Showing 24001 words to 27000 words out of 129558 words

Chapter 9 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

abunda *_Ibrahim Khalilullah Nurudden_* zai aikata." Yana gama fad'in haka ya wuce fuuuuuu ya nufi pharmacy domin d'auko mata magunguna don tun d'azu yake lura da ita jiri take gani kuma babu k'arfi a jikinta. Shi kuwa doctor Kamal da mugun tsananin mad'aukakin mamaki yabi _Khalil_ d'in da idanu. Don ya mugun sanin hakinsa. In fact tare suka yi karatu a _London_ har kammalawan su. Yasan yanda ya tsani Zina da kuma mazinatan. Sannan yaga mata kyawawa iri-iri, turawa, indiyawa, larabawa duk bai fad'a halaka ba sai akan wannan tatsitsiyar yarinyar duk da ita ma kyakykyawar ce. Shafa kumatunsa da suka ji mari yayi tare wucewa ya bar wajen. _Khalil_ kuwa sai da ya d'auko duk magungunar da yasan Sarah zata buk'acesu sannan ya dawo office d'in hannunsa d'auke da leda mai tambari da sunan asibitin still kuma fuskansa a mugun d'aure. "Ki tashi in mayar dake gida." Ya fad'i sounding command. Cikin sauri ta mik'e shi kuma ya fita tabi bayansa. Kulle k'ofar yayi tare da fad'i, "Kiyi tafiya a hankali kar ki fad'i. Ko in rik'e ki?" Da jin haka tayi saurin yin gaba don taga alama sam bai da kunya. Har wajen motarsa suka isa, shi ya bud'e mata gidan gaba ta shiga sannan ya zaga ya shiga driver sit sannan ya tada motar yayi reverse ya bar cikin asibitin. A hankali ya dunga tafiya ba tare da ya k'ara ce mata ko uffan ba har suka isa k'ofar gidansu Sarah. Parking yayi tare da kashe motar ya juyo ya tsura mata idanu. Tana jin idanunsa na yawo a jikinta amma tak'i kallon wajen. Ledan maganin ya d'auko tare da fiddo da magungunan ciki sannan yace, "Hey, kalle ni nan." Kamar baza ta juyo ba, sai kuma ta juyo ta kallesa tana mai turo baki gaba. Tsurawa kyakkwar bakinta kallo yayi yana tuno ranar da tsautsayin ya afka. "Kin san wani abu? Tsiwarki ita ke ja mutun yayi maki abunda bai yi niyya ba. Ko wancen ranar ke kika ingiza ni har mai afkuwa ta afku. Idan kika b'ata rai ko kuma kika turo baki, wani irin kyawu kike k'ara yi sosai. Sai ki rik'a looking very sexy!" Wani irin kuka Sarah ta fashe dashi jin abunda yace. Bak'in ciki take ji idan yana maganar cikin dake jikinta. "Kin san Allah idan kina kukan nan, wancen ranar ba'ayi na gaske ba, amma ina ganin soon an kuwa zuwa wajen." Hannu ta kai zata bud'e k'ofar taji sa a gark'ame. Kallonsa tayi tare da shagwab'e fuska tace, "Dan girman Allah ka bud'e min, kaji ma kiran sallah ake yi!" Kallon maganin da ta fito dashi yayi tare da fad'in, "Kalli nan, wad'annan guda ukun kullum sau d'aya zaki rik'a sha, wannan kuma safe da dare. Allah ya k'ara maki lafiya Matata. Kiyi min magana da Mama idan kin shiga ciki. And lastly, wallahi kar in k'ara kiranki a waya kik'i d'agawa. Don wallahi komai dare sai nazo, kuma ni kai na ban san mai zai faru ba idan nazo d'in." Yana gama fad'in haka ya cire lock d'in yana kallon fuskanta. Bud'e motar tayi ta fita a hankali ba tare da ta d'auki ledar ba, sai da ta rufe k'ofar sannan ta lek'o ta window kasancewar ya zuge glass d'in tare da fad'in, "Ba zan d'auka ba, dan girman Allah kar ka fasa abunda kace za kayi. Kuma bazan sha maganin ba. Ka tafi da tsiyarka. Kuma