Showing 114001 words to 117000 words out of 150033 words
Chapter 39 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
ƙare shikenan zan sallame Ki seki Koma gida"
Hawaye ne me ɗumi yazubo wa farha batare data san ya zubo mata ba Ga abin da take nuna mai amman sam yaƙi fahimta.
Murya a shaƙe tace.
"To Ammi Ko yan zu ma zan iya komawa tunda dare be yiba"
Sakina ce tai zaraf tace.
"Kaji ƴar rainin hankali da baƙar magana irin ta mutanan ƙauye yanzu Ammi ɗin kike gayawa magana haka?"
Safna ce tace
"Ai da yake ba uwarta bace......
Adaidai Lokacin Aliyu ya shigo falon sanye yake da jallabiya ash colour mai Dogon hannu ƙamshin turaren shine ya soma sanar da zuwan shi Kafin ya bayyana bai ko kalli sai tin da farha ke tsugunne ba Kona ce da ƙyar ma idan ya kula da ita ya ƙarasa wajan Ammi ya zauna yana fito da wayar shi Musa ne Ke kiran shi akan Ko zasu je Gidan su Farha kamar yadda yace ɗazu sukai magana da Musa se Da ya gama wayar sannan ya shiga gaishe da Ammi a nutse suka gaisa da Sadiƙ Sakina da jamila dasu Bashir Suka gaishe dashi.
"Wai Baba yau ina ka shiga sallah Guda kowa se tambayar ka yake Kuma kamar haɗin baki mami ma yau ko leƙo mana batai ba"
Ya ɗan shafi kanshi se Lokacin ya kula da ita ya basar kamar bai ganta ba dan har Lokacin Haushin ta yake Ji dan tayi masifar ɓata mai rai Seda yayi Controlling kanshi ma ya iya zuwa sashin Ammi.
"Ammi na shiga meeting ne mai muhimmanci se yanzu na sami kaina"
Ammi tace "Allah ya temaka" cikin kulawa kafin ta mayar da hankalin ta wajan farha wadda take raɓe a tsugunne se ruwan hawaye ke faman Biyo Kuncin ta.
"Tashi kije ɗaki Ki aje kayan ki seki Fito ki tattare mana falon nan kinga yadda ya koma"
Farha batai Ko Motsi ba dan ji take Zuciyarta kamar Dutse.
"Ba magana nake Miki ba kika sakani gaba" Ammi ta faɗa a hasale
"A,a ni zan koma kawai kamar yadda kika buƙata Inna ɓata Muku rai a iya zamana daku Ku yafe Mini"
Daga haka ta Miƙe Bashir da sauri yayi gabanta ya riƙe Trolly ɗin kamar ze Kuka ya dubi Ammi.
"Haba Ammi Haba Ammi abin da kike sam babu kyau Ammi meye ribar wulaƙanta ɗan adam wanda baka san baiwar da Allah yayi masa ba"
Kafin ya dubi farha a hargitse yace.
"Babu inda zaki je a wannan tsohon dare Koda zaki tafi wallahi se an baki haƙƙin gaɓarki kuma gari ya waye sannan ki tafi"
Aliyu cikin rashin fahimtar abun da ya faru yake Bin kowa na falon da kallo kafin ya dire akan Farha data ɗora hannu a fuska tana Gursheƙen Kuka.
"Bashir ni kake gayawa haka akan wata Ƴar ƙauye yayi maka kyau nike da damar ɗaukar masu aiki a gidannan to nace Na gaji da ita dama alfarmar Baba taci Idan gidan kane seka barta bama a darannan ba a yanzu zata bar Mini Gidana ni wannan masifa ta ishe ni"
Sadiƙ ne ya shiga bawa Ammi haƙuri wadda take masifa kamar ana tinzirata ga bashir ya Tsaya akan Farha ba zata bar Gidan da wannan daran ba Su Safna dariya suke sakina kuma se faman zuga Ammi take Aliyu yaji ranshi ya ɓaci da wannan Cin zarafi da mahaifiyar shi take Ƙoƙarin Yiwa matar shi jiyay gwara ya tauna tsakuwa a wannan karon Ko aya zata ji tsoro.
