Showing 21001 words to 24000 words out of 129558 words

Chapter 8 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

dake duk'e a k'asa tana kuka tayi tare da jan dogon tsaki ta kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Baka dai ji warning d'in da nayi maka ba kenan? Kana wahalar da kanka ne. Don tabbas gidan mu ba'a aure." Tana gama fad'in haka ta fad'a cikin gidan. _Khalil_ ya jima a tsaye mamaki kamar ya kashe sa kamun ya duka ya kalli Sarah cike da dakewa yace, "Mik'e.!" Yanda yayi maganar cike da command ya saka bata san lokacin da ta mik'e tsaye ba. Jiri ne ya kwashe ta tayi baya zata fad'i yayi saurin tarota ta fad'o jikinsa dai-dai lokacin da Lami ta fito hannunta rik'e da wata doguwar paper. Wani dariya tayi tare da fad'in, "Kaiii jama'aa! To ai da shigowa kuka yi daga ciki sabida idanun jama'a. Ka san fa unguwar nan an saka mata idanu." Wani irin kallo ya jefi Lamin dashi, don wani irin tsanarta yaji ya darsu cikin zuciyarsa. "Ungo amshi nan!" Fad'in Lami tana mai mik'a masa paper d'in. Da kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya mik'a hannu ya amshi paper d'in yana kallon cikin idanunta. "Sai na ji sak'on ka, kuma da kanka nake son kazo." Tana gama fad'in haka ta juya ta koma ciki. Da idanunsa da suka rikid'e suka koma jazur yake kallon Sarah tare da daga mata wani gigitaccen tsawa yace, "Mai kike nema? Nace mai kike so da baza ki iya fad'a min ba? Mai yasa kika min haka? Mai yasa kika bawa wani kanki Saratuuu??" Bakinsa har rawa yake yi don har hasaso yanda abun ya kasance yake yi a idanunsa. Kuka Sarah ta fashe dashi don sosai ta tsorata dashi. "Ke! Ba kuka nace kiyi min ba, bayani zaki yi min. Uban wa yayi maki ciki?" Yanda yake maganar da k'arfi da kuma tsananin b'acin rai sai ya sanya jikin Sarah soma wani irin rawa tana kallonsa. "Ki bar kallo na ki bani amsa. Waye kika bawa budurcinki?" Bata san lokacin da ta bud'e baki tace, "Na rantse da girman Allah babu namijin da ya tab'a sanina matsayin mace." Wani kallo ya watsa mata tare da fad'in, "Ke nan karya ko kuma ince k'azafi aka miki." Da k'arfi kuma cike da tsoro tace, "Eh ina da ciki kuma uban cikin......." Bai bari ta k'arisa ba ya fizgi hannunta da k'arfi tare da nufar inda motarsa yake yayi. Da dannu d'aya ya bud'e gaban motar tare da jefa ta ciki ya kunne sannan ya zagaya ya koma mazaunin driver tare da shiga yayiwa motar key, "Ina zaka kai ni? Ka bud'e min mota in fita. Na shiga uku mai zaka min?" Wani irin kallo keep quiet yayi mata tare da jan motar ya figeta a guje ya bar layin. Kuka sosai Sarah keyi tana fad'in, "Stop the car I'm begging you. Dan girman Allah ka tsayar da motar nan inyi maka bayani. Kar ka cutar dani a karo na biyu bawan Allah! Ka dubi girman Ubangiji! Idan har baka da y'ay'a, kana da k'annai ko kuma y'ay'an y'an uwa. Dan Allah ka mai dani gidan mu." "Quite!" Ya fad'i da mugun k'arfi tare da taka wani irin burgi dai-dai gate d'in asibitinsa. Sai da Sarah tayi gaba ta dawo ta buge guiwarta. Kallon asibitin tayi a firgice, sabida tsananin rud'ewa bata gane asibitin ba, ta d'auka hotel ne. "Na shiga uku ni ka mai dani gida dan Allah!" Ko kallonta bai yi ba sai ya danna wani mahaukacin horn mai kashe kunnuwan mai sauraro. Da mugun sauri mai gadi ya bud'e gate d'in shi kuma ya danna hancin motar ciki tare da naiman waje yayi parking tare da fitowa daga cikin motar