Showing 36001 words to 39000 words out of 150033 words
Chapter 13 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
ka"
Sale ya dubi ɗan uwan mahaifin nashi tare da cewa.
"Allah yasa ba wani laifi tayi muku ba kawu"
Kawun nashi yace.
"Ko ɗaya mu dai mun gaji da ganin ta haka kada kaga ba ran mahaifan ka muma masu tsaya maka ne saboda haka na baka Ƴata Saude kazo ku daidaita mu irin haihuwa ne dan ba zan so yadda iyayen ka suka haife ka kai kaɗai ya zamana cewa Ka mutu baka da magaji ba"
Sale yayi ƙasa da kanshi yana tunanin haƙuri da nagarta irin na salma idan yayi mata kishiya akan rashin haihuwa bai mata adalci ba.
"Kawu nagode, amman kai hakuri bani da matsala da matata Ni gaskiya ba zan mata kishiya haka kawai babu wani dalili ba"
Kawun sale ya harzuƙa ya fara cin Mutunci.
"To dole ka amshi saude ko kaƙi koka so dan kaga bani na haifeka ba to bari kaji cikinmu ɗaya da mahaifin ka ko kaƙi koka so ba'a canzawa tuwo suna sabida haka kazo gida kaga saude ku sasanta a saka ranar ɗaurin aure in kuma ban isa dakai bane ba to"
Saleh yayi ƙasa da kanshi sai faman Haƙuri yake bawa kawun nashi sannan yayi masa alƙawarin zai zo yaga saude.
Kawun sale yayi tafiyar shi batare daya tsaya amsa haƙurin da salen yake bashi ba.
Koda ya koma gida ya rasa ta yadda zai gayawa salamatu maganar da sukai da kawun shi sabida kunyar ma gaya mata maganar yake yi.
Ta lura sam bai da sukuni har dare ganin haka yasa ta saka shi a gaba da tuhumar meke damun shi? da ƙyar ya aro jarumta ya dube ta.
"Salamatu kin san ina son ki, Kuma ina ƙaunar ki"
Tayi murmushi tace masa.
"Nima in ka cire Allah da ma'aiki da iyayena da suka rasu to sai kai sai kuma ƙanwata Amina da muke shirin auren ta"
Yayi dariya sannan yace.
"To kawu ne ɗazu yazo min da batun cewar zai bani ƴar shi saudatu na aura"
Bai ƙarasa ba ta katse shi cikin murna tace.
"Dama gidannan yayi min girma tsoro nake ji in baka nan Allah ya tabbatar da alkairi kaga na sami ƙanwa"
Duk ta yadda Yaso kushe abin taƙi sai ma ƙarfin gwiwa da take bashi haka ta shige masa gaba akan auren shi da saudat har yaje ya gano saude aka tsaida maganar aure ba da jimawa ba.
Sai dai me Tunda aka saka maganar auren ma salamatu ta soma laulayi wanda ya hanata lafiya gaba ɗaya Sale ya mayar da hankali akan kula da lafiyar matarshi a daddafe ya auri saude wadda tazo gidan da tashin hankali dan saude akwai zafin kishi da zargi haka dai zaman nasu ya cigaba salamatu rabi haƙuri take da saude sabida saude akwai saka ido zargi ga zafin kishi abu kaɗan sai ta kai sale ƙara ƴan uwansa suzo su zage salamatu ba zata tanka musu ba haka Taita cigaba da zaman gidan cikin haƙuri Har Allah yasa ta soma naƙuda wanda sale Baya nan ranar Tana ɗaki tana ta fama Duk ta fita daga hayyacin ta saude tana tsakar gidan ta ware Rediyo tana wanki ko kallon salamatu batayi ba kwatsam Allah ya jefo Amina ƙanwar salamatu ce wadda akai wa aure a kwanakin Cikin su ɗaya kuma su kaɗai ne mata a wajan iyayen su sai yayan su Namiji guda ɗaya da yake zaune anan gidan Da mahaifan nasu suka rasu suka bari.
