Showing 66001 words to 69000 words out of 150033 words

Chapter 23 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

ba wanda ya isa yasan gaibun Allah shine mabuwayi masani mai ilimin da babu wanda ya san iyakar shi Shine yaga ƙarshen mulkin kowa nasa kuma ya gagara aga ƙarshen shi To Allah cikin Ilimin sa da ikon shi da hikimar shi ya ƙaddara ƙaddara giftacciya data ƙullah auren Aliyu da fatima cikin hikimar sa a yau yasa suka kasance to koyaya Wannan lamari ze kasance Muje zuwa Mudai Munsan ƙarya sakina da tawagarta suke Ta Allah ce gaskiya cikin mami ma wallahi ba sakina bace ta zubar daman can Allah ya ƙaddara bama su rayuwa bane kawai taje wajan mashirikai ne suna amfani da Kuɗinta suna gaya mata ƙarya dan su ci kuɗinta amman abin da Allah ya ƙaddara babu mai kawar dashi babu mai hana shi Allah ne yasan mai ya Ɓoye dabai bawa mami ciki tsayayye ba Kuma Bahaushe Yace Rabo idan ya rantse se me shi rabo dangin ajali ne................
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*A LOVE STORY 50*

Zaro idanu farha take tana jan Numfashi da ƙyar sabida itama adaidai wannan Lokacin zazzaɓin ne ajikinta sedai zafin Jikinsa yafi nata sosai Kuma Jikinsa rawa yake wanda har abin yaso ya bata tsoro, Tinawa tai da addu'ar da Manzon Allah ( S.a.w ) yace muddun mutum nayi babu wanda ya isa ya cutar dashi ƙafa uku ce a hankali ta Lumshe idanunta ta soma karanto addu'ar. Bayan tayi Bisimillah seta soma cewa.
"Bisimillahil lazi layadurru ma'asmihi shai'un fil ardi wala fissama'i wahuwassami'ul Alim"
Cikin azaba take addu'ar Kuma idan tayi haka take tofa masa itama ta tofa har takai ƙafa uku Kuma tana tofa masa taji Yana wata irin karkarwa Yana ƙara shigewa Jikinta a Lokacin ta saka kuka tana cewa.
"Ya Allah! na shiga uku wallahi rabani Biyu zakai nifa ƙarama ce ka bari"
Matseta ya kuma yi Numfashin sa yana fita da wani Irin sauri Kafin ya fara cewa
"Fatima please ki rufeni sanyi nake ji Mutuwa zanyi lulluɓe ni wayyo Allah na"
Farha ta ruɗe tana kuka kuma gashi ya matseta ba damar ta miƙe a haka taji ya dena rawar Jikin kuma jikin nasa ya dena zafin Se saukar Numfashinsa taji a saman wuyanta da alama bacci yayi awon gaba dashi ta sauke ajiyar zuciya sedai har Lokacin hankalinta bai kwanta ba seda ta tabbatar Baccin sa yayi nisa sannan taɗan sami Nutsuwa Kuma lokacin Raɗaɗin ƙasanta ya dawo Fil amman da tashin hankali ya hana taji Bata iya Motsiba sabida daga ta Yunƙura zata Motsa ze ƙara janyota Jikinsa yana sakin ajiyar zuciya kamar ɗan da uwarsa ta Fita ta barshi agida ta dawo ta tarar yasha Kuka ya Ƙoshi shima haka ya koma mata har asubahi yaƙi sakinta duk kafaɗar ta ciwo Jikinta yayi tsami wiyanta ya Sanƙare sabida rashin Juyi.
Har aka tada sallah a masallaci bai iya tashi ba abin da ya bata mamaki Kenan itama baccin ne ya ɗauketa sabida kwanan datai tana gadin sa dan wani Irin tausayi ya bata dama ai babban Mutum kamar shi ze wuya ya rasa maƙiya dan abun da yayi ya bata tsoro.

