Showing 141001 words to 144000 words out of 150033 words

Chapter 48 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

a wajan Ammi.
"Kin san ammi bata jin daɗi gasu safna basa gida dan Allah kada Ki jima"
Tace masa to seda aka idar da azahar sakina ta Nufi Gidan su mahaifiyarta tsohuwa tukuf Mutuniyar arziƙi tana kwance a tsakar Gidan su tana Shan iskar hanyar soro sakina tayi sallama Suka gaisa.
"Ina jamila?"
Ta tambayi babar tasu wadda tsufa ya Cimmata dama mahaifinsu ya rasu Kuma Su uku ta haifa daga Anty babbar yayar su se Sakina se Jamila Ko kaɗan sakina batai halin mahaifiyarta ba dan Mahaifiyarta Mutuniyar arziƙi ce Ko kaɗan bata da hannu akan abun da sakina take yi, Ita ko Anty babbar yayar su ƴar abi yarima ce asha kiɗa kaf Cikin su bamai jin maganarta sabida talaka ce Maganar Sakina tafi ƙarfi a tsakanin su dan Hatta ita ma Antyn se abin da sakina tace Kuma duk abin da suka ce mata bata ja da tsayi kwantar da kai take taci arziƙi bambancin ɗaya ne ita bata Binsu Biye biyen su sedai In sunje Sun dawo su bata labari Dan jamila da sakina team Ɗin su guda ba'ajin kansu Shiyasa Anty yayar su ke Binsu sabida suna ɗan bata.
Hira suke tayi da mahaifiyarta wadda rabi Hirar faɗa da nasiha mahaifiyarta ke mata a fakaice har akai la'asar akai magariba duk sakina tana gidan su dama tana fashin sallah ana idar da sallar Isha'i tai wa mahaifiyarta sallama Lokacin Jamila ta dawo daga inda ta fita ita ta rakota har Titi Bayan sunyi sallama da jamila ta koma gida ita ko Sakina Hanyar sabuwar maƙabartar da aka Gina ake kai gawarwaki anan kusa dasu ta nufa Cikin Ikon Allah bakin maƙabartar babu kowa da jimawa sun taɓa wucewa ta wajan Lokacin sun zo sallah take tambayar sadiƙ shine yake ce mata sabuwar maƙabarta ce wannan Ne Tunanin daya faɗo mata harta Tuno maƙabartar shine tazo Ta buɗe Ƙofar shiga Ciki ta tsaya a kan kabarurrukan tana tunanin to ta yaya zata gano sabon kabari Duhu da kukan tsuntsaye ne a maƙabartar amman sam bata damu ba Ko ta saka tsoro aranta sabida yadda idanunta suka Rufe da son Duniya Hango wani Kabari tayi mai Tudu da alamun sabuwar gawa ce aciki ganga ganga ta nufe shi sedai ta Ɗora ƙafa dan tai taku taji wata Gigitacciyar ƙara ta cika maƙabartar ga kuma wani irin Duhu daya mamaye mata idanunta ƙarar Kuma ta cika mata kunnenta ta cikin duhun take ganin wata irin halitta mai kama da jemage tana nufo ta Aguje sakina ta juya jikinta yana wata irin Tsuma gudu take Jikinta yana rawa da ƙyar ta Ƙarasa gida tana Buɗe Ƙofar falon Ammi suka ci karo da sadiƙ wanda yake riƙe da key zeje ya zo da ita dan daya dawo ya tambayi ammi tace bata dawo ba yanayin da sadiƙ ya ganta abin ya bashi mamaki amman bai magana ba sabida yadda Sakina ta ture shi ta shiga ɗaki aguje tayi saman masai se Gudawa sadiƙ ya Bita yana tambayar lafiya? sedai Jiyo sautin Gudawar dayay a toilet yasa ya koma da baya yana zaton ita ta Korota Bayan ta fito zama tai har Lokacin bata dawo daidai ba layar ta mayar jaka ta kwanta..

