Showing 51001 words to 54000 words out of 129558 words

Chapter 18 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

Kuma wannan yarinyar da _Khalil_ zai aura, bayan binciken da marmari yayi, na saka anyi min nawa da kai na a kanta. Don haka ita kad'ai zamu kawo cikin gidan nan ba ba mahaifiyarta ko kuma matan zumunta ba. Idan aka kawo ta cikin gidan kowa ga watse ai shikenan ko? Don Allah Marwa bana son in k'ara jin wannan maganar, ya tsaya tsakanin mu kawai." Da sauri Marwa tace, "Amma Hajiy....." "Dan girman Allah ki bar wannan maganar haka Marwanatu." Tsit Marwa tayi bata kuma cewa komai ba sai ma juyawa da tayi ta bar d'akin. Tana fita Hajiya ta jingina da gado tare da fad'awa duniyar tunani don fisabilillahi ta daure ne kawai a gaban Marwa ta kare surukar tata da gobe amma ba wai don bata firgita da labarin da taji ba. "To ko dai in d'auko yarinyar nan ne har sai anyi biki? To kuma ai ba'a tab'a haka ba a al'adar hausawa. Kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah kana gani, kafi kowa sanin dalilin wannan had'i. Allah kasa alkhairi ne albarkacin soyayyar da kakewa fiyayyan halitta." A bayyane tayi magana tare da jan dogon ajiyar zuciya. "Baba, shawara zan baka, ka saka a kwaso duka kayan can na waje, idan ba haka ba wallahi duk yawon kayan can Sarah baza ta tafi da abun arziki ba." Na'ima ta fad'i ba tare da ta damu da kukan da ta iske baban nayi ba. D'agowa Baba yayi ya kalli Na'ima, bai tab'a d'auka za'a samu wacce zata iya wannan maganar hankalin a cikinsu Na'imar ba. "Na'ima kuje ku kwaso kayan tsaf ku kai gidan liman Muhammadu mahaifin k'awar Saratu. Ku kira yara su kwashe kayan zan biya kud'in." Da to Na'ima ta amsa tare da fita dama kamun tazo d'akin Baba ta saka su Nuratu sun saka idanunsu sosai a kai gudun y'an sibaren na ayye. Cikin abunda bai wuce mintuna ashirin ba, Na'ima ta had'a kan yaran anguwa da almajirai sun kwashe kayan tsaf an tafi dasu gidan mahaifin Muneeba. Lokacin Lami na d'aki ita da k'awayenta matan zumunta. Sai da ta fito domin d'ibar masu nasu kayan kamar yanda suka yi mata fanfo, sai taga wayam duk da kuwa tana jin hayaniyar yara lokacin da suka zo tafiya da kayan, amma sai tayi tunanin ko y'an ganin kaya ne. Da masifa ta hau tambaya ina kayan. "Suna gidan k'awar Saratu. Can Baba yace a kai sabida yawan mutanen da suke shigowa gudun sata." Fad'in Na'ima. "Kutumar kaza-kazan can......... To wallahi ku fita ku dawo da kayan nan yanzu. Uwar wani ce ta haifar min y'ar da har za'a ce an kai kayan y'ata wani gidan. Wallahi ba liman ba ko sarkin makka ne sai naci kaza-kazansa (Ta wulwulo zagi) idan bai saka an maido mi da kaya y'ata ba." Fad'in Lami. Baba dake d'aki ya kai wuya, bai san lokacin da ya fito daga d'aki ba tare da fad'in, "Lami, na gaji da halinki. Wallahi tallahi idan kika k'ara magana akan wannan kayan sai na sake ki. Haba! Kin takura min kin hana ni shan iskan duniya cikin salama. Kuma wallahi idan y'an iskan