wani abu ya shige masa duhu ko kuma yana fuskantar matsaloli, nan da nan yake ?ara nau'ikan ibadu akan wanda yake yi, dama kuma azumin litinin da Alhamis ya zame masa jiki da kuma sallar dare, sai ya ?ara ninkawa, almajirai yake tarawa fiye da Wari kuma ya shiga cikinsu su sauke ?ur'ani sau goma a cikin sati guda, sannan ya shiga sadaka a masallatai tare da gidajen maru, ma?owa kuwa kyautatawarsu daban take, hakan ne ya saka duk tuggun da ?an uwansa suke binsa dashi yake koma masu. Kuma ?a'ida ne lokaci da yake raye, tun su Khalil na ?anana sai ya haWa kansu har matan sun sauke ?ur'ani duk bayan kwana goma, bayan rasuwarsa da kuma yanayin aikinsu gami da mai da hankali kan tsantsan boko ya saka suka watsar da komi, kuma Lokacin da yake da rai, kullum gidan cikin sauraren karatun Al?ur'ani ake. Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da kallon Sarah tace, "Tabbas Saratu duk abunda kika faWi hakane. Wato lokacin da mahaifinsu Khalil yake da rai, wallahi kullum cikin gidan nan karatun Al?ur'ani ake saurare, sannan duk bayan wani lokaci, Alai sai ya tara almajirai anyi saukar ?ur'ani da sadaka, bayan rasuwarsa ne komai ya watse!" "Hajiya a shawarce, ya kamata komai da ake yi cikin gidan nan ya dawo har abada." FaWin Sarah. "In Sha Allah, uwata. Nagode maki sosai da tunatarwarki uwata, Allah yayi maki albarka." FaWin Hajiya. Sarah ta amsa da ameen tare da mi?ewa ta fita daga Wakin, a parlour, su twins na ganin mahaifiyarsu sai suka bar jikin Laure da sauri tare da ?arisowa wajenta, Sarah tayi-tayi su koma a atafau suka ?i, haka nan ta koma side Winta dasu, babu kowa a parlour sai tayi saurin shigewa Waki don kallo kujeran dake parlourn zai iya saka ta faWi ta mutu, don gaba Waya hoton Khalil da Sarah take gani tsirara a kan kujerar. Aina'u kuwa duk abubuwan da Sarah ta tattauna da Hajiya tana kallon komai daga Waki, wani ?u?ulun takaici ne ya tokare mata waya ganin Sarah tun ba'a je ko ina ba tana son lalata mata shirinta. Tashi tayi ta kullo ?ofar kasancewar ko da Khalil ya bar parlourn Wazu, Wakin Sarah ya shige ya kulle kansa, sai ta Wuka ta fiddo wannan tukunyar tare da tura hannun ciki ta Wauko wannan mutum-mutumin na itace ta matse saitin zuciyarsa da ?arfi tare da tsundumawa cikin tulun sannan ta kuma cirowa ta ?ara danna ?irjinsa sannan ta saki daga sama ya faWa tsumbul a cikin tulun tare da mayar da tulun ?asan gado sannan ta shafa tsakiyar tafin hannunta sai ga hoton fadwa ?ar wajen Marfu'a, Bobo da Nana ?an wajen Hassana, mimi ?a guda da ta ragewa Na'ima, Sai Sultee da haidar ?a?an Nuratu. Wani murmushi tayi tare da zana maciji a hannunta, nan take macijin ya soma motsi tare da tafiya da sauri-sauri, Waya bayan Waya macijn nan ya dunga saransu suna zuba ihu kasancewar gaba daya suna wasa ne a tsakar gidan, yayin da iyayensu suke makarantar dake gaban gidan kaWan, Na'ima ce kawai bata je saboda fama da ciwon kai da take yi kwana biyu, Lami kuma tana Waki ta saki ac tana sharar barci don bata jima da dawowa gidan ba daga gidan Aunty Rose Merry. Da gudu Na'ima ta fito jin wani irin mahaukacin ihu da Mimi ta saki sakamakon saran maciji, dai-dai nan Lami itama ta fito da sauri, a kan idanunsu macijin ya sulale yabi bayan flowers ya Sace amma su basu ga Sacewar nasa ba. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" "Lord of Jesus!" A tare Lami da Na'ima suka faWi haka sannan suka yi kan ?a?an da gudu suna jijjigasu, cikin ?an?anin lokaci har fatan jikinsu ta sauya kala ta koma green yayin da ba?in kumfa ke fita daga bakunansu suna wani irin jijjiga, kuka Na'ima ta fashe dashi tare da Waura hannu a kai, can kuma ta nufi gate da gudu ta fita ko mayafi babu tana kuka tana faWin a taimaka mata, tare suka dawo da maza biyar cikin gida, inda yaran suke ta kaisu tana kuka, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Mai ya same su?" Gaba Waya suka faWi suna mai isa kusa da yaran tare da taSa su. "Macijine ya sare su, nima ihunsu naji na fito sai naga macijin da sauri yabi bayan flowers Win na." ?aya daga cikin su ya nufi bayan flowers Win yana dubawa, "Tabbas kuwa! Ga saSarshi nan a nan wajen!" Ya faWi yana mai Wago saSar macijin. HuWun da suke kan yaran suka kalli juna bayan tabbatar da babu sauran numfashi a jikin yara, "Yaro yi min bayani, sun mutu ko?" FaWin Lami tana mai du?owa tare da taSa wuyan Mimi dake daf da ita. "Iya sai dai ha?uri, Allah ya riga ya Wauki rayuwar waWannan ?a?an." "Yesuuuuuu! Wannan azaba da jarabawar ya isa haka! Muna yabonka Ya Allah: mun dauki cewa kai ne Ubangiji. Dukan duniya tana yi maka sujadda, Uba Ma-dauwami. Agareka Mala?ku duka suna tada murya, da Sammai da Ikoki duka da ke cikinsu. A gareka Charubin da Sarafin kullayomi suna tada muriya. Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki: Ubangiji Allah Mai-runduna. Samma da kasa cike su ke da Sarautar darajarka. Jama a masu daraja ta zamaninka tana yabonka. Managarcin zumunta ta Annabawa tana yabonka. Jama a mai-daraja ta Masu-shahada suna yabonka. Ekklisiya mai-tsarki cikin dukan iyakar duniya tana shaidanka: Ya Uba mai-sarauta mara-iyaka: Danka kuma mai-girma, mai-gaskiya, ma-kadaici: Ruhu Mai-tsarki kuma Mai-taimako. Kai ne Sarkin Daraja: Ya Almasihu. Kai ne Da matabaci na Uba. Sa anda ka dauka ma kanka ka ceci mutane, ba ka yi kyamar cikin buduruwa ba. Sa anda ka yi nasara da zafin mutuwa, ka budi Mulkin Samma ga masu-bada gaskiya duka. Kana zaune ga hanun damar Allah (Astagfutullah) a cikin darajar Uba. Muna bada gaskiya za ka zo ka zama mai-shari anmu. Muna rokonka fa, ka taimaki bayinka: wandanda ka fanshe su da jininka mai-daraja: Ka maishe su a-cikin lissafin tsarkakanka, a-cikin daraja ta har abada. Ya Ubangiji ka ceci jama arka, ka sa ma gadonka albarka. Ka malke su: ka WaWWaga su har abada. Yo da gobe muna girmama ka; Muna sujadda ga sunanka kuma kullum ba matuka. Ya Ubangiji da yardarka ka tsare mu kar mu mutu da zunubi. Ya Ubangiji ka yi mana jinkai: ka yi mana jinkai. Ya Ubangiji ka bar jinkanka shi rufto mana: da shike ban gaskiyarmu tana gareka. Ya Ubangiji, a-gareka na bada gaskiya, kada ka bar ni na rude har abada. Wannan yara da suka koma izuwa gareka a yau, ka hura ruhinsu a cikin tsarkinka, ka yafesu a cikin irin yafiya naka, mu