Ganin halin da salamatu take ciki hankalin Amina ya tashi ta ruga gida ta kira matar yayan su aka saka salamatu a mota suka tafi asibiti Amman saude ko kallo basu isheta ba Koda suka je asibitin matar yayan su ta saka yaron ta yaron yace kasuwa ya kira sale sai dai kafin sale yazo har salamatu ta haifo ɗanta ƙato wanda ko kallon shi batai ba Allah ya amshi ranta iya tashin hankali wannan zuri'a sun shiga sale kuwa kamar zararre haka ya koma yaja yaro ya rungume yaƙi bawa kowa.
Sai da abokai suke ta masa nasiha sannan ya bada yaron Amina da matar yayan salma sunce zasu riƙe shi amman Sale ya ƙi har da kukan shi sai mahaifin Saude yace a bawa saude ta Dinga bashi madara sai uban sa ya dinga ganin sa a kusa dashi haka akai bakwai aka watse aka bar saude da jariri wanda Amina tai kuka tai kuka akan aka bata yaron aka ƙi.
Sale kewa Abdullahi wanda suke cewa Audu a wannan lokaci, Shike masa wanka kafin ya fita kasuwa ya bashi madara yasha ya wanke masa kayan shi tas Ba tare daya tsaya bin kan saude ba wadda take jin kamar ta jefa audu a wuta Sosai mahaifin shi ke lura da shi ga audu yaro ne mai hakuri da wiya kaji kukan shi haka yayi ta girma ta silar Kula da mahaifin shi yake bashi A haka har yaro yakai shekara biyu Amina na zuwa ganin shi sosai Dan koda yaushe tana hanya ga uban sa na son shi sai dai fa da zarar Sale baya nan Saude zata saka shi a ɗaki ta kulle ya wuni da yunwa amman in uban ya dawo sai dai audu yayta hawaye dan babu bakin magana
A haka ya taso Yakai shekara Biyar saude ta haifi ɗanta itama mai suna Usman.
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*
*26*
*A LOVE STORY 26*
Bayan usman ta haifi Ashiru daga shi ta haifi sa'adu daga shi sai Rabi'u sai salisu sai suwaiba Lokacin Audu ya zama ɗan matashi zai kai shekara Goma sha biyar wahalar Gidan gaba ɗaya ta koma kanshi komai na su Usman shi yake hatta tsarki kashin su Saude taƙi bashi abinci sai taga uban ya kusan dawowa kuma dan haƙuri irin nasa baze taɓa gayawa mahaifin shi ga abin da take masa ba sai dai yayi ta kuka shi kaɗai tuni an saka su a makaranta shida usman ƙwazo ne da audu sai dai Yadda Usman yake masa mugunta a littafinsa da zarar an sai masa haka ze yaga in Uban ya dawo yay ta masa faɗa yana kammala Firame mahaifin shi ya kaishi kasuwa ya nuna masa harkar fata Ganin haka yasa Saude tace sai an kai usman shima amman uban yace ba yanzu ba sai ya kuma wayo.
Zuwan shi kasuwa ne yasa shi yake ɗan jin sauƙin azabar saude da ƴaƴanta waɗanda suka ɗauke halin ta tsaf ga sharri haka Usman zai hau katifar audu ya maka fitsarin kwance da safe saude ta naɗawa Audu duka.
Watarana mahaifin yayi tafiya sai yace audu kada ya fita kasuwa dan bai san hanya ba dama kuma abin da yasa yake tafiya dashi kasuwar ma dan ya fahimci yana cin wahalar zaman gidan ne.
Usman da Ashiru sun maka fitsari Saude ta fito da kayan fitsarin ta saka audu a gaba tana duka yana wankin cikin haka Amina ta faɗo gidan da tsohon cikin ta yadda taga ana azabtar da ɗan yayarta har kuka tayi bata tafi ba sai da Audu har da kayan shi ta haɗa bayan sun gama zage zage da saude.
Amina ta saka audu a gaba har gidan ta dake Fagge tana auran miji mai kuɗi tana zaune lafiya da kishiyarta wadda take goyon ƴa mace itama Mijin Amina yayi murnar ganin Audu kuma yayi takaicin Yadda Amina ta bashi labarin wahalar da audu yake sha .
