Showing 27001 words to 30000 words out of 150033 words
Chapter 10 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
yarinyar kuma?"
Hajjo tace.
"Wallahi Musa yaron Alhaji ne ya kawota ɗazu taiwa Hajiya Ammi aiki Ni tausayi ta bani naji yace marainiya ce"
Ɗahare tai jugum.
"Kai hajjo ƙanƙantar yarinyar tayi yawa amman daga gani tana da shekaru damma Allah ya kawo ta hannu na gari matsalar ɗaya ce Ƴammatan Ammi suna da takurawa Mutum Musamman Bashir bai da Kirki gaskiya"
Ire iren maganganun sukai tayi har zuwa sanda suka miƙe domin suyi sallah.
Farha tana shiga Falon Ammi Sajeeda da Safna suna cin Abinci tai sallama Bata kalli saitin suba tayi hanyar ɗakin ta.
Sajeeda ce ta ɗaga Murya sosai.
"Village girl come here"
Sarai ta san da ita suke amman bata waigo ba ta cigaba da tafiyarta.
Safna da wani irin sauri ta ƙarasa wajan Farha ta finciko Hijabin ta.
"ke ƴar ƙauye kina ji ana miki magana dan rashin ɗa'a zaki tafiyarki?"
Farha tabi Safna da kallo doguwa ce sosai fara tana yanayi da shi, Daga gani ba zata wuce sa'arta ba.
"Kiyi haƙuri ban ɗauka dani kuke ba"
Dariya safna ta kwashe da ita sajeeda dake saman dining itama ta taya ta adaidai nan Ammi ta fito falon
"Ku kuma dariyar me kuke Allah ya shirya min ku"
Har Lokacin dariya suke.
Kafin Sajeeda dake dining tace wai Mun mata magana ne da turanci shine wai bata san da ita muke ba Ammi ita ce sabuwar mai aikin namu?"
Ammi itama dariyar tayi tana zama a saman kujera.
"Ita ce, Yarannan baku da dama ke fati Kibi waccan corridor ɗin zaki ga two bedroom nawa kije ki gyara min ki wanken toilet"
Ammi ta faɗa hankalinta kwance batare data tsawatar wa yaranta abin da sukai wa Farha ba.
Jikinta a matiƙar sanyaye ta nufi inda Ammi ta kwatanta matan Ɗakin farko ta shiga ta gyara shi tsaf Na biyun kuwa wanda take zaton na ƴammatan ne taci azabar gyara domin komai a zaune yake hatta panties ɗinsu sai da ta ɗauke har magariba tana faman Abu ɗaya sabida bata da saurin aiki.
Aliyu tunda ya tashi ya je station ɗin da aka kai Md Direct kotu aka miƙa md Aliyu ya kira lauyan shi suka ɗanyi maganganu dashi sannan aka tsaidar ranar shari'a ranar monday tunda Md har Lokacin yaƙi bada Shaida cikakkiya akan dalilin daya sanya ya yiwa Aliyu wannan Sharri.
Bayan ya rabu da lauyan shi gidan Kakannin shi yaje ya amsa Kiran Baba Usman wanda ya tabbatar Mishi da an ɗauro auren shi Godiya yayi wa Baba usman sannan ya baro gidan Bai shiga gida ba sai bayan sallar magariba kai tsaye kuma Ɓangaran Ammi ya nufa........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*
*18*
*A LOVE STORY 18*
Sallama yayi a falon Ammi tana zaune A falon bayan ta idar da sallah Safna da Sajeeda suna kwance a saman cinyarta suna charting da wayoyin su a hannayen su Gefe guda ga ƙatuwar Tv tana faman yi.
Ammi ta amsa mai sallamar cikin kulawa ya sami Saman kujera ya zauna da sauri su safna suka tashi zaune suna gaishe dashi fuska babu walwala ya amsa batare daya kalli inda suke ba.
"Ammi wannan abin da kike wa yarannan sam ba dacewa ta yaya yaran da suka isa suyi aure fisabilillahi zaki na ɗora su a saman cinyarki wani ma in ya shigo sai yayi dake"
Ya faɗa yana zabga musu harara sum sum suka Tashi suka nufi hanyar ɗakunan su.
A zuciye suka Faɗa ɗakin nasu Lokacin Farha tana Wanke Toilet ɗinsu Harara sajeeda ta maka wa farha.