k'awayenki basu fito sun bar gidan nan ba, sai na masu itace. Idan kuma sun ce k'arya ne, su k'ara mintuna biyar suga abunda zai faru." Matan zumunta na jin haka suka fara fitowa d'aya bayan d'aya. "Ku koma, babu inda za kuje. Wallahi dai-dai nake da kai Nuhu a cikin gidan nan. Idan ka fasa saki na, Allah ya tsine maka albarka. Kuma kaya sai an dawo dasu gidan nan." A zuciye Baba yace, "Kije na sake ki saki d'aya, bi........" Da wani irin mahaukacin gudu Sarah ta fito tare da jan burki ta kifa guiwarta a k'asa tare da fashewa da kuka tana fad'in, "Kar ka k'arisa, kar ka k'arisa Baba dan girman Ubangiji. Wallahi in har ka saki mama akan kayan akwati na, ba zan tab'a yin auren ba na fasa. Dan girman Allah ba dan halin Lami ba Baba ka mayar da ita. Baba ina wannan hak'uri da ka dad'e kana yi ya tafi? Haba babanmu." Ta k'arisa maganar tana mai fashewa da kuka. "Na gaji ne, na gaji Saratu. Saratu nayi iya hak'urin da zan iya yi da mahaifiyarku. Ta tafi kawai ai tana da dangi." D'aya daga cikin matan zumunta ta soma fad'in, "Yesu almasihu kayi mana tsari da irin wannan mutanan da ka tsine masu." Zabura Baba yayi tare da rarumo wani narkekiyar langen ya rafka mata a tsakiyar baya, sauran kuma yayi kansu. Da gudu har da k'undunbala suka fice daga gidan. D'aya har tana sakin tusa. K'afafunta Baba Sarah ta rik'e tana fad'in, "Baba dan Allah kayi hak'uri ka mayar da Lami." Baba yace, "Kiyi hak'uri Sarah, zamana da Lami akwai cutarwa. Gwara kawai ta tafi." Wani irin kuka Lami ta fashe dashi tare da fad'in, "Azzalumi ka rabo ni da y'an uwana ka kawo ni nan kana cutar dani. Yesu ba zai tab'a yi maka albarka ba. Shiyasa sabida mugun halinka ya maka mummunar tsinuwa ka zama talaka. Kuma ko ka sake ni, ina nan gidan sai dai kai ka fita ka bar gidan." "Haba Lami, kukan me kike yi. Muje na kama maki d'aki ki zauna ki bar masa gidansa." Fad'in Aina'u tana hararar Baba. "Ban yi mamaki ba Aina'u. Banyi ba! Ai kina da abunda kike rabawa maza suna baki kud'i dole kice zaki kamawa mahaifiyar taki d'aki." Su Nuratu kuwa ko uffan basu ce ba. Na'ima kuwa kumbarta take yankewa yayin da Marfu'a ke wankewa yarinyar ta kashi bayan ta cire mata pampas. "Eh d'in. Da ace ka sauke duk wani hak'k'inmu dake kanka, ai baza mu kasance a yanda muke haka ba. Kai ne mugun daka cutar dam......" Ba tare da ta k'arisa ba Sarah ta sauke mata tagwayen maruka a fuska hagu da dama sai da tayi zaman y'an bori. Dama kuma kamar jira Ainau take ta rarumo wani sanda tayi kan Sarah dashi. Da sauri baba ya shiga tsakaninsu, Aina'u bata yi wata-wata ba ta saukewa Baba sandar a k'agu kasancewar ya d'aga hannu wajen k'ok'orin kare Sarah. "Wasssh Inna lillahi!" Baba ya furta hawayen azaba na sauko masa har kan kuncinsa. Wani irin fuzgewa Sarah tayi ta kai Aina'u k'asa ta hau kai mata wani irin duka ko ta ina a jikinta. Da kyar Lami da Na'ima suka d'aga Sarah a kan Aina'u wacce bakinta bai mutu ba sai auno ashar take yi marasa dad'in fad'e. "Ki