Bayan Sale ya dawo saude ta tare shi da ƙarya da gaskiya haka yazo har gidan Amina yace ta bashi audu fafur ta hana shi abin har yakai su da ba daɗi haka ya tafi yay fushi yace ya bar mata shi ta cinye.
Mijin Amina da ita kanta Aminar sun ɗauki son duniya sun ɗorawa Audu wanda ya murje yayi kyau kuma ya koma makaranta anan faggen Mijin Amina na masifar son Amina wanda soyayyar da yake mata ne yasa ma har take samun saɓani da Kishiyarta wadda take Goyon ƴa mace mai suna tajira.
Haka Amina ta haifi ƴarta mace mai kyau kamar ta fara jajir sabida soyayyar da Mijin ta yake mata ne ya sanyawa ƴar sunan ta itama yarinya taci suna Amina Audu ke renon Amina komai ya samu ita wata irin shaƙuwa ce a tsakanin Audu da Amina wadda komai na yarinyar shike mata Wanda hakan ya ƙara jefa tsana mai ƙarfi a tsakanin Kishiyar Amina da ƴarta wadda taɗan tasa Suka tsani Audu suka tsani Amina da ƴarta Tuni Audu ya mance da rayuwar Gidan su Har ya kammala secondry Ɗinsa Lokacin Amina ita kuma tana Primary ta ɗan tasa ta zama budurwa Bayan kammala karatun Amina na firamare sai tafiya ta kama Babanta da Mahaifiyarta sai suka zauna a wajan Babar tajira ita da audu a hanyar su ta dawowa ne sukai hatsarin mota wanda Amina ƙanwar mahaifiyar audu tare da mijinta waɗanda sune mahaifan Amina Allah yayi musu rasuwa ta sanadin wannan hatsari.
Tashin hankali audu da amina sun shiga ana sadakar bawai yayan salamatu ya ɗauki amina sabida yace baze bawa babar tajira riƙon amina ba sabida itama tana fama da kanta wannan ne sanadin da Riƙon Amina ya dawo wajan Yayan mahaifiyarta shi kuma audu sai ya koma gidansu wanda ya tarar ƙannen shi dik sun girma ba yadda sale yayi haka ya komar da Audu kasuwa wannan tasa wutar ƙiyayya ta ruru a tsakanin saude da ƴaƴanta wadda suke jin kamar su jefa audu a wuta.
Yana fuskantar cin mutunci wajan ta da ƴaƴanta gefe Guda soyayya mai ƙarfi ce ta ƙullu a tsakanin audu da Amina wanda mahaifin audu ya fahimci haka bai ƙasa a gwiwa ba wajan tunkarar yayan su salamatu da batun yana son Audu ya auri Amina ba'ai wani ja yayyaba aka aurawa audu amina sashe guda sale ya ginawa Audu acikin gidan wanda Amina ta tare aciki.
Bata da wata matsala daga farko sabida audu yana samun Kuɗi fatar ta karɓe shi dan a lokacin batai shekara da auran shiba ya biya musu hajji ita da shi da babansa da yayan mahaifiyar su lokacin saude kamar tayi hauka dan baƙin ciki ita da ƴaƴanta basu jima da dawowa ba Allah ya ɗauki rayuwar Sale mutuwar data girgiza wannan ahali musamman audu.
Haka akai zaman makoki aka watse audu ya koma kasuwa sai dai abu kamar wasa kasuwa ta koma masa baya komai ya taɓa narkewa yake hatta jarin sa saida ya rasa Kawun su yayan mahaifiyar su da ƴaƴansa suke taimakon audu da kayan abinci.
Ga lokacin Amina ta sami ciki ya tsufa komai yazo kuma ya tsaya
Ga cin mutuncin saude da ƴaƴanta a kullum cewa suke sai audu ya tashi anyi rabon gado watarana Amina ta tashi da naƙuda ba yadda audu bai da Saude ba akan tazo sukai Amina asibiti sabida cikin dare ne amman taƙi daga ƙarshe ya fita ya kira matar kawun su suka tafi asibiti Amina ta haifi ɗanta namiji fari mai kyau dashi ƙato suka dawo gida da safe.