cikinka dake jikina, a leda zan juye na watso maka shi a fuska na huta da jaraba." Da wani irin hanzari ya cafki hijjab d'inta ya cukuikuyota da hannu d'aya tare da fad'in, "Maimaita mai kika ce?" A gigice tace, "Na rantse cewa nay na manta ga ledan maganin nan baka mik'o min ba. Kuma wancen farin ma ya ma kace ayi amfani dashi." Dariya ce ta taho masa sosai amma bai yi sai murmushi ya saki tare sa d'aukar maganin da d'aya hannunsa ya mik'a mata. Da sauri ta amsa har da fad'in, "Nagode" shi kuma ya saki hijjab d'in nata tayi saurin barin wajen ta nufi k'ofar gidansu ba tare da ta waiga ba. Tana bud'e k'ofar suka ci karo da Baba ya fito karo na bakwai ko Allah zai sa ya ganta. Don lokacin dasu Na'ima suka baje a tsakar gida babu labarin da suke yi sai na _Khalil_ da irin motar da yazo da ita. Jin hakan sai ya tada hankalin Baba ya soma tunanin ko Sarah ta soma hawa layin y'an uwanta ne. Ya jira kusan mintuna ashirin ko Sarah zata dawo amma yaji shuru, ya daure ya k'ara goma akai, ganin har lokacin shuru sai ya mik'e ya d'auki sandarsa ya fito waje amma wayam. Yana jin sanda su Na'ima suke dariyar ya fita nemo y'ar gwal. "Baba dama dawowa kayi kar ka wahalar da kanka. Don saurayinta yazo sun fita tare." Fad'in Hassana. Bini-bini Baba ke fitowa ya duba ko Sarah ta dawo amma wayam. Sai a karo na bakwai sannan ta turo k'ofar suka yi ido hud'u. Wani ajiyar zuciya Baba ya sauke tare da fad'in, "Saratuuu!" Sai kuma ya fashe da kuka. Da sauri Sarah ta waiga taga motar _Khalil_ na nan, sai taji hankalinta ya tashi don bata son yardar da Baba yayi mata ya rushe. A gigice ta soma magana, "Wallahi Baba ba abunda kake tunani bane. Dan Allah ka daina kuka." Ta fad'i tana mai fashewa da kukan. Da sauri _Khalil_ ya bud'e mota ya fito tare da k'arisowa wajen ya duk'a tare da fad'in, "Ina wuni Baba?" Baba dake matsar hawaye ya d'ago ido ya kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Bawan Allah na rok'e ka da girman ubangijin idan ba alkhairi bane ya kawo ka wajen Saratu kayi tafiyarka Allah ya had'a ka da dai-dai da kai. Ka dubi Allah da annabi kar ka lalata min tarbiyan y'ata guda d'aya da ta fita zakka!" Shuru _Khalil_ yayi na y'an dak'ik'u tare da fad'in, "Baba wallahi alkhairi ne ya kawo ni wajen 'yarka ba sharri ba. Ni da niyyar aure nazo k'ofar gidan nan ba da niyyar yaudara ba." Da sauri Sarah ta kalli Baba tare da fad'in, "Baba kar ka yarda da maganarsa, fatar bakinsa ne fad'i amma cikin zuciyarsa ba haka bane. Shine sanadiyar duk abunda ke faruwa dani yanzu. Shine dalilin rugujewar farin cikina. Shine dalilin fasuwar aure na. Baba wannan dake durk'ushe a gabanka shine uban cikin dake jikina." Ta k'arisa maganar tare da fashewa da kuka. Baba kuwa ji yayi kamar an d'iga masa dalma a kunne. Rintse idanu yayi cike da k'una a zuciya yace, "Bawan Allah mai muka maka? Mai d'iyata tayi maka ka tarwatsa mata rayuwa? Kana ganin kayi min adalci kenan? Ban tab'a b'ata d'iyar wani ba, wannan jarabawace kawai daga mahalicci!" Idanun _Khalil_ gaba d'aya sun kad'a kun yi jazur ya d'ago tare da kallon Baba yace, "Baba, dan alfarmar ubangiji halittu ka saurare ni ko da na mintuna biyar kacal. Wallahi, tallahi rantsuwar musulmi ban zo nan da niyyar cutar kowa ba, zuwa na nan k'ofar gidan nazo ne domin in auri 'yarka." Hakanan baba ya d'an ji _Khalil_ ya kwanta masa. Kallon Khalil d'in yayi tare da fad'in, "Shiga masallaci kayi sallah, idan an idar kayi sallama zan aiko Saratu ta shigo da kai har ciki. Bari na shiga nima nayi sallar." Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar _Khalil_, cike da ladabi yace, "Nagode Baba!" Ya fad'i hakane tare da mik'ewa ya nufi masallacin gaban gidansu Sarah wanda yake daga hannun hagu, yayin da nasu gidan yake daga dama. Baba ma shigewa yayi Sarah na biye dashi kanta a k'asa hannunta rik'e da ledar magungunan da _Khalil_ ya bata. Gaba d'aya suna tsakar gida har da y'ay'ansu. Rabo d'an wajen Na'ima ya kalli Sarah tare da fad'in, "Lami ga Saratun ta dawo daga wajen saurayin nata." A fusace Sarah tace, "Daga wajen ubanka na dawo." Na'ima mahaifiyarsa ta taso a fusace tare da fad'in, "Zan ci ubanki a cikin gidan nan wallahi idan kika ce zaki rik'a takurawa d'ana. Babu ruwana da cikine a jikinki duka zan maki." Harararta Sarah tayi tare da fad'in, "To ai sai ki kashe ni kawai. Banza kawai." Yunk'urawa Na'ima tayi zata taho wajen Sarah karaf Lami ta rik'e ta tare da fad'in, "Barta! Yanzu haka duk salon kar ta bamu abunda ta samo ne daga hannun saurayin nata." Juyowa Baba yayi tare da kallon Sarah yace, "Saratu wuce ciki kinj." Babu musu Sarah ta shige ciki. "Ban gane abunda kake nufi ba Nuhu anyi yamma da kare!" Ko kallonta Baba bai yi ba ya shige d'aki. "Ahafff! Ba na fad'a maki ba Lami. Baba fa ya san duk tsiyar da Sarah take shukawa. Raba kud'in suke yi a tsakanin su shiyasa kike ganin yafi sonta akan mu gaba d'aya." Fad'in Aina'u. "Na ko tabbatar da maganarki yanzu Aina'u. Aikuwa dani suke zancen." Fad'in Lami tana kwafa. Dai-dai nan Sarah ta kuma fitowa ta nufi fanfo Lami na harararta. Alwala da d'auro sannan ta kuma komawa d'aki. Tana idar da sallah ta jiyo muryan Baba yana kwad'a kiran sunanta. Da sauri ta fito ta nufi baranda inda ta ganshi tsaye a bakin k'ofar d'akinsa, "Yi maza gashi can yana kwad'a sallama, je shigo dashi." Da "To Baba" Sarah ta masa tare da juyawa. Na'ima kuwa kallon Hassana tayi wacce itama kallon nata take yi sannan gaba d'aya suka mai da dubansu ga Lami wacce tayi suman tsaye tana kallon Baba cike da mamaki. Mintuna biyu sai ga Sarah tafe, _Khalil_ biye da ita a baya. Bai kalli kowa a cikinsu ba, don har yanzu bai gama tabbatar da cewar Lami ita ce cikakkiyar mahaifiyarsu Sarah ba. Dama kuma tuni baba ya shige cikin d'aki. Sallama _Khalil_ yayi tare da shiga don tuni baba ya amsa tare da bashi damar shiga. Yana shiga Sarah ta bar wajen zata wuce d'aki Lami ta shak'o ta tare da fad'in, "Dan ubanki shine zaki kai sa wajen mahaifinku! Wato kin fi k'aunarsa dani ko? To wallahi baku isa ba komai dani za'a ci." Tana gama fad'in haka ta fad'a d'akin babu sallama lokacin _Khalil_ suna k'ara gaisawa da Baba. "Na rantse da, girman Allah Nuhu baka isa Kaci kud'in nan kai d'aya ba. Ai nice na d'auki cikin Sarah wata har tara na kuma sha wuya nayi nak'uda na haife ta. Fito da duk wani abu da yaron nan ya baka ayi kaso." Sai kuma ta mayar da dubanta ga _Khalil_ wanda kansa ke a k'asa tare da fad'in, "Kai kuma Munafuki................



