Showing 42001 words to 45000 words out of 150033 words

Chapter 15 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

masallaci ya fita waje ganin masu neman taimako ya kuma komawa masallaci yayi sallar isha'i daga nan part ɗin Ammi ya nufa don ya sha shayin sa na ƙa'ida duk dare Ammi ta haɗo masa shayin suna sha suna hira har ya kammala Ammi tana masa maganar dawowar Mami Wadda zata dawo Gobe a yadda Mamin taiwa Ammi waya ta sanar da ita

"Ammi ni zan je na kwanta na gaji, Ƙila ma gobe Bashir zai dawo fa yayi Min waya ɗazu"

Ammi itama miƙewa tayi tsaye tana cewa.

"Nima ya gaya min ɗazu a waya har ina masa tsiya ya zauna a abuja"

Daga haka sukai sallama Ammi ta nufi ɗakinta shikuma ya Nufi hanyar fita har ya kama Ƙofar zai fita kuma sai ya tuna da Yarinyar nan ko yaya take ciki shidai baiji motsin taba kuma Ammi bata masa maganarta ba ɗakin ya nufa sai dai yana tura ƙofar yaga wayam bata cikin ɗakin yadda ya aje mata break haka ya tarar dashi da sauri ya iska Toilet nan ma bata ciki Aliyu ya yarfe zufar data gama jiƙa masa Jikin sa kardai Guduwa yarinyar nan tayi to tayaya ma zata iya guduwa.

Sai ya shiga safa da marwa a ɗakin Ta yaya zai iya tambayar Ammi zagaye ya dinga yi a ɗakin Shi kaɗai ganin hakan ba zata masa ba ya sanya shi Fitowa daga ɗakin ya nufi hanyar ɗakin Ammi........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*30*

*A LOVE STORY 30*

Bedroom ɗin su safna ya fara shiga ya zira kanshi ya leƙa ciki suna kwance ko wacce riƙe da waya suna charting gyaran murya yayi wanda yasa ko wacce ta juyo babu shiri ya tamke fuska murya a shaƙe yace musu.
"Why are you not sleeping? salon kuzo kuna samun carry over a makaranta kuzo ku ɗagama Ammi hankali alhalin kune bakwa mayar da hankali akan karatun yanzu ƙarfe nawa amman kun zauna Kuna charting da samarin da ba zasu aure kuba"
Kowacce ta shiga hankalin ta ko tari basu yi ba ya gama cin mutuncin su yaja ƙofar bayan yaja musu kunne akan ya hana su chart ɗin dare yana fita safna taja ajiyar zuciya cike da tsoro ta dubi Sajeeda.
"Sis nifa wallahi in naga Ya Ali gabana faɗuwa yake Mutum kullum sai baƙar zuciya fuska a tamke"
Sajeeda wadda take faman sakin Numfashi tace.
"Hmm nifa har yanzu ban gama dawowa daidai ba wallahi yaya akwai bala'i ko me ya ruwan shi damu oho Ammi ma bata ɗaga mana hankali ba sai shi wallahi nifa nafi son ya sadik akan ya Alin nan"
Safna ta kama baki har tana zira kanta ta window tana leƙan shi.
"Amman sis baki da kirki Nikam ko wanne ina so acikin su shi kawai Ya Ali ya cika takura ne Kin san Allah Ko Aunty mami ma haƙuri fa take da halin shi watarana naje part Ɗinsu Tea ta zuba mai By mistake ta cika masa sugar ke kinga yadda ya rufe ido yana mata bala'i kamar zai dake ta"
Sajeeda dariya take har tana riƙe ciki kafin tace
"Nikuwa har kin tina min dukan da yayi ma Aunty salma kafin tai aure har targaɗe yaji mata, Amman kuma fa ya Ali ya iya love dan ranar dana rakasu Hospital da Aunty Mami baki ga yadda yay ta mata ba nidai ina son Miji Irin ya Ali wallahi irin su nada wahalar samu ko acikin maza yana da zafi yana da kirki, kawai in baka san halin shi bane zakuyi ta samun matsala amman wallahi yana da haƙuri dan yadda Ammi ta riƙe masa wuta akan Aunty mami kin san Allah ko ya sadik ne baze yarda ba Kina kallo Mai Aunty mami keda aba kamar tsinke ni ban taɓa ganin siririn mutum irin taba Kirjinta yasin kamar na farar babe"