A hankali Aliyu ya buɗe idanunshi da sukai masa nauyi sukai jajir Jin kansa yayi yay masa nauyi kamar an ɗaura dutse Yaji bakin sa babu ɗanɗano ko kaɗan da sauri ya miƙe Jin an tada sallah da toilet Ɗinta yay Using ya tsarkake kanshi ya Ɗauro alwala This is the first time dayay Missing jam'in asubahi a rayuwar shi.
Ya shinfiɗa darduma a saman carpet ya data sallah bayan ya saka jallabiyar shi ya jima yana addu'a acikin sujjadar shi.
Shidai baze ce komai ba akan fatima tinda matar shi ce ya Lumshe ido ta cika shi da mamaki ta kai shi wata ƙorama mai cike da ruwa mai sanyi Se yace ta shayar dashi ruwan mamaki lallai dukkan cikar halittar mace baga shekaru take ba a baiwarta take ada ashe kallon Kitse yake wa rogo Har Lokacin Jikinsa bai da ƙwari sabida zazzaɓin daya kwana yana yi sam abin yazo masa sama taka ne ba tare daya tanadi wannan ranar ba har rana ta fito yana ɗakin a zaune yana gadinta Allah yasa yayi wa Ƙofar Key abin da bai taɓa yiba kenan Zaman ɗakin mace Ko mami ita ke Binsa

Ƙarfe takwas daidai farha ta farka da addu'ar tashi daga bacci ta yunƙura da Bisimillah zata tashi Ina Cinya da Jiki suka ce lah inji balarabe, suka ƙi miƙuwa dan azabar da suka ci ta Cije
baki tana rintse ido adaidai nan Aliyu ya ɗago ya kalleta aka ci sa'a itama ta kallo inda yake ido suka zubawa juna ita ta soma zare nata sabida Kunyar da take ji tasa.
"Sannu kin tashi?"
Tai ƙasa da kanta bata ce komai ba har na tsayin mintina shima hakan ce ta kasance dan bai iya mata magana ba sabida bai san yadda ake rarrashin mace da bata baki ba.
"Kayi azkar ɗin safe?"
Abin da ta faɗa masa kenan.
Shaf shi mantawa yake da azkar sabida daya tashi uziri ɗauke masa hankali yake rabon da ya tsaya yayi azkar har ya manta Sabida uziri sallah ce wannan baya wasa da ita amman bayan ita baya tsayawa yayi azkar.
Ta kuma cewa.
"Ka daina wasa da azkar sabida faɗin Annabi ne addu'a takobin mumini ce akwai addu'oin da in kayi ƙaryar Mutum ko aljan, Sannan ka dinga yawan sadakar ruwa da Niyyar Allah yay maka tsari daga dukkan sharri sannan ka dinga yawan bawa mutane sadaka kana cewa su maka addu'a saboda yawun wani yafi naka a wajan Allah daga yace Allah yayi yin yake sabida akwai manyan bayin Allah wanda ya ɓoye su batare da ansan baiwar da yayi Musu ba, Nasan kai mai kyautatawa mutane ne wannan ne ma yasa Allah yake baka kariya sabida ta yuwu ma akwai bayin Allah da kake taimako batare daka sansu ba shiyasa aka ce kada ka raina kowa koka wulaƙanta shi, domin baka san baiwar da Allah yayi wa wani ba Amman lamarin ka ya bani tsoro Allah ya tsareka daga dukkan sharri"
Tunda ta soma magana ya zuba mata ido bako Ƙiftawa kuma adaidai Lokacin data furta azkar ya soma karantowa daka wanda tuni ya haddace shi tun yana yaro har ya kammala ya shafa.
"Allah yayi miki albarka ke kam wace Irin mutum ce, Na wahalar dake na baki karatun da baki taɓa shiga ajin sa ba amman Ba burinki ciwon da Kike ji ajikin kiba Burinki ki tunatar dani abin da ze kareni ya zame min alkairi da zaman lafiya a rayuwata wannan magana ta ƙara Miki Ƙima a idanuna Allah yayi Miki albarka"
Ta sunkuyar da kanta a ƙasa a yadda take jin wutar soyayyar shi A zuciyarta Komai ma zata iya sadaukar masa dan ya zama farin ciki gare shi.

