Showing 108001 words to 111000 words out of 150033 words

Chapter 37 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

Ammi take yi miki Ammi mahaifiyata ce in kika tayani muka haɗu muka mata biyayya inna gama da ita lafiya kema ribarki ce, Ki barni dan Allah akwai tarin ƙalubale da matsaloli a gabana so nake na ture su tukunna sena sami Nutsuwa" A hasale tace masa "Matsalar ai ba zata wuce Ɓoyayyan Auren da kayi dani ba dan ɗaukar fansa to tunda Dama ba sona kake yiba base ka sake ni ba ai babu wata matsala ni a ganina tunda dai ba ɗaure ni akai a ƙafarka ba Ka zauna da zaɓin mahaifiyarka wadda take so take ƙauna dan Allah nima abarni nai rayuwar ƴanci kamar ko wace mace" ta faɗa a tunzure Aliyu ya ji hankalin shi ya tashi da irin maganganun da take jefa masa Muryarshi har rawa take kamar ba Aliyu mai saurin fushi da tunzura da rashin ɗaukar raini ba yace mata "Shikenan fatima duk yadda kika ce haka za'ayi tinda kince na sake ki Allah ya sani Bazan cutar dake ba wataƙil zaman da nake dake akwai cutarwa acikin sa tunda har kike furta kalmar Mu rabu da juna zan baki abin da kike so koda ni zan rasa nawa farin cikin Ki jira zuwana se muyi maganar a nutse" ya faɗa a hankali wanda yasa hantar cikin farha kaɗawa cikinta ya juya inya sake ta ina zata saka kanta Muryarta cikin rawa tace "Nifa baka gane nufi na bane" Ta faɗa a hankali sabida yadda jikinta gaba ɗaya yayi sanyi dajin abin da yace mata.
Cikin sanyi jiki shima yace mata
"I understand your intention fatima duk na gano inda kika dosa kuma duk abin da kike so zan miki koda nine zan cutu Tunda ni bani da ƙima da alfarmar Ki tayani Yiwa mahaifiyata biyayya tunda saki kike so shikenan baki da matsala dashi Amman ki bari na dawo"
Jikinta ya hau tsananin rawa nan da nan tahau kuka.
"Ni yau she nace maka ka sake ni kawai zaka lauya mini magana ta" Duk yadda ta ɓata mai rai seda yaɗan yi dariya ya fuskanci barazana take masa akan ya saketa amman hakan bai kai mata har zuciyarta ba"Kece kika faɗi ɗazu Ki koma ki tariyo me kika gaya min aini kin riga kinga wurin kwanciyata kin raina ni Kince ba zaki koma wajan Ammi ita ma salma da kika ganta ai agidan Mijinta take se kece sakarai zaki ƙi bin naki Mijin nikam in ba zaki koma gidan Ammi a wannan karon za muyi faɗa dake" Kuka ta saka a hankali wanda yake fitar da sautin sa shima hankali "Dama ni ce a ƙasa dole Kome kace sedai kawai nabi dama umma ta gaya min na dinga maka biyayya" ta faɗa tana kuka shima yace "Good Amman umma ta kyauta mini to shikenan zamu gani Zaki bi maganar Umma ko zaki watsar Kuma ai ba Umma ce ta fara faɗi ba Allah ne yace mata tabi Mijinta sau da ƙafa sabida haka Ki zaman shirin Komawa gidan Ammi kema kin kusan shiga naki gidan Ki haƙuri Dai mu lallaɓa duk wanda yayi haƙuri baya faɗuwa nidai nasan ina tare dakeI will never turn my back on you, I will never run away from you unless you want to run away from me,ki saka wannan aran ki fatiman Aliyu" ya faɗa mata hakan Lokacin Jikinta ya ƙara sanyi muryarta na rawa tace "Duk kasan ka gayan waɗannan kalamin amman ka kasa furta kana sona bayan kai ma ka riga da ka kamu da soyayyata kaine kawai baka san na gano kaba" ya saki tattausan murmushi "Fatima faɗin soyayya ga masoyi ƙauyanci ne sedai idan ana so a gani acikin aiki Ki kula min da kanki sosai sannan Kita cin ayaba sabida wannan Tsutsar ta Mutu" murmushi tayi mai sauti "Yawwa to yi dariya naji se muyi sallama babu wani abin da zaki bani wanda ze kwantar Min da hankalina?" ya faɗi maganar a hankali dariyar ta saki kamar yadda yace sannan tace "Hmm kai da kana tare da Aunty Mami To ai baka da matsalar kome" ya langwaɓar da kai kamar tana ganin shi "Mami fa bata nan tana wajan su Ammi Yanzu dai Kimin koɗan Kiss ne se muyi sallama" Ɓoye fuska tayi tana jin kunyar abin da yace mata "Uhmmm ina jira zan sauka ƙasa na ƙara karɓo tea wannan yayi sanyi baze shawu ba" Tace masa "Kai kullum seka sha shayi niko abin da baita ɓa burgeni ba kenan" yayi murmushi "Mu haka muka taso tun Baba yana da rai kuma ni gaskiya yana ƙara min ƙarfi Da kuzari ajikina In ban sha tea ba har Ciwon kai nake kuma bana son asa mai komai se ƙayan ƙamshi da sugar" Ta jinjina kai "Yanzu dai Ayi min Kiss" ya faɗa yana wani ƙasa da Murya "Nifa ban iya ba" ta faɗa yayi Murmushi "Haka ma zaki cemin Kinfi son na fita Compound na hotel ɗinnan nai ta kallon ƴammatan larabawa Ko?" da sauri tace "A,a zanyi maka" Ya lumshe idon shi "Uhmm tom kiyi yanzu wani kayane ajikin ki kinsa sleeping dress?" ya faɗa da wata kalar Murya "Ai bani dasu duk nawa suna gida" Ta faɗa itama a hankali "Zan siyo Miki sannan zan siyo kayan jarirai na mami ne amman ke zan bawa ajiya sabida inna Nuna mata zata ɗagawa kanta hankalin Rashin samun ciki" ya faɗa tare da kuma cewa "Se kuma me zan siyo Miki Bamma ki lefe ba amman inna dawo zamu je asiyo su Ki zaɓa duk kalar da kike so a saya" tai Jimm tare da cewa"Dabino wannan Curarren na makka shi zaka siyo Mini Allah yasa in ka siyo kayan jariran ma Kuna dawowa ta sami Wani cikin Kuma Allah yasa wannan karon ya tsaya ta haihu" ta faɗa cikin Rashin damuwa da Mami kishiyar tace waɗannan halaiyar nata yana Burgeshi bata zafafawa akan Mami sabida tasan matar shice Kuma ita taje ta samu agidan saɓanin wasu amaren da suke jin kamar su jefa iyayen gidansu a wuta dan tsananin ƙiyayya amman banda farha ita inda zega Kishinta seya yi zance wata a waje amman indai mami ce tana ƙoƙarin yin kawaici.
"Ke bakki son ki haihu?" tai dariya "In Aunty mami ta haihu kamar ni na haihu ne ai" yayi Murmushi "Ke baki son naki?" tai shuru can Kuma tace "kasan me wallahi ni ban fiye jin zafi ko kishin Aunty mami ba sabida Ai Ita ka fara aura kafin ni" da sauri yace "Kina nufin bakya kishina" tai fari da idonta "Ina yi amman na hankali" ta faɗa tana dariya sannan ta ƙara cewa "Yawwa da dabino ɗin zaka zo min sannan In zaka sai Min kayan baccin wallahi kasai manya dan nayi ƙiba sosai yanzu" Ya lumshe ido yana jin daɗin yadda yanzu ta sake tana hirarta cikin walwala "To shikenan Gimbiya Bara naje ƙasa na sha tea ɗin kiyi bacci lafiya" Fatan alkairi sukawa Junansu Farha ta kwanta ba jimawa bacci yayi gaba da ita shiko sauka yayi yaje ya amso tea ya dawo duk yaji baya da damuwa ya tabbata tana masa Musulmin so wanda yake jin Zata iya zama dashi a ko wani hali Jiyay ta ƙara shiga zuciyar shi Yana kammala shan tea ɗin yaja Pillow yayi kwanciyar shi.


