Showing 33001 words to 36000 words out of 129558 words

Chapter 12 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

yake fad'in, "Naji, duk nine. Kiyi hak'uri ki yafe min. Kin ga ai ban raba ki da budurcinki ba." A fusace tace, "Wallahi ba zan tab'a yafe maka ba. Karuwi kawai. Mijina ma ba zai tab'a yafe maka ba don ka cutar dashi ka shiga gonarsa." "Haka be naji duk ba amince. Kiyi hak'uri amma ki min afuwa. Tsautsayine wallahi ba hali ba bane." "Halinka ne Allah kuwa. Mugu mai lalata yaran mutane a hotel." Mik'ewa yayi ya tashi zaune. Da saurin ta mirgina sai ji kake tim a k'asa ta d'auka wani abun zai kuma yi mata. "Wayyooooo Allah na shiga uku k'afata." Ta fad'i da k'arfi dai-dai lokacin da ta d'auki boxer d'insa ya saka tare da saukowa ya kunna switch d'in d'akin. Da sauri Sarah ta jawo zanin gadon ta rufe jikinta tana kuka sosai da bak'in cikin abunda yayi mata. Matsowa yayi domin yaga halin da k'afar take ciki, wani irin ihu ta saki tare da k'ank'ame jikinta. Matsawa yayi yana kallonta. Ita kuwa sai k'ara kakkare jikinta take yi tana kuka. "I'm sorry kin ji. Ina zuwa yanzu bari na dawo." Ya fad'i hakan tare da d'aukar dogon wandonsa ya saka da riga ya fita da sauri. Sarah na ganin ta fita ta mik'e da sauri ta d'auki kayanta ta saka. Ko tsayawa d'aukar jakarta bata yi ba domin kada ya dawo ya idda ita. Da sauri ta bud'e d'akin ta fice daga hotel d'in tana b'oye-b'oyen fuska. Lokacin da _Khalil_ ya dawo bai d'auka bata d'akin ba ganin ga jakarta a kan gadon. Zama yayi a gefen gado hannunsa rik'e da wani magani yana jiran fitowarta daga bayi, mintuna biyar suka shud'e yaji shuru, wani biyar d'in ya k'ara shud'ewa nan ma shuru. Mik'ewa yayi tare da isa k'ofar bayin ya soma kwankwasawa, jin shuru sai ya tura k'ofar. Wayam ya gani. Da mugun sauri ya tashi ya fita ya dunga dube-dube ko zai ganta, amma babu ita babu dalilinta. Gashi babu wani makama da zai gane inda take, ko sunanta bai sani ba. Komawa cikin hotel d'in yayi tare da bud'e d'aukar jakarta da wani abu kamar d'an kwali da ta bari ya fita ya bar hotel d'in. Tun daga wannan ranar _Khalil_ bai sake farin ciki ba, kullum cikin neman Sarah yake yi. Kuma Allah bai k'ara had'a su. Sai bayan kwanaki ashirin da uku a asibitinsa. Aina'u ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba ganin irin uban kaya da _Khalil_ ya jido. Ji take kamar zuciyarta zata hudo k'irjinta ta fito tsabar bak'in ciki. "Hajiya tun d'azu ake kiran wayarki." Fad'in Laure tana mai mik'awa Hajiyar waya. Amsa Hajiya tayi bayan ta shafa addu'a don sallar magriba ta idar kuma dai-dai nan aka kuma kiran wayar. "Assalamu alaikum" Fad'in Hajiya bayan ta amsa kiran ta kara a kunne. "Wa'alaikissalam, dan Allah Ina magana da Hajiyar doctor _Ibrahim Khalil_ ne mai asibitin *_Khalilullah specialist hospital_*?" Kallon Laure Hajiya tayi tare da mata nuni da hannu alamar ta fita bayan ta amsa da "Eh ita ce. Allah yasa lafiya?" Daga can aka d'an yi jim kamun wacce ta kira wayar ta soma fad'in, "Hajiya akwai wani abu da d'anki yake b'oye maki mai matuk'ar muni wanda ke baki sani ba. Kuma a irin tarbiyan da kuka bashi idan na fad'a maki abunda yake aikatawa, sai kin girgiza." Hankalin Hajiya tuni yayi wani irin mugun tashi ta soma fad'in, "Baiwar Allah ya zaki kira ni kina fad'a min irin wannan maganganun masu d'aga hankali? Mai _Khalilullah_ yake aikatawa wanda ban sani ba?" "Uhm! Hajiya idan d'an ki ya dawo, ki tambayesa wacece Saratu?" Mik'ewa Hajiya tayi tana fad'in, "Dan Allah yarinya kiyi maganarki kai tsaye, mai _Ibrahim_ yake aikatawa wanda ban sani ba?" "Hajiya d'an ki dai yana da budurwa, ko kuma ince maki dadironsa! Don kuwa yanzu haka da nake fad'a maki, ki fara tanajin jiran isowar jika nan da wata takwas masu zuwa, don kuwa d'an ki yana neman wata yarinya wacce gaba d'aya gidansu karuwai ne kowa ya sani. Sunanta Saratu ana ce mata Sarah. Tana da yayyi mata hud'u, kuma gaba d'ayansu babu wacce bata ajiye shege ba a cikin gidan. Sannan kowa ya san su karuwai ne. Kuma abunda zai baki mamaki, a gaban uwarsu da ubansu suke. Idan kuma baki yarda da maganata ba, idan _Khalil_ ya dawo tambayar da zaki fara yi masa shine wacece Saratu. Yanayin da zai nuna kawai ta isa ya tabbatar maki da zance na. Na barki lafiya Hajiya." Tsabar tashin hankali da rikicewa Hajiya fitsari ta soma saki ba tare da sani ba, da rarrafe ta shiga bayi ta soma sakin zawon tashin hankali............


