Showing 54001 words to 57000 words out of 150033 words
Chapter 19 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
ba su ba kuma da kuturin Munafurci inji kin gaya masa wallahi sena karya ki na watsar dake Ƴaƴana ba kalar wahala bane ba abun da zasu yi kece zaki komai munafuka"
Farha dai se kuka take ta kasa magana tunda take bata taɓa ganin Mutum wanda ya tsaneta ta farar ɗaya kamar Ammi ba.
"Tashi ki bani waje Munafuka".
Ammi ta faɗa tana saka ƙafa ta ture Farha wadda ta hantsila ta Kifa Har hancinta na fashewa Kuka ta saka mai ƙarfi ta Miƙe ta Nufi hanyar fita daga falon aguje duk tunanin ta ya gushe tama mance hanyar ɗakinta wanda adaidai nan Kuma Bashir ya turo ƙofar ya shigo Karaf suka ci karo da Farha wadda tai taga taga ta faɗa saman Ƙirjin bashir da sauri Shikuma ya tarota Jikinsa ya saka hannun shi ya damƙo Ƙugunta ya riƙe gam........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 41*
Bashir shagala yayi da kallon Farha tunda yake bai taɓa ganin Macen data fusgi hankalin shi irin taba fatar Jikinta laushi Ƙugunta cikakke ya cika masa tafin Hannun shi Bashir wanda idanun shi suke a buɗe tar a harkar mata yaga fara yaga baƙa mayen mata ne Duk samun sa a gindin mata yake tafiya indai mace zata bashi Jikinta shi kuma ze mora mata komai take so kuma ze mata Gogagge ne akan mata ya ƙware sosai a fannin neman mata wanda tun yana yi a ɓoye har Maganar tazo kunnen Aliyu da Sadiƙ sedai duk yadda suka so su fahimtar da Ammi abun yaci tura domin taƙi yarda da maganar tace ƙarya suke masa Wanda suka faɗa ma sharri ne sedai inda Ammi zata saka idanu akan Bashir shine abin da zata fara fahimta ina yake kai Kuɗin sa Aliyu yace ai masa aure Ammi tace har yanzu Bashir yaro ne ita bazata aurar dashi yanzu ba wannan tasa suka tattara batun sa suka watsar tare da zuba masa ido wanda yake cin karan shi babu babbaka dan har labari aka zowa da Aliyu akan Bashir nada gidan sa inda yake kai matan banza ranar daya gayawa Ammi Seda ta kwanta a gadon asibiti tunda ga nan Aliyu yayi fushi ya zubawa Bashir Idanu.
Murza ƙugunta ya shigayi cikin wani irin salo yana kusanto da fuskarsa daidai tata wanda ita kuma take ƙoƙarin ta ƙwaci kanta gaba ɗaya hankalinta idan yayi dubu ya tashi Kokawa ce ta kaure a tsakanin Bashir da Farha shiya gigice da dirin Jikin farha wadda kallo ɗaya yayi mata ya gano karuwar Jiki gareta a haka zaka ɗauka ƴar ƙarama ce sedai ga wanda yasan mace yasan Farha ƙaramar ƙasa ce da albarkatun man fetur.
A fusace ta ɗago tana ƙare masa kallo Shima fari ne siriri kamar bafulatani sam basa kama da kowa agidan kamannin sa daban Cizo ta gartsa masa a Hannun daya riƙe ta dashi aikuwa ya sake ta yana yarfe hannun aguje ta koma ɗakin ta Lokacin Ammi bata falon key ta murza ajikin Ƙofa ta zube a wajan tana sakin Numfashi idan hankalin farha yayi dubu tofa ya tashi Kukan ma yaƙi zuwa ita tunda take ba namijin daya taɓa ratsa Ƙugunta sai shi Ko Mijinta baya gigin taɓa Jikinta ko salim da sukai soyayya Mai tsarki sukai bai taɓa kai hannu Jikinta ba gwarama bawan Allah daya ɗan riƙe ta Lokacin daya zo wajan ta.
Da ƙyar ta koma saman gado duk a tsorace take Sai da ta ɗan sami Nutsuwa sannan ta shiga Banɗaki tayo alwala ta shiga rama sallolin da suka hau kanta ranar Bacci gagarar Farha yayi tabbas Idan har wannan saurayin a gidan yake tofa zaman ta a gidan akwai hatsari tunda ta Lura Mahaifiyar su Se abin da ɗa yaga dama yake yi musamman ƙananun dan ta lura kamar tafi son su.
