Showing 75001 words to 78000 words out of 150033 words

Chapter 26 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

dayay yaji hankalin sa ya kwanta sabida haka harkokin sa ya cigaba hankalin kwance.
Farha kuwa aje wayar tayi ta zubawa Tv idanu tana saƙa wasiƙar Jaki Har zuwa sanda Mami ta fito da Tray da Kulolin abinci jere a saman tray Ɗin ta kawo gaban Farha ta aje ta koma Kitchen ta ɗauko Musu ruwa da Lemo ta dawo kusa da Farha ta zauna ta saka Musu kayan abincin a tsakiyar su........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*









*A LOVE STORY 60*

Cikin ladabi musa ke amsa wayar wadda ta nuna alamar da uban gidan shi suke yin wayar Musa mota ya shiga yaje ya ɗauko wani Abokin shi wata ƙatuwar Mota ce ta daban ke biye da bayan Motar da su Musa ke ciki wanda take ta bin su har zuwa Bakin Layin su Farha Musa ya dubi Abokin nashi ya ƙara jaddada masa abin da zece kafin ya Buɗe masa Ƙofar motar ya fita Abokin musa ya ƙarasa cikin layin su farha ya kuma sami gidan kamar yadda Musa ya kwatanta masa Yaro ya samu ya aika cikin Gidan akan yana son ai masa sallama damai gidan yaron ya shiga gidan ya faɗi kamar yadda aka umarce shi Nura ne ya fito ƙofar gidan ya bawa abokin Musa hannu suka gaisa Abokin Musa ya gyara tsaiwa yana cewa

"Dan Allah ko nan ne Gidan su farha?"
Nura yayi saurin cewa.
"Ehh nan ne yaya ake ciki?" Abokin Musa yace "Dama saƙo ne Mijinta ya bayar a bawa Babanta ina son ganin Baban nata idan babu damuwa" Nura yaɗan yamutsa fuska cikin Alhini yace "Gashi baban namu bai da lafiya yau kwanan mu biyu da fitowa daga asibiti ma yanzu haka yana kwance Dan Allah ina ne gidan da Farha take aure? ka daure kace wa Mijin nata ya kawo ta Kawu ya ganta dan dalilin aurar da ita da yayi ne ma wannan ciwo ya same shi ance zuciyar shi ce take barazanar kamuwa da ciwo yanzu haka hawan Jini ke damun shi" Abokin Musa ya jinjina lamarin kafin yace wa Nura "To idan ba damuwa ko zamu shiga daga ciki sena duba shi" Nura ne yayi gaba Abokin Musa kuma yana binsa a baya Nura ya shiga ɗakin Kawu Lokacin Umma tana bashi Koko Nura ya kalli Umma kafin yace.
"Ya samu yana amsar kokon?" Umma ta share ƙwalla tace "Ehh amman da akwai ɗan canji da an siyo masa ruwan shayi dan naga baya son kokon bai fiye amsa ba" Nura ya shafa aljihu gaba ɗaya ziro yake sabida albashin Nasu Duk ya ƙare a jinyar kawu yanzu hatta kai su Kansu Matan Gidan Ko wacce jarin ta ya taɓu sabida siyan magani Yau haka suka tashi Ko ruwa babu agidan dan tsananin Babu shiyasa a wannan lokacin Umma itama kawai dauriya take amman inda za'a gwada Jininta itama tasan yahau sabida yadda ƴaƴan Gidan da matan gidan suka sakota a gaba da habaici da faɗan Ƴarta zata kashe Musu kawu Kullum Umma setai kuka damma akwai Ya Sadiya da take yawan zuwa cin Uban kowa take agidan sedai daga ta fita zasu Ɗora shima kawun Wuni kukan a kawo masa Fatima shiyasa Kullum Jinin sa a haye yake baya sauka Kullum cikin shan magani yake.