Cikin shigar baƙar jallabiya take se ƙaton Glass data rufe fuska dashi ta shiga cikin wani super market zatai siyayya su Koma masaukin su dan su Sajeeda suna mota suna jiranta Da sauri taga wani turare mai kyau ta ƙarasa zata ɗauka seya faɗo shima adaidai Lokacin ya Sunkuya danya ɗauko mata turaren cikin rashin sa'a hannunsu ya haɗe dana junan su Ta ɗago ido ta kalle shi shima nasa idanun ya zuba mata yana kallonta kafin ya saki murmushi.
"Aminci da kusancin Allah su tabbata a gareki ya fara ma'abociyar ƙamshi"
Safna taji wata irin Faɗuwar gaba ta ziyarceta tinda take a rayuwa bata taɓa yin saurayi ba ko fita sukai ba'a cewa ana son su yauce rana ta farko da ɗa namiji ya furta mata magana wadda tai kama data soyayya ta saki fuska tare da cewa "Tare dakai" ya ɗauki turaren ya miƙa mata yana cewa "Naga kamar Siyayya kika zoyi muje nai Miki rakiya ki zagaya" tai murmushi "Nama gama ai tafiya zanyi" Ya zira hannunshi cikin Aljihun wandon shi baƙi ne siriri mai kyau dashi "Okay muje muji bill ɗin naki" batai mai musu ba suka ƙarasa shiya biya kuɗin siyayyar aka zuba mata a leda ya riƙo ledar suka fito yaɗan dakata a bakin super market ɗin yana facing ɗinta "Ni sunana Kamal Ni ɗan najeriya ne nazo yin umara nida sister ɗina nazo siyayya ne sena ganki amman ke ƴar wace ƙasa ce?" safna tai ƙasa da kanta tare da cewa "Nageria Kano state muma umara ɗin muka zo" yayi murmushi "Lahh ƴar garin mu ce okay in ba damuwa ki bani Phone Number ɗinki zan maki magana" safna ta karanto masa Number ɗinta Sukai sallama Kamal ya juya safna itama ta nufi Motar su.

