Showing 57001 words to 60000 words out of 129558 words

Chapter 20 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

zata had'a baki da wasu domin a sace ki. Amma zan je gidan gobe da safe." "To Baba Allah ya kai mu." Sarah ta fad'i tare da ficewa daga d'akin ta koma nasu. "Sarah kin tab'a karanta littafin hausa mai suna _Ayi dai mu gani_?" Fad'in Aina'u tana mai danna wayarta. Kallon Sarah tayi tare da fad'in, "Kin fara karatun novels ne na hausa?" Sarah ta fad'i tana mai kallonta. Ba tare da Aina'u ta kalleta ba tace, "Eh, yau kwana uku da na fara da wani littafi mai suna _Iska na wahalar da mai kayan kara_, yanzu kuma _Ayi dai mu gani_ nake karantawa." Girgiza kai Sarah tayi tare da fad'in, "Gaskiya ban karanta ba. Ban ga kinyi lalle ba, kuma har nan na turo mai lalli d'azu da safe. Su Na'ima duk anyi masu ja da b'aki." Tab'e baki Aina'u tayi tare da fad'in, "Ni kinsan lalli bai dame ni ba. Kuma da safe bani nan naje kitso. Za kuyi wani program ne?" Zama Sarah tayi a bak'in gadon tare da nannad'o gashin ganta ta tura cikin hula ta k'eya tare da jawo hulan har zuwa goshinta saboda kar gyaran kan da akai mata ya lalace. Tace, "Eh, naga duk su Na'ima ma sunyi kitson ai. Ni ko da da nake saka attachment, ba zan iya yin wannan uban k'ananan kitson ba. Na'ima muga naki, kamar yafi na Aina'u k'anana ko?" Sarah ta fad'i maganar tana kallon kan Na'ima wacce taja hulan kanta baya. "Wai! Gaskiya kitson yayi k'ana. Sauk'in ta ma a can inda kukai kitson ake tsefe maku." Nuratu tace, "Ni ko kinga nawa bai kai nasu k'anana ba. Ghana weaving akai min manya." Ta fad'i maganar tana mai jan hular kanta. "Ni da Hassana fixing kawai akai mata. Don wallahi naji bazan iya zaman kitson ba. Basir!" Fad'in Marfu'a tana mai zame Fadwa da ta gama shayar da ita daga jikinta ta kwantar. "Amma dai ba anan zata kwana ba ko? Don na tsani kukan daren nan da take yi. Duk ta hana mutum bacci." fad'in Aina'u. "To nan zata kwana. Ni ban san wani uban gulmar ce ta dawo dake kwana anan d'akin ba, ai da a d'akin Lami kike kwana." Cike da rashin kunya Aina'u tace, "To nan d'in naga damar dawowa da kwana. Ai gidan ubana ne." Ficewa daga d'akin Sarah tayi ganin zasu fara raba halin nasu da suka saba. D'akin Baba tayi sallama ta shiga. Zaune ta same shi a kan gado yana kallon Sunna Tv. "Baba dan Allah wayarka zaka ara min." Ba tare da yace komai ba ya d'auko wayar a gefensa ya mik'a mata ita kuma ta amsa tare da ficewa. Number d'in _Khalil_ tayi dialing, ringing biyu yayi sai yayi rejecting tare da biyo kiran. Sarah na d'agawa yace, "Assalamu alaikum Baba." Sarah sai ta canza murya tare da fad'in, "Wa'alaikassalam d'ana." A tare suka saki dariya, _Khalil_ yace, "Ke nine d'an naki? Za kiyi bayani gobe a irin wannan lokacin." Hararar wayar Sarah tayi tare da fad'in, "Bayanin mai zan yi? Ni babu wani bayani da zan yi." Dariya _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Kuma kin san na mance y'an iskan da suka d'auke min ke sun yar da wayarki, wallahi na kira yafi sau shurin masak'i, dole ma gobe da sassafe in kawo maki waya. Ba zan juri rashin jin muryanki ba." "To bayan gobe zamu kasance tare har abada." Sarah ta fad'i a kunyace. "Na'am, maimaita dan Allah love." K'it ta kashe wayar tare da mayarwa Baba wayarsa. Daga can kuwa _Khalil_ kamar ya fasa ihu, yana tsoron kira yaji wayar a hannun Baba. Washa gari da sassafe kamar yanda _Khalil_ ya fad'i, sai gashi da sabuwar waya k'irar LG mai tsananin kyau da tsada, wani tsohon MTN sim d'insa ya saka mata a ciki ya kawo mata. Na'ima ta fito zata shago ta gansu a tsaye suna magana. Wani irin kyau suka mata, sai taga kamar anyi su don juna ne don ba k'aramin dacewa suka yi ba. "K'anina ayi hak'uri haka, anjima kad'an zamu kawo maka ita." Murmushi kawai _Khalil_ yayi ita kuma ta wuce. Dai-dai nan Muneeba ta iso wajen, tana ganin _Khalil_ ta juya da sauri. Shima _Khalil_ da sauri yabi bayanta yana kiran sunanta don jiyan sunyi magana sosai da ya Abdul-Hakeem ya fahimtar dashi Muneeba bata