Showing 39001 words to 42000 words out of 129558 words

Chapter 14 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

nake jinsa." Ba tare da Aina'u tace komai ba ta fice haushi kamar ya kashe ta na rashin shan fantar da Sarah bata yi ba yanzu. Tana fita daga d'akin wayar Sarah ta soma ringing. Kai hannu Sarah tayi tare da d'auko wayar dake kan one sitter dake d'akin. Kallo d'aya yayiwa numbern ta gane _Khalil_ ne duk da kuwa bata yi saving number d'in ba sabida 3 d'in guda shidda da ya k'are da numbers d'in. Sai da ta turo baki sannan tayi picking tare da mik'ewa ta hau kan gadon sannan tace, "Assalamu alaikum!" Ajiyar zuciya _Khalil_ ya sauke tare da fad'in, "Amin wa'alaikissalam amaryata. Har kin fara bacci ne baki jira naji yanda kuke ba?" Bata ce masa komai ba sai ma mirginawa da tayi zuwa k'arshen gadon. "Baza kiyi magana ba?" Ya fad'i yana mai gyara kwanciyarsa. "To ni mai zan ce? Bacci fa nake ji sosai." Ta fad'i tana mai lumshe idanu." "To kiyi baccin ki mana. Na hana ki ne?" _Khalil_ ya fad'i yana murmushi. "To ta yaya zan yi bacci bayan ka hana ni? Ka kashe wayar to sai in kwanta." "Wato kin manta da deal d'in mu kenan ko?" Ya fad'i har da yiwa wayar hannunsa gwalo kamar tana ganinsa. Itama hararar wayar tayi tare da fad'in, "Tab! Ai yanzu babu wani zancen deal kuma." Waro idanu yayi tare da fad'in, "Inji wa ya fad'a maki haka? To ni dai har yanzu deal d'in mu na nan." Bata san lokacin da tace, "Duk da manya sun shigo cikin zancen?" Dariya ne ta kama shi, amma sai ya gimtse tare da fad'in, "Da kin haihu zan yi abunda nace maki zanyi. Zan karb'i baby na sai in fad'awa Baba na janye. Kin ga ai shikenan na zama mai cika alk'awari." Nan da nan Sarah taji bacccinta ya washe har da tashi daga kwance ta zauna tare da fad'in, "To ni ya zanyi da Baba kenan bayan nayi masa alk'awarin zan yi maka biyayya? Ni dai gaskiya a rushe....." Sai kuma tayi saurin yin shuru tana mai toshe bakinta da hannunta. Dariyar da yake ta rik'ewa ta kufce tare da fad'in, "Ashe dai ana son _Khalil_ d'in ake masa yanga." K'ok'arin yanke kiran take yi yayi saurin fad'in, "Kar ki fara ki yanke min waya tunda ba ke kika kira ba, ni na kira ki." "To wai ni kai aljani ne? Ta yaya kasan yanke wayar zanyi?" Sarah ta fad'i tana sauraran jin abunda zai ce. "Da motsin hannunki na gane. Kar kiji tsoro _Khalil_ d'inki ba aljani bane. Yanzu dai yaya kike?" "Lafiya." Ta bashi amsa kai tsaye. "Menene wani Lafiya! Sai kace yak'i. A haka ne zaki min biyayyar da kika ce kin yiwa Baba alk'awari." "Ni dai to ai babu abunda nayi maka. Tambayata kayi ni kuma na baka amsa." Ta fad'i tana mai lumshe idanu do hirar tana mata dad'i, hatta d'an bacci da take ji sai da ya gudu. "Hirar na maki dad'i ko?" "inji wa?" Sarah ta fad'i da sauri don mamaki _Khalil_ yake bata kamar wani aljani. Shi kuwa ya dai fad'a ne kawai don yaji mai zata ce. "Saurara in yi maki wata wak'a kiji." Yana fad'in haka ya soma fad'in, " _Ina kewaaa ina kewar masoyiya! Ina kewaaa ina kewar aminiyaa!! Abokiyar shawara, kece kin d'ara, kin sab In ba dake ba sai in hak'ura. Ki bani y'ar dama, a san dani nima, ki mini alfarma ki sanya ni a zuciya. Ki kau da y'an gulma, irinki ke nema, suna ta shan famaaa sun zaga ko ina. Mace ba ai ba kece, kuma kin san mun dace, a kanki na zauce! Magana d'aya ba shakka, hannu d'aya kan jinka, ta yaya zai d'auka, samunki baiwaa ce. Bakya fushi, ki murmushi, don sanki na shiga raina, ko babu ni in kin tunani wannan shine muradina. Nasan kina da buri kuma sannan kina da tsaarinki, da zaki sa cikin ranki, nine zan zama angonki. Farar tumfafiyata, daban cikin mata, a sonki nai rata a kanki na gane kaina. Kece nai wa alk'awari, mace d'aya kuma kin zarce d'ari, kin zam min bangon sukari, ko a ina kece. Sirrin ciki yazo fili, kin iya ado da d'an kwali, mai kyan ido da sa kwalli, an iya miki zanen lalli. Tun da na same ki na huta, saura sunka nazarta, bana iya kallon mata kiji kalmar dana furta. Akwai dad'i abunda kake so in ya soka, shi fatan da kakewa wasu sai ya bika. So sa'a ce, samun nasarace, ke sa ai daceee, ni kam na samu. So akwai tsada, sanyi sai randa, shanu ke hud'a furar mu nai damu. Nai nasara samunki, barni na zam jigonki, zan b'oye sirrinki ba ran da zan tona. kewa, keee, kewa! Ina kewaa, ina kewar masoyiyaaaaaa!