Da Far'a Ammi ta dube ta.
"Auta muna ta jira kin san Ina da matsalar ƙafa kikai zaman ki" Safna ta tura bakin ta gaba tare da cewa.
"Wanine fa ya tsayar dani wai yana sona shine muka ɗan tsaya dashi muna magana"
Da wata irin Murna Ammi tace mata.
"Haba auta tsakanin ki da Allah? kai Alhamdulillahi Addu'ar dana ke bata faɗi a banza ba Allah nagode maka Allah nagode maka sauran sajeeda dan Allah ya sani wannan zama naku haka babu aure yana tsanani sakani acikin damuwa to yaya kuka yi dashi? Allah yasa nagari ne Allah yasa dashi za'ayi Amin"
Ammi ta faɗa cikin maɗaukakin farin ciki wanda ya kasa ɓuya a fuskarta.
Safna tace mata yace Min.........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 88*

"Ɗan kano ne shi sun zo umara ne shima da sisters ɗinshi yazo yin siyayya ne shima Ya ganni"
Safna ta mayar wa da Ammi kamar yadda Ya gaya mata Bakin Ammi ya kasa rufuwa Haka sajeeda itama se farin ciki take dan abun yana damun su sosai ƴammata kamar su ba muni ba, ba talauci ba amman ace Ko na ɗan na rage dare basu da shi.

Har suka koma masaukin su Hirar Abu guda suke yi bayan sunyi shirin Bacci da ike suma Shirin Komawa gida nageria suke tayi Ammi ta dubi Safna"Ki ɗan taɓo yaron nan mana muji ke waya gaya miki haka akewa mazan yanzu in babu kula ai basa zama" daga sajeeda har safna dariya suke Ita ko mami da yake ba da ita aka fita ba tuni ma tayi baccinta dan tunda tazo bata da Lokacin Kowa Kullum addu'arta Allah ya bata ingantaccen rabo mai albarka, sakina kuwa masaukinta daban ita da yaranta Sadiƙ ma ba waje ɗaya suke ba, Safna ta fito da wayarta ta kunna data Tana hawa yana mata sallama da sauri ta shiga mai da masa da replay amai makon ya dawo mata da amsa se ya kira ta voice call, Ta miƙe daga wajan su Ammi ta shiga wani ɗan corridor ta tsaya amaimakon tai masa sallama se cewa tayi.
"Ina jinka"
Kamal ya kama haɓa cikin ɗaurewar kai yace mata.
"Ƙanwata kamata yayi ki fara min sallama tare da cewa yaya naje masaukina amman kince kina ji kamar wadda nai wa dole"
Sam ita safna bata san ba daidai tayi ba seda ya gaya mata sannan ta kama haɓa cike da jin kunya tace.
"Au na manta amman kai haƙuri"
Bai ce komai a wannan gaɓar ba se Magana ta gaba data biyo baya