Habawa safna mai zatai inba dariya ba.
"Haba sis ta yaya zakice Kirjinta kamar na farar babe ta yaya kika gani?"
Safna ta faɗi har Lokacin dariyar take yi bata daina taba.
Sajeeda tace.
"Tab in ta dawo ki zuba mata ido an ya wannan akwai size na bra ɗinta ma wannan halitta haka ƙananu gaskiya yaya Ali yana haƙuri, Kuma nina tabbata duk ranar daya samu wadda yake so wallahi ba baki nayi ba amman daga Aunty mami har Ammi kashin su ya bushe domin Mami ba zata same shi irin yanzu ba ita kuma Ammi zai bujere mata ne dan kawai biyayya yake mata"
Safna tace.
"Tab duk soyayyar ya Ali da Ammi ke kina zaton akwai wadda zai bijirewa umarnin Ammi akan ta kema dai sis faɗi kawai kike"
Sajeeda dariya tayi.
"To meye umarnin ammi ɗin in ba son zuciya ba Be patient with what I have to say, gaskiya ce ɗaya Ammi bata kyauta wa ya Ali ba, ki ɗauko mace mai suffar maza ba gaba ba baya ki haɗa ta da jarumin maza sai tsayo Kamar zare fisabilillahi dan kawai kina da ra'ayin kada ya auro wata tazo ta rabaku wani rabo Safna? meye baiwa Ammi ba mu maye bai mana ba kamfani guda ya ɗauka ya bawa ya sadik shike juya shi daidai da gidan da yake ciki nashi ne Ya Bashir shike da matsayin manager a kamfanin shi na kano mu meye bai mana ba daidai da Aunty salma duk shekara tare yake haɗamu Muje Hajji muje umara muje dubai Mu hau motar da muke so musa kayan da muke so mu sai wayar da Muke so Duk kudin waye bana saba? ya kamata Ammi ta rabu dashi ta zubawa sarautar Allah ido IDAN RABO YA RANTSE Fa sai mai shi Rabo dangin ajali ne ta yuwu ba ajikin Aunty mami rabon Ya Ali yake ba amman Ammi taƙi ganewa ko ita mamin tasan meye azuciyarta datake ta wannan haƙilo domin ita oho"

Safna tai shuru tana nazarin maganar ƴar uwarta tabbas komai sajeeda ta faɗi haka ne gaskiya ne maganarta.
"Hakane sis nikam na rasa wace irin soyayya ammi kewa mami Kamar aikin asiri sam kaƙi farin cikin ɗanka akan na ɗan wani shegu munafukai masu kalar Munafurci ni shiyasa kika ga bana mata da sauƙi sosai na riƙe mata wuta damma ammi na min magana ne ke nifa daga Aunty Mami har Aunty sakina wallahi basu Min ba ita ma Aunty sakina matar ya sadiƙ ina taga wani kirki sai jida kai da kallon mutane ɗaiɗai gashi ki lura ƴar bariki ce sam bata ƙaumar Aunty mami ko zuwa sukai nan kiga fa bata sakin jiki da Aunty mami wannan inda a haɗe suke ma da kishin faccalan ci zasu yi kodan kwanaki tace wa ya Ali yaje ya auri ƙanwarta yaƙi ne oho amman naso naji maganar yana gayawa Ammi"

Sajeeda Dariya ta saki.
"Au wannan ƙanwar tata jamila wadda take acan lagos ɗin wadda suke zuwa nan tare hutu ita take son taima ya Ali an cusai da ita haha lallai kam shiyasa naga tanawa Aunty mami gani gani mai ya Ali zai da jamila ai ba sa'ar shi bace ita kanta Aunty sakinar ai kamar ta girmi ya sadik"
Haka suka cigaba da hirar su har lokacin baccin su yayi suka kashe ƙwan ɗakin suka kwanta baccin su.