*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*




*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*

*_MATAR SAYYADEE_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*PAGE 13*


*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*

Abu kad'an ke saurin d'aga mata hankali. Babu mamaki yanzu idan aka duba BP d'inta aga ya hau. Ta jima duk'e a bayin kamun ta iya cire kayan jikinta tayi wanka sannan ta sake d'auro alwala ta fito ta sauya kaya. Tuni wani zazzafan zazzab'i ya rufeta sai kakkarwa take yi a bakin gado. Dai-dai nan Laure ta shigo bakinta d'auke da sallama tana fad'in, "Hajiya a kawo maki zogalen yanzu?" Da sauri ta k'arisa shigowa d'akin tana fad'in, "Hajiya lafiya? Mai ke damun ki? Yanzu fa na barki lafiya kina amsa waya." Dakyar Hajiya tace, "Tafi ki kira min Maryamu yanzu a b'angarensu." da sauri Lauren ta juya ta bar d'akin har da had'awa da gudu ta nufi side d'in aunty Maryam tare da danna doorbell. Mijinta Yaya Abdul-Hakeem ne yazo ya bud'e k'ofar tare da fad'in, "Lafiya Laure na ganki a rud'e?" Ya fad'i don shima dawowarsa kenan daga wajen aiki. Yanzu nan kuma yake son shiga wajen Hajiyar. "Yaya Abdul Hajiya ce ba lafiya shine tace in kira mata aunty Mar....." Ko kamun ta k'arisa maganar har ya tureta ya fito da sauri ya nufi side d'in Hajiyar kamar zai tashi sama. Aunty Maryam ma da sauri ta fito don fitowarta kenan daga kitchen taji abunda Laure ke fad'awa mijin nata. Bin bayansa suka yi ita da Lauren hankali tashe. Ko da yaya Abdul ya isa d'akin Hajiya, gaba d'aya ta gama firgicewa. Jikinta yayi mugun zafi musamman ta wajen kanta. Zama yaya Abdul yayi tare da tallabo Hajiyar yana fad'in, "Inna lillahi! Hajiya mai ya same ki. Ai bamu ga ta zama ba. Mu tafi asibiti kawai." Dai-dai nan aunty Maryam d'in ta shigo ita da Laure. "Abdul-Hakeem d'au wayarka yanzu ka kira min _Khalilullah_." Hajiya ta fad'i hakan da kyar. Yaya Abdul bai kawo komai a ransa ba sanin k'anin nasa ai doctor ne. Maybe don yazo ya duba tane don Hajiya ta tsani zuwa asibiti. Wayarsa ya fiddo tare da kirar _Khalil_ d'in. Ringing yayi har ya katse ba'a d'aga ba, zai sake kira kenan sai ga shigowar kiran _Khalil_ d'in. D'agawa Abdul-Hakeem yayi tare da fad'in, "Kana ina?" Daga can _Khalil_ yace, "I'm sorry yaya, na fito da wayar kenan zan d'auka sai katse. Gani kusa da gida." "To kayi maza ka shigo yanzu. Hajiya ba lafiya." Yana gama fad'in haka ya katse wayar. _Khalil_ kuwa ji yayi gaba d'aya hankalinsa ya tashi. K'ara gudun motar yayi duk da yana gab da layin. Mintuna biyar suka k'ariso dashi gidan. Ko parking mai kyau bai yi ba ya shigo gidan ya nufi d'akin Hajiya kai tsaye. Nan ya tarar dasu sun yi curko-curko. "Hajiya mai ya same ki, taso mu tafi asibitina dan Allah." Da kyar Hajiya ta d'ago kanta ta zubawa _Khalilullah_ idanu tare da fad'in, "Abdul-Hakeem ku d'an bamu waje." Tana fad'in haka gaban _Khalil_ ya yanke ya fad'i. Don har ji yayi wani k'aramin zufa ya gangaro daga goshinsa. Abdul-Hakeem babu musu ya mik'e ya fita, aunty Maryam da Laure suka bi bayansa tare