"Dallah wuce ki bawa mutane waje jaka! har yanzu kina abu ɗaya gaskiya sai kinbar gidannan dan ba zamu shirya dake ba"
Safna ce ta tankaɗa ta waje suka datso Ƙofar Ran Farha ya Ɓaci, Nan da nan kuka ya tawo mata wanda ta durƙusa a wajan tana yinshi ba ƙaƙƙautawa ta jima tana kuka kafin ta nufi Hanyar ɗakinta sam bata lura da waɗanda suke falon ba ta shige ɗakin faɗawa saman gado tayi tana Cigaba da kukan ta dan abin da su safna sukai mata ya ƙona mata ranta harda ce mata jaka.
"Nace kaji ɗazu musa ya kawo Min mai aiki?"
Aliyu ya sosa kanshi bai nuna alamun ya san da maganar ba.
"A,a ni kam ta yaya zan sani Ammi"
Ya faɗa a taƙaice.
"Yace marainiya ce, ya kawo min ita nidai gaskiya ina da masu aiki da Lagos zan sa akai ta gidan Sadiƙ Ko Sharaɗa gidan salma"
Da sauri Aliyu yace.
"A,a Ammi ki duba ai ba zaki rasa abin da zata yi agidan ba, Tunda yace marainiya ce ai beci ace Kin kaita wani wuri ba shima Musa yaji hakan ba zeji daɗi ba"
Ammi tai murmushi tare da cewa.
"Ni ma tunanin haka dana yi yasa kawai nace zata dinga Muku girki a part Ɗinku tunda ɗazu salamatu tazo Min da batun zatai tafiya ƴarta ta haihu"
Aliyu ya wani haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba.
"Gaskiya Ammi ni bana son ƙazanta kawai daga kawo yarinya daga Ƙauye sai ta hau yi mana girki, Duk dani bana cin abincin kowa sai Na Mami ko naki amman bazan so Mami tana cin abincin wadda bamu sani ba"
Ya faɗa yana wani lumshe ido.
"Ai daga gani yarinyar tana da tsafta haƙuri zakai tana muku, Tunda ita mami koda ta dawo ɗin Jikinta bai ƙarfi sosai ba, Sannan kuma ba wai iya girkin zatai kaɗai ba zata Dinga gyara min ɗakina dana su auta tare da wanke mana Toilet"
Aliyu bai ce mata komai ba harta gama maganar tana cewa bari na kirata sai a ji nawa za ake bata a albashin wata.
Ammi ta ɗaga Murya sosai tana kiran.
"Ke Fati zonan"
Cikin hanzari farha ta dafe ƙirjinta dake faman duka.
Ta gyara hijabinta ta fito falon daga nesa dasu ta tsugunna muryarta a dashe wadda take nuni da taci kuka ta Ƙoshi tace.
"Gani"
Ammi ta bita da kallo.
"Matso mana nan dallah malama wa ze ɗaga muryar yi miki magana"
Da sauri farha ta matso daidai saitin Kujerar da Ammi take saman ta wanda ya bata damar kallon inda Aliyu yake zaune ya Fito da wayar shi yana dannawa ya nuna kamar bai san da ita a wajan ba.
"Ka ganta sunan ta fati"
Murya can ciki yace.
"To ni ammi ina ruwana da jin sunan ta duk ma'aikatan dake gidannan nasan sunan su Wasu ma ban san dasu ba, Gaskiya"
Ya faɗa idanun shi akan wayar shi.
Farha takaicin sane ya kamata ta sanya hannu tana share hawayen dake faman zubo mata wai Bawan Allah ne yake nuna mata Ko in kula.
"Nima abin da yasa na gaya maka sunanta har na kirata dan naga Musa ne ya kawota Shiyasa, Fati nawa kike ganin za mu dinga biyan ki?"
Farha tai shuru Aliyu yaja tsaki mai ƙarfi yana Danna wayar Hannun shi.
"Kin min shuru malama, wannan kuka naki baze Fishsheki ba in ma zaki haƙuri ki haƙuri ki dangana in kuma kukan zaki zan kira Musa na gaya masa"
Da sauri Farha tace.
"Ni dama zaki gaya masa ɗin dan Allah yazo ya fitar dani daga gidannan wallahi bazan iya aikin nan ba na haƙura zan koma ƙauyen kawai"
Daga Aliyu har Ammi zuba mata ido sukai ita ammi tana, tunanin ko sangartata iyayenta sukai da rashin aiki Suka mutu suka barta da aiki, shi kuma Aliyu jinjina ƙuruciyarta yake ko in ta bar gidan ina zata je oho mata.