Sannan Kuma tana tsoron gayawa Bawan Allah tasan halin shi kada itama yaje ya dake ta, ko kuma babar su taji tace sharri ne ɗaga hannu tayi tana addu'a akan Allah ya kawo mata ɗauki acikin wannan hali se can dare Bacci ya ɗauke ta mai cike da firgici da mafarkai marasa kan gado.
Bashir ya jima a tsugunne a wajan yana yarfe hannun shi kafin ya koma da baya ɗakin shi ya buɗe ya shiga ya faɗa saman gado yayi ruf da Ciki Kamannin yarinyar yana masa yawo Acikin idanun shi Wacece ita me ya kawo ta gidan su.
Tashi yayi zaune yana shafa ɗan Guntun gemun daya tara.
"Ina son ki kuma da aure, ko ke wacece zan aure ki dan na hango kala tace tabbas zatai Juriya ta haɗa dukkan abin da nake so dama bana son mace ta cika kyau bana son mace ta cika tsayi bana son mace ta cika ƙiba bare wannan tana jin maza kyau zatai ta ciko tai Ɓul ɓul kuma zatai daɗin harka"
Shi kaɗai yake maganganun kamar zararre.
Tashi yayi ya shiga wanka dan dole seya shiga wanka sabida ta haɗa masa hazo ƴar wannan rungumar data masa gaba ɗaya jikin shi ya miƙe kawai harka yake buƙata baku ma da kowa ba seda ita sedai ita yana jin a wannan karon ze tunkari ammi da maganar ya sami macen aure, amman baze gaggawa ba seya gama sanin wacece ita kuma yagama sakar mata kuɗi ya ruɗe ta dasu.
Har ya fito wankan tunanin ta yake ya tsane jikin sa da guntun towel ya sauya kaya ya shiga falon Ammi ko ina shuru ya isa bakin Ƙofar ammi ya tura ya shiga ciki ya same ta zaune a gefen gado.
Da tsananin ɓacin rai Aliyu yabar part ɗin Ammi be shiga part ɗin saba seda yayi sallar isha'i lokacin daya shiga falon shi ya tarar da komai ya sauya alamun matar gidan ta dawo beko kalli setin ɗakunan ta dake Falon ƙasa ba ya haura saman benen shi wanda anan ɗakunan shi suke kayan shi ya shiga tuɓe wa ya faɗa wanka ya fito ɗaure da ƙaton blue towel a ƙugunshi yana tsaye bakin madubi yana fesa turare mami ta turo ƙofar ta shigo fara ce siririya mai tsayi sanye take cikin wasu irin english wears masu tsadar gaske riga ce me hannun vest se guntun skirt ƙafafunta kamar na kaza Ɓingil Ɓingil acikin skirt ɗin wanda idan tai motsi kaɗan za'a iya hango pant Ɗinta ta cikin madubin yake hango fuskar ta wadda tazo bayan shi ta tsaya tare da kwantowa Jikin shi.
"I miss you my hero"
Ta faɗa cikin narkar da murya ta fara Goga fuskarta a cikin kafaɗar shi zameta yayi ya nufi wardrobe ya ciro Gajeran wando da single ya saka agabanta batare data matsa ta bashi wuri ba.
"Yaya baka ce min komai ba nafa dawo tun ɗazu"
Ta faɗa cikin shagwaɓa.
Ya zauna a bakin gado yana ɗaukar wayar shi da sadiƙ ke kira ya katse kiran yana cewa.
"Na ganki mamy sannu da dawowa kawo min black tea"
Ta fita soƙai soƙai ya bita da kallo ya taɓe baki minti kaɗan ta kawo masa tea ɗin ya karɓa yana kurɓa ta zauna a gefen shi tana wasa da sajen shi ya aje Cup Ɗin a bedside drawer ya janyo ta ya ɗorata saman cinyar shi yana buƙatar mace sosai duk da ta ɓata masa rai amman ta gane Kurenta dan wannan baƙin shayi seda Aliyu ya shanye mamy tamkar shi, se kuka mamy take bayan lafawar Komai ya miƙe ya shiga toilet Minti kaɗan ya fito ya tsaya yana sharce ruwan Jikin sa ya dube ta ya rasa yaushe zata saba koda yaushe raki shikuma baya ƙaunar wannan raki duk da dai tana matiƙar Ƙoƙari.
