Showing 15001 words to 18000 words out of 129558 words

Chapter 6 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

kujerar dake gaban teburinsa. Zama tayi tana mai wasa da hannunta. Shi kuwa doctor wani rubuce-rubuce yake yi a jikin wani file. Ya d'auki mintuna uku kamun ya ajiye file d'in ya zare glasses d'in dake fuskansa sannan ya juyo da computer yayi danne-danne tare da fad'in, "Saratu Nuhu ko?" Ya fad'i hakane tare da juyowa ya kalleta dai-dai lokacin da itama ta d'ago kai idanunsu suka sark'e dana juna. A mugun firgice Sarah ta mik'e tare da tura kujeran da take kai baya gabanta na wani irin mugaba kamar yanda dak'ik'an agogo yake bugawa. Bakinta na rawa tace, "kkkk.... Kai!" Shima da matuk'ar mamaki ganinta ya furta, "Ke ce?" Da sauri ta juya ta fita daga office d'in har tana k'ok'arin kifawa tayi saurin dafe bango. Aina'u dake charting ganinta kawai tayi ta fito kamar wacce aka biyo ta tayi waje da sauri. Ita ma mik'ewar tayi tana fad'in, "Sarah! Sarah!! Lafiya?" Dai-dai lokacin ya fito shima ya bita a baya, Aina'u na ganin haka ta rufa masu baya amma suna isa wajen gate d'in suka ganta har ta hau napep, napep d'in ya wuce. Juyawa Aina'u tayi ta kallesa tare da fad'in, "Lafiya? Mai ka mata? Ko HIV kuka gano tana d'auke dashi?" Wani irin kallo Khalil yayi mata tare da fad'in, "Ni ko dubata ban yi ba. Kin santa ne?" Ya tambaya duk da kuwa yana ganin kamannin jini a fuskar Aina'un. "K'anwarta ce ni. Ni ke binta." Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in, "Ko zaki shigo mita muje in sauke ki sai in san gidan naku daga nan." Wani kallon up and down tayi masa, ganin babu k'arya sai tace, "To amma kai mai yasa kake son zuwa kaga gidan mu?" Kai tsaye ya bata amsa da, "Saboda ina son had'uwa da yayarki. Auren ta nake son yi. Na jima ina naimanta sai yau Allah ya had'a ni da ita." Wani dariya rainin hankali Aina'u ta kwashe dashi tare da fad'in, "Lallai! To ka ko san abunda ya kawota nan asibitin? To bud'e kunnuwanka da kyau in fad'a maka. Ciki ne da ita har na tsawon watanni uku, kuma zuwa tayi nan domin a zubar mata da cikin. Mu gidan mu bamu aure. Kar ka wahalar da kanka don baza ka tab'a samun Sarah matsayin mata ba. Ko da yake, ban san tsananin son da kake mata zai saka kayi auren ragowar wani ba. Ni na barka lafiya." Tana gama fad'in haka tayi gaba. Shi kuwa Khalil mutuwar tsaye yayi kansa na wani irin juyawa jin wai wacce yake matuk'ar k'auna ce take d'auke da juna biyu. Tirr ya auri mazinaciya a rayuwarsa. Idan kuma hakan ta faru, daran ranar da ya fahimci haka, a ranar zai korata gidansu. Don ya san zama da zargi babu aure, shi kuma ba zai tab'a iya auren yarinyar da zuciyarsa zai rik'a kokwanto a kanta ba. Har ya fara tafiya ya tsaya cak tare da maimaita abunda Aka Aina'u tace masa cikin zuciyarsa "Ciki wata biyu? Kai ba zai tab'a yuwuwa ba." ya fad'i a bayyane tare da bin bayan Aina'u da sauri.............