A wannan dare sakina bata rintsa ba sabida daga ta rufe idanunta Wannan baƙin da halittar take gani suna Nufo ta Seta Miƙe tana Rawar Jiki ta Kutsa Cikin ƴaƴanta tana rungume su sedai ƙarar na Binta Har asubahi tana faman abu ɗaya gaba ɗaya se zabura take Ranar Ko falo bata iya fita ba ga ciwon kai daya sakata gaba kamar kanta ze rabe Biyu sedai duk da haka tunanin yadda zata sami Wata maƙabartar take Sedai Sadiƙ ya ɓata mata shirin ta sabida yace ta haɗa kaya Gobe zasu wuce lagos Tasan Kuma data tafi can ba fita take ba kuma ba Ko ina ta sani ba Amman dai haka ta haɗe kayan su Ta ƙudiri aniyar koma ta yaya ne zata san yadda tai da wannan layar sedai abin mamaki awannan daran ma tsorata da zabura sakina ta dinga yi dan abun har yafi na farko dan daga ta rufe idanunta gawarwaki take gani suna Biyota acikin Likkafani seta toshe baki tana Kuka dan gudu take tai ƙara asirin ta ya Tonu.

Washe gari Sukai sallama da kowa suka wuce lagos dan sadiƙ Ta gidansu sakina ya biya sukai wa mahaifiyarta da jamila sallama Ya dubata kamar yadda sakina tace bata Jin daɗi ita ko babar sakina ta amsa sabida ta ɗauka Ko jikinta na Tsufa yake dubawa Haka suka Wuce Lagos Don gaba ɗaya sadiƙ yafi son yaje can dan ya Mayar da hankalin sa wajan kula da dukiyar ɗan uwan shi.


*KADUNA*

Yau sun sami bacci mai daɗi sabida Gidan sauron da suka ƙulla wanda ya basu kariya Wajan cizon sauron Gaba ɗaya Cikin dare Aliyu Ƙamƙame Farha yayi kamar ze mai da ita Cikin sa Haka sukai baccin su se asubahi Kiran sallah ya farkar da shi a hankali ya zare ta daga Jikinsa ya fita ya ɗaura alwala yazo ya tayar da ita dan itama tayi alwalar yau ya Ƙudiri aniyar seya tashi Mutan gidan sallah sabida ya lura kamar basa tashin asubah sabida haka Buga ƙofar ɗakin Inno yayi yace ta tashi tai sallah sannn yaje Jikin windown su shafa nan ma yace Wa mijinta ya tashi yayi sallah ya fita masallaci Bai dawo ba se wajan shiddan safe Lokacin farha ta Koma bacci Bakwai saura yayi wanka ya shirya bai tashe taba yayi tafiyar shi wajan aikin shi Alhamdulillahi bai sami matsala da kowa ba a wajan sema Girma da Mutunci da mutan wajan sukai ta bashi sedai rashin sabo da irin aikin ne yasa kafin Ya tashi wani Irin zazzaɓin gajiya ya rufe Shi Ƙarfe shidda aka sallame su bayan an basu Kuɗin su a hannu Haka ya tawo Gida duk jikinsa ya ɓaci da baƙin mai sabida ɗaukar ƙarafe.