"Ki tashi mana kije ki wanka dan Allah bana son wannan kukan shekara goma Da aure amman dan ragwanci kullum se kin min kuka"
Turo baki tayi tana dira ƙafarta ya wuce ta ya shirya ya nemi Guri ya kwanta bayan ya zare zanin gadon.
Mami ta gaji dan kanta ta Miƙe ta fita zuwa ɗakin ta, ta fahimci baya son raki amman sunyi hira da wata ƙawarta tace wai namiji yana son langwai in ana Auratayya shine dalilin daya sa take wa Aliyu haka wanda shikuma baya son hakan ko kaɗan Itako mami rabi Kirsa ce ta saka rakin ba wani abuba.
Wanka ta shiga tana yi tana danna cinyoyinta domin Aliyu bezo mata da sauƙi ba bata koma ɗakin shiba magani ta sha ta kwanta anan ɗakin nata.
Bashir ya sami guri ya zauna a gaban Ammi yana kallon ta wadda ya fahimci kamar bata jin daɗi kuma ranta a ɓace yake.
"Ammi na dawo kuma na tarar da abubuwa marasa daɗi ko gaisawa bamu yi ba naje nai wanka na dawo dafatan na same ku lafiya?"
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 42*
Ammi da har lokacin bata sauko daga fushin dukan da Aliyu yayi wa su safna ba ta kalli Bashir da kulawa tana cewa.
"Lafiya ƙalau Bashir, yaya hanya?"
Ya gyara zama ya kuma matsawa gabanta sosai, "Lafiya lau Ammi wai me autras sukai wa Ya Ali ne haka wannan duka it's too much se kace ba ƴan uwan shiba in fa a ƙasar waje ne se anyi shari'a dashi"
Bashir ya sosa wa Ammi inda ke mata ƙaiƙayi nan fa ta soma magana cikin Ɓacin rai har tana fama ƙafarta.
"Wallahi Bashir na rasa wannan baƙar zuciya ta baba se Fushin tsiya fisabilillahi dan na wanke wa su Safna Banɗaki meye ze hau dukan su idan basu Huta yanzu ba yaushe ne zasu Huta to nagaji Gwara ayi ta taƙare na kira ɗan uwan shi na gaya masa sabida haka daga yau ai masa tsakani da ƴaƴana ah to"
Bashir dariya yake sosai cikin ƙara zugata yace mata "Aikuwa dai Ammi Nima na fahimci ya tsani ƴaƴan nan gaskiya ki taka masa Burki Haba mutum se baƙin hali da Ƙuncin Zuciya kamar ta mutanan farko"
Ammi ta Kuma gyara zamanta.
"Kai ma ka Faɗa to daga yau dai yayi auta baze sake dukar Min su ina ji ina kallo ba"
Bashir ya dubi Ammi kafin yace mata "Niko Ammi ɗazu naga wata yarinya a gidannan nace Ko wacece Oho ƴar baƙa haka Marar Jiki?"
Ya faɗa yana ɗage Girar shi Guda Nan da nan Ammi ta haɗe girar sama data ƙasa.
"Anno ba wai kake Nufi Hmm musa yaron Baba ne ya kawo Min ita wai ƴar ƙanin babansa ce Iyayen suka Mutu wallahi ƙaddara ce ta saka na ɗauki yarinyar nan gashi nan ta zame Min ƙajaga"
Da sauri Bashir ya katse mata maganar tata.
"Ammi sabida me Kika ce haka mayya ce ita? ko ɓarauniya? ko Munafuka? But nasan waɗannan Sunfi komai illah ga al'umma tell me wanne ne halin nata acikin su?"