_" Gaba d'aya ya gama kashe mata jiki da zazzak'ar muryansa, sai taji wak'ar ma a bakinsa yafi dad'i kamar shi ya rera ba auta wazirin ba. "Ka tab'a shiga studio ne?" Ta jefe shi da tambaya. "A kanki dai zan fara _mine_" "Kuma ka iya wak'ar sosai wallahi." Sosai yaji dad'in yabawa da tayi har sai da ya saki siririyar murmushi tare da fad'in, "Kullum zan rik'a rera maki wak'ok'i kala-kala a kunnanki idan kika dawo kusa dani. Kina so?" "Ni dai babu ruwa na Allah!" Dariya ta bashi kuma sai da ya daran kamun yace, "Da aka yi me?" "Ai dai babu kyau irin maganganu da kake yi" d'aga idanu sama yayi tare da fad'in, "Wanne kenan a ciki?" Ya fad'i yana k'umshe dariyarsa. "Oho!" Ta fad'i don ta gane so yake ta maimaita mai yace. "To yanzu dai abunda nake so dake, ki d'aura hannunki a kan cikinki kiyi addu'a sosai, sannan kiyi addu'ar bacci ki kwanta. Will call you in the morning kamun na tafi asibiti. Bye I love you." Yana gama fad'in haka ya katse kiran tare da rungume wayar yana jin kamar Sarah ya rungume ita da cikin dake jikinta. Allah ya d'aura masa k'aunar wannan ciki. B'angaren Sarah itama wani murmushi ta saki bayan ya katse wayar. Sai muryansa yake tayi mata echoing a cikin kanta lokacin da yake rera mata wak'ar kewa na auta waziri. Cike da farin ciki bacci mai dad'i ya kwashe ta bayan tayi addu'a kamar yanda ya umarceta. Aina'u kuwa ko da ta sake shigowa d'akin taga Sarah nata sharar bacci kuma bata sha fanta ba, sai taji kamar ta danna mata pillow ta mutu kowa ya huta. Fita tayi bata sake dawowa ba sabida yanda ta shak'a. Da asubahi Sarah ta tashi domin yin salla, babu kowa a d'akin don duka yayyin nata ba gida suka kwana ba. Tana jiyo kukan Fadwa daga d'akin Lami sabida ba'a yayeta ba haka Marfu'a take tsallaketa ta barta wajen Lami ta tafi gantalin da ta saba. Fitowa Sarah tayi ta kama ruwa sannan ta d'auro alwala. Sai da ta dubo Baba taga shima ya d'auro alwalar sannan ta koma d'aki dan yau bata yi gigin zuwa d'akin Lami domin tada su ba. Bayan ta idar da sallah, wani baccin ne ya kuma fizgarta. Kiran da _Khalil_ yayi mata ne ya farkar da ita. Amsa wayar tayi cike da muryan bacci tana fad'in, "Ina kwana, an tashi lafiya?" Daga can _Khalil_ yace, "Lafiya k'alau. Halan baki tashi ba?" Gyara kwanciyarta tayi tare da fad'in, "Kiran wayarka ne ta farkar dani." "I'm sorry ki koma baccinki. Amma kuwa ki sanar da Baba zuwa anjima wasu zasu kawo kaya. A fitar da duka abubuwa dake cikin dak'unan gidan please. D'akuna uku ne ko?" Da "Eh" Sarah ta amsa tana mamakin mai kuma za'a kuma kawo masu a gidan. "Yauwa to ki koma barcinki. In Sha Allah by 11:00am zasu zo." "Allah ya kawo su Lafiya." Sarah ta fad'a shi kuma ya yanke wayar tare da saka safa sannan ya saka takalmi dama kuma abunda ya rage ya saka kenan ya fito daga d'akinsa ya kulle ya nufi d'akin Hajiya. Sai da ya kwankwasa sannan ya turo ya shiga. A zaune a gefen gado ya samu hajiyar sai ninke kayan sawanta take yi. "Ina kwana hajiya?" Lafiya kawai tace masa tare da cigaba da abunda take yi don har yanzu haushinsa take ji. "Hajiya ina Laure da kike wannan aikin da kanki." "Tuni ta koma gidan ubanka da zama. Tashi ka fice ka bani waje. Sha-sha-sha kawai." Da sauri ya mik'e yana mai fad'in, "Allah ya huci zuciyarki Hajiya. Sai na dawo." Ko kallonsa bata kuma yi ba har ya fice sai a sannan ta d'ago ta watsawa bayansa harara. Bai had'u da kowa ba kasancewar ko k'arfe takwas na safe bai yi ba. Kai tsaye wajen motarsa ya nufa tare da shiga yayi reverse ya fice daga gidan zuwa asibiti. Sarah kuwa bata iya komawa bacci ba ta sauko daga kan gadon ta nufi d'akin Lami. Sai da tayi sallama sannan ta shiga, a zaune ta samu Aina'u tana shan tea da, bread da kwai. Gefe kuma Lami ne sai gyangyad'i take yi don bata samu bacci ba jiya sabida damunta da kuka da Fadwa tayi tayi jiyan. "Ina kwana Lami." Lami bata amsa ba sabida wani gyangyad'i mai dad'i da ya kwashe ta. "Lami." Karo na biyu Sarah ta kuma kiran sunanta, firgigit ta farka har miyau na zubo mata daga baki. "Wannan wani irin iskanci ne haka Saratu? Ya zaki tashe ni kuma na san kin san ban samu ishashshen bacci ba jiya." "Kiyi hak'uri, dama _Khalil_ ne yace in fad'a maku a fitar da duka kayan d'akunan gidan b'aki za suzo anjima." Tuni Lami ta watstsake tare da fad'in, "Da gaske kike yi Sarah. Wayyo Allah arziki yazo mana har cikin gidan mu. Maza tashi