Showing 45001 words to 48000 words out of 129558 words

Chapter 16 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

ba zan tab'a bari kuyi farin ciki ba nayi maku wannan alk'awarin." Aina'u ta fad'i cikin zuciya tare da saurin barin wajen tana kuka don kalaman da _Khalil_ ke fad'awa Sarah ba k'aramin k'ona zuciyarta yake yi ba. Sarah da _Khalil_ kuwa basu san da ita ba, sai cigaba da kwararo kalaman love wa junansu suke yi har kusan goma na dare sannan suka yi sallama kamar kar su rabu. Bayan da ta dawo d'aki kuma, _Khalil_ na isa gida suka dasa soyayyar ta waya. Bayan sati biyu da sallamo Sarah, Ya Abdullah ya diro Kaduna, ko sauka gidan Hajiya bai yi ba, kai tsaye ya tafi family house d'in mahaifinsu domin ganawa dasu Uncles d'in nasa akan batun auren _Khalil_ d'in kuma dama tuni sun d'an fara maganar a waya. Kasancewar suna d'an shakkarsa, basu wani tattada jijiyoyin wuya ba, sun tsayar da magana akan zuwa gobe sai suje can gidansu iyayen Sarah a tsayar da magana. Bayan Ya Abdullah ya dawo gidan Hajiya, sai ya sanar mata yanda suka yi da Uncles d'in nasa. Sosai Hajiya taji dad'i jin babu wani tashin hankali da aka yi, duk da ta san dama basu cika yin haukar da suka saba yi ba a gaban Abdullah sabida suna shakkarsa. _Khalil_ kuwa da ya samu labari, sai da ya shiga d'aki ga kulle k'ofa sa hau tik'ar rawa kamun nan ya kira Sarah ya shaida mata abunda ake ciki. Itama dad'i ne ya kasheta. Bayan sun gama wayar ta fita tayi alwala ta dawo d'aki tayi raka'a biyu ta dunga rok'on Allah akan Allah yasa ayi wannan auren kada shima ya rushe kamar na baya. Don sosai ta saka _Khalil_ a cikin ranta. Bayan magriba _Khalil_ yazo har gida ya fad'awa Baba in Sha Allah gobe iyayensa zasu zo domin neman auren Sarah. Baba ya shaida masa babu komai sai sun zo. Bayan fitar _Khalil_ sai da Baba yayi hawaye tuno y'an uwansa na _Wamba_ don da yana tare dasu, da su zasu karb'i wannan aure. Haka nan ya aiki Sarah ta kira masa abokansa guda uku wanda suka had'a Sana'a tun suna matasa. Da sukan zo gidan su dubasa, amma ganin irin tijara da zagi da Lami take masu, sai suka d'auke k'afarsu a gidan, sai dai idan suka had'u da Sarah sai su aiketa da gaisuwa, idan kuma suna da d'an wani abu, sai su bata ta kai masa. Har gidan suka zo, da suka ji dalilin kiran kuwa, ba k'aramin farin ciki suka ji ba, kuma suka tabbatar masa da goben in Sha Allah dasu za ayi komai. Washa gari misalin bayan la'asar, sai ga jiniyar motocin sojoji, su kawu suna cikin nasu motar, shi kuma ya Abdullah yana cikin nashi a tsakiyar convoy, sai kuma wata sabuwar mota dal da wani soldier ke driving. A k'ofar gidan suka yi parking. Soldier ya bud'ewa ya Abdullah mota tare da sara masa ya k'ame. Bai fito ba, nuni kawai yayi masu da wata mota. Cikin k'ank'anin lokaci sojoji suka kwashe gaba d'aya abunda ke cikin motar suka yi ciki da su. Buhunhunan shinkafa kamar za'a bud'e shago, manya-manyan galolin manja da mangyad'a, huhunan goro, katon-katon na sweet da chewing gum, wani k'atoton