da hannu a ciki. "K'awarmu dan Allah kiyi hak'uri da abunda ya faru jiya. Tashin hankali ne ta saka nayi abunda nayi. Koma wanene a matsayina abunda nayi shi zai yi. Kiyi hak'uri kinga ma na kama kunnena. Kar ki manta ke kika ce min in kula da k'awarki sosai kada tayi kuka. To hud'ubarne ya shiga kunnena." Kuka Munee ta fashe dashi tare da fad'in, "Naji tsoro jiya, banyi bacci ba. Mama kwana tayi tana mun fad'a. Sai da baban Sarah yazo gidan mu yayi mana bayanin anga Sarah sannan hankalinmu ya kwanta. Wallahi ko a cikin mafarkina bai tab'a zuwarmin in cutar da Saratu ba." "Naji na yarda dake Muniba. Dan Allah kiyi hak'uri." Fad'in _Khalil_. Sai da ta murgud'a baki sannan tace, "Na hak'ura dan ba halinka ba." Sai ta juya ta kalli Sarah data k'ariso ta rungumeta tare da fad'in, "Alhamdulillah k'awata. Duk wanda yayi maki wannan abun Allah ya tona asirinsa." Da Ameen Sarah ta amsa tare da jan hannunta bayan ta d'agawa _Khalil_ hannu. Baki _Khalil_ ya bud'e tare da fad'in, "Har munyi sallama." Muneeba tace, "Anjima zamu kawo maka ita sai kaga dama ka barta tazo wajen mu." _Khalil_ kuwa cikin zuciyarsa cewa yayi, "Kamar kuwa kin sani. Don ina raba Sarah da wannan gidan, ko zata zo to tabbas ina jiranta a waje, tana gama gaishe da Baba zata fito mu wuce." Kan kace me, gaba d'aya gidan su Sarah ya cika da mutane har da y'an unguwa da basu tab'a shigowa ba. Don Na'ima gida-gida tabi ta kai masu chewing gum. Bamu abunda ke tashi sai k'amshin soye-soyen nama sa, rago da kaji. Don shanu k'osassu biyu aka yanka, raguna hud'u kaji d'ari da hamsin. Y'an matan zumunta kuwa sun fi hamsin sunyi ankon wani koriyar atamfa sai hada-hada suke yi baki na motsi. Sarah kuwa komawa gidansu Munee tayi don acan suke sitting. Mai make-up tazo ta tsan-tsara mata kamar ka sace ka gudu. K'arfe d'aya da mintuna sha biyu wasu uban jiniya mai tafe da convoy na ya Abdullah suka shigo layin kasancewar k'arfe d'aya da rabi za'a d'aura auren anan masallacin layinsu. Sai ga tawagar manya-manyan mutane da abokan mahaifinsu. Jos road kamar zata tsage sabida mutane. Muneeba hannun Sarah ta kama suka koma can d'akin Baba mahaifin Muneeban sabida kiran wayarta da _Khalil_ d'in yake ta yi don wayar Sarah na hannunta. Kuma nan gidan ma a cike yake da k'awayensu na islamiya da poly. Don duk sai da Na'ima ta gayyace su. Bayan ta bata wayar ta fita. Sarah na picking ta jiyo zazzak'ar muryan _Khalil_ na mata wak'a, If you make me clean I will be clean. If you make me whole I will be whole. If you make me yours I will be yours And I won't run anymore. If I seek you, will I find you there. If I call your name will you still hear
Is it too late or can I start again
Can I begin again
Oh. Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Don't ever let me go
Can you drown it in the deepest sea. Can you cast it far as west from east
Can you raise me up to live again
So I can live again
Oh... Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Don't ever let me go
I'm surrendering my will
You are crumbling all the walls I've built
My defence is coming down
Down
I can't deny you
I am broken open wide
Now you can come inside
My defences have come down
Down
I can't deny you
I'm surrendering my will
You are crumbling all the walls I've built
My defence is coming down
Down
I can't deny you
I am broken open wide
Now you can come inside
My defences have come down
Down
I can't deny you
Oh... Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Oh... Don't ever let me go
Don't ever let me go
Don't ever let me go
Don't ever let me go. "I will never let you go. Never, ever!" Fad'in Sarah. "And I'll always be there for you my love. Sai mun had'u anjima." Yana gama fad'in haka ya katse wayar. Aina'u na tsaye a tsakar gida abun duniya duk ya isheta ta jiyo shalar da ya tsayar da bugun numfashin ta zube a k'asa sume. "An d'aura auren _Ibrahim Khalil Muhammad Nurudden_ da amaryarsa _Saratu Nuhu_ akan sadaki naira na gugan nera har dubu d'ari biyar, lakadan ba ajalan ba."



_KANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER, 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH 08128755583_


*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*

*MATAR SAYYADEE*>؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*19*


Da gudu mutane suka yo kanta suna mata firfita. Lami kuwa kuka ta fashe dashi tare da, "Mun dawo gareka Yesu, munyi tuba mun nemi yafiyarka. Masu bin mu da sharri ka jefesu da mutu. Almasihu kayi tsinuwa mai tsayi a garesu." Aunty Rose Merry tace, "Elizabeth me ke faruwa? Mai ya sami Lili (Aina'u)." Ita haka take kiran Aina'u. Lami ta fyace majina tare da fad'in, "Rose, don anga yarana suna da farin jini kamar ni dai, shine ake binsu da sharri, jiya ma haka aka sace Sarah sai can dare aka ganta, yau kuma Aina'u. Kwana biyun nan haka take suma. Idan na tambayeta ko wani waje na mata ciwo ne, sai tace min basir da zazzab'i ke damunta." Wata mak'ociyar Lami tayi wufff tace, "Aikuwa Lami ki tashi tsaye, don basir mummunar ciwo ne don har hauka yana sakawa." Hannu biyu Lami ta d'aga ta kyasta yatsunta tare da fad'in, "Yesu almasihu mai tsarki ba zai tab'a bari y'ata tayi hauka ba. Over my dead body!" Dai-dai nan Aina'u ta farfad'o tana mai fashewa da kuka tare da tambayar, "An d'aura da gaske?" Y'an biki sai aka koma kallon juna. Aunty Rose Merry tace, "Lili mai aka d'aura?" Jin katob'arar da tayi sai tayi tsit ba tare da ta cewa aunty Rose d'in komai ba. D'aga ta Lami tayi tare da fad'in, "Basir d'in ne Aina'u?" Kai kawai Aina'u ta d'aga mata tare da nufa d'akinsu domin canza kaya don ruwar da aka zubar a wajen na girki ya b'ata mata jiki. Can gidan su Muneeba kuwa, a kunna Sarah aka d'aura auren don ana shirye-shiryen fara siga ya kirata a waya tana sauraran komai tana hawayen farin ciki. Ana fad'in salati goma ga annabi ta zube a k'asa tayi sujjada. Ta jima bata d'ago tana tsiyayar da hawayen farin ciki kasancewa mata aure da wanda take so. Sai da Munee dake kusa da ita ta d'ago ta tukun. Sai ta fashe da kuma tare da rungume Muneeba tana fad'in, "Alhamdulillah!" Gaba d'aya d'akin sai su hau fad'in *_('1NCN 'DDNQGO DNCN  HN(N'1NCN 9NDNJRCN  HN,NEN9N (NJRFNCOEN' APJ .NJR1M._*
*_Barakal-lahu lak, wabaraka  alayk, wajama a baynakuma fee khayr._* Ma'ana, _Allah Ya sanya albarka a gareki, yayi maki albarka kuma ya hada tsakaninku da alheri._ A tare gaba d'aya suka amsa da ameen. Ya Abdullah ba k'aramin b'arin kud'i yayi, don duk wanda ya samu halartar d'aurin auren nan ya samu kyautar k'atuwar jaka mai d'auke da kwalbar turare mai tsada wanda kud'insa ya kai 75k da agogo da kuma take away mai d'auke da lafiyayyar friedrice with chicken da kwalin exotic da ruwan gora da kuma kyautar kud'i har dubu biyar. Ko ina labarin d'aurin auren ake yi. Layin kuwa damk'an kamar ana d'aurin auren shugaban k'asa ko kuma y'ar sarki. Don ma akwai uban sojoji da y'an sanda da aka zuba sabida tsaro. Can cikin gidan su Muneeba kuwa, nan naga y'an gayyar sod'i, su Hajiya akarammiya Queen Zarah sai zazzare idanu ake yi ana yagar tsokar kaza, bayanta kuwa gaba d'aya y'an comments section ko wacce da plates d'inta mai d'auke da uban abinci da kaji ga kuma k'atuwar jaka rataye a hammata wanda za ayi guzuri.