Har ya Miƙe ya ɗagata daga saman gadon tunani take seda yakaita har Toilet sannan ya ajeta ya sunkuya yana taro ruwan zafi ya haɗa sosai A ƙaton bawon dake toilet ɗin.
"Oya shiga Ciki ki zauna naji ance haka ake yi"
Tawani narke Fuska tana kallon ruwan zafin dake Huci.
"Dafa zafi wallahi wannan zafi zeyi salon na ƙone"
Yayi wani kalar murmushi.
"Malama bafa a ƙonewa a wannan wajan Pls ki shiga kona danna ki"
Ta soma dira ƙafafunta kamar yadda yara keyi idan sun so rigima batai aune ba taji ya ɗagata cak ya zare skirt ɗin Jikinta ya dannata cikin ruwan yana cewa
"Wannan shine kwanciyar hankalina"
Runtse idanunta tayi tana jin yadda ruwan ke ratsa ta hannu tasa ta kare Ƙirjinta dan Lokacin babu kaya ajikinta.
Tsugunnawa yayi a gabanta ya zare hannun data kare Ƙirjin nata dashi, ya ɗora nashi hannun akan tudun ƙirjin nata a hankali yace.
"Gaba ɗaya ƴan gidana sunyi jajir sabida yadda na aikace su ko?"
Ya faɗi maganar da wani kalar salo mai kashe ma'abocin da aka wa shi a hankali taji hucin Numfashinsa adaidai dokin wuyanta kafin taji saukar Ɗumin bakin sa a saman Kirjin nata ya shiga sarrafawa kamar mayunwacin zakin daya sami nama.
Lumshe idanu tayi zaman bawon ya kusan gagararta Numfashi yake fitarwa sama sama ganin ze Loosing control ɗinshi ahankali tace.
"Wallahi ban gama warke ba so kake ka kashe ni"
Lokacin hawaye ya soma zarya a saman fuskarta ya ɗago kanshi a wahale gaba ɗaya idanunshi ya sauya kala.
"Zaki iya wankan?"
Ya faɗa a rarrabe da sauri ta ɗaga kanta alamar eh.
Ya tashi ya fita daga toilet ɗin yana rangaji Wankan tayi ta ɗauro alwala ta dafo bango ta fito ɗakin bata ganshi ba da alamun ya bar ɗakin gaba ɗaya a zaune tai salla dan wahala haka ta rarrafa ta koma gado sabida taga ya sauya zanin gadon taja bargo ta lulluɓa zazzaɓi da ciwon Jiki ne suka rufeta a lokacin ko ƙafarta ta kasa juyawa sabida azaba kamar ma bata shiga ruwan Ɗumin ba haka take ji tai kuka harta gode Allah kafin wahalallan bacci yayi awon gaba da ita.
_Umm Allah sarki ni kowa yana baccinsa a wannan lokacin niko na zubawa waya ido 1:22 na dare ina rubutu 😢 Allah ka ciyar damu da halak ɗinmu neman halak akwai wiya Allah ka bamu da guminmu kasa mu dogara dakai ka rabamu da bara ko maula a wajan wasun ka ya Rabbil Alamin_



*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 51*

Cikin sa'a da nasara ya fita daga ɗakin kuma beci karo da kowa ba a falon Godiya yayiwa Allah daya rufa masa wannan asiri kamar iska zata kwashe shi haka yake tafiya jinsa yake sakayau babu ƙarfi yana zuwa part ɗin sa shima kwanciya yayi wanda bacci me nauyi ya ɗauke shi bashi ya farka ba se wajan 12 na rana yana buɗe ido yaga Mami a kusa dashi a zaune duk fuskarta babu walwala.

Ya kalleta yana yamutsa fuskar shi.
"What do you need?"
Yace mata da muryarshi wadda tayi kala data wanda ya tashi daga bacci idanun shi ya ƙara girma sosai goshin sa duk ya tattare.
Hawaye ne ya zubo mata ta miƙe tsaye tana kallon shi cikin damuwa sosai wadda ta gaza ɓoyeta tace masa.
"Yaya haihuwa nake buƙata bana son na mutu ban sami ɗan kaina ba yaushe ne cikina ze tsaya yaushe zan dena ɓari nima naga ɗan kaina a duniya"
Ta faɗa tana wani irin kuka me tsuma zuciya se Aliyu yace tunda yake ganin kukan Mami be taɓa ganin mai yawa irin na wannan lokacin ba.
Ya ware mata hannayen shi muryar shi a dashe take sabida yanayin baccin daya farka daga shi yace mata.
"come here and be quiet, stop crying like that" a hankali ta faɗa saman ƙirjin shi tana wani irin kuka mai tsuma zuciya ya rungume ta cikin kulawa yake rarrashinta.
"I don't like this cry of yours" ya faɗa yana share mata hawayen dake gudana a saman fuskarta Kwanciya tayi a jikinsa tana sakin ajiyar zuciya cikin rarrashin ta yace mata "I think I am worried about this problem and it is bothering me a lot sedai ba yadda zan yi na miƙawa Allah dukkan lamurana tunda Alhamdulillahi bamu da wata matsala daga ni harke to se mu zuba wa sarautar Allah ido muga yadda zeyi damu"

