Showing 51001 words to 54000 words out of 150033 words

Chapter 18 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

kana ta fita daga ɗakin

Minti kaɗan ta dawo ɗakin da ƙaton tray a hannun ta ajewa tayi a gaban farha salma ta dubi farha

"Ci abincin amman ki fara shan tea ɗin kafin kici abincin sabida ya warware miki hanjin cikin ki"
Farha ta ɗaga Cup ɗin tea ɗin ta sanya spoon tana juyawa ta ɗaga shi tana kurɓa kamar maɗaci take jin bakin ta dan kwata kwata babu ɗanɗano ta kurɓi ɗaya biyu uku sai amai ya biyo baya awajan ta dinga kwara amai tana riƙe ciki salma nata jera mata sannu anan wajan ta kwanta tana numfashi salma ta gyara wajan ta taimaka mata suka je toilet ta wanke mata Jikinta saman gadon salma tace tahau jikinta se rawa yake zazzaɓi ne ya rufe ta ganin ta galabaita da yawa yasa salma ta shiga ɗaki ta ɗauko allura da drip ta tsira acikin drip ɗin ta haɗa ta saka mata Allurar harda ta bacci aciki salma ta rufe mata jikinta da bargo bayan bacci ya ɗauke ta taja mata ƙofar tabar ɗakin.

Se wajan la'asar ruwan ya ƙare salma ta cire mata har lokacin Bacci take Bini bini salma zata leƙa amman har aka kira Magariba bata tashi ba salma na idar da sallar magariba taga kiran Aliyu.
Ta ɗaga cikin ladabi tayi sallama tana gaishe dashi.
Cikin taushin muryashi yace wa salma.
"I'm sorry salma naga kiran ki, But kin san kan ƴan mazan a wajan nema ɗaukar zafi yake hope kuna lafiya yaya su Babana?"
Salma tayi murmushi.
"Lah dama nayi zaton haka Yaya Suna lafiya Allah ya taimaka, dan Allah yaya numbern musa zaka tura mini in ba damuwa"
Batare da tunanin komai ba dama shi bai da yawan bincike akan lamarin wani ko ya saka idanu akan Harkar da ba'a saka shi acikin taba.
Yace mata.
"Okey ba matsala amman yanzu haka na fito daga masallaci zan je gida zuwa anjima zan tura maki"
Salma tai saurin cewa.
"Yaya ko kawai bara kaji maganar wannan ƙanwar tashi ce"
Da rashin gane inda ta dosa yace mata.
"Wa kike nufi kenan?"..............
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*








Ya matsa kusa da farha kaɗan yaɗan ja bargon ya ɗora hannun shi a saman goshinta babu zafi a goshin nata.
Buɗe Idanunta tayi wanda har Lokacin bai ɗauke hannun shi a goshin nata ba.
Gabanta ya faɗi ta mayar da idanun ta Lumshe.
"Sannu"
Ya faɗa a hankali.
Ta yunƙura zata tashi jiri ya ɗebe ta, ta koma ta kwanta tana jan numfashi hannu ya sanya ya ɗagota ya jinginar da ita ajikin Bango idanunta har Lokacin a rufe yake.
"Kin yi sallah me zaki ci?"
Duka ya jefa mata tambayoyin.
Banza tayi masa dan yanzu bata son magana mai tsaho ta dinga haɗasu sabida ta fahimci ya iya danƙara baƙar magana.
"Wai ke kurma ce ina miki magana kin min banza"
Ya faɗa a hasale.
Adaidai nan salma ta shigo.
"Afuwan yaya ina hidimar babansu ne, yawwa Kin tashi ki ƙoƙari kiyo alwala ki sallah se kici abinci Yaya ina zuwa dan Allah ina haɗawa Baban su abinci ne"
Bai mata magana ba ta fita farha ta miƙe ƙafafunta ta dafa bango ta yunƙura ta shiga toilet ya bita da kallo wato yau ba bakin tsiwa tana rashin lafiya.
Tayo alwalar ta fito juya ta kuma ɗibarta zata faɗi da sauri ya miƙe ya tarota jikinsa kwanciya tayi a saman Ƙirjinsa tana jan numfashi ya kamata har zuwa Tsakiyar ɗakin zamewa tayi daga jikinsa ta zauna a ƙasan carpet tana zubo hawaye.