ya zagaya ya bud'e side d'in da Sarah take ya bud'e ya fizgo hannunta. Hankali tashe take kallonsa tare da, "Na rok'e ka da girman ubangijin ka barni na koma gida." Bai saurareta ba sai jan hannunta da yayi zuwa cikin asibitin. Nurses da idanu suka bisu ganin yana janta tana ita kuma tana kuka. Dai-dai nan doctor Kamal ya fito daga wani office daban. Da idanu shima ya bisu don kallo d'aya yayiwa Sarah ya gane itace wacce tazo tana kuka tana fad'a masa is bata san ta yanda aka yi tayi ciki ba, bayan kuma sau uku yana tura ta yin scanning kuma yana ganin cikin. Mamaki yake yi sosai ta ina _Ibrahim_ ya santa. Kai tsaye office d'in da yake mallakinsa ya bud'e tare da tura Sarah ciki sannan ya shiga ya kallo k'ofar tare da murza key. Yanda gaban Sarah ke bugawa da k'arfi har ana iya ganin hakan ta gaban hijjab d'inta sabida yanda yake d'agowa. Nuni yayi mata da gadon da yake duba marasa lafiya tare da fad'in, "Kwanta a can!" Ja da baya Sarah tayi tare da fashewa da kuka tace, "Bazan Kwanta ba, wallahi bazan kwanta ba ko zaka kashe ni." A fusace yace "Ni kike fad'awa haka?" Ya fad'i hakane yana mai matsowa, sai kawai ji tayi ya d'agata cak tare da d'aura ta a kan gadon. Yunk'urawa tayi zata sauko ya danneta da hannunsa guda d'aya tare da zuba mata tsinannun idanunsa yace, "Na rantse da ubangijin da ya busa min numfashin kika k'ara yunk'urawa da niyyar saukowa sai na maki abunda har ki mutu baza ki manta ba." Sarah na jin haka ta sadak'ar tare da komawa ta kwantar da kanta ta rintse idanunta hawaye na silalowa daga k'urmin idanunta. Gani take yi kamar tarihine zai maimaita kansa. Bata k'ara tabbatar da haka ba sai da taji hannunsa yana yaye doguwar rigar dake jikinta zuwa cikinta. Da sauri ta rik'e hannunsa da k'arfi ba tare da ta yunk'uro ba tana mai fashewa da kuka. "Sake min hannu!" Ya kuma fad'i da k'arfi. "Kayi hak'uri! Kayi hak'uri!! Kayi hak'uri d'an girman Allah!!!" Shine abunda Sarah tayi ta maimaita. Shi kuwa _Khalil_ ko sauraronta bai yi ba sai ma zame pant d'inta da yayi k'asa tare da ware mata k'afafunta. Wannan karan ta yunk'uro ya maida ta da k'arfi sai da bayanta ya bugu tare da tura yatsarsa d'aya ciki, hakan yayi dai-dai da wani irin ihu da Sarah ta kwala da uban k'arfi. K'ara k'ok'arin tura yatsar yayi cike da mamaki a karo na biyu. Wannan karan gaba d'aya Sarah ta d'ago tana fad'in, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Zare hannunsa yayi tare da jawo Vaginal Examination lamb ya haska wajen sosai. Cikin da tsananin mamaki yake kallon fuskanta bayan ya d'agota. Tausayinta sai ya rufe shi tare da dana sanin abunda yayi mata yanzu. Ja mata pant d'in yayi sama tare da kwantar da ita flat ya zuba mata _AquaSonic_ gel sannan ya soma scanning cikin. Wani mugun ajiyar zuciya ya saki ganin ga ciki nan b'aro-b'aro ya nuna a jikin screen d'in computern. "Tashi ki zauna." Ya fad'i politely. Mamaki ne ya cika Sarah jin yanda yayi mata magana a sanyaye. Babu musu ta tashi ta zauna tana kallon tiles d'in dake shimfid'e a office d'in still her heart is beating soo fast. Sauko da ita yayi tare da kai ta kan kujera ta zauna. A gabata ya duk'a yana kallon fuskanta tare da fad'in, "Sarah hakan na nufin cikin nan dake jikinki, nine ubansa?"



*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*






*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: *KANWAR MATATA*>؜?

