Showing 138001 words to 141000 words out of 150033 words
Chapter 47 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
sanyaye Jin Abin da Ammin sa tace masa Ya kalli sakina tare da ce mata..........
Autar manya ce marubuciyar......
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SON TA NAKE BA*
*ƊAN MAJALISSA*
*MURADIN ZUCIYA*
*ASHE ZUMA*
*TAURARO*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*FITAR RABO*
*DA IZZATA*
*BAƘON LAMARI*
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*RABO YA RANTSE*
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 102*
"Kodan gaba bana son ki ƙara fita baki gaya min ba wannan ai Ba daidai bane"
Ya faɗa cikin nutsuwa sakina tayi ƙasa da kanta tare da ce masa.
"In sha Allahu......"
Ɗakin Ammi yayi shuru na wani Lokaci kafin sadiƙ ya yiwa Ammi sallama ya tashi ya fita sakina ta miƙe tabi bayan shi ya juyo ya kalleta.
"Yaya jikin Maman Inna tashi da wuri zan biya Mu gaisa na duba ta"
Sakina tayi saurin cewa
"A,a bama se kaje ba sabida Sun koma asibiti tun ɗazu ita da jamila"
Sadiƙ yace.
"Okay to Allah ya bata lafiya Inna dawo Ko zuwa dare se Muje dake Ina su Minal?"
Tace.
"Suna ɗaki suna Break fast ko a kira su?" ya girgiza kai har bakin Ƙofa ta raka shi Ya kama hanyar Office.......
*Mami*
Tunda tabar falon Ammi ta koma part Ɗinsu take faman safa da marwa kamar wata zararriya seta zube a ƙasan carpet tana rusa Kuka!
"Wannan wace irin baƙar rana ce tazo Mini na shiga Uku yanzu ashe duk yadda naso wannan yarinyar Kishiya tace Duk yadda na jata ajikina Kishiyata Ce Aliyu me yasa kayi Mini haka me yasa kayi Min bazata Ko a fuska baka taɓa nuna Min kana da alaƙa da wannan yarinyar ba?"...........
A haukace ta miƙe ta ɗauko wayarta ta shiga Neman layin Hajiya tajira mahaifiyarta idanunta a rufe suke Bata Ji bata gani haka taita Kiran Number Mahaifiyar tata.
"Mami wannan Kira haka na lafiya ne yaya akai?"
Cewar Hajiya tajira wadda daga ɓarin ta tana zaune ne tana Cin Abinci.
"Mama babu lafiya mama bokayen Mu maƙaryata ne mama duba ƙarya ne ba gaskiya ba Mama babu Mai sanin abun da ze faru yau ko gobe se Ubangiji mama wannan abun yasa naji na tsani Bokaye da duk ma mai binsu.......
"Dakata mami Ki fara sanin da wa kike yin magana Ki Nutsu kafin ranki ya ɓaci Farko tunda Kin tsani mai bin bokaye har dani Kenan da kanki dan ba da ban aikin bokayen ba da baki kai matakin zama matar Ali ba"
Mami ta share majina tare da cewa.
"Dama can Allah ya ƙaddara ni matar shice ba mahalukin daya isa ya hana Ko ya saka Mune dai idanunmu suka rufe Muke zaton aikin Bokaye ne yasa Aurena da Ali ya tabbata"
"Dakata mami Ni zaki wa butulci Nida naci kashi da Fitsarin Ki......
"Mama ba zan taɓa yi Miki Butulci ba ke mahaifiyata ce amman mama ina Roƙonki da cewa dan girman Allah daga yau Mu rabu da biye biye don ƙarshen alewa ƙasa! bakin alƙalami kuma ya riga ya Bushe Bokayen mu basu gano mana faruwar Auren Aliyu ba domin zancen da nake Miki tsayin watanni Uku Aliyu yayi auren shi da matar shi Muke zaune har tana da Cikin watanni Uku daga ni har Ammi da mutan Gida bamu san da wannan aure ba ashe Ammin da Muke zargin da hannunta a matsalar da cikina yake samu har Bokan da Muka je yana tabbatar mana yana bamu maganin kawar da ita ashe Ita ke faman yin faɗi tashi akan Aliyu kada ya ƙaran Kishiya wannan dalilin Ne ma yasa ya Ɓoye mata auren Shi sabida haka iya wannan kaɗai Mama ya dace Mu kama kammu Mu gane In Allah ya baka babu mai hanaka in Allah ya hanaka babu mai baka Kinga Munje wajan maƙaryata suna Cutar damu suna karɓar Kuɗin Mu abanza suna haɗa mu da makusantan mu.......