Ammi ta haɗe Fuska kamar Farha na gabanta "Wannan ai duka ta haɗa kaga mayya ce ita ta lashe Kurwar Baba ni bantaɓa ganin mai aikin da yake Kula da ita ba se wannan yarinyar sannan ɓarauniya ce Ni ban yarda da itaba Sannan Munafuka ce Uban wa yasan abin da ta gaya masa yazo ya Huce akan ƴaƴana Allah masani ni wallahi A yau naga Musa ma seta bar Mini Gidana dan ba zan iya riƙon taba ban san me gaba zata haifar ba"
Ajiyar zuciya Bashir ya saki Tabbas tarkon sa zai kama kurciya ashe ma bata da gata ashema ƴar ƙauye ce lallai zeci karan shi babu babbaka zeje ya nemi soyayyarta koda tsiya koda tsiya tsiya yasan se ya nace har Ammi ta aura masa ita.
"Ammi kada ki saka damuwa acikin zuciyarki Ya Ali fa kin san shi da zuciyar sadaukai wallahi tausayin ta kawai yake, Kuma kinga ƙanwar Musa ce kuma shi Kinsan baya wasa da dukkan wani abu daya shafi Musa wannan shine kaɗai dalilin daya sa kika ga ya damu da ita, Sannan Ammi ki kwantar da hankalin ki Nida kaina zan koreta daga gidannan kada ma ki kulata yazo yana faɗa Kinji Ammina"
Sarai Ammi tasan waye Bashir da tijara seta ji ta yarda da abin da ya faɗa mata ware wa tayi suna ɗan taɓa Hira kafin yabar Ɗakin seda ya Leƙa Ƙofar ɗakin daya ga ta shiga yaja ta yaji akwai key yayi ajiyar zuciya yabar wajan yaso tana buɗe Ƙofar daya shiga ko Leɓanta yaɗan tsotsa yaji daɗi.
Da Asuba farha ta Miƙe ta shiga banɗaki tayo alwala tayi sallah tana nan zaune rana ta fito tayi azkar Fita tayi falon babu kowa shara tahau yi kamar yadda Ammi ta sakata tayi Ta gyara ko ina har Moping ita tayi sannan ta shiga Kitchen ta soma fere doya lokacin wajan ƙarfe takwas da rabi Doya da ƙwai tayi da miyar source seta yi musu Kunun gyaɗa da farfesun Kifi ta kammala ta gyara Kitchen Ɗin ta shiga kai kayan abincin dining ta kai na ƙarshe Bashir ya shigo falon cak ta tsaya da jera abincin ta raɓe ta ɗauke Numfashi tana jiran ya wuce sedai ya tsaya akanta yana sakar Mata Murmushi.
"Amincin Allah ya tabbata a gareki"
Gabanta ne ya faɗi Irin sallamar da ɗan uwan sa yayi mata kenan ranar farkon haɗuwar su.
"Haba baby me yasa zaki min rowar Maganarki Bayan nasan ba kurma bace?"
Ƙoƙarin Juya wa take ta koma Kitchen yayi saurin kamo gefen Hijabin Jikinta gabanta ya faɗi da sauri ta juyo idanunta sukai raurau kamar zata yi kuka.
"Please kada ki kashe ni da kallon ki kigaya min kalma ɗaya tak wadda zata sakani Nutsuwa baby tun jiya na kasa samun bacci akanki nai mafarkin ki kina bani daɗin ki Baby Plsss kimin magana"
Ya ƙarashe maganar yana shan yaji irin na ƴan iskan maza.
Ba abin da farha take nanata wa a zuciyarta se ambaton sunan Allah lallai inda ranka zaka sha kallo lallai Gidan nan akwai Mutane kala kala shi kuma da wannan salon Iskancin Yazo Allah ka kawo min ɗauki ta faɗa a zuciyarta.
"Wallahi in zamu kwana anan in baki mani magana ba bazan saki Hijabin kiba fisabilillah kashe marayan Allah zaki yi ni kawai Muryarki nake son naji" ya faɗa yana langwaɓar da kanshi kamar ze Kuka Irin sune karuwan maza.
"Ni ka sake ni aiki nake yi" daga haka taja hijabin tayi Kitchen ba abin da zatai amman zamanta aciki yafi mata rahma Har rufo ƙofar tayi tunanin ta ze Biyota Cikin haka Hajjo ta shigo Kitchen Ɗin farha ta saki Fuska.