Tashin dayay domin ya Nufi wajan Farha Jiri ya ɗebe shi babu zato suka ji ƙarar faɗuwar shi Aliyu ya faɗi baya Numfashi kwata kwata kanshi ya bugu a tiles ƙafar shi ta daki Katakon Jikin Kujera wanda yatsan ƙafar ya ce ƙass wanda ya bada tabbacin Ya sami tsagewar ƙashi a yatsan nashi ga gefen kanshi da ke zubar da Jini sakamakon faɗuwar da yayi daga Ammi har Su Sadiƙ ƴar Rige rigen zuwa gabanshi Suke yi Ammi kuka kawai take se ta fita a guje tai Compound tana kiran driver agigice suka shigo ammi na cewa
"Sadik ku saka min shi a mota in Baba ya mutu nima bin bayan shi zanyi na shiga Uku Baba Me ya same ka Innalillahi wa'innah ilaihirra'jun Allah ka farkar dani daga wannan Mummunan mafarki dana keyi"
Da sadiƙ da Bashir da ƙyar suka ɗaga Aliyu zuwa mota Su Safna kuka kawai suke yi ammi kuwa dan Kuka Ko Muryarta bata fita ko mayafi seda aka miƙa mata sannan ta shiga motar da ita dasu sadiƙ suka tafi asibiti.
Farha juwa ce take ɗibarta a hankali take dafe bango tana silalewa ƙasa zama tayi daɓas a ƙasan tiles tana sakin ajiyar zuciya ta saka hannu, ta Shafo hawayen dake Biyo Fuskarta Hankalin ta ya tashi ta kasa Nutsuwa ta kasa tunanin komai akan hakan Lallai akwai matsala kalmar Innalillahi data ke ta faɗa ita ta zama makamin bata Nutsuwa ta ɗaga kai ta hango su Safna nata Kuka in ba idanunta Gizo yayi mata ba tabbas matar sadiƙ ba kuka take ba dariya take tana Wa ƴaƴanta wasa sedai daga taga su Safna sun ɗago zata fara share hawayen ƙarya ƙanwarta bata wajan bare taga a wani hali take itan
Bata da Lokacin Tunanin dalilin dariyar sakina sabida haka tashi tayi a hankali ta nufi ɗakin da aka ware ya zama nata ada ta ƙudiri ba zata kuma kwanan Gidan ba amman yadda taga halin daya shiga yasa dole zata zauna domin kota tafi ma bata da sauran Nutsuwa wato kuka ma se da dama ake yin sa hawayen ta ya ƙafe kawai hango yadda ya faɗi take tana kuma hango yadda aka fitar dashi kamar gawa take Cikinta ya murɗa ta dafe Gefen mararta wanda ke faman juyawa kwanciya tayi a ƙasa bata damu da tarin ƙurar dake ɗakin ba Nishi take tana kiran sunan Allah har Gumi ya soma wanke ta marar ta lafa mata da ciwon Jitai kamar Ihu da kururuwa Hankalin tane ya kuma tashi bayan data tabbata daga falo take Jiyo Ihun! wanda tunaninta ya bata ya rasu Shikenan ta ɗora hannu aka ta fasa Ihu mai ƙarfi tunanin yanayin su na ɗazu yana mata yawo a idanunta da rarrafe ta fita falon Sedai babu su Ammi Mami ce take kukan daya sa taji kamar Ihu take Su safna na taya mami kukan sakina ce ta fito tana musu magana.
"Haba duk kun cika mana gida da Ihu se kace wanda aka ce ya rasu haba da Allah se kace ba Musulmi ba kema mami da Girmanki kinzo kin biyewa ƙananun yara"
Mami ta ɗago ido tana hararar sakina.
"Dole muyi kuka ai kuka muya kama da ma bama su Burin ya mutu suci dukiya ba sakina bari Kiji duk wani iskanci naki a tafin hannuna yake da duk wata gadar zare da kike haɗawa"
Mami ta faɗa tana kallon sakina wata ƴar iskar dariya sakina ta saki tare da cewa.