"Ke dallah gafara can Marar hankali se soki Burutsu Kike Min kin kasa fahimtar dani takai maimai ɗin abin da yake faruwa?"
Mami a nutse take gayawa mamanta dukkan abun da ya faru.
Tajira cilli tai da plate Ɗin abincin wanda har ya fashe a ƙafarta Jini ya ɓalle amman bata damu ba seta hau ashar! tana cewa.
"Na rantse da Allah da wanda ya haɗa auren da shi mai auren da ita yarinyar da ita Aminar gaba ɗaya Sena ɓatar dasu aduniya harni za'a kawowa maganar banza harni Amina zata rainawa hankali Kece yarinya ƙarama To bari Kiji Kitimurmura ce Ba wani tasan da batun auren nashi dani suke magana ki haɗa kayan ki da safe zanzo Mu tafi gida daga nan Kuma dole Na koma wajan Bokan daya haɗa auren Ki dana Ali shine kaɗai ze Min yadda nake so dan na nijar Ɗinnan na Kasa gane kan aikin shi sabida yadda gaba ɗaya naga Komai bai tafi yadda nake soba"
Bata jira cewar mami ba ta katse wayar.
Daran ranar mami batai bacci ba Komai ya tsaya mata cak ta kasa tunanin Komai akan wannan lamari sedai kaso goma na cikin Zuciyarta yafi gasgata cewar Duk abin da Bokaye da ƴan Tsubbu suke faɗi ƙarya ne ba mai yi se Allah ba mai hanawa se Allah da asubahi ta samu bacci ya kwashe ta wajan tara da wani abu Bugun Ƙofar mahaifiyarta ne ya tashe ta
Ta miƙe taje ta Buɗe mata Ƙofar falon ba ta tsaya jiran Gaisuwar mami ba ta tattare mata kayanta iya waɗanda zasu ci manyan akwatunan da suka Fito dasu Suka kama hanyar waje suna tafe Tajira tana tijara har zuwa sashin Ammi wadda suka tarar a ɗaki dan sadiƙ bai Jima da fita ba suka shigo a tsaye tajira ta tsaya ta kama Ƙugu tana cewa.
"To tsuhuwar Munafuka Ni zaki yaudara Kici amanar zumunta ashe aure kika wa Aliyu amman zaki wayance da Borin Kunyar banza wai bakya son ya ƙaro aure Gudun shu'uman cin matan zamani munafuka to ƙarya Kike da hannun ki a auren Aliyu har barin gidan da yayi da saka hannun ki"
Ammi ta ɗago a ɗimauce tare da cewa.
"Ki fahimce ni Yaya tajira wallahi bana da sa hannu akan Komai Yadda kowa yaji maganar auren shi Nima haka naji ki barni da tashin hankalin ɓatan yarona kaɗai ya isheni"
Tajira tai wata girgiza tare da cewa.
"Ai sha Allahu ya tafi kenan Kuma yadda kika tarwatsa min shirina kema ki kwana da shirin kinyi bankwana da farin cikin ki matsiyaciya Munafuka"
Mami ta saka kuka tana cewa
"Haba mama haba mama ammi bata da laifi akan hakan Please karki abin da zakiji Kunyar shi gaba"
Seta juyo wajan mami.
"Dama batun yau nasan tasono na haifo ba kekam Baki gadoni ba To shikenan duk abin da nake dan wa nakeyi Tunda kin zaɓi amina dani gata ga kinan Ku zauna"
Mami cikin kuka tace.
"Ba haka bane mama Yanzu Lokacin gyara kura kurai ne ba Lokacin wani abu ba rayuwar bata da faɗin da zamu ce se Munga komai daidai in ada munyi ba daidai ba yanzu akwai damar gyara"
Tajira ta juyo.
"In kika ƙara cewa tak Allah ya isa.......
Mami taja bakin ta tai shuru Ammi tace.
