Showing 18001 words to 21000 words out of 129558 words

Chapter 7 - Kanwar Matata Book 1 Hausa Novel Complete

ZULFAU SAID GTBANK SAI KI TURA DA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA 08128755583_*


*_MATAR SAYYADEE_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*PAGE 8*


Kuka take yi sosai har da shashshek'a tana jin ina ma bata zo duniyar ba balle wannan abun ya same ta. Taso ta kasance ta daban a cikin y'an uwanta, sai gashi ita ma an rubuto a cikin k'addararta akwai samun ciki ba tare da aure ba. Sosai ta tsani rayuwar da y'an uwanta suke yi wanda mahaifiyarsu ita ce ta d'aura su a kan wannan turba saboda son abun duniya. Da ana canza mahaifiya da tabbas ta jima da canza nata mahaifiyar. Mahaifinta ne ya fad'o mata a rai, ta san tabbas shi zai fahimceta, to amma wanda zata aura fa? Tuno hakan ya saka ta kuma rushewa da kuka. "Shikenan ni ba'a rubutomin aure a nawa littafin ba. Na shiga uku! Ni wallahi da nayi ta zama a cikin gidan mu ina kwasar bak'in ciki, gwara na tafi *_Wamba_* wajen dangin mahaifina nayi zama na a can. Ban damu da ko k'auye bane ko birni! Buri na in ganni a d'akin mijina ina bautar ubangiji!" Sarah ta fad'i a bayyane tare da mik'ewa ta soma tafiya a k'afa kasancewar layuka shidda ne ya rabasu da inda take. Kan titi _Kasuwar gwari_ ta mik'e tayi ta tafiya har ta iso _Jos road_ sannan tayi k'asa kasancewar can k'asan Jos road d'in suke. Ga zafin rana, ga kuma zazzab'in dake damunta da matsanaici ciwon kai wanda ya ninku sakamakon kukan da tasha. Tana isa k'ofar gidansu gabanta ya yanke ya fad'i ganin motar y'an sanda da kuma y'an sandar a kwar gidansu ga kuma uban cincirundon samari da y'an mata har da wasu matan auren layin da suka fito suna baiwa idanunsu abincin. Tana isowa gaba d'aya idanun jama'a ya dawo kanta. "Yauwa, ga d'aya karuwar ta dawo. Da gani ba gida ta kwana ba. Ai mu dai Allah bai had'a mu da makwaftar kirki ba. Ni dama tashin su za ayi daga unguwar nan don muna da y'ay'a mata dake tasowa kada suga abunda suke yi suma su soma jin sha'awar yi." Fad'in wata mata tana hararar Sarah. Sarah kuwa kutsawa tayi cikin mutanan nan ta shige cikin gidan. Turus ta tsaya ganin Baba a tsakar gida dafe da goshi gaban rigarsa duk jini yana kuka, gefe kuma su aunties d'in Farouq ne da k'annansa maza da mata a gefe sai girgiza suke yi suna fad'in wallahi baza su yarda ba. Nuratu, Aina'u, Na'ima, da Hassana kuma a waje d'aya suna fad'in babu inda zasu je kuma babu uban da ya isa fitar dasu zuwa police station. Lami kuwa sai fad'i take, "Ko kotu za'a je, aje ban jin tsoron uban kowa, sune suka biyo mu har gida da fitina, mu kuma muka kare kanmu." Baba dake kuka ya kalli officer d'in da yake magana cikin lalama akan su Lami su biyosa zuwa station yace, "Bawan Allah d'an sanda, ni na baka umarnin ka tafi dasu da tsiya, idan sunk'i kuyi amfani