kashe ta shegiya y'ar iska. Allah ya tsine maki albarka Sarah. Yesu ina rok'onka a yau ka hana Sarah kwanciyar hankali ita da Nuhu mahaifinta. Ba dai ubanki kika zab'a a kaina ba, to kije yesu ya tsine maki ke da ubanki. Ba dai ya sake ni ba." Ta k'arisa maganar tana mai jan kwafa. Wani irin kuka Sarah ta fashe dashi don ta san illar bakin uwa a wajen y'ay'anta. Da gudu ta k'ara kama k'afafun Baba tare da, fad'in, "Baba kayi min rai ka rufa min asiri kar bakin uwa ya kama ni ka mayar da Lami d'akinta. Dan Allah Baba. Wallahi idan baka mayar da Lami ba, ba zan tab'a zaman aure ba. Ko an d'aura auren sai na gudu na bar gari." D'agota Baba yayi tare da fad'in, "Share hawayenki Saratu. Bakin Lami ba zai tab'a kama ki ba don babu abunda kika yi mata. La'anarta kanta zai koma. Ki bar kuka, na mayar da ita d'akinta sabida ke. Domin ke nayi hakan ke d'aya." Fad'in Baba. "Aikin banza kawai!" Fad'in Aina'u. "Banza yi maki baki ba Aina'u, Allah ya shirye ki." Baba ya fad'i yana girgiza kai. Sarah kuwa wani d'an sauk'i taji a zuciyarta jin Baba ya mayar da Lami d'akinta. Da daddare har d'aki Sarah ta sami Lami tana kuka tana bata hak'uri akan ta janye tsinuwar da tayi mata, amma ko kallonta bata yi sabida ba k'aramin fanfo Aina'u tayi mata ba akan Sarah d'in. Sarah d'aki ta koma ta zari mayafi ta nufi pos ta ciro kud'i har dubu d'ari ta dawo gida ba bawa Lami akan ta karb'i kud'in amma ta yafe mata ta janye batun tsinuwa. Ganin Aina'u bata nan, sai ta amshe kud'in tace mata taje ta yafe mata. Ajiyar zuciya Sarah ta saki, sai a sanan taji hankalinta ya kwanta har ta iya tafiya gidansu Muneeba domin a cigaba da yi mata gyaran jikin da ake mata kullum da safe da kuma daddare. Don yanzu basa had'uwa da _Khalil_ sai dai a waya kawai. Don Mama (mahaifiyar Muneeba) da kanta tayi magana dashi a waya a kan yayi hak'uri ba zai k'ara ganin Sarah ba sai ranar aure. Ya amsa ne kawai don yana jin nauyinta. Amma kullum mak'ale take da waya. Wani lokacin sai mai gyaran jikin ta kwace wayar ta kashe sannan ake yin gyaran a nitse. Aina'u kuwa, kwana d'aya, biyu, uku, bata ji wani motsi daga gidansu _Khalil_ ba duk da gayyato matan zumunta da tayi sabida komai ya rushe. Karo ba uku kenan plan d'inta bai yin aiki. "Dole in tafi matakin k'arshe na hana auran nan." Tana fad'in haka ta fiddo wayarta tare da danna wata number tayi magana tsayin mintuna goma sannan ta yanke wayar tana murmushi. Tun daga wannan ranar Aina'u bata k'ara nuna komai ba. Daga k'arshe ma shiga cikinsu Sarah tayi ana ta hidima da ita. Sarah ba k'aramin wani irin tsananin kyau ta k'ara ba. Sosai dilkan da ake mata ya amshi jikinta. Sai wani glowing take yi kamar wata kulb'a. Ana gobe d'aurin aure, mai gyaran jiki tayi mata lalli ja da b'aki wanda ya kuma fito da kyawunta kasancewarta farar mace. Ba k'aramin kyau lallin nan yayi ba. A ranar kuma _Khalil_ ya kasa jurewa ya dunga rok'on Muneeba akan ta taimaka masa ta fito masa da Sarah da