"Mami Allah yayi Miki albarka kuma Allah yana son bawan daze laifi yazo yayi nadama ya tuba duk da ban san mai Kukai ba amman Kije Ki tuba akwai ragowar damarki sannan Kibi mahaifiyarki Ku rabu lafiya daman Allah yana sako rayayye acikin matacce ya sako matacce acikin rayayye ba tun yau nasan Wasu abubuwan tirsasaki mahaifiyarki take akan yin su ba, kamar nice da Aliyu da dama wasu abubuwan danni yake Yinsu dan ya gama dani lafiya daga ciki harda auren ki Aliyu bai taɓa son ki ba sanadin biyayyar uwa yasa yake zaune dake amman mahaifiyarki bata ga haka ba nina sadaukar da farin cikin ɗana danna Ƙara ɗanƙon zumuncin mu Allah yana kallo wallahi banda gudun sharrin matan zamani babu wata manufar Ɓoye data sa na hana Aliyu ƙarin aure sedai kash yaya tajira Kin bani mamaki yau se gashi akan abun da duk ya shafe mu Kinzo kina Kumfar baki kina aibatani Kina jawa yarona jafa'i lallai Ɓoyayyan Nufin ki akaina da zuri'ata ya bayyana Kuma kin saka min shakkar auren da kika nace akan se ɗana ya auri ƴarki tabbas akwai manufar hakan dan Inda Kina ƙaunata baza kice Aliyu yayi tafiyar da baze dawo ba, sannan Sekin tarwatsan farin cikina mai nayi Miki tajira in ba alkairi ba dama alkairi yana zama sharri? Allah ya sani bani da Mugun Nufi akan ƙara auren Aliyu se Gudun kada ya auro mana ɓata gari wanda nasan Inzan haɗiyi kur'ani sabida rantsuwa ba ko wa ze yarda ba wani ma cewa zeyi sabida naga matarshi bata haihuwa ne yasa na hana shi ƙarin aure gudun kada ya auro wadda zata haihu Ya sami ɗan kanshi yanzu ma haka daya bar Gida nasan Ko ita matar tashi Kusan tunanin hakan zatai aranta Ni kuma nasan Ko kaɗan bani da wannan manufar manufata ɗaya ce Kuma na faɗa Nasan mami ba juya bace Ko min daɗewa zata haihu tunda Allah yana bata cikin zama ne kawai bayayi Shiyasa duk sanda yazo Min da batun Ammi zan ƙara aure nakan ce masa Baba Ina gudun sharrin matan zamani kai haƙuri ka zauna da mami sabida kada ka auro ɓata gari wadda zata tarwatsa mana zumuncin Mu da zaman lafiyar mu mami kuwa Jinin kace In ma haihuwa kake so mami zata cika maka gida da yara To ashe gwara ma da Allah yake ƙaddara Dukkan Cikin da mami take samu yake zubewa shi kaɗai yasan abin da ya ɓoye da ban haɗa zuri'ata daku ba sabida jiya kaɗai dana je Gidan su yarinyar da ya aura ban sani ba na gano lallai akwai wata Rahma da Allah ya ƙaddara Aliyu ya auri wannan yarinyar har rabo ya shiga tsakanin su"
Ammi ta ƙare maganar a nutse wata irin dariya tajira tayi.
Tare da cewa.
"Ranar wanka ai ba'a ɓoyen cibi komai ya ƙare ai tunda har Kika haɗa munafukin auren ɗanki har ya sami ƙaruwa da amaryar shi sedai ki sani yadda Kike zubar da Cikin mami Nima sena zubar dana amaryar shi sabida nasan kece Kika haɗa wannan aure amman dan Gulma kince bake bace ba Kuma Ki san nasan kece Kike Zubar wa da mami dukkan Cikin da take samu sabida Kina baƙin cikin kada ƴata ta haihu itama ta dandali arziƙi to ta Allah ba taki ba Amina"
Ammi tai dariyar takaici.
"Haka Mashirikan naki suka gaya Miki? to na fiki da sauri na faɗi Allah! wanda shine yake bawa Mami ciki Kuma shike Rabata dashi wanda Duk Ɗinmu bamu san manufar Allah akan yin hakan ba, Kuma Alhamdulillahi dama ya ƙaddara hakan da ban haɗa iri daku ba, An gaya Miki Nima irin kice mai bin mashirikai Sabida dukkan kalaman ki sun yi Nuni da zahirin Kina Biye Biyen banza dana wofi Toni ba haka nake ba na dogara ga Allah Kuma In sha Allah da kaifin addu'ar mahaifiya Ɗana ze sami kariyar Allah Kuma cikin matar shi zezo duniya lafiya Allah baze baki wannan sa'a ba"
Ammi ta faɗa babu tsoro!