centre carpet wanda kud'insa ya kai 500k, sai wasu had'ad'd'un takalma k'afa ashirin da wani k'atoton akwati wanda babu komai a cikinsa sai lesses da atamfofi masu tsadar gaske da kuma Key d'in mota. Gaba d'aya uban kayan, kayan saka ranar auren Sarah da _Khalil_ ne. Har dasu gas da manya-manyan stainless steel irinsu bokiti da. Irin dai al'adar da ake yi. Ga manya-manyan juices na kwali da na goro har da ruwan gora kala-kala. Lami kuwa mad'aukakin mamaki ne ya kamata don bata san da zuwansu ba. Baba bai fad'a mata ba, haka ita ma Sarah bata ce komai ba. Sai da aka gama shigar da kayan tsaf sannan ya Abdullah ya ziro k'afarsa ya fito dai-dai lokacin da su uncle suma suka fito. Abokan Baba su suka yi masu jagora har cikin d'akin Baba, sosai ya Abdullah yaji dad'in ganin gyaran da _Khalil_ d'in yayi wa baban da kuma ganin ya soma samun sauk'i. Bayan gaishe-gaishe sai suka fara magana akan abunda ya kawo su. "Aure dai bama so a saka ki da tsayi. Idan ma baku shirya ba, mu ashirye muke don bama buk'atar komai naku." Fad'in uncle Ridwan. Sam maganar bata yiwa ya Abdullah dad'i ba. Kuma sai da hakan ya nuna a fuskansa. A natse ya Abdullah ya soma magana, "Baba, uncle yana nufin idan babu takura, muna so kar bikin ya wuce sati biyu. Kar ka takura kanka, Saratu kawai muke buk'ata a gidanmu, amma idan kana ganin kana da naka uzurin, za muyi na'am da duk lokacin da ka saka." "Kaji d'an iskan yaron nan yana k'ask'antar damu a gaban wannan wulak'antaccen fak'irin mutumin. Shi har ya isa yana talaka ya ja da maganar mu" fad'in Uncle Ameeru amma cikin zuciya. Ba Baba bane yayi magama, abokinsa Baba Isma'ila ne yace, "A'a babu komai. Lokacin da kuka saka d'in ma yayi. Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi." Cike da girmamawa ya Abdullah yace, "To mun gode Allah ya saka da alkhairi. Ga wannan makullin motar, Hajiya ce ta bada kyauta a bawa mai sunan mahaifiyarta Sarah, kaya kuma gasu nan duk Hajiya ce ta lissafa mana muka sayo, tace na al'ada ne da ake yi idan za'a saka rana. Ga kuma sadaki nan." Ya fad'i hakan yana mai mik'a bunch d'in dubu-dubu guda biyar, jimilla ya kama dubu d'ari biyar cif. "Wannan kud'in ai sunyi yawa. Ba sayar da Saratu za muyi ba ai. Makullin mota kuma, ina naiman alfarma ku rik'e a wajenku duk lokacin da Sarah ta shigo gidan, sai ku damk'a mata." Sosai ya Abdullah yaji dad'in rashin ganin kwad'ayi a fuskan baba, sai yayi murmushi tare da fad'in, "Baba ai sadaki bai yawa duk da albarkan ake nema. Amma duba ga yanayin da muke ciki yanzu, ko billion aka bada kud'in sadaki, ai bai yi yawa ba. Zan dai mayar da makullin motar sai tazo tukun kamar yanda ka buk'ata, amma maganar rage sadaki kam ayi hak'uri." "To Allah ya sanya alkhairi ya sa ayi damu." Gaba d'aya d'akin aka amsa da amin. Bayan tafiyarsu, Baba ya ce su Baba sama'ila ko wannen su ya d'auki buhun shinkafa d'aya ya tafi dashi. Nan Lami ta daka tsalle tace ba zai yuwu ba tunda ba ubansu ya kawo ba. Ai kuwa Baba ya haukace mata kuma basu bar gidan nan