Tashin hankalin da suka tarar yafi gaban kwatance dan su Usman da suke samari a lokacin sun watsowa Amina kayanta sun rushe ɓangaran Wai ai rabon gado basu yarda da zaman Audu agidan ba Amina na kuka Kawun su ya bata ɗaki guda agidansa anan suka cigaba da rainon ɗansu Abubakar Sadiƙ.
Sunan yayan mahaifiyar su Audu ya saka.
Rayuwar yau da gobe tai musu zafi Audu yana ji yana gani su Usman suka rabe gidan mahaifinsu kowa yaja sashin sa suka gine Sauran gado gona filaye duk basu bashi ba haka ya cigaba da zama agidan kawu Abubakar yayan mahaifiyar shi da taimakon ƴaƴan kawun shi waɗanda suke yayye garesu shida Amina suka gina masa ƙaramin gida anan ƙofar na'isa ya koma lokacin ne Amina wadda sadiƙ ke cewa ( Ammi ) ta haifi ɗanta Aliyu wanda tsiran su da sadik shekara biyu ranar data koma sabon gidan ta haifi Aliyu wanda aka sanya sunan mahaifin ta Marigayi Alhaji Ali Fagge babanta ita da Tajira.
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*
*27*
*A LOVE STORY 27*
Aliyu yafi sadiƙ kyau nesa ba kusa ba kuma yafi sadiƙ Girma tunda Audu ( baba ) da Ammi suka ɗora ido akan Aliyu suka ɗauki soyayyar duniya suka ɗorawa Aliyu wanda haihuwar shi tazo wa Baba da nasibi domin ya koma kasuwa Lokacin Aliyu na da wata ɗaya a duniya arziƙin Baba ya ninka nada tuni ya rushe gidan shi ya sake ginin zamani ya gyarawa yayan mahaifiyarsu gidan shi Lokacin Ammi Ta ƙara kyau hankalinta ya kwanta ta cigaba da rainon ƴaƴanta da suka taso kamar ƴan biyu ga kyau ga farin jini dan duk inda suka shiga ana son yaran.
Duk da yadda su Usman sukai wa Audu ( baba ) hakan bai saka yaƙi suba haka yaja su ajiki koda zasu yi aure shi yayi komai wanda mahaifi kewa ƴaƴa hatta kayan ɗakin suwaiba shine yayi mata yana kyautata musu sosai tuni an saka su Aliyu a makaranta mai tsada Yanayin ƙoƙarin Aliyu ne ya sanya aka haɗe su Aji ɗaya da sadiƙ wanda suka shaƙu sosai sai dai akwai bambancin hali.
Aliyu tun yana yaro miskili ne mai taurin kai marar far'a da son mutane baya da yawan magana sosai Kullum yana jikin mahaifin shi sai dai yadda Baba ke yawan zuwa da Aliyu cikin Gida wajan su Usman yasa Aliyu yake son dangin mahaifin nashi duk da irin abin da sukai wa mahaifin nasu wanda Ammi ta ƙullata aranta amman ikon Allah duk abin Aliyu bai taɓa riƙon su ba wani bin har zuwa cikin gidan yake ya kwana abin Allah saude tana mugun son Aliyu sabida lokacin ta tsufa tuni ta nemi yafiyar audu akan abin da tai masa suma su Usman sun nemi yafiyar shi kuma ya tabbatar daya yafe musu matsalar kawai Ammi ce da ko magana bata shiga tsakaninta dasu usman Sabida tace ita dasu har abada akan abin da sukai wa mijinta.
Komai da su Usman suka mallaka wanda suka dannewa audu yau da gobe ya ƙare tas gidajen sun ma duk sun lalace ajikin Audu suke raɓe a kasuwa shi kuma baya musu Mugunta dan ya tabbata da dama sharri ɗan aike ne Kuma tunda sun tuba sun gane Laifin su shikam ya yafe musu har ranshi dan baka fushi da naka. Allah yayi wa saude rasuwa tsiranta da kawun audu ba nisa haka dama rayuwa take.
Sai da Aliyu ya shekara biyar ammi ta haifi salma mai sunan babar Audu daga salma sai bashir daga shi sai Safna daga ita sai sajeeda.