da k'arfin ku na hukuma ku fitar dasu, amma kuma banda wancen da ta shigo yanzu, don babu hannunta a kan duk abunda ya faru." Ya k'arisa maganar yana nuna Sarah. Police d'in kuwa, bai saurari maganar Baba, sai bada baki yake yi, don babu yanda za ayi ya nuna power ya fitar dasu Nuratu zuwa police station domin Hassana budurwarsa ce, Marfu'a kuma yanzu haka ma tana d'akinsa a wajensa ta kwana jiya. Hassanar ya kira gefe, da kyar taje tana wani cin magani. Sun jima suna magana, a yanda yake lallaminta, zaka d'auka uwarsa ce ita. "To naji, amma wallahi baza mu wuce mintuna ashirin ba a can." Da sauri yace "Na maki alk'awarin haka." Sai da taja tsaki sannan ta koma tayiwa y'an uwanta magana sannan suka fita su duka banda Sarah da ta jingina da bango abun duniya duk ta ishe ta. Ta gaji da matsalar mahaifiyarta da y'an uwanta. K'arisawa tayi wajen Baba duk da jirin da take ji domin taimaka masa ya tashi. Rik'e mata hannu yayi tare da fad'in, "Bari zan iya tashi Saratu. Kema naji jikin naki da zafi sosai. Ya aka yi Aina'u ta rigaki dawowa daga asibitin, ko fad'a kuka yi?" Sai da ta taimaka masa ya mik'e tukun sannan tace, "A'a ba fad'a muka yi ba, nice na baro ta a can asibitin." Baba bai k'ara cewa komai ba sai nufa wajen pamfo da yayi ya wanke goshinsa sannan ya nufi kan baranda ya zauna a kan tabarma tare da fad'in, "Saratu, kiyi hak'uri duk laifi nane da na kasa zab'a maku uwa ta gari. Y'an uwana sun nuna basu son na auri Elizabeth (Lami) amma na nace ni ita nake so sabida yanda ta nuna min k'auna a wancen lokacin. Ban tab'a d'auka Elizabeth za tayi min butulci a rayuwata ba." Kallonsa Sarah tayi tare da fad'in, "Baba ka bani labari, ta yaya ka had'u da Lami har kuka yi aure, kuma mai yasa danginka suke fushi da kai har yanzu? Bamu san kowa naka ba, haka suma basu san mu ba. Dangin Lami ma babu wanda ya san mu, muna bamu san kowa ba sai aunty Rose Merry wanda Lami tace mana y'ar uwarta ce." Sunkuyar da kai Baba yayi tare da fad'in, "Rose Merry ba y'ar uwar mahaifiyarku bace, asali ma itace mai d'aura mahaifiyarku akan turba mara kyau. Taso mahaifiyarku ta koma addininta da ta baro, amma kuma sai mahaifiyarku ta nuna ita tana son addinin musuluncin da ta karb'a." Sarah tace, "To amma Baba Lami bata sallah, bata azumi, duk wani abu na musulunci Lami bata yi. Kuma a hakan ne take cewa tana son musuluncin?" Ajiyar zuciya Baba yayi tare da fad'in, "Nima na jima ina wannan zargin Saratu. Anya kuwa mahaifiyarku bata koma addinin kiristancinta ba kuwa? Domin duk ranar lahadi da sassafe take barin gidan nan, kuma bata dawowa Sia wajajen d'aya ko biyu." Shuru Sarah tayi tana tuno wata rana da mahaifiyar tasu ta dawo daga inda take zuwa duk ranar lahadi, sai ta ganta d'aure da wani zani mai hoton k'atoton cross a jiki, zanin biyu ne, da ta d'aura d'aya a k'ugu, sai ta d'aura wani a sama kasancewar