"Na ganki kuma kin min a matsayin matata kuma ni da gaske ina son ki da aure ni ɗan kano ne, Mazaunin hotoro nine babba agidanmu ban taɓa aure ba ina aiki a Asibitin Malam Aminu kano Ƙanne na biyu mata se mahaifiyata dafatan kin gamsu dani nai miki bayanin kaina a taƙaice kafin In mun koma nazo har gida"
Safna ta washe baki cikin farin ciki tace.
"Tom shikenan Allah yasa zamu ga lokacin zuwan naka"
Yace.
"Ke ba zaki gayan Taƙaitaccen tarihin kiba?"
Tace.
"Sedai kazo In sha Allah!"
Bai jada tsayi ba yayi mata sallama cikin farin ciki ta koma take sanarwa da Ammi har abin da ya mata gyara akai.
"Kullum dama ina gaya muku ku dinga iya kalami Mazannan da kuke gani se ana lallaɓasu Sabida haka ki dinga saita harshe in zaki magana Bari Mu koma in Allah ya kawo shima mu ashirye Muke"
Har Sukai bacci maganganun suke yi na Saurayin safna ɗin da suka haɗu dashi a saudi'a.

Gabaki ɗaya al'ummar musulmi yaro da babba kowa murnar tawowar sallah ƙarama yake sabida sallah ce wadda ake sada zumunci ake ɗinka sabbin kaya a saka aje hawan idi a dawo a cigaba da zaga gari.

Yau sauran kwana ɗaya sallah har Lokacin Aliyu bai dawo ba kamar yadda farha take Lissafi tuni ta saki ranta domin ta ɗauka baze dawo bama ko se bayan sallah tun safe suka fita wajan gyaran gashi ita da Salma anan akai musu har Kitso sannan aka zana musu baƙin lalle da Farha tana mitar ita baze mata kyau ba amman Cikin Ikon Allah ana mata seya fito a saman fatarta yayi mata kyau gwanin sha'awa Daga wajan Saloon ɗin kuma wajan karɓar Ɗinki suka tafi Farha tana mota salma ta shiga ta amso se suka wuce wajan saida takalma da jaka A tare suka fita salma tace ta zaɓi wanda yayi mata baƙi ta ɗauka tace bata son jaka dan bata dame taba suka je wajan mayafai nan ma ta zaɓa tare da sarƙa da ɗan kunne da turare salma ta biya kuɗin suka wuce Gida a falo suka tarar da mai aikin salma tana ta gyara farar shinkafar wainar da za'ai gobe ga kaji da kayan miya nan Mijin salma ya kawo Ita dai farha kayan Sallar ta buɗe zaro idanu tayi sabida ganin haɗaɗɗan Jan lace da yasha buba mai azababban kyau se material da shadda wadda aka mata aiki dan murna Farha kasa magana tayi data gwada ɗinkin kamar an auna yayi mata cif sedai Ko wanne daga sama ya kamata ta rasa wannan cika da Ƙirjinta yayi har ƙasa ta zube tana cewa.
"Aunty salama nagode da Hidima Allah ya saka miki da alkairi ya raya zuri'a" salma ta kama baki cikin mamaki.
"Kai bari kada ki kuma min Godiya ai ya zama dole"
Farha kwashe kayan tayi duka takai ɗaki sannan tayi alwala tayi sallar la'asar ta fito waje domin kamawa mai aikin salma aikin Sallar da take yi ita kuma salma ta fito Cikin shiri tace zata je Gidan Ammi ta dawo yanzu suka sauka Jin haka yasa Jikin farha yayi sanyi haka dai suka yiwa Salma adawo lafiya ta fita aikin ya kaisu har dare dan har su ƙwaɓin cincin sukai wajan taran dare salma ta dawo Lokacin farha ta bar mai aikin ta ita kuma ta koma ɗaki wanka tayi ta gasa Jikinta dan ta gaji sosai bata kuma fitowa ba bacci yayi gaba da ita.