"Wato ke ba zaki zauna ki nemi na kanki ba Kin saba rashin aiki ƙila iyayenki sun sangarta ki gashi sun Mutu sun barki da aiki To shikenan zan gaya wa Musan in yazo sai ki bishi ɗin baki da rabo"
Aliyu yayi saurin cewa.
"Ammi kada ki biye mata da ƙuruciya a tare da ita, Ki barta a haka zata saba"
Kuka farha ta saka.
"Ni babu abin da zan saba gaskiyata na faɗa akira sa ya mayar dani gidanmu bazan iya wannan aikin ba daga farawa yau har yaran can suna cemin jaka ni ko agida ina da ƙannen da suka fisu girma Duk talaucina ba zan zauna inda ba'asan darajar mutane ba.......bata ƙarasa ba ammi ta wanke mata fuska da mari.
Kafin ta janyota zata rufeta da duka Aliyu yayi saurin janyo farha yayi bayan shi da ita.
"Haba ammi me kike son aikatawa ne baki san amana Allah ya baki ba ita ɗin marainiya ce in kika cutar da ita Allah zai saka mata, Bayan nan akwai Hukumar kare haƙƙin ɗan adam dan tana mai aikin ki baze yuwu ki na dukan taba gaskiya ammi wannan ba daidai bane ba, Ina zaton yarannan zaginta sukai shiyasa take wannan kukan kin san ba kowa ne yasan aci zarafin shi ya haƙura ba dole zata ma gidannan kuɗin goro tunda bata sami karamci daga mutan gidan ba"
Ammi da ranta yakai ƙololuwar Ɓaci bata iya ce masa komai ba sabida ammi mace ce mai jarabar son ɗa ko kaɗan bata ƙaunar laifin ƴaƴanta Musamman waɗannan Biyun da kata ɓasu gwara ka taɓa kowa agidan shiyasa suke cin karan su babu babbaka suke taka uban kowa a ma'aikatan ɓangaran nasu kowa haƙuri yake dasu Aliyu kaɗai suke shakka shine yake cin Ubansu kai tsaye.
"Wuce ki bani guri ƴar ƙauyen banza in baki saita bakin kiba wallahi kafin kibar gidannan sai na miki Illah akan ƴaƴana ke har wace da zaki zo gabana kina magana yadda ranki yake so, Karkiga Musa ne ya kawon ke duka zakici kamar jaka"
Da gudu Farha tabar wajan tana wani irin Kuka.
Aliyu zeyi magana Ammi ta ɗaga masa hannu alamar bata buƙatar maganar shi sai da ta ɗauki lokaci kafin tace.
"Ka kira min musa yazo ya ɗauki wannan yarinyar"
Kai tsaye yace.
"Ammi ki haƙuri gaskiya ba zan iya cewa musa mahaifiyata ta kasa riƙon ƴar uwarshi ba sabida Musa mutum ne mai sona mai ƙaunata ya ɗauke shekaru yana min hidima ganin mun zama ɗaya ne yasa har ya kawo miki ita a ganinshi zaki iya Riƙonta"
Ammi miƙewa tayi bata ce komai ba tabar falon tayi hanyar ɗakinta ta shiga ciki ranta a mugun Ɓace.
Aliyu ya jima a zaune kafin ya miƙe kanshi tsaye ɗakin da farha ta shiga ya nufa.
Rufo ƙofar yayi tare da zira key kwance take a saman gado kuka take mai sauti ya janyo stool ya ɗora ƙafarshi ɗaya akai ya zuba mata ido kafin yayi gyaran murya.
"Idan kika ce rashin kunya zaki wahala zaki sha a gidannan koni da Ammi ta haifa ina mata ladabi wajan furta magana"
A ƙufule ta ɗago ta zuba mai jajayen idanunta.
"Ni kuma da aka siyo jaka ba zan mata ladabi wajan maganar ba daga nan suyi ta dukana har mahadi ya bayyana"
Ta murguɗa mai baki ta juya mai baya tana cigaba da kukanta.
Can ta kuma cewa.