Sosai tare da cewa "Hajjo ina kwana?" Hajjo ta dubi Farha da kulawa "Hmm ƴata jiya Rigimar Gadanga ta hana na tambayeki Yaya jikin naki" farha tayi dariya "Lah hajjo dama kina ciki yake wannan dukan Nima abin yafa bani mamaki da tsoro" hajjo tace "Ina kitchen ina girki dan Hajiya Ammi ta hanani shiga Hurumin ƴaƴanta ne ajiya data min gargaɗi shiyasa nayi Shuru ai shine maganin su yara ba tarbiya ba mutunci basa ganin Girman kowa" Hajjo ta faɗa tana Ƙoƙarin Ɗora ruwan zafi a saman Gas "Hmm Wallahi Hajjo haka ne ni bamma taɓa ganin yara Irin suba amman da alama akwai saka hannun babarsu wajan ɓata su wayyo Inama ƴaƴan Gidanmu ne da sunci wuya wajan kawu" Da sauri kuma ta rufe bakinta ta manta zatai suɓutar baki "Me kike cewa ƴata?" Hajjo ta buƙaci taji abin da farha tace "A,a cewa nayi nafa gama musu abincin karin Kin san ta ce Ni zan dingayi" Hajjo tace "To da kin bari ai nazo Munyi tare amman shikenan Rigimar hajiya Ammi ce tayi yawa amman aikin yayi miki yawa tun jiya ta sanar Min nazo ne dai danna taimaka Miki" Farha tai Murmushi "A,a Ki barshi ai ba yawa ga namu ma na ɗiba mana semu ci abinmu" zama sukai a ƙasan Tiles Suka zuba doyar da Miyar da Kunun Kwano ɗaya suka ci ita da Hajjo Kuma ta saki ranta taci sosai Suna gamawa Hajjo ta mata sallama ta fita Ita kuma wanke wanken kwanu kan data ɓata ta haɗa tana yi Taji ƙarfin Jikinta sosai yau sabida gashi nan ma harta ci abinci Jifa jifa dai take Leƙe Ko wannan matashin ze Biyota ganin Be Biyotan ba yasa ta mayar da hankali wajan wanke wankenta.*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 43*
Ya ware Lumsassun idanunshi akan Ƙaton agogon dake manne a jikin Bangon ɗakin shi.
"Subuhanallahi I'm late today"
Ya faɗa a sanyaye tare da miƙar da dogayen ƙafafun shi wanda har sun dira a ƙasan gadon daya kwanta Wayar shi ya janyo yaga tarin Misscall da aka kira shi Tunda yayi sallar asubah ya kwanta bacci Bai tashi ba se yanzu wanda agogon daya kalla ya Nuna masa har 10:30am, Layin Sadik ya shiga kira wanda daga ɓangaran Sadik yana zaune a dining Sakina na serving ɗinshi break fast yaga kiran Aliyu.
"Gadanga ƙusar yaƙi zaki na Maryama shine dan rashin mutunci jiya kana ganin kirana kake katsewa ko?"
Sadik ya faɗa cikin barkwanci.
Aliyu ya saki tsadaddan Murmushin sa.
"Haba Babban yaya nina isa kawai Lokacin bani da sukunin ɗaga wayar Ne yaya su Minal da Sakina ina fatan suna lafiya"
Sadik yayi dariya.
"Gata tana Jinka tace tana Miƙo gaisuwa dama Ƙarar ka aka kawo Min fa"
Aliyu ya zaro ido wanda hakan na ƙara fito masa da kyan shi idan yayi.
"Ƙara ta kuma waye?"
Sadiƙ yayi dariya.
"Hajiya Ammi tace a zauna a Kotun Ƙoli babu kai babu autras Ɗinta Inba haka ba Duk abin da tai maka kai ka siya"
Aliyu yayi wata dariyar Rainin hankali.
"Kai kasan me sukai dan iskanci Ammi ke wankewa yaran nan Toilet har faɗuwa tayi tsakani da Allah ya dace?"
Sadik yaɗan Yi Jim kafin yace masa.
"Bai dace ba da se ta saka ƴan aiki ai tunda akwai su, Amman No need ita da kanta tana wanke masu Bayi wani ma seya zage mu"
Aliyu ya ɗage Gira guda yace "To wannan ne silar Dukan amman ita ammi sam taƙi ganin Illar sakar masu Ɗin da take kuma ni ba ruwana ko yanzu naga Sun ƙara laifi zan dake su fa"
Sadiƙ yayi dariya.
"Kaifa matsala ta dakai Mugunta Dan