Farha koda ta tashi bata ganshi ba tasan ya fita ne gyaran ɗaki tayi ta Ɗora abin karyawa ta gama ta zubawa Inno da shafa ta miƙa Musu suna ta Godiya ta haɗa wanke wanke Tayi ta share ɗaki ta ɗauko kayan sa Daya cire na jiya dana yau da nata ta fita ta wanke su ta shanya a tsakar gida suka zauna Inno ta fita dubiya Se ita da shafa wadda tai wake da shinkafa da manja da yaji ta zubawa farha wadda tace ba zata ciba Ran shafa ya ɓaci Sosai ganin haka yasa farha ta Ci waken Kuma yayi mata daɗi Hira suka Soma yi da shafa kamar dama can sun saba.
"Wallahi fatima naji daɗin zuwan ku sabida baban su baya son na shiga maƙota yanzu kuwa na sami ƴar tayin Hira"
Farha tayi dariya haka sukai ta Hirar su shafa tace.
"Na iya Kitso In naki ya tsufa Ki zo Nai Miki sabo Har da Ƙunshi sabida Kin san mazan yanzu se kana gyarawa Musamman Mijin ki na ga ɗan gayu Ne sekin da gaske"
Dariya suka sa tare da tafawa farha tace.
"Shiyasa nake Ririta abina Sabida ƴammatan yanzu"
Shafa tace.
"Ban Hanaki ba wallahi Ki gyara Ciki da waje yadda ze ƙara rikicewa ya gigice sabida Wasu matan da ƙyale ƙyale suke janye wa mazajen mu hankali Kalli hannuna da kaina Koda yaushe akwai Ƙunshi da kitso ga kuma ƙamshin Humra masu daɗi dana ke siya da kayan gyaran Jiki Duk da Mijina talaka ne ban bari kaina ya Kulle ba"
Farha ta fuskanci shafa sosai tare da cewa.
"To yanzu maman basma dame dame Ni ya kamata nai amfani dasu amman Ina da Juna Biyu"
Shafa tai Murmushi.
"Mace mai juna biyu ma ko batai Komai ba ita kanta Ni'ima ce dan yanzu Mijinki se yafi Jin daɗin ki fiye da ko yaushe amman duk da haka Ki dinga shan Kayan marmari Irin su ayaba Kankana kwakwa Dabino ki markaɗa su ki zuba madarar ruwa kina sha,Koki dinga cinsu a haka Zasu saukar Miki da Ni'ima sosai ga cukwi da dabino da Kwakwa Ni gaskiya nafi amfani dasu akan cushe cushen kayan matan nan waɗanda ban san garantin suba amman kowa ce mace akwai ra'ayinta nidai nawa na gaya Miki Kuma Alhamdulillahi Mai gida yana yabawa sannan Ki dinga kama ruwa da ruwan Ɗumi In kin gama al'ada kuma ki dinga tafasa Samfarerar lalle da ganyan magarya Kina tace wa ki zuba a ƙaton baho Ki dinga zama aciki, sannan Kuma Ki dinga amfani da turaren ƙamshi na Jiki mai kama Lungu da saƙon Jikin ki dan namiji baya son ya kawo Jiki yaji wari Ki tabbatar da tsaftar shi da taki In kikai haka kika haɗa da Ladabi biyayya ƴar shagwaɓa Kirsa da saka ƙananun kaya to In sha Allah Kin siye zuciyar Oga"
Dan dariya farha harda ƙwalla! anan suka ɓata Lokaci Sallah kaɗai ke tayar dasu Har akai la'asar shafa ta Miƙe don ta Ɗora sanwar Dare Farha Kuma ta shiga ɗaki ta Ƙudiri zata dage wajan gyara Lungu da saƙo na Jikinta dan faranta ran Oganta.
Tana zaune tana azkar ya shigo yanayin sa ta kalla ta gane kamar baya Jin daɗi tayi masa barka da dawowa ya zauna yana cewa
"Washh fatima ya wunin dafatan dai Kinci abinci ko?"
Ta ɗaga masa kai tana kallon Shi idanunshi yayi ja sosai kamar mai ciwon Ido ga kayan duk sun ɓaci.
"Mai zan dafa maka abin da yasa ban maka girki ba sabida bamu da fulas Kuma nasan baka son abinci mai sanyi"
Ya kwanta yana cewa.
"Fatima bar abincin nan bana Jin daɗin Jikina"
Ya kwanta sosai yana Ɗora hannunshi saman ƙirjinshi.
"To kaci wani abun acan ne?"
Ta faɗa tana matsa mai ƙafafun sa ya Lumshe ido yana sakin Numfashi sabida ya gaji ga zazzaɓi ga ciwon kai tashi tayi ta ɗora masa ruwan wanka ta Juye masa a bokiti takai masa bayi.
"Ka daure kai wanka se a siyo magani"
Ta shi yayi ya fita wankan ta Bishi da jallabiyar shi Bakin bayin ta Miƙa masa Koda ya fito alwala yayi kayan daya cire ta jiƙa da Omo shi kuma ya fita masallaci.
Itama sallar tayi Tana zaune ya shigo da leda a hannun shi ya aje ya zauna yana Kwantar da kanshi a kafaɗunta.
Jikinsa zafi zau amman haka ya miƙe ya fita waje wajan kayan daya ga ta jiƙa ya Nufa ya sunkuya yana wanke wa dan in ya barta ita zata wanke bayan yaga wankin data sha jiya da wanda tai yau rabon shi wanki har ya manta amman haka ya tirje kayan tas ya shanya Yana Wanke Bokitin ta leƙo.
"Au wankin kayi Nifa zan yi kai da ba lafiya ba"
Yayi Murmushi suka shigo ɗakin gaba ɗaya hannun shi ya fashe Duk yayi jajir abin ka da ba'a saba ba kamar zatai kuka ta riƙe hannun