"Amina yadda kika ɓatan shirina kema Ki kwana cikin shiri ko yau ko gobe ko anjima zancen wanin ki ake ba naki ba Wallahi ni tajira sena ga bayanki yadda mahaifinmu ya firfita uwarki akan uwata ya soki fiye dani Kika auri Mijin daya fi nawa Kika haifi ƴaƴan da suka fi nawa to wallahi sena rabaki da sauran farin cikin dayay saura a rayuwarki wannan manufa tawa ita ce jagaban haɗa auren mami da Aliyu"
Ammi tayi dariyar takaici.
"Mahaifiyata tafi taki mahaifiyar biyayya shiyasa taci ribar zaman aure! Sannan soyayyar mahaifina dani ina zaton soyayyar mahaifiyata ce ta dawo kaina Mijina Kuma Sunan shi Mijin marainiya Allah yay masa rahma ƴaƴana kuma sunan su ƴaƴan albarka ita zatai ta Binsu Kinga Illar sharri kenan Yadda kikai haka ze Koma Miki Nufin ki Allah ya duba shiyasa yaƙi bawa Mami zuri'a da Aliyu Kuma Ni yarda da Allah danai na tsarkake zuciyata Shine yasa yaketa bani kariya daga dukkan sharrin ki se wahala Kike taƙi ƙare Miki lallai Kin shiga Jerin ƴan caca Tunda har kike ja da mai tashi tsakar dare ta Roƙi Allah kariya da dukkan Buƙatun ta lallai dukkan wanda ze tashi cikin dare ya roƙi Allah tabbas se yafi ƙarfin Dukkan wata matsala sannan yayi azkar Allah ne ze sauko mala'iku don su zame masa kariya dukkan wata ƙaddara Ko Jarrabawa daze gani wannan fararriya ce Kuma a hakan Allah ze sauƙaƙa masa Ita Nina yarda Allah shine ya haɗa auren Aliyu da mami don ya zama Izna gare ni Nina janyo ku ajikina kuna Jinina ashe bina Kuke da sharri nida zuri'a ta har Kina furta sekin rabani da farin cikin dayay Min saura a rayuwata To Allah ya baki sa'a"
Ammi tana faɗin hakan ta Miƙe tabar Musu falon tai Cikin Bedroom ɗinta Tajira fita tai mami tabi bayanta sabida tace Intai magana Allah ya isa Kuma inda tana da magana da bazata wuce Neman yafiyar Ammi ba amman mamanta ta hanata tai mata Furuci mai zafi.
Haka suka fita daga gidan tajira na Tijara har kuma suka kai Gida masifar take yi alokacin mami tayi mata magana
"Mama nidai nasan nayi laifi har da na biye Miki mukai ta tafka ɓarna a baya Babbar rahmar da Allah yayi Mini shine daya sa maganin da Muka amso dan Ammi ta Mutu bai tasiri ba yau da Ammi ta mutu ta sanadin mu da yaya zamuyi da tarin zunubi bayan ga wanda Muke abun dan shima tuni yay auren shi mama bazan Ɓoye Miki ba nidai wannan auren nashi ya sanya na zubda makaman yaƙi na ada na yarda nai Laifi nai kuskure Kuma ina roƙon Allah ya yafe Mini Kuma duk ranar dana Koma zan nemi yafiyar Ammi data Aliyu akan abubuwan da Mukai Musu Sabida Nina san Ammi ba lallai ta Kuma barina da auren ɗanta ba a irin abin da kikai mata a yau, Sannan mama in danni kike Bin Mashirikai akan ganin bayan ƴar uwarki mai son ki da alkairi da Kuma Mijina daga yau ki dena Dan Allah mama zan zauna agida Ina roƙon gafarar Allah har zuwa sanda zanji matakin aurena da Aliyu"
Mami ta faɗa tana Kuka Tajira salati ta saka tana cewa.
"In sha Allahu Dana fita wajan Bokana ze duba Mini ke anya amina bata mallake Min keba Tabbas an sauya Miki tunani Mami ba yin kanki bane Kuma maganar Fita neman Nasara yanzu na fara ke baki san ciwon kanki ba"
Mami tabi mamanta da kallo tana mata addu'ar shiriya lallai wanda yayi nisa baya taɓa Jin kira iya wanda Allah yaso da rahma kaɗai yake ganar wa idan yay laifi ya gyara!