_AKWAI FA SAURAN CHAKWAKIYA A GABA SOSAI. DON HAR YANZU BA'A SOMA LABARIN BA. SHIN TA YAYA SARAH TA SAMU CIKI BAYAN TAYI RANTSUWA DA ALLAH BATA TAB'A SANIN D'A NAMIJI BA, WANENE DOCTOR D'IN DA SARAH TA GANI HAR TA TSORATA DA GANINSA TA GUDU BA TARE DA TAYI ABUNDA YA KAITA ASIBITIN BA? MAI DOCTOR KHALIL YAKE NUFI DA YACE BA ZAI YUWU BA ACE SARAH NA D'AUKE DA CIKIN WATA BIYU? A INA YA SAN SARAH, KUMA MENENE ALAK'ARSU? WACECE LAMI? WANENE BABA NUHU? SHIN MAI MAI K'ANWAR MATATA YAKE NUFI? TUN FA DA AKA SOMA LABARIN BAMU GA MATAR BA, BAMU GA MIJIN BA, BARE KUMA K'ANWAR. HMM WALLAHI Y'AR UWA KAR KI BARI AYI WANNAN LABARIN BABU KE. DOMIN AKWAI CHAKWAKIYA MAI ZAFI A CIKINSA._


*_A NAN NA KAWO K'ARSHE. FREE PAGES, GA MAI BUK'ATAR KARANTA LITTAFIN K'ANWAR MATATA, SAI YA TURO D'ARINSA BIYAR ZUWA WANNAN ASUSUN BANKIN 0592412800, ZULFAU SAID GT BANK, SAI KI TURO DA SHAIDAR BIYANKI DA WANNAN NUMBER 08128755583_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MAZA* >؜?