ba sai da buhun shinkafa kowa d'aya. Don buhunar shinkafar guda ashirin ne ciff. Nan Lami ta dunga surfa bala'i ba'a fad'a mata za'a zo kawo kud'in auren Sarah ba, sannan kuma tace dole a fito da sadakin a raba. Ko kallonta Baba bai kuma yi na ya koma d'akinsa tare da yiwa sadakin Sarah mummunar b'oye don yayi rantsuwa kwandala ba zai bata ba tunda ba hakkinta bane shima kuma ba nashi bane. Gaba d'aya yaran gidan basa nan lokacin da aka kawo kayan auren Sarah. Sarah d'in ce kawai ke gida don ita bata zuwa ko ina. Lokacin da suka dawo kuwa, ba k'aramin rud'ewa suka yi ba ganin uban kayan saka ranar Sarah da aka kawo. Da Lami ta fad'a masu har da mota, yanke jiki Aina'u tayi ta suma, babu wanda yayi tunanin bak'in ciki ya saka ta ta suman. Data farfad'o kuwa kuka ta fashe dashi. Tambayarta suka soma yi, sai tace masu ciwon kai da basir ne ke damunta. Mintuna biyar bata k'ara yi a gidan ba. Ameeru, duba nan kaga abunda aka turo min da b'oyayyiyar number, karanto muji don Allah. Ni na kasa fahimta. _ASSALAMU ALAIKUM. NA SAN ZA KAYI MAMAKIN WANNAN SAK'ON DA NA TURO MAKA. ABUNDA YA SAKA NA TURO KUWA, GANIN GIDANKU GIDAN MUTUNCI NE, KUMA MAHAIFIN KHALIL YA RASU KOWA NA GANIN GIRMA DA K'IMARSA HAR KUWA YAZU DA BAYA CIKIN DUNIYAR. NA SAN BAKU YI BINCIKE BA GAME DA GIDAN DA KUKA JE KUKAI KAYAN AURE BA. TO INA MAI BAKU SHAWARA KU KOMA DA KYAU KUYI BINCIKE, DOMIN DAI YARINYAR NAN BA TA KWARAI BACE. BATA JIMA DA ZUBAR DA CIKI BA. RUFA-RUFA AKAI MAKU. GIDAN NAN BA GIDAN MUTUNCI BANE DOMIN TAKEN GIDAN SHINE *GIDAN KARUWAI* IDAN KUMA BAKU YARDA DA MAGANATA BA, ZA KU IYA YIN BINCIKE DOMIN TABBATARWA. DON YAYYIN YARINYAR BABU WACCE BATA AJIYE SHEGE BA. IDAN KUMA HAR KUKA AMINCE WANNAN YARINYA TA SHIGO CIKIN ZURI'ARKU, TO KAMAR FA RUWAN KWATA KUKA D'IBA DA HANNUNKU KUKA ZUBA A CIKIN RUWA MAI KYAU!_


*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


Paid book 08128755583

*_MATAR SAYYADEE_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*PAGE 16*


A zafafe Uncle Ameeru ya mik'e tare da fad'in, "Na rantse da Allah ba zan tab'a bari ayi auren nan ba. Dole ne muje gidan can yanzu mu saka su a gaba muje mu kwaso duk abunda muka kai gidan. Mun janye maganar auren." Wani murmushi uncle Ridwan yayi tare da fad'in, "Gaskiya baka da hankali Ameeru!" "Rabu dashi mana, ni ai kallon wawa nake masa daga nan zaune. Ko ka manta cewa yayi ba zai auri y'armu ba saboda ta lalace? A gaban idanunmu gaba d'aya babu kunya ya fad'a mana wannan maganar. Har yanzu maganar tana sukar zuciyata. Ai ni wannan abu ba dad'i yayi min wallahi. Naji dad'i sosai da ya zam yarinyar gantalalliya ce. Kun ga kenan mun samu hanya mafi sauk'i da zamu cimma burinmu. Kawai had'a kai za muyi da yarinyar mu kashe d'an iska da ransa, musamman ma Bilkisu da ta hana mu rawar gaban hantsi. Shegiya duk hukumomi ta haifo, daga soja, sai d'an sandar farin kaya da kuma d'an iskan nan Barrister da ya gaji ubansa." Fad'in uncle Zayyanu. Uncle Shamsu kuwa cewa tayi, "Ni wallahi duk cikin