Ammi tai Kuka tai kuka a wannan rana na nadamar auren Aliyu da mami data haɗa daga ƙarshe ta Miƙe tana addu'ar Allah yayi mata tsari da sharrin tajira lallai ɗan adam abun tsoro ne wanda kai wa Alkairi ne ke Binka da zagon ƙasa.
Dukkan abin da ya faru akan Kunnen sakina............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 103*
Sabida tun Lokacin da Mami da Tajira suka shigo Gidan Sakina ta fito Ta tsaya a bakin Ƙofar Bedroom Ɗinta dama gidan ba kowa daga ita se Ammi Su Safna sun tafi makaranta, Sabida haka Dukkan abin da ya faru acikin Kunnenta ya faru sedai ta kasa gane meke faruwa sabida bata da masaniya akan Dukkan abun da ya faru don batai kwanan Gidan ba bare ta sani Sabida haka Cikin sanyin Jiki wanda ta aro shi ta Saka a cikin yanayin ta taƙarasa Cikin Bedroom Ɗin Ammi bayan su tajira sun tafi waɗan da sam basu Lura da Sakina ba.
Ammi bata ƙaramin falon ta tana Bedroom sabida haka sakina seta zauna a falon Tana jiran Ammi wadda bayan ta idar da addu'ar Neman kariya daga sharrin tajira ta shiga toilet ta wanko Fuskarta datai jajir sabida Kuka ta fito falon se taga sakina a zaune Cikin Nutsuwa Ammi ta zauna sakina Kuma ta Matsa tana mata sannu da Fitowa.
"Ammi wai meke faruwa ne? duk na kasa samun Nutsuwa sabida naji Dukkan abun da ya faru keda Maman Mami Kuma banji daɗi ba duk da ban san meya ke faruwa ba, Amman idan tambayata ta ɓata Miki rai dan Allah Ki haƙuri sabida ba Hurumina bane ba"
Sakina ta kai maganar kamar gaske Ammi ta share sabon hawayen da ya zubo mata muryarta a shaƙe tace wa sakina.
"Ai ba maganar Hurumin ki koba Hurumin kiba sabida an haɗu an zama ɗaya abin da yayi sadiƙ shine yayi baba........
Tas ammi ta kwashe duk abin da akai ta gayawa sakina wanda bata nan akai abin
"Ammi Aliyu yayi aure batare da sanin kowa ba har matar nada Ciki?"
Sakina ta faɗa cikin zare idon mamaki.
"Haka ne sakina yanzu haka baba baya gida shida matar tashi"
Cewar Ammi tana share sabon hawayen ta sallamar Bashir ce ta katse Musu maganar wanda ya fito Cikin Shirin Komawa Abuja Suka gaisa da sakina wadda ta miƙe ta basu waje
Sakina sabida Murna rawa ta dinga yi a ɗakinta bayan ta koro su Hidaya falo ta ɗauki wayarta Numbern Bokanta ta kira bayan ya ɗauka ta ce masa.
"Ranka ya daɗe ina dawowa kuma na tarar da labari Biyu ɗaya mai daɗi ɗaya marar daɗi mai daɗin shine Ƙanin Mijin nawa yabar gida bayan yace yabar wa Mijina da mahaifiyar shi da ƴan uwan shi dukkan dukiyar shi sabida auren dayay a ɓoye wanda mahaifiyar taƙi aminta da matar wanda Labarin marar daɗi shine matar na ɗauke da juna Biyu"
Daga cikin wayar ya kece da dariyar Mugunta tare da cewa.
"Sauƙi ya samu kenan sabida haka ki maza Ki Kai layar nan Sabida zaki ji daɗin mallaka da ɗaure bakin Mijin ki tunda yanzu shine akan Komai da wannan damar zaku Raya kanku"
Sakina tai dariya tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa wannan abu yayi Mini daɗi ba ɗan kaɗan ba wallahi yau ɗinnan zan fita da kaina asai da rai a nemo suna ai ba Komai bane ba a wajena"
Sallama sukai ta katse wayar Tana wata Irin dariya.
Wayar sadiƙ ta kira tace masa zata je Gidan su amman zata bar yara