*PAGE 10*


Kuka Sarah ta fashe dashi tare da fad'in, "Tun da na taso nake tsan-tsan da jikina. Bana k'aunar irin rayuwar da y'an uwana suke yi. Abun yana mun ciwo sosai a zuciyata, hakan ya saka na d'auki alwashi in Sha Allah babu wani d'a namijin da zai sanni matsayin y'a mace, sai mijin da ya biya sadaki ya aure ni. Amma ka rusa min tsari, ka cuce ni kayi min ciki. Ka jefeni da bak'in fentin da ba zai tab'a goguwa ba a rayuwata. Aure na saura sati hud'u, na dad'e ina burin zama matar aure, amma ka rushe min wannan burin, ka jefa ni a sahun sauran y'an uwana masu tab'o a goshi. Yanzu mai zan ce da wannan d'an idan ya fito duniya. Ta yaya zan yi masa bayani idan ya tambayeni ina mahaifinsa. Tabbas ka aikata abunda kace zaka aikatan, dama wancen ranar kace min sai ka min abunda har abada ba zan tab'a mancewa ba, kuma tabbas har abada bazan mance ba, kuma wannan abu zai ta bibiyata har mutuwata. Mai nayi maka bawan Allah? Mai yasa zaka min wannan cutar? Shin baka da k'anwa ne? Idan wani yayi mata abunda kayi min, ya zaka ji a zuciyarka? Baka tunanin Allah zai iya rama min abunda kayi min a kan y'ay'anka! Duk abunda kayi sai an......" Bai bari ta k'arisa ba ya saka tafin hannu ya toshe mata baki tare da k'ureta da idanu kamar zai fashe da kuka. "Nayi maki rantsuwa da girman ubangijin daya halicceki, ya halicceni da duk abunda yake cikin duniya, wallahi, tallahi ban tab'a zina ba, ba d'abi'ata bace. Na bar abunda ya faru tsakanina dake matsayin K'addara ko kuma ince maki jarabawa. Sarah tun lokacin da wannan abun ya faru, ina dai rayuwa ne kamar ina cikin farin ciki amma kuma a bad'ini abun ba haka bane. Shaidan ne da kuma zafin zuciya ya rinjayeni. Amma ni banda niyyar cutar dake. Ke shaida ce a wancan ranar da niyyata shine cutar dake, duk da na fahimci ke d'in cikakkiyar budurwace, da ba zan kyaleki ba sai na ratsa jikinki. Allah yayi sai nayi ajiya a cikin shiyasa har na samu natsuwa a wajen jikinki. Ki yafe min Saratu! Ki yafe min tabbas na b'ata maki record. Amma ina so ki saka cikin ranki, wallahi tallahi tun bayan da abun nan ya faru Allah ya jarabceni da zazzafar soyayyarki, kuma nayi maki alk'awarin sai na share maki hawaye na cika maki burinki na zama matar aure. Ni nan _Ibrahim Khalil Nasuruddeen_ zan aureki in killaceki a cikin gidana. Zan taya ki rainon d'anmu ko y'armu har ya fito duniya, bayan nan kuma ko sati baza ki k'ara a gidanku ba zan aureki." Mik'ewa Sarah tayi tare da fad'in, "Bana fatan ka kasance matsayin mijina. Domin ban san a matsayin mai zan rik'a kallonka ba. Cuta dai ka riga ka gama cutata. Ka b'ata min record. Idan har na aureka zan rik'a kallo kamar ba don Allah ka aureni ba. Kaje kayi rayuwarka nima nayi tawa. Kaje ka samu y'ar masu kud'i da asali dai-dai kai, nima kuma idan ina da rabon auren a duniya, Allah zai had'a ni da dai-dai ni." Da sauri _Khalil_ yasha gabanta tare da fad'in, "Kar ki min haka Sarah, dan Allah kar ki hukuntani ta haka. Wallahi tallahi, Allah shine shaida na akan irin k'aunar da nake maki. Dan Allah don't reject me Saratuuu." Gitta shi tayi tare da fad'in, "Y'ay'an masu kud'i zasu iya yin komai saboda suna da wanda ya tsaya masu, ko da kud'in su zasu iya taka kowa kuma ya taku. Na san idan kaso yau ba zan k'ara kwana a duniya ba, sai dai ina rok'onka da girman ubangijin ka fita daga harkata, kar ka k'ara kusanto inda nake ko kuma ka nuna ka sanni. Idan kayi min haka, wata k'ila in iya ji a zuciyata zan iya yafe maka." Kallonta ya dunga yi yana jin k'una cikin zuciyarsa, "Sarah rayuwarki a hannuna take da zaki ce idan naso ba zaki kwana a duniya ba yau? Dan Allah kar ki k'ara wannan maganar. Da mai kud'i da talaka duk d'aya ne a wajen ubangiji. Ke baki san talaka yafi mai kud'i kwanciyar hankali ba. Bama wannan ba, kin san da cewar idan Allah yaga dama sai ya kwace dukiyar da ya bawa mai kud'in ya bawa talaka har sai wannan mai kud'in ya dawo yana naima k'ark'ashin talaka. Dani dake bamu da wani bambamci Sarah. Dan girman ubangijin ki gafarceni