"Umma yau se godiyar Allah, Amman zan fita wajan Abokina se a siyo masa" Umma ta kalli Nura da tausayawa yaran ba ƙaramin Ƙoƙari suke yi da mahaifin suba kunya ta kama Umma tasan duk a sanadin Ƴarta Komai yake ta faruwa da Kawu, "A,a Nura ka bari yanzu na aika Ikram Gidan sadiya abin da ta samo se a sarrafa masa" Nura yace "Umma me yasa zaki aika mata Kinsan halin Ya sadiya da Saurin Kiɗima Yanzu seta tawo ta ɗauka ko ciwon nasa ne ya tashi kuma ai tana Ƙoƙari kaf ƴaƴan gidannan bamai kula da kawu kamar ita Kusan Kullum fa seta yo masa Girki"
Umma tai murmushi "To ai ya zama dole Nura, bada ban naga tana sana'a ba da bazan aika mata ba to sana'ar dana ga tana yi ce yasa nake aika mata ai ya zama dole" Nura ya shafa kai yace "Umma ɗan gyara shi ga Baƙo nan yazo wajan shi wai mijin farha ya aiko shi" kawu yana jingine amman se ganin shi akai ya miƙe umma ta kama shi tana cewa "Kabi a hankali" Cewa yake "Nura ina baƙon shine baka gayan ba yana ina ina fatiman take Tazo ta ganni kafin Allah ya ɗauki rayuwata" Ƙwalla ce ta kawo Idon Umma bata taɓa sanin kawu na son ƴaƴan saba se akan farha ashe duk jarabar Faɗan shi ya damu da ƴaƴan sa gashi nan Abin da yayi wa Farha yaja masa ciwo.
Abokin musa ya tuɓe takalmi ya shigo Ɗakin ya zauna a tabarma suka gaisa da Umma sannan suka gaisa da kawu Abokin Musa yace.
"Dama Alhaji ne yace nazo na duba ku, Sannan ga saƙo can A mota yace a baku" kawu yayi saurin cewa "Kai ni babu wani saƙo ina fatima take tana wani gari wani hali take ciki?" Abokin Musa yace "Baba kai haƙuri wannan Ba'a bani damar na sanar dakai ba iya wannan kaɗai aka umarceni shima abin da yasa na faɗa maka sabida kasan yadda garin ya koma mutanan duniya sun lalace kada kuga saƙo sama taka ku tsorata shiyasa aka ce na bayyana wanda ya aiko ni, Amman garin da take da sauran su wannan ba hurumina bane ni dai nasan ƴarka tana cikin Ƙoshin lafiya Kuma ka godewa Allah ƴarka ta sami Miji na nuna sa'a" Daga umma har kawu ba wanda ya iya magana domin su ba wannan bace Buƙatar su ba buƙatarsu sanin ina ƴarsu take Abokin Musa ya miƙe tare da dire damin ƴan dubu dubu har guda biyar a gaban kawu bai saurari me kawun ze faɗa ba yabar Ɗakin Matan gidan ko wacce tai tsaye cirko cirko suna sauraran abin da Baƙon yake faɗa ko wacce ta cika da mamakin wannan Aike Da Nura da Halifa ne suka bi Abokin musa mota kamar yadda ya buƙata Kaya ne na abinci buhunan shinkafa taliya makaroni mai komai daya danganci abinci akwai shi haka sukai ta fito dasu suna kawowa Gida wanda har ƴaƴan maƙota seda suka taya su gaba ɗaya tsakar Gidan su Farha ya cika da kayan abinci abokin Musa ya shiga Mota bayan sunyi sallama dasu Halifa Musa dabe Fito ba yaja Motar suka bar bakin layin.

Hankalin Umma tashi yayi data ga kayan abincin ta shiga wasi wasin wani irin Mijin farha ta aura kodai ɗan yankan kai ne da sauri ta kawar da tunanin tana ayyana alkairi Ɗakin Kusa da kicin aka shigar da kayan abincin Wanda kafin kice kwabo Babarsu Ruƙayya ta haɗa wuta an ɗora sanwar safe wadda ba'a ciba kawu kuwa Gaba ɗaya Jikinsa yayi sanyi Nura ya kira ya bawa duka kuɗin da abokin Musa ɗin ya bayar Matan gidan bakin ko wacce ya Mutu Murus sabida al'ajabi Maƙota kuwa leƙowa suke zuwa dare Gida ya cika da ƴan barka barka wasu har cewa umma suke dama sun san watarana kawu ze Huta ajikin wani a cikin ƴaƴan nashi Ikon Allah farha data fi kowa Muni agidan itace mai rabon Jin daɗi yaya Sadiya ma data zo taji kayan arziki Ihu ta saka harda rawa tana cewa Ai alkairi yanzu aka fara gani babarsu Hadiza kuwa ta kasa magana cikin dare ta kama habaici tana ayi dai su gani idan tusa zata hura wuta waya sani ma ko ɗan mafiya ne amman ba yadda za'ai farha ta auri mai kudi irin haka kunjifa Hassada seda kawu ya fito yayi mata cin Mutunci sannan tai shuru Gidan su Farha ya wadata dan Kayan abincin sun haska Gidan ƴaƴan gidan kowa murnar zeyi ci uku ta ishe shi Kuɗin Da kawu ya bawa Nura kuwa Nura bai taɓa su ba zuwa yayi ya zuba a cikin account.

