Showing 18001 words to 21000 words out of 150033 words

Chapter 7 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

ta fito Ƙofar gidan Ikram ta biyo ta tana cewa
"Yaya Farha umma tace ga jakarki"
A zuciye ta juya.
"Dan ubanki sai ki kai min ita aji munafuka"
Ta faɗa batare data lura da Aliyu dake tsaye a wajan ba ya zuba mata ido yana kallonta tsananin ƙanƙantar Yarinyar ita tafi komai ɗaure masa kai sai dai ya kula ƴar bala'i ce ta a mutu, Taɓe baki yayi yana nazarin yadda take surfawa wadda ta biyota masifa Ikram ta juya gida a guje sabida yadda Farha ta kawo mata duka.
Adaidai nan kuma Farha ta Juyo zata cigaba da tafiya ƙafarta ce tai mata nauyi sabida wanda tai arba dashi a tsaye a gabanta ya zuba mata ido babu Ko ƙiftawa............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*RABO YA RANTSE...!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*13*

luuu ta tafi zata faɗi Aliyu yayi saurin tarota jikinsa da faffaɗan hannunshi Ya wani rungumeta a cikin ƙirjinshi Ƙifta idanu Farha take tana Ƙoƙarin zamewa gaba ɗaya Jikinta rawa yake sosai tunda take a rayuwa ba namijin daya taɓa raɓata da jikinshi sai wannan bawan Allah da bata san kowa ye shiba.
Cikin Nutsuwa ya zamar da ita daga jikinsa yana sakar mata mayaudarin Murmushi.
Da sauri ta tattare Ƙasan skirt ɗinta zata Koma gida da gudu Aliyu ya kuma saka hannunshi a karo na biyu ya janyota gabanshi.
Ko Rabin tsayin shi bata kai ba ganinta yayi ƴar ƙarama a gaban shi Ya Sunkuyo sosai gabanta ya rage tsayin shi ya ƙura mata idanunshi waɗanda ya lura Suke mata kwarjini a tare dashi fiye da komai.
Lumshe idanu Farha tai Jikinta yana rawa ƙirjinta yana bugawa bata taɓa Ganin Halitta Mai kyau kamar ta wannan Bawan Allah ba, Dan ko kaɗan bata ɗauka ma bahaushe bane.
"Amincin Allah da rahmar sa su tabbata agare ki My princess"
Muryar Aliyu mai taushi ta doki dodon kunnen Farha.
Ƙara raɓewa tai Duk jikinta yayi sanyi atake anan wani irin BAƘON LAMARI Ya ziyarci zuciyarta.
"Nasan zaki mamakin yaya akai nazo har gidanku? Ba mamaki abin da kake so shi kake bibiya Naje har gidan Radio ɗin da kike aiki wanda anan hanyar na ganki amman Naga gidan Radio ɗin a Ƙone mai ya faru da shi?"
Gaban Farha ya faɗi waige take Ko wani zai zo wuce wa daga cikin ƴan gidansu ganin babu kowa yasa taja ajiyar zuciya.
"Bawan Allah kayi haƙuri dan Allah, Nima ban san mai ya faru da gidan Radio ɗin ba, Kuma kabar Ƙofar Gidannan sabida Kawun mu in yazo ya tarar dani da wani raina zai ɓaci"
Aliyu ya zubawa ɗan ƙaramin bakinta ido wanda take sarrafa shi wajan yi masa magana dashi ya wani Lumshe ido tare da warasu akanta Kana yace.
"Ina son ki kuma ni da maganar auren ki nazo in baba ma ya ganni zan sanar masa Naga matar aure agidan shi"
Farha ta firfito da idanunta waje cike da tsaro.
"Dama ana aure batare daka san Mutum ba Bawan Allah?"
Aliyu yayi Murmushi yana danne Abin da ke taso masa a ƙasan ranshi.
"Sunana Bawan Allah anan cikin gari nake nagaya miki in zaki fita aiki nake ganin wucewar ki gashi ma baki gayan dalilin Ƙona gidan Radion naku ba"
Farha ta dafe ƙirjinta dake barazanar faɗowa ƙasa dan tsabar yadda yake Luguden duka.
"Kayi haƙuri Dan Allah, Ina da wanda zan aura in Babana yazo ya ganka sai ya halaka ni"
Aliyu ya wani zaro ido wanda ya ƙara haska zatin kyansa wanda ya kuma ruɗa farha.
Yace.
"Nima ai mijin aure ne serious ina sonki kuma da gaske in da hali zan maye gurbin wancan"
A wannan karon muryar farha da ɗan tsiwa tace.
"Zaka biya dukkan hidimar daya ɗauka shekara da shekaru yana mini Idan har na Rabu dashi ai naci amanarshi na yaudare shi Kuma zan sanya Ƴan uwana da iyayena cikin damuwa"
Aliyu ya cije leɓe.
A zuciyar shi yana Cewa Ni kuma silar labarin ki ɗaya a jiya ya cillah dukkan ahalina cikin matsala ya sanya Mahaifiyata zubar hawaye Wallahi bama zan barki ba sai nai amfani da ƙarfin soyayyata na ruguza dukkan farin cikin ki yadda kika min.