Ta ɗago tare da kallon fuskar shi.
"Yaya zaka iya samun haihuwa daga wajan wata matar tunda ni ga yadda matsala take zuwar min, sedai zanyi baƙin ciki ga wannan rana da bana fatan tazo min na ganta dan nafi son ni kaɗai na zama giwar ka uwar ƴaƴan ka in sha Allah"
Ya shafa kanta batare daya ce mata komai ba ya cigaba da Gaya mata kalaman kwantar da zuciya tare da dogaro ga Allah Mami taji hankalinta ya kuma kwanciya da kalamin dayayi mata kuma tasan yanzu tana da muƙami a zuciyar sa.
"Bara nayi wanka duk jikina ciwo yake and ki ɗauko min panadol da ruwa marar sanyi" ya faɗa yana zare ta daga jikin sa ya miƙe ya shiga wankan wanda ya jima acikin Bathroom yana gasa jikinsa da ruwa mai zafi kafin ya fito yana tsane ruwan dake sakko masa daga Jikin sa ya shirya kanshi cikin white trouser and black shirt wanda suka ƙara haska zatin kyan shi tare da fito da ƙarfafan surorin jikinsa ya ƙarasa gaban dressing Mirrow yana feshe Jikinsa da turare mami tayo sallama a ɗakin hannunta ɗauke da maganin da ruwa ta buɗe masa murfin gorar ruwan ta miƙa masa ya amsa yasha ya fita daga ɗakin yabar mami aciki domin gyara masa zata yi.
Ya sauka ƙasa dinning ya nufa ya haɗa tea kaɗan da bread ya zauna yana ci har aka kira sallah yana dinning ɗin Lokacin Mami ta sauko ta gama masa gyaran ɗakin nashi zama tai a gefen shi da alamun yau baze fita ba sabida hira suke sosai har tana tsokanar shi da yau ya tsuke wa zece ma yana da aure yayi Murmushi yace.
"Ba su san ni matana har biyu bane ba"
Mami dariya tayi zaton ta wasa yake mata ya duba agogon hannunshi ya miƙe ya fita ta raka shi har bakin Ƙofa alwala ya ɗaura a famfon dake Bakin shiga part Ɗinshi ya tafi masallaci yayi sallar azahar kowa yau mamaki yake me ya hana oga fita Ya jima zaune tare da ma'aikatan gidan yana sauraran Ƙorafinsu Har albashi seda ya yi musu alƙwarin zasu ga ƙari a ƙarshen watan sannan ya bawa mai gadin shi Kuɗi yace yaje ya siyo Pure water Mota guda ya rabawa dukkan Gidajen dake kusa dasu amman kada yace daga shine sadaka ce yana faɗi ya Barsu suna ta masa Godiya Sashin Ammi ya shiga Lokacin Bashir ze fita Office suka gaisa kona ce Bashir ya gaishe dashi ba yabo ba fallasa ya amsa ya Shiga falon Ammi da sallama da ita da su safna suna zaune A falon yau da alamun ƙafar akwai sauƙi a ƙasan carpet ya zauna yana gaishe da ita su Safna suka gaishe dashi Ya zaro wayar shi yana danne danne da alamun yau baya jin yawan magana ne.
"Baba baka jin daɗi ne?"
Cewar Ammi ya ɗaga girar shi yana cewa.
"Me kika gani Ammi Nikam lafiyata lau"
Tayi Murmushi "Baba kenan kai dai zaka ɓoye min amman naga rashin ƙarfin Jiki a tare dakai"
Ya shafa kanshi "Ammi driving danai from kano to katsina shine na gaji amman ba abin da ke damuna"
Ya faɗa yana Murmushin daya ƙara masa kyau.
"Ammi zan sami farfesun kayan ciki wajan ki?"
Ya faɗa yana kallon ta Ammi taɗan tsuke fuska.
"Muma ba wanda yayi karin kumallon sabida kace Hajja ta daina zuwa waccan yarinyar Kuma tun ɗazu Muke dukan Ƙofarta taƙi Buɗewa waya sani ma kota Mutu"
Gabanshi yayi wani irin faɗuwa yana fatan kada Allah ya amsa maganar Ammi.
Ammi tace "Sajeeda leƙa ko ƴar gwal ɗin ta buɗe ki taso ta" sam ya kasa magana sabida yadda bakin shi yayi nauyin furta komai har Sajeeda ta Miƙe se rakatan da yayi da ido.
Tana zuwa bakin Ƙofar ɗakin Farha By Lucky ta miƙe ta zare keyn jikin Ƙofar ta shiga toilet sabida yadda ta farka da fitsari da ishirwa ta buɗe Ƙofar ne akan tana fitowa daga toilet ta fita ta sha ruwa sedai tana fitowa taga sajeeda tana faman kallon ɗakin gaban farha ya faɗi hankalinta ya tashi da sauri tace wa Sajeeda.
"Lah lafiya me me kike nema?"
Ta faɗa har tana raba maganar tata sajeeda ta taɓe baki tare dajan wani wawan tsaki tare da cewa....................*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 52*