"Dan Allah ka dinga bari ina yi kalla fa hannun ka"
"Fatima ina tausaya Miki ƴar ƙarama dake Allah ya jarabce ki da abubuwa kala kala a gidan auren ki"
Hannu tasa ta toshe bakin ta.
"Kada ka kuma faɗin haka Kaji"
Ledar ya janyo kankana ya siyo se Biredi da kayan tea Shine yasha kankanar kaɗan dan yace kada tayi girki shi iya kankanar ta ishe shi Bayan sunyi sallar Isha'i suka kwanta tsakar dare zazzaɓin ya Rufe Shi sosai farha ta gigice ta riƙe shi gam tana kuka tana masa sannu xuwa asubahi ya sami bacci itama baccin tai dan bata san ma ya tashi ya fita ba se tashi tai taga baya nan.
Haka rayuwar taita tafiya Tun Aliyu yana zazzaɓin rashin sabo har ma yazo ya saba Suna rayuwar sune Cikin rufin asirin Allah dan duk inda ake Neman matar Rufin asiri farha takai ta wuce Don komai in ya kawo tattalawa take, Duk tsurfa irin ta mai ciki farha tana mugun kawaici da cewar yayi mata kaza ko Ya sai mata kaza in da tayi Lokacin suna da shi yanzu rayuwar ta sauya Tuni ya yankar mata kati a wani asibitin Kuɗi ƙarami anan take zuwa awo Inno ke rakata Suna zaman su lafiya da shafa haka Mijin shafa ashe rashin abinyi ke saka wa baya Biyan Inno Kuɗin haya sabida magini ne se kuma sanda Ginin ya faɗo seda Aliyu yasan yadda yayi ya samarwa Mijin shafa gyaran Mota anan Tashar da yake sabida shi ya iya gyaran Mota ranar su shafa kamar xasu ari baki dan Godiya Zaman su Yayi daɗi Cikin farha na daɗa Girma yana cikin wata na bakwai sedai in ka kalle shi zaka ce a ranar zata haihu sabida yadda cikin yayi Mugun Girma gaba ɗaya ta Koma ƴar ƙarama Se Girman ciki wanda idan ta zauna shima Cikin zama yake dan girma Ma Sha Allah.
Watan su Huɗu a kaduna sedai Koda Wasa Aliyu bai taɓa mancewa da Ammin sa ba Koda yaushe tana ran shi Wanda Lissafin Cikin farha ya kama wata na bakwai kenan.

*KANO*
Haka al'amura suke ta faruwa Ammi gaba ɗaya ta rame ta Koma wata iri Koda yaushe Likita yana kan zuwa duba Mata lafiyarta sabida Koda yau she jinin ta hawa yake Tun su sadiƙ na Mata Nasiha har sun Zuba,mata ido sadiƙ har kano ta zame masa Gida koda yaushe yana hanya sabida Jikin Ammi daya tsananta wanda Har Likita ya kafa dokoki akan dole seta cire damuwar ranta.
Koda yaushe kukan ta Ina baba ya shiga tayi nadamar abin da tai wa baba da matar shi.

Tun washe garin da mami ta koma gidan su Tajira.........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE 104*
Ta shirya fita wajan Bokanta.
"Mama dan girman Allah ki haƙura da biye biyen nan mu Nemi yafiyar waɗanda muka zalunta har yanzu fa muna da sauran dama nidai babu ruwana Allah ma yasani in har danni zaki Fita wajan boka Akan ki cutar da rayukan da suka yi mana alkairi dan Allah mama ki bari sabida ni Jikina yana bani Ba lallai Na ƙara zama da Aliyu ba"
Tajira ta juyo a fusace.
"Dallah gafaracan matsa ki bani waje wadda bata san abun da take yi ba to in kin ga na aje makaman yaƙin yaƙar Amina da zuri'arta sedai kwana ne ya ƙare"
Ta figi mayafinta tabar gidan Hassana ƙanwar Mami tai murmushin takaici tare da cewa