Su Ammi ne suka sauka da wajan magariba shiko se wajan Goman dare Jirginsu ya sauka Musa yaje ya ɗauko shi Mami kamar gawa ya tarar se bacci take shima dai wanka kaɗai yayi yasha tea ko wajan Ammi bai iya zuwa ba se Bacci washe gari ta kama sallah Gidan Ammi gaba ɗaya ya cika da Hidima sabida su Hajja tun ana jibi sallah suka dawo kuma da yake komai an tsara kafin su ammi subar ƙasar shiyasa gidan ya cika da Hidimar ɗora sauke.
Wajan ƙarfe takwas Aliyu ya fito cikin Babbar rigar shadda fara takalmi da Hula baƙaƙe yayi masifar kyau da dardumar shi a kafaɗa ya ƙaraso falo mami taci gayu cikin shadda turare ta fesa masa ta ɗauko waya tana masa Hoto shi dariya ma ta bashi yadda duk yaga ta ruɗe da shigar tashi Mayafi ta yafa suka jera zuwa sashin Ammi wanda ya cika da ƴan uwan Ammi waɗanda dama duk sallah haka gidan yake cika Suka gaggaisa da juna Lokacin sadiƙ shima ya shigo sabida haka tare suka Miƙe da Aliyu domin tafiya masallaci.
"Ba zaku ci ko waina bane tunda masallacin da kuke sallah se tara suke tayarwa" cewar Ammi Aliyu murmushi yayi tare da cewa "Haba Ammi ai mukai zaman cin waina makara zamuyi Dan Allah yaya sadiƙ kazo Mu wuce" sadiƙ da yake ta tsokanar Safna wadda taci kwalliya wai saurayin da suka haɗu dashi a saudia ne zezo Shine yabi bayan Aliyu wanda tuni ya ɓace daga falon

Musa ne yaja su zuwa babban masallacin Gidan sarki anan sukai sallah Shidai Sadiƙ gida yayo sabida Yadda mutane suka yaɓe Aliyu tun bayan idar da sallar wanda har seda yaje suka gaisa da mai girma gwamna sannan ya samu ya fito daga cikin Taron mutanan da ƙyar matasa se kirari suke masa Da ƙyar ya shiga Mota kansa har ciwo yake masa dan yawan matasan har yayi yawa Har Motar shi tabar wajan Mutane basu dena bin bayanta ba.
"Musa kaini Gidan su fatima na gaishe da mahaifanta kafin mu wuce"
Musa yaɗan juyo tare da cewa.
"Ranka ya daɗe ka manta yau sallah kowa yana gida idan har kaje Gidansu tofa za'a san kaine gwara ma kai shigar dare amman innai ba daidai ba a yafe ni"
Aliyu ya lumshe ido.
"Haka ne kuma musa to kaini sharaɗa Gidan Salama kokuma kaga kawai Ka bani key ɗin motar zanje da kaina kaikuma zan sauke ka a ƙofar Gidana se ka ɗauki mota ka wuce harkokin ka"
Musa yace.
"Mai gida duk yadda kace daidai ne"
Musa ya nufi Gidan Aliyu a bakin gate Aliyu ya sauke Musa shikuma yaja motar zuwa gidan salama dan ya matsu yaga ƴar budurwar sa.

"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta sarkin daya shinfiɗa sammai Guda bakwai ya shinfiɗa ƙassai Guda bakwai gaskiya yau inda ɗan uwana ze ganki Aunty fatima daya susuce"
Salma ta faɗa lokacin data ga farha ta fito daga ɗaki sanye take Cikin Lace ɗin da suka amso jiya daga Ɗinki, Yayi mata shegen kyau Sabida fuskarta tai fiyau Dalilin sabon Kitson da akai mata ga Fulawar Datai mata kyau a hannunta ga sarƙa da ƴan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login