"Kuma Allah zai saka min abin da kayi min, Bazan ji ko mai akan duk wata matsala da zata sameni ba tunda nina ƙi bin maganar iyayena kuma alhakin salim ma baze barni ba amman daɗina ɗaya addu'ar umma ba zata taɓa barina na sha wahalar da kake son ganina cikin taba"
Ta faɗa cikin kuka har da shashsheka!
Murmushi yayi mai sauti.
"Burina na ganki kullum kina kuka masifaffiya, Kin yi jagora wajan jefani acikin matsala sabida ƴar ƙaramar Buƙatarki wadda in da zaki biyo jerin Masu Roƙona na taimaka musu dana baki ninkin ta amman kika gwammace kiɗa akan karatu"
Cikin kuka tace.
"Allah ya kiyaye nazo na roƙi abu a wajan wanda bai san darajar ɗan adam ba mai karya alƙawari wallahi mutane kallon Kitse suke wa rogo amman kai asalin Mugune mayaudari"
Wata irin tsawa ya buga mata cikin har gagi kamar ze doketa ya ce mata.
"Be quiet to me ke har kin isa ina magana kina magana dan baki da mutunci ni sa'anki ne? kada ki ga nai miki maganganun soyayya a baya ko kaɗan maganar ce kaɗai a harshena amman ko Haƙorina bata taɓa ba ban taɓa jin son ki araina ba kamar yadda kika sani na aure kine danna Hukuntaki akan laifin ki, wanda son zuciya ya sanya kika aikata shi gaba in aka ƙara yi miki tayin Aiki irin nawa ba zaki ƙara yi ba stupid"
Cikin kuka tace.
"Ai aiki nayi ba maula ba kuma wallahi ko yanzu nabar gidannan sai nayi maka abin da yafi wannan Mayaudari macuci wallahi na tsanake Allah ya saka min"
Yayi murmushi wato rashin kunya a jininta yake ya lura bata tsoro tana da kafiya irin su basa Saduda barin hali sai Mutuwa.
"Ke har kina tunanin barin gidannan? to bari kiji Naga alama baki san ciwon kanki ba shiyasa naga kinfi dacewa da wanke wanke da sharar gidannan dan baki kama da ƴan jarida ba sai Ƴar aiki sabida ɗan jarida mutum ne mai nutsuwa mai ilimi mai bincike da hangen nesa Amman ke asalin jahila ce marar kan gado ke in banda baki da hankali ko igiyar takalmina kin kai matsayin ki riƙe bare Kiji nace ina son ki har ki yarda lallai rashin tunanin ki yayi yawa Duhun kai da jahilci yasa kikai gigin aurena zaki mutu da igiyar aurena akanki Ko Ƙofar gida ba zaki Ƙara leƙawa ba zaki zauna ki dawwa ma anan kina mana bauta nida mahaifiyata da matata in kinga kin fita daga gidannan to gidan zoo aka kaiki ganin dabbobi ƴan uwanki"
Daga haka yaja ƙofar da ƙarfi yabar mata ɗakin.
"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un"
Farha ta faɗa da ƙarfi tana sakin wani irin kuka tashin hankali ba'a saka maka rana.......
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*
*19*
*A LOVE STORY 19*
Farha tayi kuka har ta godewa Allah gashi babu mai rarrashinta ga wani irin tsoro daya cika mata zuciya sabida ta lura ɗakin tane kaɗai a falon su ɗaku nan su yana cikin wannan corridor ɗin data je ta gyara musu Haka ta ƙudundune Jikinta waje Ɗaya Har bacci ya fara ɗiban ta sai ta tuna batayi sallah ba ta miƙe taje toilet tayo alwala ta shinfiɗa Ɗankwalin ta tayi sallah ta jima tana addu'a Akan Allah ubangiji ya kawo mata mafita acikin halin data shiga kafin ta shafa addu'ar ta jingine kanta ajikin gado Bacci Ɓarawo ne ya sace ta wajan.
Aliyu yana shiga part ɗinshi tuɓe kayan jikin yayi ya rage daga shi sai Dogon wando fari da single ƙasa ya sauka ya haɗo coffee sai tururi yake ya zauna a saman sopa yana sha ya kammala ya jona system ɗinshi a charging, ya rage hasken ɗakin ya kwanta tare da janyo ƙaramin Pillow ya matse shi.
