Showing 6001 words to 9000 words out of 129558 words

Chapter 3 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

Ni wallahi kyama yake bani. Wanda Allah yayi maki ma ya ishe ki Sarah." Hawaye na zuba a idanunta ta furta, "In sha Allah daga yau ba zan k'ara saka d'aya daga cikin abunda ka lissafo ba." Ajiyar zuciya Farouq yayi tare da fad'in, "Allah ya miki albarka amaryata ta sati hud'u masu zuwa. Ki shiga gida hadari ne sosai a gari. Sai mun yi waya." Bata iya cewa komai ba sai murmushin da tayi tare da yi masa bye-bye ta shige cikin gidan. Tana turo k'ofa ta jingina da k'ofar tare da dafe k'irjinta da hannu d'aya sannan ta toshe bakinta da d'ayan hannun tana kuka sosai. Juyawa tayi ta lek'a ta wani d'an rami a jikin k'ofar, ga mamakinta sai ganin Farouq tayi tsaye a wajen amma ba k'ofar gidan yake kallo ba, wani wajen yake kallo daban. Can kuma ya saki ajiyar zuciya tare da tsallake kwatar dake gaban gidan ya wuce. Sai a sannan Sarah ta zame k'asa ta fashe da wani irin kuka mai tafasa zuciya. Ta jima a wajen tana kuka kamun ta mik'e ta nufi cikin gidan. D'akin su ta shiga ta cire hijjab d'in jikinta ta ninke tare da rataye sa a hannun wardrobe sannan ta cire suwaitan jikinta ta mak'ale a abun rataye jaka sannan ta kashe wutar d'akin don babu kowa a ciki, sauran y'an uwanta suna d'akin Lami kamun masu zuwa fita dasu su k'araso. Hawa kan gadon tayi ta kwanta rigingine tana sak'awa da warwarewa akan cikin dake jikinta. Sosai tayi zurfi a tunanin ta yanda aka yi ta samu ciki, sai dai duk iya zurfin tunaninta, bata gano bakin zaren ba, don zata iya dafa Qur'ani tayi rantsuwa bata tab'a sanin wani d'a namiji ba a duk tsayin rayuwarta. Daren ranar bacci b'arawo ne ya kwasheta. Kiran sallar asubahi kuwa, a kunnanta ladani ya kwad'a shi. Saukowa tayi daga kan gadon tare da kunna wutan d'akin haske ya kawo, babu kowa a d'akin, hakan ne ya tabbatar mata da ita kad'ai ta kwana a d'akin. Don da ace y'an uwanta sun dawo daga yawon banzan su jiya, babu abunda zai saka su kyale ta ta kwanta a kan gado ba tare da sun turo ta k'asa ba. Kai tsaye d'akin mahaifinta ta nufa, kamar yanda tayi tsammani hakan ce ta faru. Zaune ta samu mahaifin nata ya fuskanci gabas yana sallah a zaune. Don ciwon k'afar nasa bai barin sa yayi sallah a tsaye. Tun kusan shekaru biyar baya sallah dare ta zame masa tamkar jinin jikinsa. K'arfe uku kamar a kunnansa take bugawa saboda sabo da tashi. Bai kuma komawa bacci sai gari yayi tarwai tukun. Sarah d'aukar roban pentin da yake yin bowali tayi ta fitar dashi tare da zubar dashi a makewayi sannan ta dawo dashi ta ajiye sannan ta fita ta koma bayin ta kamo ruwa sannan ta fito ta d'auro alwala. Kamar zata wuce, sai kuma wani zuciyar ta jata ta nufi d'akin Lami. Tun daga bakin k'ofar take jin wani wawan munshari mara dad'in sauraro kamar an danne rago. Hannu ta d'an d'aura akan k'ofar ta tura, sai taji k'ofar a bud'e. Tura kai tayi ta shiga d'akin tare da lalubar bango ta kunna globe d'in dake d'akin. Lami ta hango tayi wani irin washarere a kan gadon kamar gawa, babu riga a jikinta daga ita sai d'aurin k'irji, shi kansa zanin yayi