Abokin Musa ne ya dubi Musa yana gaya masa duk yadda ya sami mahaifin yarinyar Musa ya jinjina lamarin tare da ɗaukar alwashin sanar da Aliyu duk yadda ake ciki bayan Musa ya sauke abokin sa waya yayi wa Aliyu ya gaya masa duk yadda sukai musa ya ƙara da cewa.
"Kasan yayin ta suna aiki a kamfanin mu shiyasa ni banje sun ganni ba na tura abokina dan nasan baka Buƙatar su sanka a yanzu"
Aliyu yayi Murmushi daga nasa ɓarin kafin yace.
"Haka ne Musa ina son ka gayawa manager a ƙara musu Kuɗin albashin wannan watan harma da sauran watannin gaba sannan ka koma akai Baba asibiti mai tsada a duba shi sannan ina son a samu Leburori masu aikin sauri Su fara gyara Musu Gidan su inda hali ma har Bene a ɗora sannan wannan kayan abincin duk sati Biyu zaku dinga kai Musu amman na cikin azumi yafi ko wanne son samu ma a ƙara masa mota ɗaya wadda ze rabawa Maƙotan shi musa kada ka Bada fuskar da zasu sanni kasan har yau Ammi bata san nai aure ba wannan shine dalilin daya sa ban so su san ni wanene"
Musa ya amsa cikin bin umarni kuma beyi mamakin hidimar da Aliyu yace ayi ba dan wanda bai haɗa komai dashi bama yayi wa bare surukan sa.

Washe gari Abokin Musa ya koma wajan kawu Asibitin Kuɗi ne mai tsada aka kai kawu aka duba shi aka bashi magani Wani ɗan gida anan kusa dasu Suka koma wanda abokin Musa ya kama musu haya ranar dasu ka kwashe kayan su daga gidan Masu aikin suka fara aiki wanda motar yashi Bulo sumunti ta cika layin su farha Kawu da ƙyar yabar wannan aiki dan seda Su Halifa sukai ta bashi baki da cewa ai ya godewa Allah daya sa ta silar aure farha ta sami wannan cigaba bata silar bariki ba kuma su sun yarda Mijin Farha nagari ne mai gaskiya da ire iren wannan kawu yabari ayi gyaran Gidan ma'aikata suka soma fashe Gida aka fara gyara dakin aka ɗora a ka fara sabon gini a saman Gidan kafin kace Me cikin kwana biyu abin ka da aikin Kudi an ɗora bene agidan su farha Ƙasa kuma anyi ƙaton falo da ɗakuna da Kitchen aciki saman ne ɗakuna uku daga na kawu sena su Halifa ƙasa ne ya zama Ɗakuna Huɗu ɗakin Umma ɗakin babar su hadiza ɗakin babar su Ruƙayya se Ɗakin yara guda ɗaya se wani Kuma ɗakin ɗan ƙarami a gefen na Umma se Store da kitchen Se Ƙaton gate da aka saka cikin kwana Huɗu suka gama aikin aka saka sola akai painti aka saka famfuna idan ka kalli Gidan ba zaka gane shiba ma'aikatan suna gama gyaran Maƙota da ƴan uwa akaita zuwa gani kowa na santi wasu na murna wasu na ƙananun maganganu Sabbin kayan Ɗaki aka zuba a falon an saka saitin Kujeru labulaye tv da sauran su haka ɗakunan su saitin sabbin kayan gado ƴan uban su store kuma an cika shi da kayan abinci ga sola haske Kota ina kawu daya ga alatun daka danƙara masa kuka ya saka yana Godiya ga Allah lallai haihuwa mai rana dama akwai ranar daze Huta har haka Ashe rabon arziki ne yasa Farha ta turje seta auri wannan Mutumin Ita ko Umma daran da suka koma gidan kasa bacci tayi alwala tayi ta dinga sallah akan Allah yasa dukiyar Mijin farha ta halak Ce Allah yasa ya kawo farha ta ganta Allah yasa farha tana cikin Ƙoshin lafiya.
Cikin lokaci kaɗan rayuwar Gidan su Farha ta sauya daga Ƙunci zuwa farin ciki daga matsi zuwa wadata ada ana damben abinci agidan yanzu kuwa sema ayi abincin babu mai ci da kuɗin wajan Nura aka sauyawa yaran Gidan makaranta aka kaisu Private school, Babar su Ruƙayya ta koma Gindin Umma wanda Babar su Hadiza kuwa taƙi kwantar da hankalin ta sabida baƙin ciki Kullum fatan tsiya take tare da aibata farha wanda Kuma hakan baya hanata Cin abincin da Mijin farhan ya kawo da Kuma zaman gidan da Mijin farhan ya gyara Ƴaƴanta faɗa suke mata amman taƙi Ji ita ko babar su Ruƙayya sun haɗe da umma har wata biyayya take mata shi kansa kawu yanzu ba wannan faɗan idan yana wa Umma magana har ƙasa yake da Murya wani bin idan umma ta damu da wannan Hidima yakan ce yaji ajikinsa mijin farha ba macuci bane ba da wannan yake kwantar wa Umma da hankalinta...........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 61*