da rufo masu k'ofa. _Khalil_ shuru yayi kamar ruwa ya cinyesa, don hakanan jikinsa Hajiya ta gano abunda yake b'oyewa. " _Ibrahim_" Hajiya ta kira sunansa da muryanta da yayi rauni. Hankalin _Khalil_ ta tashe yace "Na'am Hajiya." "Wacece Saratu?" A mugun furgice duk da kuwa zuciyarsa na bashi ta gano ko kuma wani ya fad'a mata ya d'ago bakinsa na rawa yace, "Haj..... Hajiya ban gane abunda kike fad'i ba." Hannu Hajiya ta d'aga ta wanke masa fuska dashi tare da fashewa da kuka tace, " _Khalilullah_ ka b'ata wayanka. Baka kyautawa kanka ba. Dadiro _Ibrahim_? Yanzu har kayi rik'an da zaka ajiye dadiro a waje _Khalil_. Kana da kud'i, kana da wajen zama, duk wani abu da namiji zai mallaka kamun yayi aure, ka mallaka _Mu'azzam_, amma shine sabida shaid'an ya buga maka gangi, giyar kud'i na janka, shine zaka butulcewa Allah ta hanyar yin abunda ya haramceka dashi. Ka bani mamaki _Khalil_. Ashe irin tarbiyan da muka gina ku a kai ni da mahaifinku, watsar dashi kayi? _Khalil_ baka yi wa kanka da mu adalci ba. Ka b'atawa zuri'ar suna. Ashe dai da gaskiya su Ameeru da suke cewa ka ajiye dadiro. Shiyasa a kullum burinsu shine suyi maka aure sabida sun san lalatar da kake yi a waje. Baka min adalci ba _Mu'azzam_!" Ta k'arisa maganar tana mai fashewa da kuka takaici. Shima _Khalil_ d'in kukan ya soma yana fad'in, "Hajiya dan girman Allah kar kiyi mani kuka. Kukanki bala'i ne a gare ni. Ki tsaya inyi maki bayani. Duk wanda ya fad'a maki na ajiye dadiro wallahi sharri yake min kawai yana son shiga tsakanina dake ne. Wallahi tallahi ban tab'a ajiye dadiro ba a rayuwata. Kuma Hajiya ban tab'a ratsa jikin wata y'a mace ba. Ban san ta yanda zan yi maki bayani ba ki fahimceni ni." Hajiya tsagaita kukanta tayi tare da fad'in, "Kenan sharri ake maka baka san wata Saratu ba." Girgiza kai yayi tare da fad'in, "Na santa Hajiya, amma ba ta yanda kike tsammani ba. Ita ce wacce nake fad'a maki ba tsayar matsayin wacce zata zama uwar y'ay'ana." Wani ajiyar zuciya Hajiya ta saki, sai kuma tace, "To maganar ciki fa? An ce kayi mata ciki in tsammaci zuwan jika nan da wata takwas. Ya matsayin wannan maganar take?" Shuru _Khalil_ yayi yana kallon k'asa. Sai kuma ya d'ago tare da kama hannayen Hajiya duka biyun yace, "Hajiya dan girman Allah kiyi hak'uri da abunda zan fad'a maki yanzu. Amma ki saurare daga baya sai ki yanke hukuncin da kika ga ya dace. Dagaske Sarah tana d'auke da ciki, kuma nawa ne." Tass Hajiya ta sauke masa mari tare da nuna masa k'ofa tace, "Fita! Fita nace ka bar min d'aki yanzun nan!!" Ta kuma fad'i a tsawace. Da sauri ya mik'e tsaye tare da fad'in, "Haj......" "Fita _Khalil_ kar ka sa nayi abunda zan dawo ina dana sani. Fita nace kar in fad'i mummunar kalma a gare ka." Fad'in Hajiya tana matsar hawaye. Da sauri _Khalil_ ya fita tare da rufo mata k'ofar. Shi babban tashin hankalinsa, kar jininta ya hau. Yana fitowa daga d'akin ya nufi waje ya zauna tare da kama kansa har akai kiran sallar Isha sannan ya mik'e ya nufi masallaci. Hajiya kuwa kuka tayi sosai har da majina. Bayan ta idar da