gefe, mamukanta kuwa d'aya ya kalli arewa, d'aya ya kalli kudu. Gata Ma sha Allah irin jibga-jibgan matan nan ne. Hatta bakinta a bud'e yake. Kau da kai Sarah tayi ta kalli d'ayan gefen da autarsu y'ar shekaru goma sha bakwai da watanni take. Ita ma dai bacci take yi cike da rashin tsari domin bacci ne irin wanda ba'a son musulmi ya rik'a yi wato ruf da ciki. Hannu Sarah ta kai ta d'aka mata duka cinyarta ta baya da yake a kwaye. Da sauri Aina'u ta kai hannu wajen ta Sosa ba tare da ta yanke baccin da take yi ba. Wani dukan Sarah ta kuma kai mata, wannan karan a furgice ta mik'e tana mitsitsitsike idanu tare da sakin wani irin hamma kamar d'iyar arna. Sai da ta ware rass sannan ta k'arewa Sarah kallo wutar balbalin bala'i na taruwa a kwayar idanunta. Don Aina'u irin fitsararrun yaran nan ne wad'anda duk girman mutum ko da kuwa jikinsa kaf furfurace bata raga masa. Y'an unguwanmu sun ce ita ce tayo sak halin Lami, wasu sun ce tafi Lami d'in ma. Tun tana k'ank'anuwarta makirar yarinya ce ta bugawa a jarida. Ga salo kamar wata uwar mata. "Uwar me zan maki cikin daren nan da zaki zo ki katse min bacci na!" Fad'in Aina'u kamar harcenta zai zazzago, don ta kasance irin matan nan masu harshe. Duk yanda tayi magana a hankali, ji za kayi kamar a kwar gida take magana. Da dare da rana basu da bambamci a wajenta. Yanzu haka da tayi magana kasancewar dare mai d'aukar sauti, har sai da mahaifinsu dake d'akinsa ya jiyo sautin muryanta. Hatta Lami mai bacci kamar gawa sai da ta farka a firgice tana sambatu. "Sallah nazo tashin ki kiyi. Don gashi can shirin tada sallar ake yi a masallaci. Ace duk k'arar speaker d'in masallacin can ba zai iya tada ku kuyi sallah ba!" Fad'in Sarah tana mai k'ok'arin juyawa ta bar d'akin duk da kuwa ta san cewa ba sallar za suyi ba. "Dan ubanki baza muyi sallar ba. Idan mun d'aga k'afa zamu shiga aljanna sai ki dawo damu baya saboda ta ubanki ce! Fita ki bar d'akin nan tsohuwar annamimiya!" Fad'in Lami tana mai nuna mata hanyar k'ofa. Komai Sarah bata ce ba, sai ma ficewa da tayi daga d'akin ta koma nata d'akin ta shimfida darduma ta tada salla. Tana nan zaune ko da ta idar da sallar har sai da gari ya waye tass, lokacin k'arfe bakwai sannan ta soma jin bacci a idanunta, amma kuma bata son yin baccin. Burinta ta shirya ta kuma fita domin yawon bin asibitoci ko za tayi dace da asibitin da scanning machine d'insu zai k'aryata cikin da wasu asibitocin da suke cewa tana dashi. Ta yunk'ura zata tashi daga kan sallayar taji muryoyin mata na tashi a tsakar gidan su. Gabanta ne ya buga da k'arfi sai tayi saurin d'aga labule kad'an ta lek'a waje. Da sauri ta saki labulen tana mai dafe k'irjinta da zuciyarta ke barazanar fasowa ta fito saboda arba da tayi da yayyin Farouq mata uku da kuma aunties d'insa guda biyu, gaba d'aya fuskokinsu a turbud'e..............


_Ko mai zai faru a gaba?>??_



*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Akwai ingantaccan maganin
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
[09/09, 10:03 AM] Matar Sayyadee: >؜?
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: _K'ANWAR MATATA_*>؜?