Yau saura kwana ki Biyu azumi gaba ɗaya al'ummar Musulmi sun cika da farin cikin gabatowar wannan wata mai daraja watan da Allah yake Buɗe ƙofofin rahmar sa wata mai albarka wata mai daraja yau tun safe su Farha suke ta kwalema a part Ɗin Ammi an fitar da Kujerun falon an sauke labulayen falon duk an fitar dasu sabon Paint ake tayi a part ɗin zuwa azahar an sake sabbin Kujerun falon tare da labulaye Komai ya sauya Falon sai tashin Ƙamshi yake yi.
Gaba ɗaya jikin farha ciwo yake mata haka ta shiga ɗaki ta cire kayanta ta shiga wanka tana wanka tana tunanin Bawan Allah matar sa tace kwana takwas zeyi yau gashi har ya kwana Goma sha huɗu bai dawo ba, Haka tayi wankan ta fito tana zaune a bakin Gado tana shafa mai Safna ta shigo ɗakin ta ɗan kalleta.
"Kizo Ammi tana kiran ki"
Daga haka ta juya bata jira cewar Farhan ba, Farha ta gama shafa man sama sama ta je gaban kayan ta Riga da skirt na atamfa ta ɗauka Sedai data zo saka rigar kaɗan tai mata taƙi shiga Musamman daga wajan Ƙirjinta Seda ta cire bra sannan ta saka rigar skirt ɗin ma da tsalle ta saka shi aikuwa se Nishi take Numfashin ta har sama yake da ƙyar take janyo shi Hijabi dogo ta saka har ƙasa ta fita daga ɗakin zuwa Ɗakin Ammi shima an sauya kayan gadon ɗakin dan bana da bane Ammi ta dubi Farha yau babu wannan Ɗaure fuskar tace mata

"Fati yanzu me zaki yi?"

Farha tana wasa da yatsun hannunta tace.
"Babu komai Ammi, wanka dai nayi"

Ammi ta ɗan dube ta.