Gani yaƙi cewa komai yasa ta juya zata shiga gida, Hannun shi ya ɗora a saman ƙafaɗunta ya juyo da ita tana kallon Fuskar shi.
Ya matso gabanta har yana fesa mata Hucin Numfashin sa

"Ni ina son ki, Kuma auren ki zanyi ina son ki min list na duk abin da yayi Miki ni zan ninka masa"
Daga haka ya turata soron gidan da ƙarfi ya juya yana tafiyarsa mai cike da burgewa.
Zubewa tai a wajan tana Mayar da Numfashi wata sabuwa!
Da ƙyar ta shiga cikin Gida duk maganar da Umma kewa Farha sam taƙi bata amsa gado ta haye tana tunanin anya ba aljani bane ba Ita dai bata san shiba sannan kuma bata taɓa ganin Mutum mai kyanshi ba ɗan gayu ga ƙamshinsa ya cika mata hancinta Tsintar kanta tayi da Lulluɓe Jikinta duk rufe idanun da zatai hoton shine ke yawo acikin idanunta tashi tai ta Zabga tagumi Ganin hakan baze fishsheta ba ta miƙe ta fita tsakar Gida ta ɗauro alwala ta soma nafila.

********
Yana murmushin samun nasara ya shiga Motar Ko kaɗan batai masa ba hasalima bata burge shiba kawai zai aure tane dan ya ƙuntata mata ya kuma sanya takaicin ta acikin zuciyar mahaifanta ya fahimci daga ita har mahaifanta suna bala'in son wannan saurayin nata sabida haka zai amfani da ƙarfin Soyayyar shi wadda zai cusa mata ta ƙarfin tsiya dan ya wargaza dukkan farin cikinta ita da mahaifanta kamar yadda tai jagaba wajan Yaɗa sharrin sa.
Sam baze miƙata ga Hukuma ba aurenta kaɗai da zeyi shine dorinar dukan dukkan laifi kan data masa Sabida ta yaya ma zai tsaya yana shari'a da mace.
Gumi ya share sanda ya tuno da Ammi yasan ko yasha giyar wake baze tari Ammi da batun zai auri yarinyar nan sabida Hukunci ga laifin data masa ba to meye mafita zai boyewa Ammi auren sane Girgiza kai ya shigayi ammi bata cancan ci haka daga gareshi ba Sannan kuma yasan inta sani bazata yarda ya auri yarinyar ba Shi kuma ta hanyar aure kaɗai ya zaɓi Ƙuntata mata dan shi ba mazinaci bane bare yay amfani da wata dama dan ya tarwatsa mata Farin cikinta Kuma shi ya tabbatar wa zuciyar shi cewa baze taɓa barin Wannan yarinya ba wallahi sai ya ɗauki fansar Abin da ta masa.
Har suka ƙarasa gidan shi bai sami mafita ba sallama sukai da Musa wanda bai san yadda Aliyu Yayi da yarinyar ba kuma bai sami fuskar tambaya ba bare ya tambaye shi.
Part ɗin Ammi ya nufa ta tirsasa shi akan dole sai yaci abinci yana ci tana masa Bayanin Maman Mami tazo da Ƴaƴanta Dan su masa jaje, Sannan ta buƙaci Daya Musu alfarma Mami zata ɗan kwana biyu agida ta huta.
Taɓe baki yayi tare da cewa.
"Nifa Ammi cikin satin nan ma zanje chaina dan zan shigo da sabbin Motoci kamfanina dake lagos sabida haka bani da matsala da zamanta agidan nasu"
Daga haka ya tashi yayi mata sallama yabar part ɗin.
Kwanciya yayi akan gadon shi yana hasko fuskar yarinyar Ƙaramar yarinya ce sosai Shi dariya ma ta bashi yadda yaga duk ta tsorata in banda Abin shiri na zuciyar mace ina ita ina shi Ya kuma gyara kwanciya yana hasko ƙanƙantar ta Lallai wannan ma in yace zai haɗa ƙirji da ita tabbas Mutuwa zatai dan yayi mata girma shi bai ma taɓa ganin Halitta ƙarama kamar ta wannan yarinya ba komai nata ƙarami hatta yatsun hannunta daya kalla ƙananu ne.
ALIYU KENAN.
Yaja Bargon shi ba jimawa bacci yay awon gaba dashi.
Da safe ya fita kamfanin shi tuni ya watsar ma da batun wannan yarinyar ya shiga sabga da ma'aikatan shi wanda yawanci Jaje ne suke masa akan abin da ya faru Dan nacin Ƴan jarida har can suka bishi akan suna son jin ta bakin shi fafur ya hana ma'aikatan shi barin ƴan jaridar su shigo masa haka ya wuni a office yana saka hannun a takardun Motocin da aka tura wasu jahohin bai tashi ba sai wajan Magariba ƙofar Gidan shi ma ba masaka tsinke tun yana magana muryarshi tana fita har muryar tashi sai da ta dashe sabida amsa gaisuwar jama'a bai shiga gida ba sai wajan 12 na dare Yana mai jin farin cikin yadda al'umma suka nuna rashin jin daɗin su na abin da ya same shi lallai ya yarda jama'a rahma ce Kuma alkairi Daɗi gare shi wanka yayi ya kwanta jikinsa fal gajiya Hutu kaɗai yake buƙata..........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
          