_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_


&? *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*&?

Page 4

"Ah'aaa! Yaya haka, menene haka kuma zuwa da sassafen na sai kace karb'an kud'in bashi? Ni fa bani son irin wannan naci tun ba'a je ko'ina ba." Fad'in Lami wacce fitowarta kenan daga d'aki baki duk miyan bacci. Bayanta kuma Aina'u ce ke mik'a tare da hamma babu addu'a sai wani "umm'iyyyyyyy!" Take fad'i kamar k'atuwar rago ko kuma bijimin sa. D'aya daga cikin matan wacce sai jijjiga take yi, ga dukkan alamu tafi kowa a cikin su hassala tace, "To dama uban me zai kawo mu wannan wulak'antaccen gidan wanda babu albarka cikinsa in ba tsautsayi ba. Banda fitina da jawowa kai jidali irinta Umar Farouq, menene abun so a cikin y'ay'an gidan nan wanda gaba d'aya kowa ya gama sanin karuwan gida ne su." D'ayar siririyar cikin sy tayi saurin cafe zancen wajen fad'in, "Aunty Bilkisu ai gansama-gansaman zaurawar gidan nan sun wuce karuwan gida, don ni kam ba zan Kira su da y'an mata tunda tun daga kan babbar har k'aramar babu wacce bata san dad'in d'a namiji ba." Saurin cafe zancen k'aramar cikin su tayi tare da fad'in, "Yo aunty Halima ai ga zahiri tunda kina ganin shegu ta kowani lungu na gidan an ajiye. Kai Allah yai wadaran naka ya lalace. Wallahi ko wucewa ta kwar gidan nan ban k'aunar yi balle har in tako k'afata cikin gidan nan." Lami kuwa dake tsaye suke fad'in duk abunda yazo bakinsu, wani shewa tayi tare da nuna wacce aka kira da aunty Halima tace, "Alhamdulillah, ko yau na fad'i na mutu za'a nuna abunda na bari ace Allah sarki ga y'ay'an wance da ta bari. Ke kuwa fa? Ko b'ari kin tab'a yi ne? Idan fitsari banza ne, kaza tayi ma. Kuma y'ay'ana Kainuwa ne, babu yanda aka iya dasu. Duk wani munafurcin ku da k'ananun maganganunku, kanku zai koma." Aunty Halima wani tsalle ta daka kamar za tayi wasar y'ar gala-gala sannan ta bugi k'irji kare da fad'in, "Haihuwa idan har irin taki ce Lami, kada Allah ya bawa ruwan maniyy d'in mijina isa ga mahaifata. Ai da Haihuwa irin y'ay'anki wallahi gwara b'arinsu. Lami haihuwa irin taki ko, na gwammaci har in koma zuwa ga ubangijina ban ajiye ko kwai d'aya a duniya ba. Kuma ki bud'e kunnuwanki dakyau kiji, idan har ni k'anwar mahaifiyar Umar Farouq ce, to wallahi auren sa da Sarah sai dai bayan raina. Domin Na'ima har gida taje ta samu mahaifiyar Umar ta fad'a mata y'arki da ake son mak'alawa d'ana, tana d'auke da ciki. Dama kuma banda hauka da rashin hankali, mai Farouq zai ci da d'iyar karuwa, tubabbiya wacce sana'ar danginsu kenan karuwanci! Mun bar maku duk wani abu da aka kawo gidan nan da sunan naiman auren y'arku, sai dai amma ki sani, babu aure tsakanin zuri'arki da namu zuri'ar." Wani irin rushewa da kuka Sarah tayi jin abubuwa da Aunty Halima take fad'i