"Ai duk kanwar jace Ni ma kallon ku nake an gaya miki ana shiga dawa dan ƙarya ne to bari Kiji kifi na ganin ka mai jar koma gwara ma kowa yay takan shi tun kafin ai mutuwar kasko haihuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance"
Daga farha har su safna hankalin su bai kai kansu mami ba har sukai suka gama ita mami manufar maganarta akan sakina shine Tana sane da yadda take cusa mai ƙanwarta ya aura sannan kuma taga yadda kowa yake kuka amman sakina batai ba shine dalilin daya sa ta faɗawa sakina haka wanda ita kuma sakina Jikinta seyay sanyi ta ɗauka ko mami tasan shirin tane Shiyasa itama ta yanko tata baƙar maganar ta yaɓa wanda tasan dai Aliyu baya son mami ammi ta haɗa auren amman bata san komai ba bayan haka Dukkan su Jikinsu yayi sanyi kuma sun shiga ɗarɗar kamar wani yasan sirrin wani mami Kukan dai ta Cigaba dayi ganin dare nayi yasa farha ta ƙarasa wajanta tana rarrashinta Mami tace wa farha tazo suje part Ɗinta su kwanta haka tabi mami Ranar farha dai batai bacci ba daga ƙarshe alwala ta ɗauro tazo tana ta sallah duk hankalinta yaƙi kwanciya tai kuka ta gode Allah kanta har ciwo yake mata ga ciwon mararta wadda ta ɗaure tai gam.
Duk yadda likitoci suka so dawo da Numfashin sa abin yaci tura A taƙaice har ya shafe awanni Biyu yana a tsakanin halin rayuwa da Mutuwa ne Likitan ya fito yana yarfe zufa sadiƙ ya Miƙe da gudu bawan Allah ko takalmi babu a ƙafar shi ya tari Hanyar da Likitan ze wuce.
"Doctor yaya mai jikin da Muka kawo?"
Likitan yaɗan dubi sadiƙ tare da cewa.
"Sorry ka kwantar da hankalin ka"
Bashir ya taso ido jajir yana cewa.
"Kaga malam in kun kasa zamu ɗauke shi a yanzu zamu yanki ticket ɗin ƙasar waje wannan wani irin iskanci ne asibitin kuɗi mai tsada kamar wannan amman Ku kasa aikin ku"
Likitan ya dafa kafaɗun Bashir Lokacin Ammi ta karaso wajan yaɗan kalli sadiƙ yace masa.
"Muje Office"
Bashir yace.
"Wallahi babu inda zaku seka gayan a wani hali ɗan uwana yake ciki idan ya rasu kawai ku gaya mana mu ɗauki gawar shi"
Likitan ya dubi bashir wanda yay kamar baya hayyacin sa.
Kafin yayi magana wata Nurse wadda ya bari a ɗakin ta fito da sauri tana cewa.
"Doctor yana numfashi yanzu"
Da gudu Likitan ya koma dama ya fito ne dan ya ƙaro kayan aiki Taimakon gaggawa suka cigaba da bawa Aliyu har Allah yasa Numfashin sa ya dawo Normal allura sukai masa tare da gyara masa Yatsan sa daya bugu sannan suka manna mai plasta a Kanshi wurin daya fashe Likitan yaja mai ƙofa bayan yace kada wanda yaje Inda yake.
Sadiƙ likitan ya kira Office ai da sauri ammi tabi bayan su.
Likitan ya zauna sadik da ammi suka zauna.
Likitan ya dubi sadiƙ.
"Gaskiya yallaɓai ku kiyayi abin da ze dinga ɓata masa rai dan zuciyar shice ta Buga wanda bada ban Allah ya taimaka ba ze iya rasa ranshi sannan Jininsa ya hau lokaci ɗaya tabbas Allah ne yayi akwai sauran kwanan shi akwai abin da akai agaban sa wanda ya ɗaga mai hankali ya kuma ɓata masa rai se a guda in ba haka ba akwai matsala"
Salati ammi tahau yi tana tunanin me yake damun Baba haka Da har waɗannan lalurori suka far masa lokaci guda.
"Hajiya ai ita ƙaddara ba'a mamaki da faruwarta Amman dai a kula dashi sosai dan Allah in ba so kuke ku rasa shiba" shawarwari likitan ya basu tare da Bawa sadiƙ Bill ɗin su yaje ya biya Ammi cewa tai anan zata kwana Bashir yace a,a shima ya sadiƙ ya koma gida shi seya kwana a wajan Aliyu tunda Likita yace sallama se zuwa gobe da yamma kafinnan ya ƙara warewa.