           *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                        *14*

Juyi kawai take yi a gado jikinta sanye da ƙaramar riga mai hannun shimi hannunta dafe da daidai ƙasan mararta wanda take dannawa sai Nishin azaba take Kukan ma yaƙi zuwa tun bayan datai sallar Asubahi take jin ciwon Marar ta na taso mata kaɗan kaɗan adaddafe tai sallah ta koma gado ta kwanta tana faman Juyi
"Wai yau ba zaki fita aiki bane Farha? jiya dai baki da lafiya amman yau ya kamata ki fita kada suce kina wasa da aikin ki"
Cewar umma da take tsaye a kanta.
Ɗago idanunta tai wanda yayi jajir sabida azaba Murya can ƙasa tace.
"Umma nai wa ogan waya na gaya mashi bani da lafiya bazan iya fita ba"
Umma tabi ta da kallo tana nazarinta.
"Yaya naji muryarki a haka Ko jikinne?"
Cikin tsananin azabar zafin marar tace mata.
"Umma marata ciwo ji nake numfashina yana fita da ƙyar"
Ta faɗa cikin azaba Umma ta ɗauki wayarta ta soma haska saman sif ɗinta Maganin farha ta lalubo wanda saura ɗaya ya ƙare ta miƙa mata fita tayi waje ta ɗebo mata ruwa lokacin data dawo har ta miƙe zaune.
"Ungo kisha kafin Ikram ta tashi sai ta amso maki wani"
Ta amshi ruwan ta watsa maganin cikin bakinta Tashan ye tana mayar da Numfashin wahala Jim kaɗan ta miƙe tai tsakar gida aguje tana kwarara amai wanda shine ya Tada jama'ar gidan su.
Babarsu Ruƙayya ce ta tsaya akanta tana mata sannu Babarsu Hadiza kuma ta wanke mata Aman Ƙannenta sai sannu suke mata tana amsawa da ƙyara Duk abin Matan gidan da ƴaƴan gidan in abun jaje ya samu suna ƙoƙarin karantawa Amman in tashin hankalin su ne ya motsa ba sauƙi.