kuma ka karemu kar muyi mutuwa irin nasu, Yaaa Yesu Almasihu uba!" Kallon-kallo mutanan nan suka shiga yi, don duk a tunaninsu Lami musulmace duk ganin da suke yi mata, sai yaji da suka ji uban yabo da ta kwararo suka fahimta, "Ashe aljihun baya ce!" ?ayan ya kalli ?an uwansa ya faWi, shi kuma mai ri?e da fatar maciji yace, "To Allah ya ?ara nauyin ?asa!" A fusace Na'ima tace, "To ba amin ba! Wannan wani irin Magana ce haka kuke yi? Ai ko da ace a cikin addinin Kirista aka haifi su Mimi bai kamata kuce haka ba tunda dai basu san komai ba, kuma ko yanzu a makarantar Annabi Ibrahim zasu tashi in Sha Allah! Balle kuma Ni uwarsu acikin musulunci aka haife ni kuma, na furta kalmar Ashhadu Allah ilaha Illallah, Wa Ashhadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu!" Da sauri mutumin yace, "Allah ya baki ha?uri, kiyi ha?uri dan Allah!" Na'ima bata kuma cewa komai ba sai kukan da take yi. Ita ta ri?a Waukar ?a?an tana kaisu Waki tare da rufesu har kai, bata yarda ko gawa Waya Lami ta taSa ba, sai da ta kulle Wakin sannan ta fito sanye da hijjab tana kuka ta nufi makarantarsu, shugabar makarantar ta sanarwar komai tare da ro?onta akan tazo tayiwa yaran wanka ta shiryasu. Sosai shugaban makarantar mai suna Malama Nusaiba ta tausaya mata tare da lallashinta ta kuma bata baki sannan ta kira su Nuratu don saura mintuna goma a tashi a islamiyar, suma sai da tayi masu nasiha mai ratsa jiki sannan ta shaida masu abunda ke faruwa, kuka suka fashe dashi duka, bata hanasu ba kasancewar ba kururuwa suke yi ba. Tare suka koma gidan har da Malama, kuma kamar yanda Na'ima ta bu?ata, malamar ce tayi masu wanka sannan ta suturtasu da kikkafani. Khalil na kwance yayi ruf da ciki akan gado, ya rasa duniya mai ke yi masa daWi, gaba Waya ji yake ya tsani kansa gaba, "Why am I even alive?" Be san sanda ya faWi hakan ba yana mai kaiwa katifa nausuka kamar zararre! Burum Aina'u ta faWo Wakin tare da kama ?ugu tana kallonsa idanu a ?an?ance, da sauri ya mi?e zaune yana kallonta gabansa na faWuwa don duk lokacin da ta zuba masa idanu haka, matsanaicin tsoronta yake ji har gabansa na bugawa da sauri-sauri. Nuna kanta tayi tare da faWin, "Ni! Ni zaka wula?anta Khalil saboda kaga matarka da ?a?anka? Wato idan mutuwa zanyi sai dai in mutu ko? Ka san cewar ban kawo ba, amma saboda tsabar iskanci da wula?anci shine ka sauka ka barni da wahala ko?" Ko mai Khalil bai iya ce mata ba, ji yake ?irjinsa yayi masa wani irin zafi da ?unci, hawaye ne yaji suna neman zubowa amma bai basu sararin haka ba, yana jin mugun tsanar Aina'u kamar ya kasheta, amma yana jin sam ko afuska ba zai iya nuna mata hakan ba, duk haushi da tsanar da yake yi mata, idan har suka haWa idanu sai yaji komai ya washe. "Ina magana ka min shuru! Mahaukaciya ka mayar dani ko kuma me?" Ta faWi a tsawace. Sam Khalil bai tsorata da tsawarta ba, amma yana Wagowa suka haWa idanu da Aina'u be san lokacin da ya furta, "Kiyi ha?uri dan Allah" ba. Harararsa tayi tare da faWin, "Idan kana so inyi ha?uri in yafe maka, ka tashi yanzu ka sauka ?asa ka samu ruSaSSiyar matarsa ka koreta ita da ?a?anta, idan ba haka