Aina'u a fara aiki tun yanzu kamun sauran y'an uwanki su dawo." Tsabar bak'in ciki Aina'u ko magana bata yi ba sai ma mik'ewa tayi ta bar d'akin don ji tayi bread d'in da ta saka a baki d'aci yayi mata kamar tana taunar magani. Lami kuwa tashi tayi ta soma fitar da wasu kayan. Ganin Aina'u ba taya ta za tayi ba, sai ta fita ta kira almajirai suka shiga fitar da kaya. Sai da suka fitar da kayan d'akinta kaf sannan suka soma fitar da na Baba kasancewar Sarah taje tayi masa bayani. Zuwa k'arfe goma sun gaba fitar da duka kayan gidan har da nasu d'akin Sarah. Lami tsabar zari har ta kira dillaliya ta saye gado da katifar d'akinta da na Sarah. Taso had'awa har da katifar Baba amma ya hanata. Sai da hakan ya kai su ga rigima har Lami na zaginsa tana kiransa matsiyaci. Lokacin da sauran y'ay'an nata suka dawo suka ga gaba d'aya babu komai a d'akunan gidan suka shiga tambayar ba'asi. Nan Lami ta shiga fad'a masu cewar ai _Khalil_ ne zai kawo masu sabbin kayan d'aki yau shiyasa aka fitar da komai ta sayar. Sarah kuwa mamaki ne ya cika ta ko yaushe suka yi hakan da Lami d'in. Ita dai ta san _Khalil_ ce mata kawai yayi a fitar da kayan d'akunan gidan. Gaba d'aya su Na'ima suka hau murna banda Aina'u da ta bar gidan sabida mugun hali. K'arfe sha d'aya dai-dai kamar yanda _Khalil_ ya fada sai ga tsayuwar motar company a k'ofar gidansu Sarah. Kwalaye suka dunga shigowa dasu suna ajiyewa a tsakar gidan. Sai da suka gama kwaso kayan tsaf sannan suka tambaya inane d'akin Baba. Da hannu Sarah dake tsakar gidan ta nuna masu, caraf Lami tace, "Wallahi tallahi babu uban da ya isa, da d'aki na za'a fara. Ai ni ce na sha wuyar mak'uda ba shi ba." Ma'aikatan ba tare da musu ba suka d'auki kwalayen tare da shiga d'akin Lamin da aka share tsaf aka goge, don ita d'akinta akwai tiles. Cikin mintuna talatin saboda kwarewarsu har sun kammala had'a gado da komai. D'akin ba k'aramin kyau yayi ba. Gadon kalar b'aki da purple. Wardrobe d'in kuma irin mai cin bangon nan ne mai k'ofa shidda. Hatta labule sabo suka saka mata sannan suka mak'ala mata TVplasma sannan suka fita suka koma d'akin Baba. Shima haka suka jera masa nasa kayan irin na Lami sak sai dai akwai bambamcin launi. Shi nayi farare ne k'al. Kuma kamun su saka sai da suka shimfid'a masa lallausar carpet da ya mamaye d'akin mai tsada kalar blue-black. Sannan suka saka masa TVplasma irin flatscreen d'in nan wanda kud'insa zai kai 250k zuwa 300k, dama kuwa akwai masu had'a dish a waje kuma har sun kammala, sai kawai suka shigo suka yi settings kasancewar ko wani d'aki yana da decoder d'insa. D'akin Baba har da tvstand mai kyau. D'akin su Sarah suma ab had'a masu nasu furniture d'in wanda ga kasance white and baby pink. Kuma gadonsu six by seven ne yayin da su d'akin Baba ya kasance six by six. Gaba d'aya gidan sai ya koma kamar gidan amare. Komai sabo. Don har da dank'areran deepfreeze da kuma fridge _Khalil_ ya siya masu. Wajejen k'arfe biyu suka kammala komai suka wuce. Lami kuwa sai uban gud'a take yi. Lokacin da ta shiga d'akin Baba domin taga irin nasa gyaran, sai bak'in ciki ga rufe ta ta shiga surfa bala'i mai yasa ita ma ba'a saka mata Tvstand stand ba. Baba kasancewar baya son tashin hankali yace ta d'auka ta kai d'akinta. Babu kunya kuwa ta kama ita da Nuratu suka mayar d'akin nata. Aina'u kuwa ba ita ta dawo gidan ba, sai bayan magriba. Tana sauka daga napep ta taras da zambad'ed'iyar motar _Khalil_. Wani mugun tsaki ta saki tare da isa k'ofar gidan ta tura ta shiga kuma a dai-dai lokacin ta hangi bayan _Khalil_ d'in zai shiga d'akin Baba. Tsayawa tayi tana k'arewa d'akunan kallo ganin ko Wanne da sabbin labulaye. Dai-dai nan Sarah ta fito daga bayi hannunta rik'e da buta, tazo dai-dai inda Aina'u take, sai ta saka mata k'afa tayi wani irin mugun fad'uwa, ji kake tim. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Sarah ta fad'i da k'arfi tana mai kai hannu k'asan mararta. Aina'u kuwa sai tayi saurin sunkuyawa tana fad'in, "Sannu Sarah, garin yaya kika fad'i haka." Gaba d'aya gidan suka fito, _Khalil_ ya riga kowa fitowa da gudu jin muryan Sarah tana salati. Ita kuwa Sarah sai cewa take "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, cikina, wayyo Allah cikina." Rintse idanu _Khalil_ yayi da k'arfi ganin zini na gangarowa daga k'afafunta...............






