Showing 90001 words to 93000 words out of 150033 words
Chapter 31 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
juya masa baya da sauri ya sauke kayan Kwaɗayin daya jere a gabanta Kana ya ɗagota yana cewa.
"Ki daina irin wannan kwanciyar kada na ƙara gani kinyi"
Ya faɗa lokacin daya ɗorata a saman cinyar shi Yana kuma zira hannunshi a ƙasan mararta dannawa yake a hankali yaji ɗan tauri a wajan kaɗan Ta rintse ido tana Cije bakinta a hankali ya sunkuyo da kanshi saitin Fuskarta har Lokacin kuma hannun nashi yana ƙasan marar tata bai cire ba"Akwai zafi?" Rufe ido tayi tana ƙara cusa kanta adaidai saitin Cikinsa Ya kuma raɗa mata "Ki daure ko kazar da yoghurt ɗin kisha Kinji" yadda ya furta Kinji ɗinne ya jefa ta cikin wani hali Kuka take masa ƙasa ƙasa wanda yasa yaɗan susuce kaɗan ya ɗagota yana kallonta "Wai menene haka kita kuka kita kuka tun ɗazu se kace dukan ki nake yi" Cikin Muryar kukan tace "Hannun ka fa naga ka ɗora akan nata Fisabilillahi ba dole nayi kuka ba kwartanci da Mijina da cikin dare" Saka yatsa yayi ya ɗane bakinta kafin yace "Nine kwarton ko ita?" Turo baki tayi "Oho muku nidai aka ci amana ta Allah....." bai bari ta ƙarasa ba Ya ɗora bakin sa a saman nata Ji kake tai Ƙus tana amsar darasin nashi tsayin Lokuta yana hukunta tata da Kissing lips ɗinta kafin ya ɗauketa ya saukar da ita ƙasan carpet ya shiga yago kazar yana saka mata abakin ta Haka ta dinga amsa tana ci tana Lumshe ido harta ƙoshi takura mata yayi seta sha kankana A wajan shan kankanar seda tayi Kuka dan cikinta ya cika Tana gama sha ya ɗagata Ya kaita tai Brush tare da ɗauro alwala aikuwa tana zuwa ta haye gado se bacci Ya tattare Komai daya zube sannan ya shiga Toilet ya ɗauro alwala Carpet ya shinfiɗa ya soma nafila har wajan ɗayan dare yana saman carpet Kafin ya tashi ya Ninke ya cire jallabiyar Jikinsa ya hau gadon bai takurata ba dan ya fahimci tana jin daɗin baccin janyota yayi Jikinsa ya haɗeta da Ƙirjinsa yaja masu bargo ƙarfe huɗu ya farka sabida sahur dan Gobe za'a tashi da azumin watan ramadan Ba abin da ya iya ci se dabinon daya shigo ɗakin dashi se ruwa marar sanyi sannan ya tashe ta tai sahur Ɗin itama daga falo ma yana jin su Ammi na hidimar yin sahur Ɗin farha Tsire taci da sauran Yoghurt ɗin data rage yaɗan kalleta "Zaki iya azumin amman?" ta ɗaga masa kai Ita dai tana gama sahur wani baccin ta kuma komawa shikuma jiran asubahi yayi ana kiran assalatu ya fita masallaci daga nan kuma bai Kuma dawowa ba part Ɗinshi ya wuce.
Farha da ƙyar ta iya sallah ta koma bacccin ta..........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 72*
Ganin hasken falon Part Ɗinshi a kunne yasa ya ƙarasa cikin falon da sassarfa Lokacin Mami ta fito daga kitchen hannunta riƙe da cup da shayi aciki tana ta juyawa da spoon Jiyay gabanshi ya faɗi yana addu'a Allah yasa mami bata leƙa ɗakin shiba dan ya manta bai saka key ba ta ɗan kalle shi tana yi mai hararar wasa.
"Shine koka tashe ni nayi sahur ko?"