ba kuma...." Ta ?arisa maganar tare da jan Wan yatsarta akan kuyanta. ?ura mata idanu Khalil yayi ko kyaftawa bai yi ba, wani uban tsawar ta kuma daka masa tare da faWin, "Ko baka ji bane?" Da sauri ya mi?e tare da faWin, "As you wish Ai'n!" Yana gama faWin haka ya gittata ya fita daga Wakin. Wani irin tsalle Aina'u ta daka tare da faWin, "Yyyesss!" Khalil na fita daga Wakin wasu zafafan hawaye suka shiga zubowa daga idanunsa har zuwa kan ?irjinsa, kamar kwai ya fashe a cikinsa haka ya ri?a takawa har zuwa ?ofar Wakin Sarah. Ya jima tsaye kamun ya saka hannu ya murWa handle Win ?ofar ya shiga, du?e take a bakin gado tana sakawa Sam'an wando, da farin ciki gami da ihu yace, "Daddy!" Yana mai nuna shi da hannu. Da sauri Sarah ta waiga tana kallon Khalil Win dake bakin ?ofa yana kallon ?asa hawaye na tsiyayo masa har yana Wiga a ?asa. Kallon su Sam'an tayi tare da faWin, "You two should go and play in the parlour, will meet you there in the next two minutes!" Da sauri Sauban yace, "With daddy?" Ya faWi hakane yana mai nunasa da hannu. ?aga masa kai tayi tare da sauko dashi daga kan gado, dukkansu sai da suka yi shaking hannun daddynsu, har zasu wucesa sai ya dawo dasu baya ya rungume a jikinsa tare da fashewa da kuka yana mai shafa fuskansu. Sarah ce ta ?ariso wajen itama kukan take yi sosai tare da kama hannunsu ta fitar dasu sannan ta jawo ?ofar ta rufe. Kallonsa ta ri?a yi hawaye na zubar mata, shi kuma kansa a ?asa yana zubda hawaye kuma ya kasa Wagowa ya kalleta, "Happiness!" Ta kira sunansa a hankali. Da wani irin ?arfi ya jawota jikinsa ya rungume ?as tare da sakin kuka kamar yaro, irin ru?on da yayi mata sai da taji kamar ha?ar?arinta zai SaSSalle, "?an sassauta kaWan." Sarah ta faWi muryanta na rawa don wani irin shau?i da missing Win mijinta ne ya dirar mata, "Saraaah!" Ya kirayi sunanta cikin wani irin raunataccen murya tare da ri?eta gam-gam yana jin wani irin natsuwa na mamayesa, don ba zai iya tuna when last ya ri?eta haka ba. "Sarah meke faruwa damu! Sarah na haukace, ban cikin hayyacina, ban san meke faruwa dani ba, ina jin kamar an Wauke Khalil Win dake cikin jikina, Saratuuuuuu." Ya ?arasa kiran sunansa tare da fashewa da kuka jikinsa na rawa. Wani irin tausayinsa ne ya mamaye zuciyarta, soyayya da ?aunarsa na kuma ruruwa a zuciyarta, a lokaci guda kuma tana aikawa Aina'u da kwandon tsinuwa na raba tsakaninsu da tayi. Don Sarah duk wannan abubuwan dake faruwa har ganinsa turmi da taSaryan da tayi da Aina'u, bai taSa sakawa taji ta tsaneshi ba, saboda tayi imani duk abunda yake yi ba'a cikin hayyacinsa yake ba, sai dai ba?in ciki da takaici kam ta Webe shi iya Wiba, don ta tabbata da za'a gwada zuciyarta, za'a tabbatar ta samu matsala, Hassan jini kuwa idan yana kaiwa million, to nata sai ya wuce, don babu ranar da bata kwana ta kuma tashi da ciwon kai mai tsanani. "Addu'a itace makamin mumini daddyn twins, ka tashi tsaye ka kai kukanka gaban Ubangiji! Ka rage bacci ka raya darenka wajen ro?on ubangiji, ka yawaita saurarar karatun Al?ur'ani in Sha Allah duk wani abun da yake damunka a zuciyarka zai yaye kuma zaka samu