*_Na rok'e ke ki da girman ubangiji kar ki fitar min da littafi. Kud'in karatu kawai kika biya ba kud'in mallakar littafi ba. Kiji tausayin marainiyar Allah don wallahi Sana'a na d'aukesa ba nishad'i ba. =?O?_*


*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*



*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*PAGE 11*


"Kai kuma Munafuki! Ya muka yi da kai d'azu?" _Khalil_ ko d'agowa bai yi ba, balle ya kalleta har ya amsa maganar ta. "Lami wannan wani irin rashin hankaline haka? Yaya zaki shigo min d'aki babu sallama kuma kin san ina da bak'o! Wannan ai rashin hankaline. Malama fitar min daga d'aki." Harara ta makawa Baba tare da fad'in, "Ba zan fita ba wallahi. Sai anyi komai a idanuna. Wato daga kai sai y'arka ne zaku rik'a cin kud'in ko? To wallahi baza ta sab'u ba bindiga a ruwa!" Karkacewa _Khalil_ yayi ya fiddo da rafar kud'i y'an dubu-dubu ya mik'a mata tare da fad'in, "Gashi. Ni magana nazo muyi da Baba ba wani abu ba." Fizge kud'in Lami tayi da sauri don a zatonta Baba zai kawo hannu ya warci kud'in tana mai sakin murmushin ganin tashin farko an bata dubu d'ari. "Yauwa to ko kaifa. Ai wallahi da baka ban kud'in nan ba, Sarah baza ta k'ara cin ko loma d'aya a cikin gidan nan ba. Kuma duk aikin wahalar gidan nan ita zata rik'a yinsa. Babu ruwana da tana d'auke da k'aramin ciki." Taga gama fad'in haka ta harari Baba tare da ficewa daga d'akin. Da idanu _Khalil_ yabi Lami yana mai tabbatar wa kansa ba ita bace mahaifiyarsu Sarah. Baba kuwa kunya ce ta kama shi kamar k'asa ta tsage ya shige ciki. Da kyar ya iya bud'e baki tare da fad'in, "Dan Allah kayi hak'uri. Haka halin Lami yake. Sam bata da girma sai na jikinta." Kallon Baba _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Baba wacece ita?" Sai da Baba ya sunkuyar da kai don kunya yake ji ainun ya nuna Lami matsayin matarsa uwar Y'ay'ansa. A hankali cike da rauni Baba yace, "Matata ce. Uwar y'ay'ana!" Fad'in Baba hawaye na wanke fuskansa kasancewar mai sauri kuka. "Amma Baba ba ita bace mahaifiyarsu Sarah ko?" Hannu Baba ya kai ya sharce hawayen idanunsa tare da fad'in, "Ita ce. Wallahi samari ita ce ta haifi duk Y'ay'an dake cikin gidan nan." Wani irin ajiyar zuciya mai k'arfi _Khalil_ ya saki yana mai jin matsanaicin mamaki. "Kana mamaki ko? Na san za kayi mamaki Samari. Ba kai kad'ai ba, da yawan mutane basu yarda Lami itace ta haifi su Sarah sabida irin tarbiyan da tayi masu sakamakon son abun duniya. Ita gaba d'aya kallon wad'annan yaran take yi matsayin babban jarinta. Sam ta mance su d'in amane Allah ya