sallar isha'i wanda tayi sa da kyar, sannan ta lalubi wayarta ta dannawa babban wansu soja mai muk'amin *_LTG (Lieutenant general)_* dake zaune a abuja, a can yake da iyalansa gaba d'aya kasancewar aikinsa a can yake. Bugu d'aya yayi rejecting tare da karanta, "Assalamu alaikum Hajiya." "Amin wa'alaikassalam." Tun daga yanayin yanda ta amsa kiran ya tabbatar babu lafiya, mik'ewa yayi d'aga kwancen da yake ya zauna tare da fad'in, "Hajiya lafiya? Mai ke faruwa?" Kuka Hajiya ta fashe dashi tare da fad'in, "Marmari daga nesa (Bata kiran sunansa kasancewarsa d'an Faari) duk abunda kake yi ka d'auki sakuis (excuse) kazo gida gobe, kuma ka kira wancen yaron na Kano shima ina son ganinsa har da k'anwarku Aisha. Duk kuzo ina neman ku gobe." Gaba d'aya tunanin _LTG Abdallah_ akan maganar gadonsu ne, don wani lokacin haka uncles suke sako mahaifiyar nasu a gaba duk akan dukiyar da mahaifin nasu ya bari. "Dan Allah Hajiya ki kwantar da hankalinki, in Sha Allah gobe zan biyo jirgi ni da Aysha. Zan kira mijinta yanzu ina gama waya dake." Fad'in LTG Abdullah don Aysha d'in a nan Abuja tayi aure, kusan a hannunsa take, don shi ya aurar da ita. Ita ma soja take aure ana Abujan. Katse wayar Hajiya tayi tare kifa kanta a kan pillow tana zuciyarta na mata zafi, gaba d'aya Y'ay'anta daga maza har matan lafiya k'alau ta aurar dasu, Nafeesa ta je gidan mijinta lafiya, haka Aysha. Mazan ma gaba d'aya babu wanda ya d'auko mata abun kunya sai _Khalilullah_. Kuma duk cikin y'ay'anta shi, yana da wani special guri a zuciyarta. Don shi d'in favourite d'inta ne. Duk da kuwa ba shine auta ba. Nafeesa ce autarta. B'angaren _Khalil_ kuwa yanda yaga rana, haka yaga dare. Abun duniya duk yabi ya ishesa. Sam ba ta haka yaso hajiya taji wannan maganar ba. Yaso ya shaida mata da kansa ta hanyar da ko zata jijjiga ba kamar h???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aka ba. Tunani ya dunga yi wanene ya san abunda ke faruwa har ya d'aga waya ya kira Hajiya, "Doctor Kamal!" Fad'in _Khalil_ a bayyane. Da sauri ya mik'e zaune yana jin wani irin matsanaicin b'acin rai da tsanar doctor d'in. "Wallahi sai na baka mamaki Kamal. Ni zaka had'a da mahaifiyata. Zaka san koni wanene. Daga kai na baza ka k'ara irin wannan munafurcin ba." Saukowa yayi ya nufi bayi yayi alwala tare da fitowa ya shimfid'a darduma ya dunga yin sallah yana rok'an Allah sauk'i da sassauci akan lamarin. Bai tashi daga kan darduma ba sai da yaji kiran sallar asubahi na shiga masallaci sannan ya mik'e ya fito. Sai da ya fara bi ta d'akin Hajiya tukun, da sand'a ya murd'a k'ofar a hankali tare da bud'ewa. Karaf suka had'a idanu da Hajiyar dake zaune a kan darduma, don kamar yanda ya kwana sallah haka ita ma. Da sauri ya jawo k'ofar ya rufe tare da barin wajen ya nufi masallaci. Sai bayan da aka idar da sallah har fito zai koma cikin gida yayansa Abdul-Hakeem ya tare sa, bayan sun gaisa yake ce masa, " _Khalil_ mai ke faruwa Hajiya tayi kiran kowa na gidan nan cikin gaggawa? Yaya Abdullah ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login