Ya shafa saman kanshi wanda baya barin suma ko ɗaya tare da cewa
"Ai duty ɗin kine ni me yasa baki zo kin tashe niba, Ko abin da zanyi sahur ɗin ma baki bani ba haka na kusan makara dan kin san bakya azumin ke"
Dariya tayi tare da wucewa saman Kujera ta zauna tana shan tea ɗin nata ajiyar zuciya Aliyu ya mayar bayan ya tabbata mami bata Je ɗakin shi ba ya haura saman shi yayi wanka Wajan 6:00am ya fito cikin shiri ze fita ya ƙarasa ɗakin Mami tana kwance ta dunƙule cikin Bargo yaɗan tsaya akanta yana duba tsadaddan agogon shi Ƙirar samfirin exporer ya ɗan bugi pillown da mami take kai ta buɗe idon ta tar akan shi kafin ta yunƙura tana cewa.
"Ina kwana har ka fito?"
Ya saki murmushi yana cewa.
"Ehh na fito mamy zani dutse yau sannan kuma zani gidan Alhaji akan case ɗin Hanan"
Mami tai masa fatan alkairi ya fita ya wuce sashin Ammi ba kowa a falon se ƙarar Ac da fanka da suke faman yi da alamun kowa bacci yake yi Sabida dama azumi ya gaji haka Ɗakin Farha ya buɗe ya shiga.
Itama tana kwance kuma bacci take sosai ya zauna a gefen gadon ta ya fito da wayar shi ya kira musa akan yazo su wuce sautin maganar shice ta farkar da farha ta tashi zaune duk fuskarta a kumbure take tashi tayi daga zaunan ta sauka banɗaki ta shiga ta wanko fuska ta dawo har Lokacin waya yake yi ta zauna a ƙasa tana kallon shi ya gama wayar taɗan saci kallon shi kaɗan tare da cewa
"Ina kwana" da kulawa yace mata.
"Lafiya lau yaya azumin?" tace masa "Alhamdulillahi"
Shuru suka yi su dukan su kafin ya miƙe tsaye.
"Zan je dutse daga nan kuma zan shiga Gidan Alhaji"
Bata gano me yake nufi ba tace masa
"To Allah ya tsare hanya" ya zuba hannayen shi cikin aljihun shi.
"Baki buƙatar komai wanda zanzo Miki dashi me kike sha'awa kici idan an sha ruwa?"
Tai jimm tana tunani kafin tace masa.
"Ka tawo min da Nono mai tsami, se Kuma Ɗata da Mangoro" setai shuru tana kuma tunano abin da take so can kuma tace "Yawwa da fara" dariya yayi tare da cewa "Duk zanzo dasu amman ni baza'aci fara ba" Turo baki tayi tana ƙunƙuni "Nidai ina so ka siyo min" Dariya ya kuma yi mata tare da cewa "Tom shikenan zan duba Miki" ya fita daga ɗakin ta bishi da kallo wani bin yana da kirki Musamman a lokutannan ta rasa mai yasa yake lallaɓata Komai tace masa yana mata batare daya danƙara mata baƙar magana kamar da ba.
Bata koma bacci ba tashi tayi ta wanke Toilet ɗinta dan yau ta tashi da ƙarfin Jiki rahmar Allah kenan, tana azumin amman yau kuma tana jin kuzari sosai ajikinta Bayan ta wanke toilet ɗinta Ta Cire Zanin gadon ta, takai Cikin Injin wanki ta sauya wani Gyaran ɗakin nata tayi sosai ta tattare kayanta dasu kai datti duk ta fitar dasu Ta kunna turaren ƙamshi a ɗakin nata.
Aliyu fita yayi ɗakin Ammi tana bacci se kawai ya fita suka wuce dutse shida Musa.
Gidan Ammi wuni akai bacci kamar babu ɗan adam agidan Farha gajiya tayi da kwanciya ta fita sashin hajja anan tayi sallar la'asar sannan suka rankayo tare kitchen suka shiga Ƙosai suka fara soyawa sannan suka soya dankali Sannan sukai farfesu suka dafa ruwan shayi Nan da nan suka haɗa dukkan abin da za'ai buɗa baki dashi wajan magariba kuma akaita shigo dasu kankana gwanda lemo ayaba Hajja tasa farha Yayyanka su acikin ƙaton Bowl ko wanne daban Farha ta gaji iya gajiya sabida a ƙalla sunyi kayan shan ruwa kusan kala goma hajja tana tsaye da Dabino a hannunta tana wankewa Farha ta ɗago ta dube ta.