dabara ya ganta ko na mintuna biyar ne. Muneeba tace masa kar ya damu bayan Isha zata fito masa da ita. Don tun saura kwana biyar biki Sarah ta koma gidansu Muneeba da zama gaba d'aya. Kamar yanda suka yi alk'awari kuwa, ana idar da isha'i _Khalil_ yayi parking ta bayan gidansu ga kira Munee a waya. Sarah bata san shirinsu ba, kama hannunta kawai Munee tayi tare da ce mata tazo ta nuna mata wani abu. Har gaban motar _Khalil_ ta kaita ta, a jingine ta same sa jikin motar yaci kwalliya cikin wasu k'ananan kayan da suka yi masa matuk'ar kyau. Da kallo kawai yake ta bin Sarah da idanu ganin wani mahaukacin kyau da ta k'ara yi masa. Sai yaga kamar canzo masa ita aka yi. "To gata nan, dan Allah kar ku dad'e kaga mama ta fahimci bama cikin gidan." Sai a sannan _Khalil_ ya kalli Muneeba tare da fad'in, "Godiya nake k'awarmu. In Sha Allah baza mu jima ba." Wucewa tayi ta bar su tsaye suna kallon juna. "Nayi kewarki" a tare suka fad'i. "Ba wani nan kin ba kiyi kewa ta ba tun da baki tab'a cewa mu had'u ko a sace ba." Fad'in _Khalil_. "To ai ni tsoro nake ji kar mama ta gane." Sarah ta fad'i a shagwab'e. Shima shagwab'ewar yayi kamar yanda tayi tare da maimaita tace. Rufe fuska tayi da hijjab d'inta tare da fad'in, "Ni dai bana so." Nan ma ya kuma kwaikwayonta. K'afa ta bubbuga a k'afa tare da fad'in, "Ni dai ka bari." dariya yayi tare da fad'in, "To naji, mu shiga mota naga kamar tsayuwar yana damunki." Da sauri tace, "A'a ni dai na sai na shiga ba. Ai ka ganni, zan wuce kada mama ta gane bana nan." Waro idanu yayi tare da fad'in, "To ai ko mintuna biyar d'in basu cika ba. A hakan d'in ne kike cewa kin yi kewata?" Ko kamun Sarah tayi magana wayarta ta soma k'ara, ganin Muneeba ce duk sai ta rud'e ta shiga fad'in, "Munee ce ke kira na, shikenan na shiga uku watak'ila Mama ta gane bana gidan. Dan Allah zan wuce gida." ta k'arisa maganar tare da marairaicewa. Bud'e mota yayi tare da fiddo leda ya ya kama hannunta tare da fad'in, "Ungo wannan inji Hajiya. Amma dan Allah ki tsaya in miki hoto guda d'aya kawai." ya fad'i tare da fiddo wayarsa yayi mata hoto a jikin motar. Kallonta yayi tare da fad'in, "Haba mana, smile." Yanda ya fad'i smile d'in ne ya bada dariya. Sai hoton yayi kyau sosai don hatta dimples d'inta sai da suka lob'a duka. "Kayi wa Hajiya godiya, bye sai da safe." Ta fad'i hakan tare da saurin juyawa ta soma tafiya. _Khalil_ bai bud'e motarsa ya shiga ba sai da yaga tasha kwana. Taku uku tayi taji an jawota da k'arfi an toshe bakinta tare da shak'a mata wani abu a cikin tsumma. Take ta sune jikinta gaba d'aya ya saki. Cikin sauri maza ukun suka tura ta cikin wani k'atoton buhu suka d'aura akan wheelbarrow tare da turawa har zuwa wajen wata mota golf sannan suka bud'e booth suka jefa ta ciki Sannan suka rufe tare da shiga suka bar wajen..........











*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =د?muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=د?
Nono=د?