dama farar rigar less ce a jikinta. Ga wani k'aramin Bible a kan gado. "Lami! Wannan wani irin kaya ne haka a jikinki irin na y'an coci?" Saurin kallon jikinta Lami tayi tare da fad'in, "Kai, kin ganni nan d'azu da na fita, shine wata mota tayo kaina, garin na kauce mata sai na fad'a cikin kwata, kuma dama kusa nake da gidan auntynku Rose Merry, shine ta bani wad'annan kayan na saka. Yanzu ma Allah-Allah nake in cire su." Sarah ta kalli Bible d'in tare da fad'in, "Wannan kuma fa Lami!" A harzuk'e tace, "Ke dan ubanki uwata ce ke? Kin cika ni da tsinannun tambayarki. To Rose Merry d'in ce ta bani na ajiye mata a nan anjima idan zata wuce gida zata biyo tanan ta karb'a." Kallonta Baba yayi tare da fad'in, "Lafiya Saratu kike dogon tunani haka?" Sauke ajiyar zuciya Sarah tayi tare da fad'in, "Baba ina tuna wani abu ne. Ina ji a jikina Lami ta koma addinin kiristanci." Daga nan ta kwashe duk labarin abunda ya faru wancen ranar ta fad'a masa. Da mugun mamaki Baba ke kallon Sarah, sai kuma ya girgiza kai tare da fad'in, "Babu abunda Lami ba zata iya aikatawa ba. Lami ta daina bani mamaki sai dai tsoro. "Baba mai ya same ka a goshin ka?" Fad'in Sarah ganin har goshin ya tasa. Sai da ya shafa wajen sannan yace, "Lami ce taje jifan y'an uwan saurayinki da suka yi cincirundo domin d'aukar fansar abunda suka yi shine ta same ni a goshi, kuma kin san budar ba ta roba bace. Don ma Allah ya tsare." Cike da tausayi Sarah yace, "Allah ya k'ara tsareka Baba." Da ameen ya amsa tare da kallonta yace, "To Sarah ya ake ciki? Mai likitocin suka ce wannan karon?" Fad'in Baba yana kallon Sarah data sunkuyar da kai tana hawaye. "Baba akwai cikin?" Sai da gaban Baba ya fad'i da jin haka, amma ya d'aure tare da fad'in, "Kuma Saratu har yanzu baki gano bakin zaren ba?" Shuru Sarah tayi don bata san ta inda zata fara yiwa Baba bayani ba. Hawaye ne kawai ke zubowa daga idanunta yana d'iga a kan tabarmar da suke kai. "Saratu ni mahaifinki ne. Kuma kin san duk fad'in gidan nan babu wanda na shak'u kuma nake jinsa har cikin raina cikin y'ay'ana idan ba ke ba. Kar ki damu, zan fahimceki. Zan kuma yi maki nasiha matsayina na mahaifinki kuma in karb'i k'addararki da hannu bibbiyu. Sai dai ba zan tab'a jin dad'i ba idan har ke da kanki kika kai kanki wajen wani namijin bayan kin yi mi alk'awarin baza ki tab'a yin irin rayuwar da y'an uwanki suke yi ba." Kuka Sarah ta fashe dashi tare da fad'in, "Na rantse da girman ubangijin halittu ban tab'a kaiwa wani namijin jikina ba domin yayi amfani dani. Wallahi, tallahi duk abunda ya faru tsausayi ne Baba. Ban san ta yanda zanyi maka bayani ba Baba. Amma wallahi ban tab'a karya maka alk'awarin da ba d'auka ba." Ko kamun Baba yayi wata maganar wani yaro ya kwad'o sallama tare da fad'in, "Wai ana sallama da Sarah a waje. Wai dan girman Allah ta fito mintuna biyar kawai!"