Aliyu yana barin ɗakin su safna wanda dama neman Farha yaje sai ya wayance da musu faɗa ɗakin Ammi ya shiga by lucky tana toilet ya duba bai ga Farha ba yaja mata Ƙofar yabar ɗakin sai da ya fito parlou ma yake tunanin meze kaita ɗakunan su kama Ƙugu yayi tunanin shi ya ɗauke yama rasa meze yi a wannan Lokaci haka yaja ƙafafun shi da suka masa sanyi ya fita daga parloun Ammi part ɗin shi ya koma yayi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya fara mai dogon hannu daga ciki ya saka dogon farin wando mai santsi ya fesa turare mai ƙamshi Ya sauka ƙasa ya haɗa tea yana sha yana nazari a ƙa'ida yanzu ba abin da yake buƙata sai bacci amman ina yaga ta yin bacci bega yarinyar mutane ba wadda yasan ko ba daɗe ko bajima Mahaifanta zasu Buƙaci ganin ta in yayi sake tayi wani gurin meze ce musu duk ranar da suka buƙaci ƴar su.
Aje tea cup ɗin yayi a center table ya ɗora dogayen ƙafafun shi a saman Table ɗin ya sanya hannun shi yana cakuɗa sumar kan shi yana hasko Rashin mutuncin daze mata idan ta yarda ya ganta a duk inda taje.
Daga bisani miƙewa yayi ya fita daga parlou ɗin duk inda ya Shiga ma'aikatan gidan maza suna Masa barka da fitowa zagaye ƙaton Gidan yake Har ƙarshen katanga daga ƙarshe yaje wajan masu gadi.

"Salamu Alaikum"
Da sauri masu gadin suka ƙaraso wajan shi suna amsa sallamar.
Ya harɗe hannaye a ƙirji.
"Malam ɗalha baku ga yarinya ƙarama ɗazu ta fita ba?"
Suka ɗan yi jimm kafin malam ɗalha yace.
"Gaskiya yallaɓai bama wanda ya shigo yau a mata bare a fita Ina fatan dai lafiya?"
Girgiza kai yayi tare da juyawa a lokacin ranshi ya soma ɓaci hankalin shi kuma ya soma Tashi a karo na farko daya soma jin Ammi ta sosa masa rai na yadda tai buris da lamarin ƴar mutane wadda inda tana saka idanu akanta ba zata Fita ko ina ba dukkan laifin kuma ya ɗora su akan Ammin sane sai dai baya da yadda zeyi ya Tuhume ta dan an ce wata fuskar tafi gaban mari.

Shi kaɗai a harabar gidan har wajan 11 yakai ya komo baccin ma ya ƙaurace masa da sauri ya nufi wajan mota ze driving yaje gidansu kota je sharf kuma ya manta bai ɗauko key ba ya juya suka ci karo da Hajjo.

"Ɗana barka da dare?"

Ya juyo yaɗan saki ranshi kaɗan.

"Hajjo daga ina da wannan dare baki bacci ba?"
Hajjo tai dariya.

"Bacci ɗana ai har yayi mini yawa yanzu ma fita zanyi titi goro na ya ƙare nasan zan sha faɗa da masu gadi amman haka nan zasu barni kaina har ciwo yake in banci ba"

Aliyu yay murmushi yana cewa.

"Hajjo bada ban goro nada illah ba dana sa an kawo maki hunhu dan ki daina fitar dare bani so hajjo kada watarana Mota ta kaɗe min ke"

Dariya tai tana cewa.

"Allah zai kiyaye bara nai sauri na baro Ƙanwar musa marainiyar Allah kada ta farka daga bacci taji tsoron ɗakin dan duk su Tasallah sunyi bacci"

Aliyu ya sosa kai.

"Hajjo gashi ban fito da canji ba dana baki na goron"

Tayi dariya.

"Kada ka damu, Niko ɗana wannan ƙanwar Musan itama ƴar ƙauye ce ni dai banga tayi kama da mutan garinmu ba ɗazu taita karanta Min sunayen kayan abinci a kicin"


Sai lokacin ya gano Hajjo da wadda take Nufi da kanwar musa Ɓoyayyar ajiyar zuciya yaja kafin ya tamke fuska.

"Hajjo ina zan sani Bana nan ya kawo ta Kije kada dare yayi kinga lokacine na Damuna sabida ruwa"

Hajjo da sauri ta juya tana tafiyarta har da saurin ta.

Juyawa yayi direct sashin su Hajjo ya nufa Sashin nasu babu kowa duk sun rufo ɗakunan su ya gane ɗakin hajjo sabida yafi na duk ma'aikatan tsari ya tura Ƙofar ta.

Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi daya hango farha tayi ɗaiɗai a saman gadon Hajjo tana sharar Baccin ta hankalin ta kwance ya jima a tsaye yana kallon ta yay kamar ya rabu da ita tunda yaga inda ta kwanta ɗin sai kuma yaji baze iya ba.

Ya shiga buga gadon Hajjo da sauri yana furta.

"Fatima ke fatima tashi"

Cikin magagin Bacci ta buɗe ido tana cewa.

"Ni dan Allah umma ki rabu dani bacci nake yau ba zani aikin ba"


Yayi murmushi ya rasa ƙaunar fatima da wannan aiki.

"Ke tashi mana kona zuba miki ruwa, Kin san kina son umman kika Lalata aikin ki kika ci amanar aikin ki son zuciya ya kaiki ya baro to nan a kurkuku kike ba'a gidan umma ba"

Da sauri ta watsake ta zuba masa jan idanunta wanda bacci ya sanya ya koma jajir ɗin........


*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*31*

*A LOVE STORY 31*
Yana tsaye a kanta fuskarshi ba yabo ba fallasa kamar koda yaushe ƙamshin mayen turaren shi mai azababban ƙamshi ta shaƙa tana ƙoƙarin juya masa baya yayi saurin ce mata.
"Kada ki kuskura ki koma baccin nan ko ni sa'an wasan kine ina miki magana shine zaki koma bacci"
Ya faɗa a hasale.
"Toni me zan maka da tsakar daran nan mutum sai Mugunta na gudo nan ɗin ma ba zaka barni ba"
Ta faɗa tana turo baki gaba wanda ya fito da zallar ƙuruciyarta ta kwaɓe fuska kamar zata zubo da hawaye
Ya gyara tsaiwa ya harɗe hannun shi ido ya zuba mata yana hukunta ta da kallon shi mai azababban saukar mata da dukkan wata rashin kunyarta
Tsit tayi ta sunkuyar da kanta a ƙasa dan ba zata jure wannan kallon nashi ba.
"Don't let me count to three before you wake up"
A kausashe ya faɗi maganar wadda ta sanya farha miƙewa ta ɗauki hajib ta saka Fuww ta wuce shi tana gunguni tana tafe yana binta a baya kamar jela har suka bar part ɗin su Hajjo.
Adaidai Hanyar part ɗin su Ammi taga ƙaton Farin Muzuru zai shiga Falon Ammi ai da wani uban sauri tayo baya direct kanshi tayi ta cakume shi tana sakin ajiyar zuciya da sauri ya Ɓamɓareta daga jikin shi.
"Ke dallah meye haka zaki taɓa min jiki na kamar na sa'anki"
Muryarta na rawa take nuna masa.
"Wani farin abu na gani zai shiga falon Dan Allah kayi gaba in koma bayan ka"
Banza yayi mata dan takaici ta bashi yayi gaba tana binshi da sauri har ya ƙarasa bakin Ƙofar Falon ya tsaya ta Ƙi tafiya.
"Wai ke kamar wata ƙaramar yarinya tsaiwar me kike ba zaki shige ba"
Turo baki tayi wanda ya zama ƙa'idarta
"Ni ka rakani to tsoron wannan abun nake"
Ya bita da kallon Minti guda ya kawar da kanshi bai ce mata komai ba taga ya juya yayi tafiyar shi.
Wani tsoro ne ya kama farha tattare rigarta tayi da gudu ta shige Falon Ta nufi ɗakin data ke sai mai da Numfashin Tsoro take yi Ƙofar ta sanyawa Key ba kowa a falon Haka ta kwanta ta jima bata yi bacci ba tana ta faman Juyi a saman gadon can dai bacci ya ɗauketa.

Hajjo tana dawowa taga wayam bata ga farha ba aranta tai tunanin ta tafi makwancinta shiyasa bata damu data Bibiyeta ba haka ta kwanta a saman gadonta itama baccinne yayi gaba da ita.