Sanyi=د?
Karin kiba=د?
girmar hips=د?
Ni'ima=د?
Sabulai=د?
Humra=د?
Turarukan wuta=د?
Matsi=د?
Miski=د?
Dilka=د?
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*

*_MATAR SAYYADEE_*
[9/30, 10:43 AM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*18*


"Ke, bana son hauka! Kaza ce ita da zata b'ata? Ba ke kika kira wayarta ba? Kamun na juyo yanzu ki nemo min matata a duk inda take idan ba haka ba a kaf zuri'arku bana tunanin akwai wanda zan iya kyalewa ko jaririne." Yana gama fad'in haka ya katse wayar tare da yin reverse ya fizgi motar da gudu don har yayi nisa da layin. Muneeba kuwa jikinta ne ya soma wani kakkarwar tsoro zufa na yanko mata. Wayarta ta haska ta soma bin hanya tana kwala kiran "Sarah" ko Allah zai saka ta amsa. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Fad'in Munee tare da saurin d'ukawa ta d'auki takalmi da kuma ledar da _Khalil_ ya ba Saran. Kuka Munee ta fashe dashi tare da fad'in, "Inna lillahi wa'inna ilaihir, Allahumma arji'ini fi musibati. Saratu kina ina? Mun shiga uku, wayyo Allah, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." Haka ta dunga yin gaba tana dawo baya tare da ambatan sunan Allah. _Khalil_ nayin parking ya nufi hanyar da Sarah tabi a gaban idanunsa, kicib'is suka yi da Muneeba dake kuka tana kiran sunan Allah. "Ke!" Ya daka mata wani irin tsawa tare da fad'in, "Ki bar?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? wannan haukan kukan ki fad'a min ina matata take." Gaba d'aya sai Muneeba ta sake rikicewa saboda yanda yake daka mata tsawar. Takalmin Sarah da ledan hannunta kawai ta mik'a masa jikinta na rawa. Hannu ya kai ya amsa yana kallon ledar da kuma takalmin. Tabbas ledar da ya bata ne kuma takalmin ma nata ne. Ransa ne ya k'ara b'aci, bai iya yi mata wani magana ba sai wayarsa da ya fiddo ya danna number d'in ya Abdullah-Hakeem. Ringing uku ya d'auka yana fad'in, "Ango kasha k'amshi." Shi kuwa _Khalil_ cewa yayi, "Yaya motocin mutanan ku uku nake so yanzu. An sace Sarah. So nake gaba d'aya daga farkon Jos road har zuwa k'arshe a zuba mutanan ku, duk wanda aka yayi kala da rashin gaskiya a kama shi." Tashi zaune ya Abdul-Hakeem yayi tare da fad'in, "An sace Saratu? Wannan ma k'arya ne. Ka kwantar da hankalinka yarinyar nan in Sha Allah baza ta kwana ba. Yanzu zan kira yaya Abdullah domin ya turo mana da sojoji, kuma zan kira abokina ACP Lawal Yakubu domin a bamu police guda talatin. Gamu nan zuwa yanzu. Koma wanene yayi wannan aikin zai san ya tab'o jinin Chief Justice Nurudden Muhammad Ibrahim." Yana gama fad'in haka ya katse wayar tare da soma kiran yaya Abdullah. Yaya Abdullah ya fisa ma d'aukar zafi don kamar zai fito ta wayar. Kuma take yayi waya bariki aka turo motar sojoji har biyar. Tun daga Katsina round about mutanan dake Jos road suke jin jiniyar y'an sanda da sojoji. Matasa gaba d'aya hankalinsu ya tashi. Mutane sai firfitowa suke daga gidajansu suna kallo, wasu kuma suna dannawa nasu gidan sakata. Y'an daba da y'an shaye-shaye kuma sai nemar mab'oya suka soma yi. Tun daga farkon Jos road y'an sanda da sojoji suka samu position suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login