Duk rufe idanun da zeyi Hoton fuskar yarinyar yake gani tana kuka, yadda Ammi tai mata abin ya dame shi sosai yadda ƙannen shi suka cimata mutunci abin ya taɓashi sosai ya mirginawa gefe yaji Muryarta tana amsa kuwa acikin kunnen shi lokacin da take ce masa tasan baze cutar da ita ba.
Tashi yayi zaune tausayin tane ya rufe shi sabida shi mutum ne mai tsananin tausayi duk zafin ranshi da kafiyar shi yana da saurin tausayi.
Miƙewa yayi tare da ɗaukar jallabiyar shi daya rataye ya ɗora ta a saman Wandon jikinshi ya zira slipers, Ya sauka ƙasa Ya buɗe ƙofar falon ya fita gidan yayi shuru sosai sabida dare daya soma yi, Kai tsaye ɓangaran Ammi ya nufa ya Buɗe Ƙofar Falon ya shiga hatta Tv ɗin ba'a kashe ba Hasken falon ma haka da alamun tun tashin da Ammi tayi ta shiga ciki bata kuma fitowa ba kashe hasken falon yayi ya kashe tv Sannan ya shiga ɗakin Farha Hasken ɗakin yana kunne Tana zaune akan ɗankwalinta da alamun sallah ta idar bacci ya ɗauketa a wajan Ya ƙarasa gabanta ya tsugunna ya zuba mata ido murmushi ya saki Aranshi yana Jinjina ƙanƙantar ta sai Masifa da rashin kunyar tsiya.
Ɗagata yayi cak ya ɗora a saman gadon ya zare mata hijabinta ya ƙara mata Ƙarfin Fankar ɗakin sannan ya kashe mata ƙwan ya rufo Ƙofar ya fita Mayar da ajiyar zuciya yayi ganin tayi bacci bata cigaba da kukan ba.
Shima koma yayi bai kwanta ba alwala ya ɗauro ya cigaba da sallah har wajan ukun dare sannan yayi sha'i da wutiri ya kwanta bacci ana asubahi kuma ya farka yay raka'atul fijir ya fita masallaci daga masallaci Kayan training Ɗinshi ya zo ya saka ya fita Filin motsa Jiki wanda ya kwana biyu baiyi Morning training Ɗin nashi ba, Bayan ya dawo kuma wanka yayi ya kwanta bacci kafin zuwa anjima ya fita office
Bacci take mai cike da firgita haka kawai take firgita acikin baccin nata wataƙil ko sabida rashin sabon kwanciyar kaɗaici ne oho! sabida ta saba da kwanciyar Gidansu duk da ita kaɗai take kwana a uwar ɗakin umma amman Tana jin hayaniyar Mutan gidan nasu.
Sam bataji kiran sallar asubahi ba haka taita bacci har rana ta fito batayi sallah ba dama al'adar Ammi da sunyi sallar asubah baccin su suke koma In su safna basu da lecture ma har wajan 12 bacci suke Hajjo zata jera musu abincinsu masu gyaran falo su gyara Su kuma duk sanda suka ga damar Fitowa zasu fito suyi break ɗinsu su kunna kallon su batare da wata damuwa ba.
Sai wajan 11 wayar bashir ta farkar dashi wanda yake masa bayanin motocin sun iso kamfanin shi na abuja duk kuma abin da ya dace sunyi shida manager sabida haka gobe ko jibi ze tawo kano.
Suna gama wayar da Bashir ya miƙe Ya kuma shiga bathroom ya jima aciki kafin ya fito da ruwa ajikin sa alamun wanka ya sako, Ya shirya cikin black trouser tare da white shirt mai dogon hannu wadda ta fito da zatin Ƙirar Jikinshi Ya fesa turare ya maƙala Baƙin agogon fata a tsintsiyar hannun shi ya ɗauki Black shoe mai Buɗaɗɗan sama ya sanya ya ɗauki wayarshi kai tsaye Part Ɗin Ammi ya nufa domin su gaisa ya fita Office Duk inda ya gifta ma'aikatan gidan na zubewa suna gaishe dashi har ya shiga Falon Ammi abin mamaki babu alamun sun tashi daga bacci ya ɗaga kai ya dubi agogon bangon dake ɗakin Ƙarfe sha ɗaya har da Mintuna arba'in.
Zama yayi a saman one seater har wajan 12 babu motsin kowa miƙewa yayi ya shiga ɗakin Farha abin mamaki ya bashi yadda ya kwantar da ita haka yazo ya same ta a sheme