Wajan Sha biyun dare su Ammi da driver suka kamo hanyar gida daga asibitin suka bar Bashir.........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 91*
Lokacin da su Ammi suka shigo gidan tsit yake sabida kowa yayi bacci Ammi ta wuce ɗaki sadiƙ ma ya tafi masaukin sa Gaba ɗaya hankalin Ammi ya gaza kwanciya don ita ma babu mamaki idan aka duba Jinin nata yahau sedai rashin Lafiyar Aliyu Yafi Komai ɗaga mata hankali har Lokacin kuka take idan ya rasu tasan da wuya itama zata ƙara Moruwa Duk ƴaƴanta yafi soyuwa azuciyarta yafi mata biyayya to me yake damun sa haka da wannan matsaloli suka taru sukai masa yawa Haka bata kwanta ba alwala taje ta ɗauro ta dinga Sallar nafila se wajan asubahi bacci yayi awon gaba da ita.
Sadiƙ yana shiga ɗakin daya sauka mamaki ne ya kama shi ganin sakina a zaune cikin shirin kayan bacci tana ganin shi ta saki Murmushi ta miƙe ta shiga banɗaki ta haɗa masa ruwan Ɗumi tazo gabanshi ta shiga cire masa kayan jikin shi bai musa mata ba sabida yadda ya gaji Shima hutu yake buƙata da taimakon ta ya samu yayi wanka ya fito ta kawo mai kayan bacci Catton na maza ya saka yana umartarta akan ta kawo masa ruwan Shayi taje ta kawo mai.
"Abbansu yaya naga duk jikin ka yayi sanyi ka shigo babu kuzari?"
Sadiƙ ya kurɓi ruwan zafin tare da aje cup ɗin a center table ya kalli sakina fuska babu sukuni
"Jikin Aliyu ne ya bani tsoro wallahi duk hankalina a tashe yake na rasa Nutsuwa ta"
Ta ɗan kalle shi cikin zaƙuwa da taji abin da ke damun Aliyu ɗin.
"Mutuwa likitan yace zeyi ko cutar ɓarin jiki ce ta kama shi?"
Sadiƙ cikin tsananin mamaki yace.
"Ban fahimta ba sakina dama akwai wanda yasan ranar Mutuwar wani ne In ba Allah ba?"
Ta ɗan sosa kai tare da cewa "To naga duk ka ɗaga hankali ne In ba haka Likitan yace maka ba to meye zaka wani zo duk ka damu kanka so kake kuyi Mutuwar kasko shi a kwance kai ma a kwance a,a gwara anyi ɗaga shiɗin dai ya kwanta"
Sadiƙ ya zubawa sakina ido cikin Nutsuwa yace "Ban gama gano nufin ki ba Ai ni a tunani na duk abin da ya shafi Aliyu nima ya shafeni kamar duk abin da ya shafe ni shima ya shafe shi" Ƙaramar dariya sakina tayi.
"Kai dai kake ganin haka Ni jikina ma ya bani Mutuwa zeyi babu mamaki mutuwar Fuji'a ce Faɗuwar ajali yayi dama abu ne irin nasa ya auri jamila yaƙi da tuni yaga ɗan kanshi to ai yanzu gashi nan ya tara mana dukiyar ze mutu yabar mana ita muyi yadda muka so" wata irin tsawa sadiƙ ya bugawa sakina yana toshe Kunnen sa tunda take bata taɓa ganin sadiƙ a irin yanayin data ga ya shiga a yanzun ba ya shiga girgiza kai yana Hawaye "Ya Allah idan har ka ƙaddara Aliyu mutuwa zeyi Ya Allah ka dawo da wannan ajali kaina ni na mutu domin rayuwar sa tafi tawa amfanuwa ga Al'umma duk da Allah ba wanda ya isa yayi maka dole ba mai saka ba mai hana ka yadda kaso kake yi a lokacin daka so kaga dama"
Sadiƙ ya faɗa yana wani irin kuka wanda ya bawa sakina mamaki zatai magana ya ɗaga mata hannu dan baya buƙatar tace masa komai.
Cikin Tsiwa da rashin Kunya ta miƙe tsaye akan shi.