"Wai hajja yanzu Kullum wannan aikin zamuyi har ƙarshen ramadan gaskiya zamu sha wahala"
Hajja tayi dariya tare da cewa
"A,a ai nan da ɗan lokaci ma zasu wuce saudiya umara Dukka gidan ina ga Salama ce kaɗai wannan karon babu amman gaba ɗayan su zasu tafi"
Farha ta jinjina kai cikin mamaki tace.
"To Ku kuma ina zaku je?"
Hajja tace.
"Ni gida zan koma sauran ma'aikata ma duka gida zasu wuce se kuma ana gobe sallah zamu dawo sabida ana jibi sallah suke dawowa"
Farha ta jinjina kai batare data ce Komai ba sedai taji daɗin wannan tafiya tasu sabida Ko banza itama tasan zata je Gida ta zauna kafin su dawo.
Ana magariba suka kammala komai farha ta ɗauki kayan buɗa bakin ta taiwa hajja sallama tana shiga ɗakinta wanka da alwala ta ɗauro tazo tayi sallah tunda ta idar da sallah ta kwanta a ƙasan Tiles bayan ta naɗe carpet ɗin ɗakinta ruwa kaɗai take ta sha dan jitayi bata sha'awar Komai haka taita malelekuwa a ƙasa sanyin wajan yana ratsata ba ƙaramin daɗi take jiba dan har wani Lumshe idanu take yi.
Can bayan sallar Isha'i wanda a ƙa'ida se Lokacin mutan gidan suke cin abinci sabida idan an sha ruwa Dabino da ruwa kaɗai suke amfani dashi Safna ta shigo ɗakin Farha tare da ce mata tazo Inji Ammi farha ta Ɗauki hajib ta saka gaba ɗaya iyalin Gidan suna kan dining kowa yana Cin abinci Ta Tsugunna tana gaishe da Ammi wadda ta kalli Farha da kulawa tare da ce mata.
"Ke kin sha ruwan naki ne?"
Farha ta ɗaga kai tana wasa da yatsun hannunta.
"Yawwa to masha Allah, Nan da wajan jibi haka ko ranar sati zamu tafi umara ki haɗa kayanki waje ɗaya Idan Baba yazo zewa Musa magana seki Je gida ana jibi sallah zaki dawo kafin nan Mun dawo In sha Allah"
Farha ta saki fuska sosai tana dariyar Farin ciki kafin tace.
"Dama Ammi komai nawa ma a haɗe yake ko yau ma zamu iya tafiya gidan Ko musa be zoba Ni zan gane hanyar Gidan Namu"
Ammi tace.
"To shikenan tashi kije sena neme ki"
Miƙewa tayi zata shiga ɗakinta Bashir ya kirata.
Ta ƙarasa gaban shi Turo mata Plate yayi tare da cewa ta zuba masa Soyayyan dankalin dake gaban shi ta ɗauki Plate ɗin ta zuba mai ta tura masa gaban shi ta lura daga Matar yayansu har wannan Budurwar se harararta suke taɓe baki tayi zata Juya ta koma ƙamshin farfesun da sakina keci ya doki hancin ta Wanda nan da nan cikinta ya hautsine da sauri tabar wajan tana zuwa ɗaki ta dinga sheƙa amai wanda shine ya galabaitar da ita a bakin Toilet ta kwanta a ƙasan tiles tana mayar da Numfashi dan bata da Kuzari ko kaɗan.
Lokacin daya shiga Gidan Alhaji Hamishi ana kiran sallar magariba...........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 73*
Sabida haka sauka sukai daga mota suka shiga cikin wani ƙaramin masallaci dake Ƙofar gidan suka yi sallar magariba Ya miƙawa Musa dabino Wanda ya ɗauko daga cikin aljihun farar shaddar dake Jikinsa a tare da Musa suka shiga cikin Gidan marigayi Alhaji Hamishi a Madaidaicin Falon gidan suka tarar da Momcy a zaune tana shan Kunun Buɗa baki zama sukai a ƙasan carpet Momcy tayi juyin duniya akan su tashi su zauna a saman kujera Amman suka ƙi tashi tayi ta shiga Kitchen tray ta fito dashi wanda ke shaƙe da kayan ciye ciye ta dire a gabansu tana cewa.
"Nasan bakuyi buɗa baki ba ga ɗan abin Motsa baki nan"
Haɗa baki sukai wajan yi mata godiya Musa ya ɗauki kankana yana sha shiko Aliyu ruwan gorar faro ya ɗauka ya buɗe ya ɗaga seda ya shanye tas sannan yayi hamdala ga sarki Allah Ya dubi Momcy tare da cewa.