*7*


Da sauri yabi Aina'u yana kwala kiran "Ke! Ke!! Dan Allah tsaya." Aina'u najin muryansa ta k'ara sauri don bata fata ko cikin mafarkinta wannan doctor d'in ya kasance mijin Sarah. Cikin sauri ta tari Napep ta fad'a ciki. Cak Khalil ya tsaya yana mai bin napep d'in da idanu har ya daina ganinsu. Ya jima tsaye a wajen yana jin wani abu na tasowa a k'asan zuciyarsa. Hannu ya kai ya yamutsa gashin kansa kamun yayi wani irin tsayuwa tare da tura hannunsa cikin aljihun wandonsa yana kallon sama. Can kuma ya juya da sauri tare da komawa office d'insa. Yana jin ana gaishesa amma ko juyawa bai yi ba balle ya amsa. Direct wajen computer ya nusa ba tare da ya zauna a kan kujera ya d'an rankwafo yayi danne-danne jikin computer tare da saurin d'aukar wayarsa ya kwashi numbers d'in Sarah dake rubuce a file d'inta sannan ya kashe computer d'in ya zira wayarsa cikin aljihu ya fita daga office d'in bayan ya rufo k'ofar ya saka key. Wayarsa ya fiddo ya danna ya lalubo numbern doctor Kamal tare da shaida masa ya bar asibiti yazo yayi replacing d'insa akwai wani abun gaggawa da zai je ya aiwatar. Yana gama waya da doctor Kamal ya fita ya nufi parking space. Wata arniyar mota *_Pagani Zonda HP Barchetta_* that worth 17 million ya shiga tare da yi mata key ya bar asibiti. Sai da ya hau titi kuma sai ya rasa inda zai je. Juya kan motor yayi ya nufi Sokoto road inda gidan su yake. A wani k'atoton mansion ya danna horn, cikin sauri mai gadi ya wangale gate shi kuma yayi shiga tare da yin parking anan harabar gidan ba tare da ya isa parking space ba. Fitowa yayi daga cikin motar ya shiga cikin gida da sassarfa, babu kowa a parlor do haka kai tsaye ya haura sama ya saka key ya bud'e d'akinsa tare da shiga ya maida key d'in ya rufe k'ofar sannan ya nufi wajen wani wawaken waje da aka rufe sa da tinted glass ya danna wani abu glass d'in ya zuge. Wata jaka ya fiddo y'ar karama mai hannun chain kalar pink. Sai da ya jujjuya jakar a hannunsa sannan ya k'arisa wajen gado ya zauna a bakin gadon tare da zuge zip d'in jakar ya zazzage a kan gado. Abunda ya fara cin karo dashi shine d'an kunne guda d'aya kalar bak'i hook d'insa ya b'alle. Murmushi yayi tare da maida d'an kunnan cikin jaka sannan ya d'auki kud'in dake kan gadon wanda a cikin jakar ya fad'o. Dubu d'aya ne da d'ari bakwai, Sai turaren soft da lipgloss. Sune kawai abunda yake cikin jakar. Mai da komai yayi a cikin jakar tare da kwantawa rigingine yana tuno wasu abubuwa da suka wuce a cikin idanunsa kamar yanzu komai ke faruwa. Cikin sauri kamar an tsikaresa ya tashi zaune tare da zaro wayarsa k'irar Samsung mai matuk'ar kyau da tsada yayi dialing number Sarah da ya d'auka. Sai dai tayi ringing har ta gaji ba'a d'auka ba. Ya kira yafi sau goma amma babu amsa. Tsaki yayi tare da jefar da wayar a kan gado. Yana bala'in bak'in cikin ya kira waya ba'a d'aga ba. Shi a k'a'ida sau d'aya yake kira bai k'ara na biyu. Mirginawa yayi tare da mik'a hannunsa ya jawo drawer ya tura hannu ya d'auko _Mastika Gum_ ya b'are ya watsa a baki ya hau tauna yana mai lumshe idanu. B'angaren Sarah kuwa tun da ta hau keke napep gabanta ke wani irin bugawa sai da ta saka hannunta ta dafe k'irjinta don ji take yi kamar zuciyarta zai faso k'irjin ya fito. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Shine abunda ta dunga maimaita tun tana yi cikin zuciyarta har ya soma fitowa fili. Matar dake kusa da ita ta kalleta tare da fad'in, "Baiwar Allah lafiya?" Sarah bata bata amsa ba sai cewa mai napep d'in tayi, "Tsaya, tsaya zan sauka anan." Parking mai napep yayi ita kuma ta sauko gaba d'aya bata cikin hayyacinta. Mik'a masa d'ari biyar tayi tare da juyawa ta soma tafiya ko karb'an canji bata tsaya yi ba. Shi kuwa mai napep yaja napep d'insa yayi gaba. Sarah kuwa tafiya ta cigaba dayi a k'asa tana kalle-kalle. Tayi tafiya mai nisa kamun Allah ya had'a ta da wani asibiti a gabanta. Hamdala tayi tare da nufa cikin asibitin kai tsaye. Bud'e kati tayi sannan ta zauna domin jiran layi yazo kanta. Kamun layi yazo kanta har wani zabura take yi tana mik'ewa saboda tsabar k'aguwa. Sai da mutane takwas suka ga likita sannan aka kira sunanta. Cikin sauri har tana tuntub'e ta fad'a cikin office d'in a burkice. Doctor yayi saurin d'agowa ya kalleta, ganinta a hargitse