"Daga faɗin gaskiya zaka hau Kuka, Me yake tsinana maka kai kenan Kullum Yi masa hidima ya mai da kai kamar yaron sa Baka da komai se Masa hidima in da yana ƙaunar ka ya mallaka maka kamfanin sa na lagos mana ai yaƙi Se aikin matar sa kullum taci tai kashi waya sani ma ko mu yake tarawa dukiyar Wallahi bama zan ɓoye maka ina jin matiƙar haushin biyayyar da kake yi masa"
Sadiƙ ya ɗago idanun shi jajir yace mata.
"Wallahi sakina baki isa kin rabani da Aliyu ba naji bani da komai ɗin tun da ke baki da godiyar Allah duk ni'imar da Allah yayi mana kin take ta Aliyu kike hangowa to bara Kiji kamar yadda ci bezo ɗaya ba To ƙoshi ma baze zo ɗaya ba Ko yatsun mu in muka duba ba daidai suke ba, kuma ni bana baƙin ciki da arziƙin Aliyu dan ta hanyar halak Allah ya bashi maganar Matar sa kuma ai bake ce Kike bada haihuwar ba Allah ke bada wa ba ita zaki wa Gori ba don ba ita zata bawa kanta ba jamila kuma ni kaina bana masa sha'awar auren ta dan bata da kamun kan da Aliyu ze zauna da ita a matsayin uwar ƴaƴan shi kema nadamar auran ki nake bada ban darajar ƴaƴana ba da tuni Kinyi gaba wallahi su kaɗai nake dubawa amman ki cigaba da yadda kika so na baki Lokaci ne kaɗan, Dan babu wata macen da zata shiga tsakanina da ƴan uwana in zuba mata idanu"
Sadiƙ ya faɗa a zafafe Sakina jitai ƙafarta na rawa Lallai ashe akwai sauran aiki a gabanta Duk haƙilon da take dan wa take idan ba dan shiba ashe ma shi bai san tana yi ba Jikinta se ya ɗauki rawa muryarta na karkarwa "Abbansu yau ni kake gayawa haka akan Aliyu? dan wa nake haƙilon nan dan kai nake yi kai ma ka shaƙi iskar ƴanci kai ma ka tsaya da ƙafafun ka, ka fita daga jerin yaran kamfanin sa Amman har ni zaka buɗi idanu ka jefawa waɗannan maganganu to Allah yasa a budurwa ka same ni bare kace nayi yawon ta zubar tun da kace Jamila bata da kamun kai"
Cikin fushi sadiƙ yace.
"Da bana shan iska kenan Look sakina kada ki yarda na same ki da wata manufa akan ɗan uwana na rantse da Allah in kika bari na kamaki da wata manufar ɓoye akan ɗan uwana wallahi senai shari'a dake kuma bari Kiji har yau har gobe babu macen da zata raba mana kai nida Aliyu soyayyarmu daga Allah take Kuma abin da kika kasa ganewa Aliyu yana da kamfanin Mota ne A lagos da sunan sa amman Komai na kamfanin ya sakar Mini se yadda nai dashi In har na cuci Ali kona zalunce shi ba zan gama da kyau ba sabida babbar nadama ce ka cutar da wanda ya baka yarda da amana In kuma ban godewa Allah akan ni'imar da yayi min ba zan godewa azabar sa Ko yau na mutu nagode Allah dan yayi min dukkan suttura ƴaƴana kuma nina san Aliyu ze aurar Mini dasu Muddin yana raye ze tsaya musu a komai"
Da sauri sakina tabar ɗakin sadiƙ be kwanta ba alwala ya ɗaura yana jero sallar nafila akan Allah ya bawa Aliyu lafiya ya kuma shirya masa matarsa ya cire mata hassada da ƙyashi da baƙin ciki.
Yadda Sadiƙ ammi farha basu rintsa ba haka sakina ma bata rintsa ba asubar fari ta tashi jamila suka bar gidan dan fita tai wajan bokanta akan ya bata maganin mallaka da ɗaurin baki wanda bata ɗauka sadiƙ ze bata matsala haka ba shiyasa batai tunanin bi ta kan shiba a gidan su suka aje ƴaƴanta ita kuma da jamila suka nausa ƙauyen da Bokan nata yake.
Farha tana zaune a saman darduma a tsakiyar ɗakin mami sabida a ɗakin mami suka kwana tare bayan ta idar da sallar asubahi ta ɗaga hannunta sama idanunta yana zubar da hawaye addu'a take yi akan Allah ya bashi lafiya kafin ta idar ta shafa