y'ay'an Bilkisu nafi tsanar d'an iskan yaron nan _Khalil_ da wansa Abdullah. Kun ga da ace yaron nan soja a Kadunan nan yake, wallahi watarana sojoji zai saka su b'alla k'afafuwanmu. Bakwa ganin yanda yake nuna isa yana wani fankama kawai don ya kasance soja. Ni dama a kashe d'an iska acan wallahi." "Shegu taurin rai garesu kamar ubansu. Wani irin farmaki ne bamu kaiwa Nura ba, amma yana nan kamar kainuwa har sai da lokacinsa yayi. Mun sha wuya wallahi." Fad'in uncle Ameeru. Uncle Shamsu yace, "To yanzu dai mu tsayar da mafita. Mai kuke ganin za muyi? Ta yaya zamu b'ullowa ita yarinyar da zai aura?." Uncle Ridwan ya fad'i. "Ku bar min duk wannan a hannuna." Fad'in uncle Ameeru. "Yauwa Ameeru. Na sanka indai ta wannan fannin ne. Da ace yarinyar nan da ta turo sak'o ta bar wani makama da za mu bibiyeta, da ta cab'a don ta hanyarta zamu samu bayanai masu dama. Don ga dukkan alamu bak'in ciki take yi shiyasa ta tona asirin wancen, watak'ila kuma k'awa ce. Duk da hakan dai kuma za mu bincike gaskiyan labarin da ta bamu a kan gidan sabida mu san ta yanda zamu b'ullowa abun." "Yauwa nima abunda nake so in fad'a kenan." Uncle Zayyanu ya fad'i. Hajiya babu abunda take yi sai shirye-shirye. Gaba d'aya ta gama kiran dangi na kusa da na nesa na shaida masu auren _Khalil_ da za ayi nan da sati biyu. Aunty Maryam kuwa har ta gaji da zuwa kasuwa ita da aunty Khairat, don tun da aka saka bikin Aunty Khairat tazo don tuni har sun koma Kano, sai dai can ta baro Barrister shi sai ana saura 2days biki zai zo sabida aikinsa. Duk da kayan lefen kusan gaba ki d'aya a Dubai suka sayo har da akwatin, don private jet suka bi suka yo sayayyar kasancewar duka bangarori hud'un sun saki kud'i, Yaya Abdullah 5million ya bada, ya Barrister kuma ya bada 3million, ya Abdul-Hakeem ya bada 2.5million, shi kuma mai gayya 10.million ya bada. Hajiya kuma ita ta saya akwati set d'aya mai guda goma sha biyu. Gaba d'aya jimillar kud'in suka kama 20.5million. Dasu gaba d'aya su aunty Maryam, aunty Khairat da wata autar su Hajiya suka tafi Dubai. Sai da suka sayo akwatina set uku, na hajiya dozen, sauran biyun kuma mai guda six-six sai dai masu d'an karan tsada kuma gaba d'aya sai da aka cika su da mahaukan kaya masu tsada, don lesses d'in da aka saka babu na k'asa da 200k, kaya dai kamar za'a bud'e shago. Bayan sun dawo gida Nigeria kuwa, haka suka dunga yawon kasuwa suna k'aro wasu abubuwa don sai da suka dawo Hajiya tayi ta fad'a ganin babu kayan uwa da uba. Ana Nigeria suka k'ara had'o set d'in akwatuna guda uku irin mai biyu d'innan da kit. D'aya shaddojine da takalmar maza da turare da huluna masu tsada wanda ya kasance na Baba, sai d'ayan set d'in kuma aka zuba atamfofi da lesses da manya-manyan mayafai da takalma da turare. Shi kuma na Lami, sai d'ayan set d'in akai wa y'an uwan Sarah komai kala biyar-biyar, lesses kowa ta samu biyu, haka shadda da atamfa, sai takalma uku-uku da jakunkunarsu har da sark'a da y'an kunne. Gaba d'aya a parlourn Hajiya aka zube