A bayyyane ta soma fad'in, "Shikenan, Farouq d'in ma ya sub'uce min. Dama na sani ba zan tab'a aure ba a rayuwata." Ta fad'i hakane tana mai kaiwa cikinta duka da duka hannunta biyu. Lami kuwa kitchen d'in dake tsakar gidan ta nufa tare da d'auko katoton tab'aryarta mai nauyi da tsayi tayo kan su Aunty Halima don har cikin ranta taji zafin maganganun da aunty Haliman tayi mata. "Aunty Halima, aunty Halima!" Siririyar mai suna Najma ta kwad'a kiran sunan aunty Halimar tare da fizgo hannun aunty Bilkisu ta janye ta baya saboda kawo tab'aryar da Lami tayi. "Barta, barta ta jawowa kanta bala'i Najma. Wallahi ba zan gudu ba, karyar hauka take yi, idan ta isa ta buga min taga abunda zai faru da ita yau d'in nan." Fad'in aunty Halima amma deep down tana jin tsoran kar Lami ta buga mata zabgegiyar tab'aryar dake hannunta. Lami kuwa k'ara yowa kansu tayi da tab'aryar ta d'aga sama zata kwad'awa aunty Halima da tayi k'arfin hali tak'i guduwa. Caraf taji an rik'e tab'aryar ta baya, a fusace ta juya suka yi idu hud'u da Sarah wacce idanunta suka kad'a suka yi jazur alamar tayi kuka. "Cika min tab'aryana ko inci ubanki cikin gidan nan!" Lami ta fad'i da k'arfi tana mai zarowa Sarah idanun. "Dan girman Allah Lami kar ki tab'a su, ki kyale su. Yanzu idan kika bugawa d'aya daga cikin su, RAI kuma yazo yayi halinsa, ya za kiyi?" Fizge tab'aryar tayi tare da fad'in, "To idan na kashe sai me? Ko kotu aka je babu wanda za tuhume ne don sune suka biyo ni har cikin gidana. Duba kiga cikin zuri'ar da kike son shiga, su kansu tun daga yanayin shigarsu zaki fahimci babu abun arziki a gidan. Daga ganin kayan jikin wannan shanyayyiyar matan (Tai nuni da aunty Bilkisu) kayan jikinta kwance ne. To a nan wajen mai na sama yaci balle ya baiwa na k'asa. Shashasha! Ni Allah ya yiwa Na'ima albarka da har taje gidan su Farouq d'in ta fad'awa mahaifiyarsa kina d'auke da juna biyu. Dama kuma nayi rantsuwa idan har ni y'ar Samuel da Debora ce ba zan tab'a bari kiyi aure da d'an iskan yaron nan ba. Sai gashi Allah ga kawo hanya mafi sauk'i. Ke bama shi ba, babu ke babu aure da kowani namiji a duniya nan." Salati gaba d'aya su Aunty Halima suka d'auka suna tafi. "Eh lallai! Yau na tabbatar da ke d'in cikakkiyar arniya kuma bakatafiya ce ke. Kin fi k'aunar suyi ta gantali a titi suna yawon hotel-hotel suna kawo maki kud'i kina musu goyon shegu ko? Tirr! Shiyasa aka ce idan za kayi aure ka auri uwa ta gari domin ta haifo maka y'a'yana nagari. To kema kan ki ba tarbiyar gare ki ba balle ki bawa y'ay'anki tarbiyan." Kamun Lami tayi magana, sai ga Na'ima da Nuratu sun shigo gidan a tare ko wacce hannunta rik'e da manya-manyan ledoji. Washe baki Lami tayi tare da fad'in, "Ka ga y'ay'an albarka wanda aka haife su tsiya na barci!" Baki sake su Aunty Halima suke kallon su Na'imar da sai wani yatsine-yatsine suke yi. "Lami akwai ruwan wanka kuwa a gidan nan? Don ni wallahi a mugun gajiye na dawo. Mutun hud'u suka yi ciniki na." Amshe maganar Nuratu tayi tare da fad'in, "Wallahi nima a gajiyan nake tib'is. Ni mutum d'aya ne ma ya d'auke ni muka tafi _Asa pyramid_, wallahi ko runtsawa banyi ba. Ruwan zafi nake buk'ata sosai in galgasa jikina." Washe baki Lami tayi tare da fad'in, "Y'ay'an albarka, y'ay'an gwal kenan. Babu ruwan zafi amma yanzu nan zan had'a wuta na d'aura maku, ku shiga daga ciki naga alama babu