"Aunty mami addu'a ce kawai mafitar mu Allah ya shirya mama danni ban ga amfanin Bin Bokayen nan ba basa ƙarar ka da komai se Cin kuɗi yanzu dai ki duba tsayin shekara Goma kuna abu ɗaya amman babu wani sauyi Da aka gani daga ƙarshe ma dai Jiba yayi auren shi tuni har matar nada Ciki inda duba gaskiya ne mai yasa ba'a gano muku ba sabida haka abin da Allah yaso kaɗai yake bayyanawa bawan sa Amman abin da ya ɓoye babu wanda ya isa ya gano shi"
Hassana ta faɗa a nutse.
Mami taja ajiyar zuciya.
"Nidai Har ga Allah na tuba wallahi ba zan kuma kai ƙafata wajan wasu mashirikai ba laifin dana ɗauka ma Zanje na nemi yafiyar su Ammi amman yanzu kam wani tsoron Allah ne ke yawo adukkan sassan Jikina in Allah ya baka bamai hanaka in Allah ya hanaka babu mai baka Ya rabbi Mun tuba"
Wuni sukai suna tattaunawa Ita da Hassana sabida Hussaina ta fita makaranta Itama tana dawowa suka ɗora Kuma dukkan su Sunyi Allah wadai da halin Mahaifiyar su.
Tun suna sa ran dawowarta har suka rufe gida dan ba baƙon ta bane kwana a wajan Bokayen ta.

Tajira cikin wani ƙauye dake jahar katsina wajan Bokanta taje wanda tai Imanin Aikin shine yaci sanda Aliyu ze auri Mami Ta sami damar ganin Bokan wanda ya haɗa mata Mugayen ayyuka wanda daga ciki harda haukata Farha matar Ali sabida tace base da lafiya zatai rayuwar auren ba sannan Ita kuma Ammi a sakar mata Cutar shanyewar Jiki Aliyu Kuma a birkita masa tunanin sa ya zama baya daji ko gani se Mami a duniya waɗannan zafafan ayyukan aka haɗowa tajira ta zube masa manyan Kuɗi Ta kamo hanyar gida tare da sharaɗin nan da kwana uku sheɗanun da Bokan ze tura Jikin su zasu fara aikin sedai ya bata wani baƙin magani yace ta saka A kusurwa uku ta Farha data Ammi data Aliyu wanda shine kan Aikin Kuma yace lallai ta saka wannan magani in ta kuskura to aikin ze juya kanta

Sedai a hanyar dawowar ta Allah yayi Ikon sa akan motar su wadda ta ɗebo mutane daga wannan ƙauye zuwa kano wata ƙatuwar Motar katako tabi takan Motar tasu wanda motar ta gangara Gefen hanya Mutanan ciki duk sun sami raunika Wanda Har da tajira acikin waɗanda suka sami Rauni wanda nata yafi Na kowa shahara dan ta karye a cinyarta Ƙashin kwankwasonta ya ɓalle Kanta ya fashe da ƙyar aka haɗa wayarta data yashe can Ƙasa aka kira Numbern da aka gani acikin wayar tata. ALLAH KENAN!


wajan ƙarfe Ukun Dare wayar Hassana ta fara Ringing wadda ta manta Bata kashe taba.
Cikin magagin bacci ta ɗaga wayar Muryar wani namiji ce yace.
"Da Allah da Hassana Muke magana?"
Hassana ta watsake tare da cewa.
"Nice"
Se yace mata.
"Mun sami Numberki a wayar wata mata naga kece ƙarshen Kiranta to bamu san dai halaƙar ku ba Sabida bata hayyacinta Motar su ta sami hatsari ne a tsakanin Hanyar dawowa katsina zuwa kano yanzu dai Mun samu an saka su a wata motar Muka tawo dasu babban asibitin murtala dake Cikin kano yanzu haka muna sashin ƴan gaggawa"
Wayar ce ta Mutu hassana ta ɗora hannu aka tana cewa.
"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un mama kin jawa kanki Babu wa'azin da Aunty mami batai Miki ba Amman kika Murje dama in baka godewa Allah akan Ni'imar saba zaka godewa azabarsa"
Maganganun Hassana ne suka tada mami da sauran ƴan uwan haka suka fita da ƙyar suka ƙarasa Asibitin dan akwai tazara tsakanin fagge zuwa asibitin Murtala sabida dare ne babu abin hawa Koda suka je asibitin ma seda suka sami ɗan sanda sannan suka sami ganin tajira wadda sam bata gane Kowa Mami kuka tasa a haka suka zauna har asubahi taimakon gaggawa aka bawa tajira Wanda ta samu ta dawo hayyacinta sedai Likita ya tabbatar wa su mami sedai su ɗauketa su kaita asibitin ƙashi ai mata Hotuna a wajan data samu rauni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login