=?? K'arfe bakwai dai-dai sai ga wasu had'ad'd'un mota sun shigo layin na d'aukar amarya. Wata arniyar mota *_Czinger 21clC_* wacce kyauta ce ga ango zuwa ga amarya ita ce a tsakiyar convoy d'in motocin, kuma a itan ne za'a saka amarya. Y'an comments section sai tureniyar shiga mota ake yi. Can na hango Oum Muslim dake fama da laulayi suna y'ar matsatsi ita da Mrs dimples. Su takwas suka gwamutsu a bayan motar, Rahamanatou kerere na hangota a saman cinyar Hadiza Mbello. Mama mahaifiyar Muneeba ta kama hannun Sarah wacce ke rizgar kuka har gaban Baba ta durk'usar da ita sannan ta fita daga d'akin. Baba ma hawayen yake yi, don duk kaf Y'ay'ansa babu kamar Sarah. "Saratu! Ni dai alfarmar da nake nema a wajenki shine, ki tausaya min ki tausayawa kanki ki natsu a gidan mijinki. Yi, nayi, bari na bari. Dan girman Allah ko da wasa kada ki yarda ki b'ata masa rai, kar ki cutar dashi kuma kar a had'a baki a cutar dashi, ki rik'e sirrinki, duk rintsi kar ki yarda ki rik'a yad'a tsakaninki da mijinki. Ki koyi tauna magana kamun ki firtawa mijinki, ko kiyaye cikinsa, sannan ki kar ki yarda ki nuna farin ciki yayin da yake cikin bak'in ciki, haka kar kiyi b'akin ciki yayin da yake cikin farin ciki. Kar ki yarda ki soma kai k'ararsa wajen mahaifiyarsa idan ba abun bane da ya zama dole iyaye suji, yawan kai k'ara na sa duk yanda mutum yake jinki a ransa lokaci guda ko gunduresa tare da fita ransa. Saratu ina baki shawarar nan ne cike da umarni a matsayina na mahaifinki. Idan har kika rik'e wannan abubuwan da ba fad'a maki, zaki ci ribar zaman aure in Sha Allah. Allah yayi maki albarka ya baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba." Yana kawowa nan Sarah ta fashe da wani irin kuka tare da rungume Baba k'ank'am tana fad'in, "Ka yafe min duk wani laifin da na tab'a yi maka wanda na sani da wanda ban sani ba. In Sha All???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ah nasiharka babu wacce zata bar kunne, ruhina har zuwa gangan jikina. Baba ka yafe min." Hawaye Baba yake yi yana fad'in, "Baki min komai ba sai biyayya Saratu, na yafe maki duniya da lahira. Allah ya maki albarka. Kuzo ku tafi da ita gidan mijinta." Baba ya k'arisa tare da d'aga murya don su Maman Muneeba suji. Dakyar maman Muneeba suka janyeta zuwa d'akin Lami, "To, Lami ga y'arki nan zata wuce gida miji. Kiyi mata nasihar zaman aure." Gaba d'aya k'awayen Lami y'an Zumunta suka had'a baki wajen fad'in, "Yesu almasihu ya tsareki a gidan mijinki, ya kare ki daga idanun mak'iya da munafukai. Yesu ya kawo zuri'a mai yawa da albarka." Lami kuwa cewa tayi, "To Sarah, ni dai abunda zan fad'a maki shine kar ki dai manta duk rintsi nice na kawo ki duniya, idan kika samu hutu da abun arziki kika kyale ni, daga nan zanyi rok'o Yesu ya tsinewa zaman aurenki. To, ni dai babu ruwana." Da sauri maman Muneeba tace, "Haba Lami ke kuwa, ke da zaki saka albarka sai ko b'ige da wannan irin maganganu haka. Bai dace ba." Mik'ewa Lami tayi tare da fad'in, "Naji k'arar bus d'in da nayi maku haya ta iso. Ku firfito kuje kada motoci d'aukar amarya su tafi, ni bazan samu zuwa ba sabida har yanzu Aina'u na kwance babu lafiya." A cikin zuciya maman Muneeba tace, "To ai mu Alhamdulillah za muce da wannan rashin lafiya, don da kije ki bar abun kunya gwara kinyi zamanki. Dama kuma mai zai kai uwar amarya kai amarya." Amma a zahiri sai d'ago Sarah tayi tare da fad'in, "Tashi muje Allah zai albarkaci aurenki in Sha Allah." Sai da ta saka ta cikin motar sannan ta shiga, mutane biyu daga cikin mak'ota suma suka shiga tare da rufe motar sai da motocin suka yi gaba kamun sauran tawagar y'an sanda da sojoji suka bisu a baya har gidansu _Khalil_. Matan zumunta sun buga uban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login