"Dafatan Kun sha ruwa lafiya" da kulawa tace "Alhamdulillahi" falon ya ɗauki shuru na wasu daƙiƙu Musa ya ɗauki Kankana a plate ya fita daga falon dan ya basu guri Falon ya rage daga Aliyu se Momcy Aliyu ne ya katse shurun su da cewa.
"Yanzu yaya ake ciki ne da maganar Hanan ɗin naso nazo to ban sami Lokaci ba ga shi zan je Umara To bana son na kuma tafiya Kuma na dawo ban zoba yanzu ma haka daga Dutse Muke ko gida banje ba"
Momcy ta ɗan kurɓi Kununta kafin ta aje a center table ta fuskanci Aliyu.
Cikin damuwa tace.
"Kaga shidai wanda yake zuwa wajanta abokin Shashancin nata Wallahi data masa maganar ya turo yaƙi dan da faɗa ma suka rabu amman bari kaji daga bakin ta"
Momcy ta soma kiran Hanan wadda take ɗaki a kwance ko ruwa bata sha ba se aikin kuka take idanunta sunyi jajir sabida kuka duk sun Kumbura Hijabi ta saka ta fito falon Tunda ta doso Yaɗan zuba mata ido kafin ya kawar yana kallon ƙasa ta durƙusa a gabanshi Murya a dashe tace.
"Yaya Aliyu ina yini An sha ruwa lafiya?" a taƙaice yace "Lafiya" daga haka ta zauna acan nesa dashi tayi Shuru Momcy ganin Bai ce komai ba yasa tace "To seki gaya masa yadda kuka yi da saurayin naki"
Kuka Hanan ta saka mai fitar sauti tana fyace majina kafin tace.
"Yaya Aliyu kace na fitar da Mijin aure sedai wanda na ƙwallafa raina akan shi tashi ɗaya ya gujeni, Kuma shine silar darwatsa mini rayuwata"
Aliyu ya ɗago da mamaki ya tallafi Haɓarsa yana kallonta kafin yace mata.
"Kamar yaya kenan?"
Hanan ta share hawaye tace.
"Tun bayan rasuwar Dady Na Haɗu da Anwar a school ɗinmu Anwar class mate ɗinmu ne tun bana kulashi har yazo ya cusa mini soyayyarshi anwar ba wani ɗan masu dashi bane amman ni da yake ina son shi sam ban damu ba haka nacigaba da soyayya da anwar wanda Harta kai ga yana taɓa Min Jikina batare da wata shakka ba inna nuna masa Ɓacin raina se yace ai aurata zeyi har takai ta kawo da ina wa Momcy ƙaryar zamuyi Karatu da ƙawayena in fita naje na haɗu da Anwar Kuɗinmu da momcy ta sakar mana dashi nake wa Anwar Hidima harta kai nike biya mai kuɗin makaranta kullum burinmu muyi aure dashi Baya da geji da jikina Sex ne kaɗai bai taɓa yi dani amman a hankali na lura anwar na ɗan shaye shaye wanda shine ya koya min afa ƙwaya wadda nake sha nai ta bacci batare da Momcy ta lura da halin da nake Ciki ba Lokaci ɗaya dana buƙaci Anwar yazo muyi aure nina yarda Komai ma zan masa inze aure ni buɗar bakin sa se yace ai ko ɗan iska tagari yake nema, yanzu ko wayata baya ɗagawa Yama yi Blocking ɗina dama Tunda muka gama school ganina dashi yayi wahala"
Ta faɗa tana wani irin gunjin kuka.
Aliyu yaja tsaki yafi sau goma da ɓacin rai a saman fuskar shi yace.
"Kin cuci kanki hanan mai yasa wasu mazan suke cutar mata ne da zasu aure su suyi ta more albarkatun Jikinsu, dama akwai namijin daze zo maki da maganar taɓa Jikinki kuma ki yarda auren ki zeyi har ma ya koya Miki shan ƙwaya ki yarda son ki yake sabida ke mahaukaciya ce to wallahi wannan Mutumin ya cuce ci kuma kema Momcy kinyi Kuskure mai yasa baki lura da shige da ficen ta baki lura da yanayin ta Kai innalillahi wa'innah ilaihirraju"un"
Aliyu ya faɗa da wani irin tashin hankali.