k'arfi a jikin ku gaba d'aya duk kun yi laushi." Su aunty Halima kuwa, wannan ta kalli wannan, sai wannan ta kalli wannan, haka su kayi tayi tsakanin su suna mamakin hali irin na Lami. "Way'annan kuma mi suke yi a nan gidan?" Fad'in Nuratu tana kallon su d'ai-d'ai. Sai da Lami ta balla masu harara sannan tace, "Wai zuwa suka yi su fad'a mana sun janye auren da suke nema na Sarah. Baki ganni da tab'arya a hannu ba, ai tahowa nayi in sheme y'an iska." Gaba d'aya daga Nuratun har Na'ima kallon Aina'u suka yi tare da fad'in, "Ke dan ubanki tsayuwar mi kike yi da baku tare ke da Lamin kun kakkarya k'ashin bayansu ba!" Aina'u tayi wani tafi tare da fad'in, "Ai ni jira kawai nake yi Lami ta fara kai hannu kiga suga yanda ake yi a cikin gidan nan, don billahil lazi babu wacce zata fita da kaya a jikinta. Sai na tabbatar mun yi masu tsirara sannan mu hankad'a su waje." Cire siririn gyalenta Na'ima tayi sannan taci d'ammara dashi tare da kallon Nuratu tace, "Maza je rufo mana k'ofar gida saboda kar su samu damar fecewa." Da gudu Nuratun ta nufi k'ofa ta saka lock tare da sakata sannan ta dawo. Wani dogo sanda wanda aka ajiye a barandar d'akin mahaifinsu Nuratu ta d'auko, Na'ima kuma ta d'auko muciya, ita kuma Aina'u ta koma d'aki ta d'auko wata murd'ad'd'iyar bulala. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Nasiba sai da nace maku kar muzo gidan nan. Mu kira kawai a waya ya wadatar. Yanzu kinga d'aya daga cikin jahilci da rashin hankalin nasu ko." Fad'in aunty Lubabatu wacce bata cika fitana ba, asalima ita taso abi komai a hankali amma Mama ta matsa su tafi su fad'a masu sun janye neman auren. "Wai nan tsoro kike ji? Ai wallahi sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, mu biyar ne fa!" Fad'in Rahima wacce ita ma tunda aka fara fad'an bata ce komai ba sai yanzu. "Baki da hankali hala? Gidansu fa muka iske su. Wallahi mune a ciki ko kotu aka je!" Ko kamun wani ya fara magana a cikin su, Nuratu ta shak'o wuyar aunty Halima ta baya ta kaita k'asa. Ganin haka ya saka gaba d'ayan su suka hau Nuratu da duka domin ceton aunty Halimar don tana kaita k'asa ta hau dukanta da sandar da ta d'auko. Suma su Lami na ganin haka, sai suka hau kansu da duka. Aina'u sai zabgawa ko waccen su zambad'ed'iyar bulalan hannunta take yi, Na'ima kuma tana maka masu muciyar hannunta. Kan kace kwabo, kasancewa su Nuratun da makami a hannunsu, tuni jini ya fara sharara a goshin aunty Luba, Aunty Halima da Najma. Don sun fi kowa buguwa. Ga shaidan bulala ta ko'ina a jikinsu. Sarah kuwa gefe ta koma tayi ta rusa kuka don ita kanta ta samu nata rabon wajen ceton su aunty Halimar. Baba ne ya samu ya fito da kyar don k'afar na matsa masa da ciwo sosai. Yana fitowa tsakar gidan ya tsaya turus, don tun shigowar su aunty Halimar yake sauraran komai daga ciki yana share hawayen bak'in ciki. Babu wacce yake tausayi banda Saratu don ya san ba k'aramin damuwa zata shiga ba na fasa auren nan nata da ake shirin yi. "Ke! Nuratu, Na'ima, Lami, Aina'u, wallahi kamun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login