*_Kuyi hak'uri da wannan, anticipate a long page tomorrow _*


*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*


*_ZULFA'U SA'EED IBRAHIM AKA =?I?MATAR SAYYADEE_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: >؜? *KANWAR MATATA* >؜?

*PAGE 9*


Kallon yaron Sarah tayi, sannan ta maida kallonta izuwa wajen Baba tare da fad'in, "To kuma wanene? Na san dai Farouq ba zai sake dawowa k'ofar gidan nan domin ni ba." Baba yace, "Kije kiga ko wanene ke kiran naki. Allah yasa dai lafiya." B'ata rai Sarah tayi tare da fad'in, "Da kuma so nake na kora yaron yaje yace bazan zo ba." Girgiza kai Baba yayi tare da fad'in, "Ba'a haka Saratu. Ba'a wulak'anta d'an Adam. Kije kiga ko wanene." "Je kace tana zuwa!" Sarah ta fad'i tare da mik'ewa don har yanzu tana ganin jiri-jiri ga kuma yunwar dake kwakwular cikinta. D'aki ta koma ta canzo hijjab d'in jikinta ta saka wani brown wanda ya kai mata har guiwa sannan ta fito tana dafa bango ta nufi waje. Baba na kallonta har ta fice kamun ta ya sunkuyar da kai yana tsiyayar da hawayen tausayinta. Sarah kuwa tana fita taci karo da wata arniyar motar da bata tab'a ganin irinta ba k'irar *_Aston Martin Vulcan_* kalar ash mai duhu. Ba ita kad'ai ba, hatta jama'ar layin fitowa suka yi suna kallon motar. Shi kuwa _Khalilullah_ sai da ya gama k'are mata kallo ta cikin tinted glass d'in motar sannan ya bud'e tare da ziro k'afarsa d'aya. Farar kyakkwar k'afar ta soma bi da kallo kamun taga ya fiddo da gangan jikinsa, tun daga d'an yatsan k'afarsa take kallo har ta sauke a kan fararan manya-manyan idanunsa masu matukar d'aukar ido. Wani irin lumshe idanu tayi jin daddad'an k'amshin turaren *_Imperial Majesty_* da ya bugi hancinta. Sosai take matuk'ar son k'amshi musamman a yanayin da take ciki. Folding hannunsa yayi tare da jingina a jikin motar yana kallonta. Bud'e idanu tayi a hankali ta kuma sauke idanunta a kansa karo na biyu tayi saurin b'ata fuska tare da k'ok'arin juyawa zata koma cikin gida. Cak ta tsaya sakamakon jin abunda yace, "Kul! Kar ki sake ki bar wajen nan idan ba haka ba zan baki mamaki." Juyowa tayi ta watsa masa harara tare da bud'e baki za tayi magana shi kuma ya d'aura d'an yatsansa a kan bakinsa tare da fad'in, "Ssshh! Ko kalma d'aya." Yana fad'in haka ya tako cike da isa ya iso inda take a tsaye tare da fad'in, "Kin yi missing d'ina ko?" Karo na biyu ta kuma watsa masa harara tare da d'an matsawa baya kad'an jin kamar zasu had'e da juna ga kuma wannan mayataccen k'amshin nasa dake naiman sumar da ita a tsaye. "Zan kwakwule idanun nan naki idan suka kuma hararata." Kallon gefe Sarah tayi tare da fad'in, "Menene matsalar ka dani ne? Mai yasa ka addabi rayuwata? Dan girman Allah ka kifa daga rayuwata in samu salama. Ka barni da bala'in daka jaza min dan girman Allah!" Sarah ta k'arisa maganar tare da fashewa da kuka. Kallonta ya dunga yi ba tare da ya ce mata tayi hak'uri ta daina kuka ba. Sai da tayi mai isanta sannan ya saka hannu cikin aljihu ya fiddo da wani d'an ma daidaicin handkerchief ya mik'a tare da da fad'in, "Come on, wife those tiers of yours!" Karb'an handkerchief d'in tayi tana mai watsa masa harara sannan ta kai kan fuskanta, kamun ta share hawayen sai da ta zuk'i k'amshin turaren tukun. "To bani abuna." Ya fad'i yana mai mik'a mata hannunsa. Mik'a masa tayi tare da fad'in, "Ai dama bani na rok'a ba." Amsa yayi tare da yin murmushi ya maida cikin aljihunsa sannan yace, "Kin matuk'ar bani wahala Sarah! Kin san kuwa irin naiman ki da nayi?" Kamar ta shak'e masa wuya haka take ji, wani tsaki tayi tare da fad'in, "Idan abunda ya kawo ka wajena kenan, juya ka bar k'ofar gidan nan yanzu. You're not welcome here. Out of my sight. Kuma yanda ka tarwatsa min farin ciki, kai ma baza ka tab'a samun farin ciki ba." Maimakon maganganunta su bashi haushi, sai yayi wani irin murmushi mai sauti tare da fad'in, "Idan har bazan tab'a samun farin ciki ba, to kema baza ki tab'a samu ba Sarah. Domin an halicceki ne domin ni