A wajan ta kwanta har rigarta na yayewa Ƴan cilli cillin cinyoyinta Suka bayyana a waje Kawu ne ya fito yana kallon ta.
"Wannan kuma lafiya ko jikinne?"
Umma data ke ɗagota Zuwa jikinta tace.
"Ciwon marar tane ya tashi shine tasha magani take amai"
Kawu ya koma cikin ɗakin sa.
Can jimawa ya fito da ɗari Biyu.
"Ga wannan ku tafi asibiti a dubata Allah ya sawaƙe"
Umma tabi Naira Ɗari biyun da kallo tana cuɗa yadda zata musu Kuɗin mota har da ganin likita ba abin kai magana ba yayo maka caa.
"Allah saka da alkairi"
Daga haka ta ɗaga Farha suka nufi ɗaki da taimakon umma ta shirya Suka fito domin zuwa asibiti.
Da ƙyar aka kaisu bakin asibiti a naira ɗari Layi suka tarar sosai a asibitin Farha na zaune tana jin yadda wasu mata suke magana ɗayar ce tace.
"Ai tuni an ƙona gidan radion tun ranar, Naji ance ma an kama mai gidan radion ita kanta yarinyar datai labaran an kamata, Wai gwamna da kansa yace zai ɗauki mataki akansu shi kuma Hasken matasan yace a,a abar shi da kanshi zai ɗauki mataki"
Farha tai tsuru tana jin wannan ƙarya wai an kama wadda tai labarin bayan gata a zaune.
Tana jin yadda matar take ta zabga wa mutanan wajan ƙarya akanta alhalin gata a zaune kuma tana wa Allah godiya abisa rufin asirin dayay mata daya sa babu wanda ya kama sunanta har yanzu.
Haka layi yazo kansu suka shiga ganin likita wanda ya rubuta musu magani Daga asibitin Zage suka shiga Gidan yayar umma anan suka ci abincin rana da ƙyar ma umma ta yadda ta zauna sabida tasan halin kawu da faɗan tsiya.
Ita kam farha bacci ta samu bayan taci abinci wanda Umman zage tace wa umma tabar farha zuwa yamma sai ta tawo gida Haka umma tai wa Umman zage sallama ta tafi gida.

Koda Umma taje Gidan kawu faɗa ya kamayi akan me zata baro masa ƴa a wani waje ta kamo hanya ta tawo umma tasan za'a rina sabida yadda tasan shi mutum ne mai taka tsantsan akan ƴaƴanshi.
Shuru tayi masa ta shige ɗaki sai ya bita yana cewa ta mayar dashi mahaukaci Umma dai bata yi magana ba tazo ta tarar da gidan A bushe ba ai abinci ba inda bata biya zage ɗin ba da haka zasu dawo da yunwa damma ta tarar da Ikram ta tafi gidan fa'iza.
Zuwa yamma Halifa ya kawo garin tuwo kwano Biyu yace a tuƙa sabida yau Mai gidansu yasa an musu kyautar Dubu goma goma Shi kuma nura ya bada dubu biyu yace ayi cefane.
Amman Fafur Babarsu Ruƙayya tai ɗakinta da garin, tace babu wanda zata tuƙawa tuwo da garin Ganin haka yasa itama Babarsu Hadiza ta bada Dubu biyun da Nura ya bata tace  Zuhuriyya ta siyo musu taliya da mai da Kayan miya haka kowacce ta saka tukunyarta tare da ƴaƴanta dama umma tasan za'a rina shiyasa bata fito tsakar gidan ba har wajan Marigaba tana ɗaki Sai da aka kira sallah Ikram ta dawo daga gidan Fa'iza Lokacin data shigo ɗakin Hannunta riƙe da fulas wanda Fa'iza ta ciko shi da awara da naira ɗari biyar tace a kawo wa ummansu.
Kawu ne ya ƙara zuwa bakin Ƙofar Umma.
"Hasiya wai har yanzu fatima bata dawo ba kinga bana son irin haka kada ki ƙara bar min Ƴaƴana a wani wuri"
Umma data zuciyo dama da taƙaicin matan gidan a ranta duk da tasan cewar kawu bai san abin da sukai ba.
"wai kai dan Allah in farha ta zauna acan gutsirar namanta za'ai? ina ba wajan yayata taje ba in ta zauna anan wani abun zaka mata nan maganine aka rubuto mata kazo ka tambayi kuɗin sai aikin tambayar ta dawo"
Bala'i ne ya kaure a tsakanin Umma da kawu abin da bai taɓa faruwa ba haka ya fita ƙofar gida ya tsaya yana sauraran ta inda farha zata fito har ya gaji ya nufi Bakin titi wajan zaman shi sai dai a ranshi ya ƙudiri aniyar sai ya mata arnan duka idan ta dawo gida.