Momcy kuka Hanan kuka an rasa mai rarrashin wani acikinsu.
"Tabbas nayi kuskure Aliyu wallahi hankalina da tunanina bai taɓa kaini ga na gano Lamarin hanan ba seda abun ya soma ƙwaɓewa Maƙota na suka fara nausar dani halin da take Ciki ranar dana soma shiga ɗakin hanan na ganta cikin halin maye tana surutai wallahi ban rintsa ba, Kuma abin takaicin har yanzu shi saurayin nata bai taɓa zuwa gidannan ba sedai ita ta ɗauki Mota ta fita suje su haɗu wanda ni ƙarya take shatamin tace Min wai karatun jarrabawa zasuyi da ƙawayenta babban kuskuren danai shine kuɗin dana sakarwa Hanan bata da geji duk Adadin kuɗin da zata ɗiba ban taɓa Hanata ba sabida ina ganin nasu ne ashe ita tana can tana Bawa saurayi suna shaye shaye suna shashancin su kaga yanzu da maganar aure tazo ai ya gudu yama kashe wayoyin sa"
Shuru Aliyu yayi aranshi yana jin Tsananin takaicin halin da hanan ta shiga a sanadin soyayya wai yaushe ne ƴammata zasu farga daga baccin da suke yi ne wani wawan ne zeje wajan mace ya gama taɓeta sannan ya aureta ai in kika bashi jikinki zargin ki zeyi ya ɗauka kowa ma haka yake miki.
"Bani Number wayar shi"
Aliyu ya faɗa yana zaro wayar shi daga aljihun Rigarshi Hanan daka ta dinga karanto mai Number ɗin Anwar Ringing ɗaya Anwar ya ɗaga Aliyu yayi sallama Anwar ya amsa.
"Nine yayan Hanan yarinyar daka ɓatawa Lokaci akan ƙaryar zaka aureta ina son ka turo iyayenka Ni zan baka aiki kuma zan baka gida zan maka lefe sadaki kaɗai Muke Buƙata in ka amince ko gobe ma muna jirank"
Dariya Anwar yayi tare da cewa
"Wasan yara ma kenan, Yarinyar da bata jin maganar mahaifiyarta a wani labarin ma ance baƙin cikinta ne ya kashe ubanta yarinyar da take zuwa ɗakina Duk abin da nake so A tare da ita na samu duk abin da yake Burgeni na ganshi Duk abin da ke tsolen ido na taɓa to me yayi saura Ta yaya zan ɗauko baragurbi na saka cikin Zuri'ata iyayena ma ba zasu yarda ba yanzu haka akwai yarinyar da nake so ɗanya jagwab Zan aura mai tarbiya ƴar manyan Mutane"
Daga haka Anwar ya kashe wayar yabar Aliyu sake da baki.
Kuka Hanan take sabida ta gama Jin komai da Anwar ya faɗa.
"Wallahi yaya ban taɓa zina ba nasan dai yana taɓamin Jikina........
Ai ɓata ƙarasa maganar ba Aliyu ya daka mata wata uwar tsawa wadda ba Hanan ba hatta Momcy seda ta Firgita.
"Kin cuci kanki kin cuci rayuwarki na tausaya miki wannan masifa ita zatai ta Bin rayuwarki Sabida darajar mahaifinki Kinsan ance baka alkairi ka lalace baka sharri ka gama lafiya to Kinci arziƙin mahaifin ki Ni zan samo miki Mijin aure daga yanzu ki fara shiri koda yaushe zaki iya ganin wanda zaki aura sauran Ki nuna masa ke shasha sha ce"
Daga haka ya miƙe beko yi musu sallama ba yabar falon.
A mota ya tarar da musa ya shiga Musa yaja suka tafi Gida........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 74*
Tunda ya shiga mota ƙasa yayi da kanshi baƙin ciki na nausar zuciyar shi bai ɗago da kanshi ba seda yaji Musa yana ce masa.
"Yallaɓai Mun iso gida" Buɗe murfin motar yayi ya fita Yana tafe yana dafe kanshi har ya ƙarasa part Ɗinshi yanayin shi kaɗai mami ta kalla tasha Jinin jikinta tunda ta masa sannu ta Kama kanta ya haye saman shi kwanciya yayi sabida kanshi ciwo yake masa