kar ki min azaba da rashin amincewarki." Kau da kai Sarah tayi tare da fad'in, "Bud'e min k'ofa in wuce gida, don idan zamu wuni mu kwana mu kuma k'ara kwana amsa ta d'aya ce a gare ka. Kaje ka naimi dai-dai da kai." Wani abune yazo ya tokare wuyarsa, tun da yake a duniya bai tab'a furtawa wata mace Kalmar so ba a rayuwarsa, sai dai shi ba zai iya k'irga adadin matan da suka furta masa kalmar ba. Y'ay'an masu kud'i, turawa har da indiyawa, amma bai tab'a bawa d'aya daga cikinsu full attention d'insa ba balle har soyayya ta k'ullu. Amma wai yau gashi gaban k'aramar yarinya yana rok'onta akan ta soshi tana wasa da zuciyarsa. Ajiyar zuciya ya sauke, miskilancinsa suka hau kai tare da jik'imarsa, wani irin kallon gefen idanu ya bita dashi tare da fad'in, "Haka kika ce? So be it! Amma kuma ni zan tabbar maki babu wannan macen da _Khalil_ zai bud'e baki yace yana sonta ta k'i. Kamar yanda d'ana yake kwance a cikin mahaifarki, to haka _Khalil_ zai kasance cikin zuciyarki, sannan kuma wallahi babu wannan namijin da ya isa ya shiga gonar _Khalil_. Idan har ba _Khalil_ zaki aura ba, to zo rubuta ki ajiye babu ke babu aure!" Yana gama fad'in haka ya koma ya zauna ya soma danne-danne cikin computer yayi kamar ya manta tana cikin office d'in. Sarah kuwa da ta gaji da tsayuwa sai ta sulale k'asa ta zauna tana mai da numfashi. Da gefen idanu ya kalleta, sai kuma ya d'ago gaba d'aya tare da fad'in, "Wallahi wallahi idan baki tashi a k'asan nan ba kika bari nazo wajen nan zan baki mamaki!" A fusace Sarah tace, "Wani mamaki? Nace wani mamaki ne kuma ya rage baka bani ba." Ba tare da yace komai ya mik'e a fusace. Ko kamun yayi taku d'aya ta mik'e da sauri ta zauna a kan kujeran dake fuskantarsa. Wani dariya ne ya taho masa amma yayi saurin mayar dashi tare da kau da kai yana murmushi don dama ba zuwa wajenta zai yi ba, kawai barazana ce domin ta bar tiles d'in saboda sanyi. Zama yayi tare da cigaba da abunda yake yi. Ita kuma Sarah sai harare-harare take yi. Sun kwashi kusan awa guda sannan ya mik'e tare da fita ya kullo k'ofar. Sarah na ganin ya fice kuma ya kullo k'ofar ta kifa kanta akan desk d'in ta fashe da kukan bak'in ciki. Shi kuwa _Khalil_ yana fita suka ci karo da doctor Kamal dama kuma wajen _Khalil_ d'in zai zo. "Wajenka dama zan zo." Gyara tsayuwa yayi tare da yin bake-bake a k'ofar office d'in ya wani ci d'aci tare da fad'in, "To gani!" Sai da doctor Kamal ya kalli k'ofar office d'in sannan yace, "Ka kira ni emergency akan inzo nan kai zaka je yin wani abu, sai kuma gaka na ganka tare da wannan yarinyar. _Khalil_ ba halinka bane. Dan Allah kar kace zaka zubar mata da cikin dake jikinta. Y'an iskar yara sai sun gama yawon banzan su a tit....." A mugun tsawace _Khalil_ yace, "Enough! Enough doctor Kamal Isah Bashir! Kar ka k'ara jifan Sarah da wad'annan kalmomin. Sarah ba irin matan da kake tunani bane." Baki bud'e doctor Kamal ke kallon _Khalil_ don bai tab'a ganinsa a irin wannan yanayin sabida mace ba. Macen ma mai d'auke da cikin shege. A iya sanin da yayi wa _Khalil_ ya tsani y'an iskan mata. " _Khalil_ this lady that you're protecting haka, she's prostitude! Duk abunda zata fad'a mak......" Bai kai k'arshen zancen ba yaji wani gigitaccen mari ya sauka akan kuncinsa sai da yayi saurin saka hannu ya dafe kuncin yana mai kallon gefe-gefe. Ganin babu kowa kuma babu wanda yaga komai sai ya kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Ibrahim ni ka mara? Ni ka mara saboda ina fad'a maka gaskiya." Wani kallon banza yayi masa tare da fad'in, "To h???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ell with the fucking stupid gaskiya gaskiyarka. Idan bakinka ya kuma kuskuran kiran matar da zan aura da karuwa, na rantse maka da ubangijin rana da wata sai na d'aureka kuma babu uban da ya isa ya fito da kai. Kuma cikin jikinta it's mine. Na fad'a da babban murya, cikin dake jikin Sarah, nawa ne! Kuma duk uban da ya isa ya kira ta da karuwa yaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login