Farha sai Bayan magariba tai shirin dawowa gida bayan sunyi sallama Da umman zage wadda ta bata kuɗin Mota katin ta na wajan Likita daya rubuta mata magani ta ɗauko ta fito daga gidan cikin ikon Allah tana fitowa ta sami abin hawa.

Yau Aliyu bai wunin Office ba yaje wajan visa ɗin sa ta fita chaina wadda yay cuku cukunta yana dawo wa gida kuma ya wuce cikin gidansu mahaifin sa rabon kuɗi yayi Musu kamar yadda ya sanya musa ya rabawa kaf ma'aikatan sa dake kamfanin shi Kuɗi Ya jima wajan ƙannen mahaifinshi Kafin ya fito Yaja face mask ɗin shi ya rufe fuskar shi sabida mutane Ya laluba aljihun shi da ƴan canji Napep ya tare yace masa ɗandago A bakin layin su Farha ya sauka ya shiga cikin layin lokacin gari ya fara duhu.
A ƙofar gidan ya tsaya ba yaron da ya fito daga gidan sai dai Yana jiyo kukan yara da hayaniyar matan gidan ya jima a wajan duk sauro ya gama cije masa jikin shi.
Yarinyar jiya ce ta fito da kuɗi a hannunta daga gani shago zata je yay saurin matsowa kusa da ita.
"Ke ina masifaffiyar yayarki ta jiya?"
Ikram da bata gane ko waye bane sabida abin kare fuskar dayay amfani dashi ta soma ƙifta ido cikin tsoro tace.
"Farha bata nan tana zage"
Ta faɗa cikin sauri tare da tsoro.
Ya nanata sunan
"Farha"
Lallai kam.
"Sunan ta kenan Shi ake gaya mata?"
Da sauri Ikram tace.
"Eh ko kace fatima ba"
Jin Muryar Halifa dake fitowa yasa Ikram ta Nufi hanyar shagon aguje Halifa yabi Aliyu da kallo wanda bai gane ko waye bane Aliyu ma baiwa halifa magana ba ya cigaba da tsaiwar shi a wajan Har Ikram ta dawo daga aiken ta ta shige cikin gida.

Adaidai nan kuma farha ta shigo layin sanye take da hijabi har ƙasa ja Wanda ya rufe mata har tafin ƙafafunta Daga hannunta ma yatsun hannunta kaɗai ake gani.

Tana ƙoƙarin Hawa dakalin gidan wanda bata lura da Aliyu dake tsaye ba Taji yo muryar kawu wanda garin saurin ta shiga gida har faɗuwa tai ta miƙe tana kaɗe hijabin sai dai kafin ta shiga har kawu ya ƙaraso wajan Aliyu yay saurin matsawa daga jikin gidan ya zuba wa Tsohon ido wanda yaji muryarshi yana cewa.
"Fatima sai yanzu kika dawo to ki jira zuwana daga ke har uwar taki data ɗaure miki gindi ni kinsan ba'a yawo a gidana ba zan lamunci wannan ɗabi'a ba Shiyasa na matsu wannan yaro ya turo ni koba lefe aurar dake zanyi"
Takaicin tijarar kawu ya kama farha shi haka yake in yaso cin mutuncin sa a ko ina yi maka yake yanzu meye abin wannan maganar a ƙofar gida damma ba kowa a layin.
Kawu ya juya ya koma titi Ita kuma ta nufi Gida zata shiga.

Da sauri Aliyu ya sha gabanta.
"Kinga shima ya matsu ki aure to mai kike jira ga miji a hannun ki kin samu"
Taji muryar BAWAN ALLAH a cikin dodon kunnenta cikin taushin murya yayi mata maganar.
Yana zare face mask ɗin daya rufe fuskar shi da ita.

Da sauri ta ɗago kai tana kallon shi.........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login