"To dan Allah zaku shiga kitchen Keda Hajja, zaku yi girki kamar kala Biyar sabida yau Sadiƙ zezo da iyalan shi, da Bashir da Baba duka yau zasu zo Ina so kuyi girki mai kyau dan Allah"

Farha cikin ladabi ta amsa wa Ammi, sannan ta baro ɗakin sallah tayi sannan ta fita har Hajjo tazo Kayan miya farha ta soma gyarawa ita kuma Hajja tana ɗora sanwa.
"Hajja wai waye Baba ne? naji Ammi tana yawan cewa baba?"
Cewar farha wadda take Cire hancin attaruhu, Hajja tayi dariya tana cewa.
"Nawa zaki biyani na gaya miki waye baba"  Itama farha dariyar tayi tana cewa "Hajja zan baki jakaliyan Ɗari" Dukansu dariyar sukai kafin Hajja tace.
"To Alhaji Ali shine Baba Kinsan sunan Baban Hajiya Ammi gare shi" Farha ta cika da mamaki domin sam bata ɗauka shi bane Baban dama yau ze dawo wato shiyasa Aunty mami tun safe tace ta fita gyaran Jiki da ƙunshi da Kitso Ah lallai.
"To Hajja sadik fa naji tace yau zezo da matar sa shima anan yake?".Hajja ta ɗora tukunyar akan gas sannan ta juyo "Eh yayan Alhaji Ali ne yana lagos yana aiki a ɗayan kamfanin Alhaji Ali, Tare akai Musu aure sadik nada mata ɗaya da yara Uku duk zasu zo anjima sabida zasu je umarar azumi ne nan da ƴan kwanaki" Farha bata ce komai ba aikin su suka cigaba dayi Wajan Magariba suka kammala Lokacin Mami ta shigo kitchen ɗin tai kyau ma sha Allah Fuskarta tai fiyau sabida  sabon Kitso warmers ɗin abincin ta shiga dubawa tana ta yiwa su Hajja sannu.
"Ina abincin Ammi?"
Cewar mami tana kallon farha.
"Ai gaba ɗaya aka haɗa abincin sabida tace anan zasu yi dinner"
Cewar Farha, Mami ta yatsina fuska tare da cewa

"Da anyi wa Ammi ko tuwon semo ai ina zata iya waɗannan ciye ciyen ai se mu" Hajja tayi dariya tana cewa "Hajiya mami ta ammi wannan soyayya taku har tayi yawa to ni dai na tashi sedai Fati tayi mata" Farha jitai kamar tace wayyo Allah dan ba ƙaramar gajiya tayi ba ga ciwon mara ga zafin hannu wanda gyaran attaruhun data yi ne yaja mata shi ga ciwon baya ga wani yawu da yake tarar mata abaki zuciyarta na tashi tun ƙamshin tafashen naman data yi bata sami sukuni ba.
"To Farhan ɗan yi mata tuwon Before ai magariba" Mami ta faɗa tana fita daga kitchen ɗin farha dan haushi Ko sallamar da hajja ke mata bata amsa ba ta ɗora ruwan tuwon sannan ta fita daga kitchen ɗin ta koma ɗakinta Da gudu ta shiga Toilet ta riƙe Ciki tana sheƙa amai a galabaice ta fito tana Numfashin wahala jagwab ta kwanta a gado hannunta dafe da ƙasan mararta daya ɗaure yana mata ciwo Miyau ne ya tarar mata taje ta tofar ta kuma dawowa Kitchen ɗin ta shiga ta Buɗe Fridge ta ɗauki lemon tsami ta yanka tana tsotsa seda tayi sallar magariba sannan ta tuƙa tuwon ta kwashe sannan ta ɗora Miyar Kuka wani haɗaɗɗan Ƙamshin turare taji wanda kafin ta ɗago mami ta shigo kitchen ɗin taci adon golden lace ɗinkin Bubu wanda yayi mata cif ajikinta ga wasu uban gwala gwalai sarƙa ɗan kunne awarwaro data zuba fuskar nan tata taci kwalliya, Kallo ɗaya Farha tayi mata taji zuciyarta ta motsa wani irin zafin Kishi na taso mata yanzu fa duk wannan kwalliyar Domin Mijinta tayi ta ko, maganar mami ce ta katse wa farha tunanin da take.
"Farhan nayi kyau kuwa? Yaya yayi min waya suna airport taimaka ki ɗora masa ruwan tea mai kayan ƙamshi amman mai ɗan yawa sabida ta lagos ya biya tare suke da su Ya Sadiƙ Ni bara naje wajan Ammi, amman kafin na ɗauko min wancan Ludayin na sama"
Farha tayi Murmushin yaƙe.
"Kin yi kyau mana Aunty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login