kawai. Farin cikina yana tare dake, haka kema farin cikinki yana tare dani ne. Sannan kuma ina so ki saka wannan maganar da zan maki yanzu cikin kwakwalwarki, ba ai min tsaki! Kar ki sake." D'ago jajayen idanunta tayi zata saki masifa sai ga keke napep ya tsaya a bayan motar _Khalil_. Aina'u, Nuratu, Na'ima da Hassana a baya, sai Lami dake zaune a gaba ta rik'e k'arfe. Fitowa suka yi gaba d'ayansu suna k'arewa motar _Khalil_ kallo. Lami ce ta riga kowa magana tare da fad'in, "Kun ga wata arniyar mota! Wallahi tunda uwata ta haife ni ban tab'a ganin mota mai kyawu ba irin wannan." Na'ima ta kalli Nuratu tare da fad'in "Kamar fa *_Aston Martin Vulcan_* nake gani." Nuratu tace "Ya kike fad'i da kaya a jikinki! Ai kuwa tabbas ita ce wallahi." Zagayawa suka yi domin su k'arewa motar kallo dakyau. Idanunsu ya sauka akan Sarah dake kallonsu tana addu'ar Allah yasa kar su nuna halinsu _Khalil_ ya raina ta. Sai dai Addu'arta bata karb'u ba domin da sauri Lami ta k'arisa wajen tana k'arewa _Khalil_ da Sarah kallo. "Eh lallai! To yau dai Allah ya tona asirinki kin kawo sa har k'ofar gidanku. Wato saboda kin ga bama gidan ko?" Sai ta maida dubanta ga _Khalil_ tare da fad'in, "Samari kalle ni nan, nice mahaifiyar Sarah." D'an sunkuyar da kai _Khalil_ yayi tare da risinawa yace, "Sannu da zuwa Mama, ina wuni, mun sameku lafiya?" Shan mur Ki tayi tare da waigawa ta k'ara k'arewa motar _Khalil_ kallo sanna ta maido dubanta ga _Khalil_ d'in tare da fad'in, "Bafa lafiya ba. Domin dai yanzu haka daga police station muke ni da sauran y'ay'ana gasu nan kana kallonsu." Tayi nuni da su Nuratu da suka k'ariso suma. Kallo d'aya yayiwa Aina'u ya shaidata, kuma itama ta gane sa. Kau da kai tayi tana tsaki cikin zuciyarta. Shuru _Khalil_ yayi yana sauraran Lami. Ita kuma ta cigaba, "To ni bama duk wannan ba, ashe kai ne uban cikin dake jikin Saratu, amma don tsabar iskanci da mugunta irin nata, sai tak'i fitowa ta fad'a min gaskiya don kar a dangwali arzikin dani, to yau dai Allah yayi sai mun yi foureyes da kai. Don haka akwai list d'in da nake rubutawa in ajiye sabida irin haka. Don fisabilillahi bazan iya ciyar da y'ay'ana kuma in ciyar da nasu y'ay'an ba. A k'a'ida ta zama cikin gidana, a cikin su kaf...." Tayi nuni da su Nuratu tare da cigaba da fad'in, "Duk wacce tayi ciki to kawo saurayin take gidan nan muyi tsada dashi domin d'awainiya da cikin, bayan ta haihu kuma, ni can cigaba da kula da babyn, cinsu, wankansu da duk wani abun da suke buk'ata. Don haka kai ma zan baka wannan list d'in, na ganka da maik'o a jikinka, don haka list d'inka daban ne." Kuka Sarah ta fashe dashi tare da durk'ushewa a wajen. Lami kuwa da baki ta nuna ta tare da fad'in, "Munafuka! Kiyi kukan jini ma. Wallahi sai na kawo masa list d'in nan kuma sai anci arzikin dani." Turo baki Aina'u tayi tare da watsawa Lami harara tace, "Sai kuma aka ce maki shi yayi mata cikin? To bashi bane!" Ta k'arisa maganar a tsawace. _Khalil_ kuwa mutuwar tsaye yayi yana kallon Lami da sauran y'ay'anta. So yake yaji ana tashinsa ana fad'a masa cewar mafarki yake yi, amma sai tsungulin cinyarsa yake yi ta baya, da yaji zafi sai ya tabbatar fa lallai ba mafarki bane. "Wannan wani irin gida ne na kawo kaina?" Fad'in _Khalil_ cikin zuciyarsa, amma a zahiri bakinsa ko motsi ya kasa yi sai bin Lami da idanu yake yi. Zuciyarsa na tabbatar masa da cewar Lami ba ita bace mahaifiyarsu Sarah. Ga dai y'ay'a nan kyawawa Allah ya bata, amma kuma babu tarbiya. "Jira ni, bari na shige na kawo maka list d'in." Fad'in Lami tare da shigewa cikin gidan. Na'ima kuwa, kallon Sarah tayi tare da fad'in, "Lallai Sarah kinyi babban kamu babu k'arya! Ina jiran nawa kason a cikin jira. K'anina a bata nawa kason ta kawo min." Fad'in Na'ima tare da shigewa. Nuratu kuwa sai kallon motar take yi ita da Hassana suna Santi. Don har hotuna suka yi a jikin motar kamun suka shige cikin gidan. Aina'u kuwa wani kallo tabi Sarah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login