sai yayi mata nuni da wajen zama tare da fad'in, "Have a sit." Zama tayi da sauri dama kuma abunda take jira kenan. K'ura mata idanu doctor Alpha yayi kamun yace, "Young lady, how can I help you?" Ai kamar Sarah jira take sai ta fashe da kuka, bai yi yunk'urin hanata ba, sai ma jingina da yayi da jikin kujera yana kallonta, sai da tayi mai isarta sannan ya mik'a mata tissue ta karb'a ta goge hawayen. A karo na biyu doctor da ya kasance bayarabe kuma bai jin hausa sannan kuma a haife ya haifi Sarah, yace, "My daughter what's the problem? Feel free to tell me exactly what's wrong with you. Let's have heart to heart conversation." Ajiyar zuciya Sarah ta sauke tare da fad'in, "Sir can I ask you a question?" Hannunsa biyu ya d'aura akan desk d'in dake gabansa ya bata full attention d'insa tare da fad'in, "You can ask any question. I'm here for you." Sai da ta sunkuyar da kai sannan tace, "Doctor can someone get pregnant without sexual penetration?" Sai da doctor yayi wani murmushi sannan ya kalli Sarah tare da fad'in, "What's your name young lady?" Ba tare da ta d'ago ba tace, "Sarah, Saratu Nuhu." Murmushin ya k'ara yi a karo na biyu tare da fad'in, " *_Pregnancy happens when a sperm fertilises an egg, which can happen even if you've not had sexual intercourse (penetration)._*
During vaginal penetrative sex (where the penis enters the vagina) semen can be ejaculated. Semen is the liquid produced during ejaculation and contains millions of sperm.
As soon as the penis is erect, (before ejaculation), a liquid called pre-ejaculate or "pre-cum" is produced. This liquid can contain thousands of sperm. The ovaries release 1 or more eggs (ovulation) 12-16 days before a period starts.
The sperm enters the body through the vagina, then travels through the cervix and womb to the fallopian tubes, where the egg is usually fertilised (conception). The egg can be fertilised by sperm contained in semen or pre-ejaculate." Kallon doctor Sarah kawai take yi alamar bata fahimce sa ba. Ganin hakan a fuskanta, sai ya sake yin murmushi tare da fad'in, "Here is the explanation, *_It is possible to get pregnant if sperm comes into contact with the vagina, if for example:_* *_your partner ejaculates very close to your vagina your partner's erect penis comes into contact with your genital area (vagina or vulva)_* *_The risk of getting pregnant in this way is very low because sperm can only live for a short time outside the body._*" A tsorace Sarah ta mik'e tsaye, shima doctor mik'ewa tsayen yayi tare da fad'in, "Hey calm down. Have a sit let talk." Da kyar ta iya zama tare kallon doctor babu kyaftawa. Shima doctor zama yayi tare da fad'in, "Sarah are you pregnant?" Ai fad'in haka da yayi Sarah bata san lokacin da ta mik'e da sauri ba ta fice daga office d'in har da had'awa da gudu. Shima doctor da mamaki yabi bayanta yana kiranta amma bata jo juyo ba ta bar asibitin. Tana fitowa ta nufi asibitin _ZAKARIYYA_ dake magajin gari. Cikin sa'a ita ce mutum na biyu da doctor ya gani, tana shiga tayi ta soma rab'e-rab'e har sai da doctor Usman ya d'ago yana kallonta har ta naimi waje ta zauna. Bai ce mata komai na tsawon mintuna biyu, ita kuma sai wasa da jelar hijjab d'in jikinta take yi. "Me ke damun ki?" Taji saukar muryansa a cikin kunnanta har sai da hantar cikinta ta kad'a. A hankali ta d'ago hawaye shab'e-shab'e a fuskanta. Doctor Usman bai yi mamaki ba don idan da sabo sun saba da ganin haka a wajen y'an mata sabon shigan fara iskanci idan sun yi ciki ko kuma masu fama da cutar HIV sabon shiga, ko kuma irin shagwab'ab'b'un yaran nan masu kuka idan basu da lafiya. "Me ke damun ki?" Ya sake tambaya karo na biyu. Bud'e baki Sarah tayi zata fara magana bakinta ya soma rawa sai ta kuma fashewa da kuka. Bai yi yunk'urin hanata kukan ba, ita da kanta tayi mai isarta sannan tace, "Doctor da gaske ne mace na iya d'aukar ciki ba tare da namiji ya kasanceta ba?" Cikin zuciyar doctor Usman yace, "Anzo dai-dai wajen!" Amma a zahiri sai kallonta yayi tare da fad'in, "Ciki gare ki?" Gyad'a masa kai tayi tare da fad'in, "Duk asibitin da naje sai ace ina d'auke da juna biyu, kuma ni wani namiji bai tab'a kusantata ba." Mik'ewa doctor yayi tare da fad'in, "Tashi ki hau wancen gadon zanyi maki scanning." Babu