kayan. Sosai Hajiya taji dad'i don gaba d'aya babu k'arya. Yawan kayan ya saka ba komai Hajiya ta iya gani ba daga cikin kayan Sarah don akwatuna har set uku, wanda gaba d'aya jimillar akwatunanta kawai sun kama 24. _Khalil_ kuwa sai dad'a gyara b'angarensa yake yi wanda ya kasance four bedroom a k'asa da wawakeken parlour guda biyu mai d'auke da, dinning sai kitchen da store wanda girmansa da tsaruwarsa ma kawai abun kallo ne. Sama kuma two bedroom da parlour d'aya. Can gidansu Sarah kuwa, Lami da Aina'u ne kawai basa farin ciki da wannan aure da za ayi, gwara ma Lami ita gani kawai take yi idan akai auren shikenan za'a daina kawo mata abun arziki, yayin da Aina'u ita tsabar hassada ce da mugun hali. Babu kuwa kullum bakinsa bai rufuwa sabida farin ciki, sai shirye-shirye yake yi. Don yanzu Alhamdulillah har waje yana iya fita ba tare da sandar ba. Yana zuwa wajen abokansa suna ta shirye-shirye don Baba yace har walima sai yayi. Sarah kuwa babu wacce ke fad'o mata a rai irin K'awarta Muniba, duk duniya ita kad'ai ce k'awarta, gashi kuma tuni iyaye sun raba tsakaninsu. Kamar Baba ya san halin da take ciki, har gida yaje ya samu liman (Mahaifin Muniba) ya bashi katin gayyata sannan kuma ya rok'eshi alfarmar ya bar Muniba tazo wajen Sarah suyi shirye-shiryen biki don duniya bata da wata k'awa sai Muniba. Mahaifin Muniba yaji dad'i sosai jin Sarah za tayi aure kuma yace wa Baba in Sha Allah Muniba zata zo. Sarah na zaune tana sak'awa da warwarewa, do???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n basu jima da waya da _Khalil_ ba yake shaida mata zuwa anjima zai zo suyi maganar shirye-shiryen da za tayi na auren tunda gaba d'aya bikin yanzu ya rage saura kwana bakwai don har anci sati d'aya daga cikin ranakun auren da aka saka. "Assalamu alaikum!" Da mugun gudu Sarah ta fito jin kamar muryan Muniba. "Munibaaaaaaaaaa!" Ta fad'i sunanta da k'arfi cike da farin ciki ta rungumeta tana fad'in, "Wayyooooo Allah na, Muniba kece? Zo mu shiga daga ciki." Ta kama hannunta suka shiga cikin d'aki. Sakin labule Aina'u tayi, don tun jin sallamar Muniban ta d'aga labulen d'akin Lami tana kallon su. Dogon tsaki taja tare da fad'in, "Duk ku gama zumud'inku, wallahi wannan aure ba mai yuwuwa bane. Bamu y'an iska marasa sanin darajar kai irin y'an uwan mahaifin _Khalil_ d'in ma, ace a tura maku irin wannan sak'o amma baza ku tashi kuyi bincike tare da d'aukar mataki ba. Y'an iska kawai!" Duk a zuciya tayi maganar tare da shigewa tana mai yin kwafa tare da fad'in, "Ina da shiri a k'asa mai zafi, duk sai kunci ubanku." "Ke kuma dawa kike kwafa?" Fad'in Lami. A zafafe tace, "Babu ruwanki dani. Tom!" Tana gama fad'in haka ta zari gyale tare da ficewa daga gidan. "K'awata nayi kewarki. Ya aka yi su Baba suka bari kika zo gidan nan?" Sarah ta fad'i bayan ta bud'e d'an k'aramin fridge d'in dake d'akin ta d'auko mata ruwan sanyi da exotic. "Masha Allah! Haka kuka yi gyara a gidan? Wuri yayi kyau. Wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login