*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*

*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*

*_MATAR SAYYADEE_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*PAGE 15*


_Jinjina a gare ku my fans, kuna nishad'antar dani musamman y'an K'ANWAR MATATA comments section, irin su my besty (Queen Zarah), Rahamanatou, Oum Muslim, Mrs dimples, Halimatouu, Maman auwal k'awata, Jik'amshi collection, Mrs Z A musawa, Hadiza Mbello, Tatiesha Rufa'i, My Rabi'a, Yayata maman Islam, Bab??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yshamas, da abokiyar fad'ata Ummu Muhammad da sauran da basu ji sunasu ba duka. Ina maku sonso. Allah ya bar k'auna mutanan Lami da Aina'u=??_


Ba tare da jin wani kunya ba _Khalil_ ya ciccib'i Sarah yayi waje da ita Lami biye dashi ita da Nuratu da Na'ima. Aina'u kuwa wani irin murmushi jin dad'in hak'arta ta cimma ruwa duk da bata tab'a kawo cewar abunda ya faru da Sarah zai iya faruwa da ita ba sanadiyar fad'uwar da tayi. Ita tayi ne kawai sabida mugunta. A baya ya shimfid'ar da ita, da sauri Lami da su Na'ima suka shiga cikin motar, _Khalil_ kuma ya zagaya ya shiga mazaunin gaba tare da tada motar ya bar unguwar da gudu ganin ba k'aramin jini ke zuba daga jikin Sarah ba. Baba kuwa kamar ya fashe da kuka, gashi babu k'afar bin bayansu. Sai dai abunda yayi matuk'ar bashi mamaki ganin Aina'u tana bin jinin Sarah da ya zuba a k'asa tana wani dariyar k'ata. Kwata-kwata bata lura da Baba dake bakin k'ofa yana kallonta ba. "Aina'u kar dai kece sanadiyar abunda ya samu y'ar uwarki yanzu?" Da sauri ta kalli inda baban yake a tsaye tare da fad'in, "Da aka yi yaya kenan Baba? Shikenan babu damar nayi dariya. To ni dariyata wani abu take nufi can daban." Juyawa Baba yayi tare da komawa d'akinsa don ya dad'e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login