musu Sarah ta hau kan gadon tare da d'age rigar jikinta sama tana mai lumshe idanu hawaye na zirarowa daga k'urmin idanunta. _AquaSonic_ (gel d'in da ake zubawa a ciki kamun scanning) ya zuba mata tare da soma yi mata scanning. Kallon fuskanta dake a rufe yayi tare da mayar dashi kan screen d'in computern dake nuna b'aro-b'aro tana d'auke da ciki. Bai fad'a mata ba sai mik'awa mata tissue yayi tare da fad'in, "Goge jikinki ki koma ki zauna ina zuwa." Gaban Sarah na fad'uwa ta goge cikin nata tare da sauka daga kan gadon sannan ta koma inda ta taso ta zauna tare da had'a kai da guiwa tana addu'a a zuciyarta Allah yasa wannan karon an gano babu ciki a jikinta. Dawowa Doctor yayi hannunsa d'auke da paper d'in da yayi printing ya zauna sannan ya kalleta na kusan second goma sannan yace, "Saratu Nuhu!" A firgice ta d'ago gabanta na bugawa. Kallon paper d'in hannunsa yayi sannan ya kalleta tare da fad'in, "Scanning machine ya nuna kina d'auke da ciki har na tsawon sati a jikinki. Fad'a min gaskiya tsakaninki da Allah ko na iya taimakonki, ta yaya kika yi ciki?" Kuka Sarah ta fashe dashi sosai tare da soma bubbuga k'afarta a k'asa tana jujjuya kanta. "Ba kuka za kiyi ba, fad'a min gaskiya za kiyi ko hakan zai iya sakawa na taimaka maki." Jin haka ya saka Sarah ta tsayar da kukanta cak tare da fad'in, "Wallahi tallahi doctor ni ba y'ar iska bace." Murmushin yayi don idan da sabo ya saba da jin haka a wajen wasu y'an matan. "Naji, fyad'e aka yi maki?" Girgiza kai tayi tare da fad'in, "Bai kai ga jikina ba wallahi. Bai kusanceni ba." Shuru yayi yana kallonta, sai can kuma yace, "Bari na amsa maki tambayar farko da kika min lokacin da kika shigo. Cewa kika yi, Doctor da gaske ne mace na iya d'aukar ciki ba tare da namiji ya kasanceta ba? To amsarki ita ce, dagaske ne mace na iya d'aukar ciki ba tare da d'a namiji ya shiga cikin jikinta ba. Amna idan har mace zata bari namiji yayi wasa da al'aurarsa a jikin nata al'aurar har ya kawo, ma'ana ya fitar da maniyi a kan al'aurarta, to tabbas zata iya samun ciki sai dai kuma sai dai the risk is very low sabida kwayoyin halittar dake cikin maniyi zasu iya rayuwa ne na k'ank'anun lokacin a wajen jikin mace, amma a cikin jikin mace zai iya d'aukar kwanaki biyar zuwa shidda kamun su mutu. Idan har mace ta soma jinin al'ada (Menstruation) to a ranar idan ta fara k'irge, d'aya, biyu har zuwa kwana goma sha hud'u, to a ranar take samar da kwai, kuma a wannan lokacin she's not safe, namiji na kusantarta, zata samu ciki. Kuma sannan kar ki manta na fad'a maki sparm zai iya rayuwa a cikin jikin mace har na tsawon kwana biyar, hakan na nufin idan aka kusanceta 11, 12, 13, ko ba'a kusanceta 14 ko 15 ba zata iya samun ciki. Shiyasa yake da tsananin kyau mace ta rik'e kanta ko da wasan banza kada ta bari wani namiji yayi da ita idan ba mijinta ba. Amma ban san mai yake janku ku y'an mata ba kuke fad'awa tarkon *_Samarin Shaho_*! Su babu abunda suke so sai jikinku, kuma da sunyi amfani daku a k'arshe yar daku zasu yi sune su naimi ta kirki su aura." Kuka sosai Sarah keyi, bata san ta yanda za tayiwa doctor bayani ba, sai cewa kawai tayi, "Nagode doctor da bayanin da kai min." Sosai yaji tausayinta, amma har ga Allah babu wani abunda zai iya yi mata. Kuma ba zai iya bata shawara a kan ta zubar da cikin ba. Sarah kuwa mik'ewa tayi tana jin kanta kamar zai tsage tsabar yanda yake mata azabar ciwo, gashi irin bayanin da wancen doctor d'in yayi mata, shi wannan doctor d'in yayi mata. Sabida haka babu wani buk'atar sake zuwa wani asibiti domin tabbatarwa. Doctor Usman na kallonta har ta fice ta bar cikin office d'in. Ko da ta fito, a wajen asibitin ta samu wani d'an dandamali ta zauna saboda jirin dake d'ibanta sosai. Ga wani uban yunwa dake kwakwular cikinta. Had'a kai da guiwa tayi tana tariyo abunda ya faru kwanaki go??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ma sha takwas da suka wuce................



*_DAN DARAJAR GIRMAN UBANGIJI KAR KI FITAR MIN DA BOOK. WALLAHI TYPING AKWAI MATUK'AR WAHALA DA CIN RAI. KI TAIMAKA MIN Y'AR UWA!_*

*_DUK MAI SONA TA HANYAR SAYAN BOOK D'INA KAWAI ZAI GWADA MIN, TURA D'ARIN KI BIYAR KI SHA KARATU CIKIN SALAMA BISA WANGA ACCOUNT 0592412800

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login