Lokacin raino yayi wa Ammi yawa sai aka ɗauko mata mai aiki Hajjo wadda suke zaman lafiya hajjo na taya ammi rainon su safna su Aliyu na Secondry Lokacin Jss 1 bashir da salma kuma na primary dan duka lokacin Sadik na shekara sha biyar Aliyu sha huɗu salma tara bashir bakwai Safna huɗu sajeeda ɗaya adaidai wannan Lokacin Allah ya ɗauki ran Audu ya rasu yabar Ammi da waɗannan ƙananun yara bida da bi ya rasu yabar tarin ƴan uwa da masoya mutuwar data tarwatsa farin cikin Ammi bata da uwa bata da uba bata da Miji yayan mahaifiyarta mai jin ƙanta shima babu sai ta rungumi ƴaƴanta sune komai nata tasaka su agaba tana hira tana dariya tana kuka Hajjo ce mai bawa ammi baki tana rarrashin ta Yau da gobe kayan Allah komai yazo ya ƙare domin zara bata barin dami Ammi ta cinye komai da audu ya rage sai gidansu da suke cikin sa.
Suma su Usman lokacin nauyin ƴaƴa yayi musu yawa ƙananun ƴaƴa garesu dan aure auren tsiya gare su gashi babu Suma basu samu ba bare su taimaki Ammi.
Makarantar su Aliyu suka koro su sabida basa biyan kuɗin term dan makarantar Kuɗi ce Lokacin Ammi tai kuka tai kuka kamar ranta zai fita domin abin da zata ci ma ya gagare ta cikin haka ta fara sana'ar sayar da abinci da goyon Sajeeda Hajjo na riƙe da Safna haka zata fita kasuwa ta siyo kayan girki agidanta take sayar da abincin da wannan ribar suke ci suke sha har ta biya musu Kuɗin makaranta ita dai Burinta ƴaƴanta su rayu cikin farin ciki.
Sannu sannu jarin ma yazo ya ƙare tas Lokacin su Aliyu na Jss 3 Ammi dole tasa tace wa hajjo ta koma gida ta nemi sana'a dan itama ta kanta take yi amman hajjo taƙi tace ita kam ba zata rabu da Ammi ba haka suke zaune Cikin girmama juna dan hajjo nawa Ammi biyayya kamar lokacin da suna da shi bata taɓa sauya wa ba.
Ganin halin da suke ciki yasa Aliyu Kullum in sun tafi makaranta baya zuwa sai yayi tafiyar shi kasuwa dako yake duka lokacin ba wani girma yayi ba zai samo ɗari ɗari biyu sai ya sami banki ya Ɓoye Haka yay tayi lokacin jarrabawa yazo Malamin su yazo har gida ya shaidawa Ammi Aliyu baya zuwa makaranta.
Hankalin Ammi ya tashi Aliyu yana dawowa ta rufe shi a ɗaki tana tuhumar sa tana kuka sabida tana tsoron kada yabi abokan banza dan yafi sadiƙ wayo, Buɗar bakin Aliyu sai yace mata dako yake zuwa kasuwa yayi har ya fito mata da tarin da yake yace zai biyawa salma da Bashir ne Kuɗin makaranta kuɗin Sun kama dubu Uku ammi tai kukan tausayin yaron Haka ta mayar dashi makaranta sai ta sami aikin sharar titi ta dalilin yayanta ɗan wajan kawun ta da sassafe take fita tayo sharar ta ta dawo a wata ana biyanta dubu sha biyar bata cin ko kwabo a wannan Kuɗi haka take biyawa su Aliyu kuɗin makaranta da sauran Hidimar rayuwa.
Ganin wahalar da ammi take yasa Aliyu da safen kafin ya fita sai yaje yayi mata sharar tun tana hana shi harta barshi da wannan Ƴan kuɗin da kuma wanda ƴan uwanta ƴaƴan kawunta suka haɗa mata taja jarin Sayar da manja da man ƙuli a daddafe su Aliyu sukai candy daga nan yace bai san zancen komawa makaranta ba.
Ammin sa na cikin wahala gwara ya tashi ya nemi na kan shi haka Aliyu yake fita kasuwar Ƙofar Ruwa