Aliyu tafe yake yana tsaki har ya ƙarasa part Ɗinshi

Ya haura saman shi rigar Jikinsa ya zare ya kwanta a saman gado yana ta jan tsaki har Lokacin Yarinya kamar Ƴar yaye komai sai an mata ga rashin Kunyar tsiya shifa wannan ne dalilin daya sa sam ƙarin aure baya Burge shi itama bada ban taja wa kanta ba da baze aure taba, Shi ina ze iya auran ƙaramar yarinya wadda kullum cikin baka ciwon kai take Shifa ko fushi yayi mami ke rarrashin sa shi bai saba da lallaɓa mace ba shiyasa idan tayi wani abun yake jin kamar ya rufe ta da duka dan takaici.

Ya mirgina yana shafa ƙasumbar data taru a fuskar shi wadda kwana biyu bai yi gyaran fuska ba.

Adaidai wannan Lokacin wayar shi dake yashe a gefe ta soma ringing Ya lalubota ya ɗaga.
Muryar mami a narke tace.
"Aminci da rahmar Allah su sauka a gare ka Mijin Mami"
Kadaran kada hakan yace.
"Tare dake"
Taja ajiyar zuciya.
"Ka soma bacci ne Sweet me?"
Ta taɗa muryarta a narke kamar zatai Kuka.
"A,a"
Ya faɗa a taƙaice
"Me yasa baka yi bacci ba ko tunani na kake yi?"
Ya janyo pillow ya matse.
"Mami inna ce Miki bakya gabana yanzu ba zaki yarda ba?"
Taji gabanta ya faɗi shifa wani bin idan ya saki magana se kace goyon gwauro sam bai iya magana ba duk yadda tazo masa haka yake faɗar ta amman bata sani ba ko ita kaɗai yake wa hakan oho.
"Kamar yaya bana gaban ka ina matarka ta sunna me kake nufi?"
Ta faɗa kamar zata saki kuka!
Ya lumshe ido burin shi ya ɓata mata rai kamar yadda ta ɓata masa.
"Understand me, idan nace zan tunanin ki hakan ze jefani cikin wani hali ai kin san yadda nake Kuma kin san ke kaɗai gareni kika tsallake kika tafi hutu kika barni, Ni me yasa in kina gida ko tafiya zanyi dake nake tafiya amman ni sabida ban da ƙima da daraja a idanun ki shine kika tsallake with out my permission kikai tafiyar ki Mamy"
Gaba ɗaya jitai hankalinta ya tashi.
"Kamin afuwa Hubby Mama ce tace nazo na huta amman hakan baze sake faruwa ba In sha Allah gobe ina tafe da tanadi mai zafi"
Bai wani ji maganar tata ta shige shi ba yace.
"That will be later"
Ya aje wayar.
Ya ja pillow yayi kwanciyar shi batare da ya sanya tunanin Mamy a ran shi ba.


Baki ta saki tana bin wayar da kallo kafin taja tagumi hawayen takaici yana zubo mata a haka Hajiya tajira ta shigo ta sami Mami.
"Ke kuma lafiyar ki kukan me kike haka?"
Mami ta aje wayar.
"Mama yaushe zan sami yadda nake so a wajan Aliyu? me yasa Aliyu bai ɗauke ni da daraja a rayuwar shiba?"
Tajira ta zauna gefen mami.
"Sabida ke matar tushe ce kuma bahaushe yace matar tushe bata daraja"
Mami cikin tashin hankali tace.
"Mama har ladan noma ana bada mata kuma hakan besa mazajen su sun raina musu Aji ba, Amman ni cikin shekara goma da aure ina masa hidima ina ɗaukar cikinsa yana zubewa bai taɓa Nunan Kulawa cikakkiya ba Shi kamar mai Jinnu kullum cikin ƙunci wallahi nina tabbata arziƙin Ammi nake ci a wajan sa nina rasa yadda zanyi Aliyu ya soni Wani irin maganine bana sha na gyara ba amman daga ya gama dani baze ƙara waiwayata ba sai wani Lokacin"
Ta faɗa batare data tuna da wa take maganar ba Jitake kamar da ƙawarta take magana ba uwarta ba

"Kece na gaya Miki abin da zaki amman kinƙi yarda Nifa zuwa yanzu na dena son auren ki da Aliyu burina ya mutu Mu gina kammu"
Mami tayi ƙasa da kanta.
"Mama ina son Aliyu ba zan iya sanadin barin shi duniya ba ada na auri Aliyu da tarin manufofi Amman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login