sau?i. Mun samu jin daWin duniya, mun bar ubangiji shiyasa Allah ya barmu, amma idan muka mi?a wuya zuwa ga mahalicci, komai zai wuce kamar ba'a yi ba." ?ara rungumeta yayi tare da faWin, "Hakane! Hakane!! Maganar ki haka take Mine." Sun kusa mintuna biyar a haka suna jin bugun zuciyar juna kumun zuwa can yayi saurin janyeta a jikinsa ya nufi wardrobe tare da soma zubo da kayan sawanta dana su twins a kan gado kuma a lokaci guda yana kuka. Da sauri ta nufesa tare da kamo hannunsa tana faWin, "Haoli????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? i menene haka? Mai yasa kake fiddo mana da kayan sawarmu?" Fincike hannunsa tayi ba tare da yace mata komai ba ya cigaba da fito da kayan kuma yana hawaye. ?ara kamo hannun nasa tayi tare da faWin, "Menene haka Khalil!" Da ?arfi yace,"Ki sake ni Mine, ki sake ni dan Allah!" Ya faWi tare da sakin rigar da ya Wauko ya zauna a bakin gadon tare da ri?e kansa yana kuka. Du?awa tayi a gabansa itama tana kukan tare da soma faWin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir!" Tun tana maimaitawa ita kaWai har shima Khalil Win ya Wauka, duk sai suka cika Wakin da faWin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." Aina'u dake Waki tana kallon komai a tafin hannunta ta kwaso da uban gudu har tana a dungure a steirs, ko kamun ta ida dungurowa ta saka yatsa ta caki tafin hannunta da ?arfi, a take Khalil dake zaune ya zabura da ?arfi tare da ture Sarah ya shiga faWin, "Tashi! Ki tashi ki kwashi duka kayanki ku bar min gida ke da yaranki sai na neme ki!! Ki tashi nace!!!" A kiWime Sarah ta tashi don ba ?aramin ruWewa tayi ba da jin wawan tsawar da ya buga mata. ?aton akwatinta ya jawo tare da soma loda kayanta dana yaran a ciki dai-dai lokacin da Aina'u ta banko ?ofar Wakin ta shigo tana huci, "Wato kai kake haWa mata kayan ko? To zo ka fice ta haWa da hannunta." Idanu jazir Sarah ta kalli Aina'u tare da faWin, "Aina'u ke ?ar wuta ce babu tantama! Baza ki taSa gamawa da duniya lafiya. Fir'auna Kina samanki yake Aina'u. Uwa da uba Waya suka haife mu, amma wallahi tallahi billahil azeem bazan taSa yafe maki ba ko da zanga kabarinki naci da wuta! Kin shiga tsakani na da mijina, kin shiga tsakani uwa da ?a?anta, Aina'u mutuwarki abun tsoro ce wallahi." Wani irin shu'umin murmushi Aina'u tayi tare da kallon Khalil tace, "Kana jin abunda take faWi baza ka Wau mataki ba?" Khalil dai bai ce komai ba, Sarah kuma a zuciye ta ?arisa wajen Aina'u tare da wanke fuskanta da mari hagu da dama tare da fashewa da kuka tana faWin, "Allah ya tsine maki Aina'u, Allah ya tsine maki albarka muguwa azzaluma, mara imani! A kafuran ma ke dutse ce, makamashin wutan jahannama! Yanzu baki ji komai ba Aina'u? Ki kwanta da mijina agaba da ?a?ana Aina'u! Mijin yarki Aina'u!! Anya akwai tsoka a ?irjinki kuwa? Aina'u ke ?ar wuta ce!" Wani kallo Aina'u tayiwa Khalil tare da faWin, "Kamar yanda ta Waga hannu ta wanke fuskata da mari, haka nake so ka Waga naka hannun ka wanke fuskanta da mari, ka nuna mata babu wanda ya isa ya taSa ni a gabanka ya zauna lafiya ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login