"Nida gidanmu har zaki tambaye ni abin da na zoyi a ɗakin nan? to idan na ga dama wallahi seki kwashe kayan ki, Ki koma wajan Ƴan uwanki masu aiki dabba"
Farha tayi ƙasa da kanta tana jin hawaye na shirin zubo mata amman bata bari hawayen ya zubo ɗin ba ta nufi Bakin gado domin tsaiwar ma gagararta zata yi sabida rashin ƙarfin Jiki da take fama dashi.
Sajeeda ta tako har gaban farha ta ɗora ƙafa ɗaya a saman gadon har tana shurin ta tare da cewa.
"Daga yau in kika kuma barin mu bamu karya ba wallahi sena karya ki shegiya da muni kamar daran Mutuwa jaka Kucaka Kizo Ammi na jiranki Mtsss"
Ta tofa mata yawu  a fuska tabar ɗakin Farha dan takaici Kuka ta saka seda tayi me isarta sannan ta Gyara Hijabin nata ta fita daga Ɗakin gudun cin mutuncin Ammi, Aliyu ya sauke ajiyar zuciya hangota da yayi tana dafa bango tana fitowa daga ɗakin nata zuciyar shi rawa take Ji yake dama ya ɗaukota ta dena wannan tafiya yasan tayi matiƙar ƙoƙarin iya ɗauke lalurarshi.
Ammi zuba mata ido tayi wanda yasa Aliyu yaji duk hankalin shi ya tashi a hankali ta ƙaraso gabansu ta zauna tana rintse ido kamar ta zauna a saman ƙaya.
"Ke me kike yi haka da baki ɗora mana abincin karyawa ba?"
Ammi ta faɗa tana binta da kallon Tuhuma.
Tayi ƙasa da kanta bata yarda ta kalli setin da Aliyu yake ba Ammi ta kuma daka mata tsawa!
"Ni sa'arki ce da ina miki magana ma kina min shuru kosu yarana bayin ubanki ne da zasu ɗora miki abincin Eye? to saurara kiji wallahi wannan shine karon ƙarshe da zaki Ƙi dafa mana abincin kinji na gaya miki"
Ita dai Farha har Lokacin kanta yana sunkuye tayi shuru A hankali taji muryar shi yana magana
"Ammi ki mata a hankali baki ga kamar bata da lafiya ba, Bara na saka ayo muku takeaway ko yarannan su dafa ai dama su nace su dinga yi amman ammi kika hanasu"
Farha taɗan saci kallon shi Fuskarshi bata nuna yana da alaƙa da ita ba Magana yake hankalin shi a kwance yana danna wayar shi sedai yau babu wannan ɗaure fuskar ba masifa dan ga ƙannen shinan har sun sami zarafin zama a falon wanda da in yana falon ta lura basa iya zama a ciki sabida tsoron shi.
"Baba nifa ba zan saka su Safna girki ba wallahi bama zan ɓoye maka ba tunda ka dakatar da Hajja to sedai ita ta dinga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login