bata. Na'ima ita ce y'arta ta fari, sai Nuratu, Lukman, Hassana, Marfu'a, sai auta Aina'u. Duk Y'ay'an Lami ne. Ita ta haife su da cikinta." Hassana ma y'an biyu ne, d'ayan tun a ciki ya mutu. Da yanzu su takwas ne, shidda mata maza biyu." Da tausayi _Khalil_ ke kallon Baba tare da fad'in, "To Baba ya aka yi irin haka yake faruwa a cikin gidanka, amma baka da ta cewa?" Sunkuyar da kai Baba yayi yana mai jin d'aci da k'una sosai cikin zuciyarsa tare da fad'in, "Lami tafi k'arfi ba Samari! Duk yanda zanyi maka bayani, baza ka gane ba. Amma Lami ta raina ni, bata ganin mutunci da darajana tun da na samu karayar arziki. Shiyasa y'ay'ana suma suka taso da d'abi'un da suka ga tana yi min. Guda d'aya ce ta fita zakka. Saratu na tausayina sosai, tana bani girma, tana kula dani kuma tana gudun b'acin raina. Tana sona sosai kuma duk abunda nace tayi, shi take yi, idan na hane ta kuma har abada ta bar abun nan kuma baza ta kusance shi ba." Gyara zama _Khalil_ yayi tare da soma fad'in, "Baba da farko dai hak'uri zan soma baka, dan Allah ka yafe min domin na cutar da kai. Tabbas 'yarka Sarah mutuniyar kirki ce. Kuma duk wani abu da ya faru tsakani da ita, wallahi ba da son ranta bane. Ban san ta yanda zanyi maka bayani ba Baba. Amma wallahi nima ba mazinaci bane. Tsautsayine ya afka mana daga ni har ita Saratun. Kuma wallahi ban d'auka sanadiyar abunda ya faru tsakani da ita ta samu ciki ba. Na jima ina naiman ta, amma ban ganta ba sai yau da Allah ya kawo ta asibitina. Baba dama ni ina son Sarah, kayi hak'uri ya yafe min kar kace zaka hanani ita saboda wannan abu da ya faru, ni nayi alk'awarin Sarah na haihuwa sati baza ta zagayo ba sai da aure na a kanta. Tun daga yau da na san Sarah na d'auke da cikina, d'awainiyarta gaba d'aya ya dawo kai, cinta, shanta da komai nata. Dan Allah Baba kar ka hana ni Saratu." Shuru Baba yayi yana wani tunani a cikin zuciyarsa. Ya jima bai yi magana ba, kuma bai d'ago ba. _Khalil_ kuma addu'a kawai yake yi Allah yasa Baba ya amince. Ajiyar zuciya Baba ya sauke tare da fad'in, "To! Ni bazan ce ban amince ba, matsalar guda d'aya ce. Shin idan kai ka amince zaka auri Saratu, iyayenka fa? Kai da kanka kaga irin gidan da kake neman aure. Kasan su wanene y'an uwan Sarah da kuma mahaifiyarsu. Gaba d'aya unguwarnan anyi masu tambari. Karo na biyar kenan ana fasa auren Saratu saboda bak'in fentin da y'an uwanta suka goga mata. Kud'in goro ake yi masu. Gani ake yi ita ma Saratun yawon banza take yi. Idan kai ka amince, iyayenka zasu amince ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login