Ya miƙo mata hijab ɗinta.
"In ba zaki iya tashi ba kiyi sallar a zaune mana"
Ya faɗa mata cikin kulawa.
Ta amshi Hijabin ta saka ajikinta a zaune tayi sallar tana idarwa yace mata

"To me zakici Mu wuce gida"
Kuka ta saka tana rufe fuskarta.
"Ni ka barni anan gidan ni bazan koma gidan kuba"
Shi dariya ma abin ya bashi Ya jingina da bango yana tsaye akanta yana kallonta.

"To anan zaki ta zama bakya ganin itama gidan mijin tane nan waya gaya miki ana gudun Gidan Miji?"
Ya faɗa can ƙasan maƙoshin sa.
"Ni na haƙura da auren ai dama nice na ce ina son ka"
Da sauri yace.
"Yan zufa?"
Tana kuka tace masa.
"Na dena son naka na haƙura koka kaini gida koka barni anan amman na haƙura dakai"
Aliyu dariya yayi sosai har da riƙe ciki.
"Oh fatima kenan danja wutar baya, Ai ƙarya kike kice bakya sona duk bakin daya furta so yazo yace Ƙi to ɓacin rai ne Ni ɗindai ne bana son ki tunda ke kinji kin gani kina sona a haka seki ta haƙuri dani"
Kukan ta ya ƙara ƙarfi fiye dana da.
"To nima nace bana son ka ko ana so dole ne
Ta faɗa tana cigaba da kukan....

Arewabook autarmanya
Paidbook 500 naira into 0078174806 sterling bank evidance of payment 09022260850

https://www.arewabooks.com/chapter?id=6509e2f03057a0e54cceafe1





*RABO YA RANTSE 38*

Aliyu da ranshi ya ɓaci na jiran data saka yake mata ya ɗago yana hangota tana tawowa tsaki yaja ya kunna motar ya buɗe mata kusa dashi harta ƙaraso kuka take kanta a sunkuye da ledar da salma ta bata a hannunta


Zama tayi taja murfin motar ta ɗora kanta a saman cinyarta se kuka take Aliyu ya kunna Motar suka bar Gidan.
Duk yadda ƙarfin radio ya cika motar Hakan be saka yaji sautin kukanta ya ragu ba tsaki yaja a karo na barkatai sam ya tsani kuka a rayuwar shi yaɗan rage speed ɗin motar ya juyo yana kallonta hannun shi riƙe da sitiyarin Motar.
"Wai ke wace irin mutum ce kita wahalar da kanki da koke koke wanda nida ban sanshi dake ba amman yanzu kin koye shi kullum idanun ki cikin kuka me yasa hakan?"
Shuru tayi masa wanda ya ƙara fusata shi aguje yaja motar bai kuma sake yi mata magana ba sai faman Huci yake ta fahimci shurun data masa ne ya fusata shi hakan yayi mata daɗi har ranta ..........
Arewabooks autarmanya
Paidbook 500 naira in to 0078174806 sterling bank evidance of payment 09022260850

https://www.arewabooks.com/chapter?id=650af5e90d776a5748dfe4b4
*A LOVE STORY 39*

Da sauri ta ɗago idanunta ta kalle shi wanda shima ya zuba mata nasa idanun gaba ɗaya sunƙi ɗauke idanun su akan na junan su kuma kowa akwai tunanin da yake saƙawa acikin zuciyar shi A hankali ta zare idanunta daga cikin nashi wanda shi kuma har tallafe fuska yayi yana kallonta kamar ya sami tv ga kuma hannunta daya damƙe mata wanda har ya fara mata zafi sabida riƙon tsauri yayi mata.
A hankali sautin Muryar shi yake fita inda yake ce mata.
"Tell me what he said to you that bothers you in your heart?" ya faɗa cikin ƙaramin sauti mai kama da yana mata raɗa.
Kanta ta kawar sabida kusancin su yayi yawa sosai.
Ta sanya hannu tana share hawayen ta.
Ƙasa ƙasa ya kuma ce mata.
"Tunda ba zaki gaya min ba shikenan, Amman wannan kukan ina son ki rage shi koda baki dena ba sabida wani idan ya gani se yace min ina cutar dake kuma nina san ban maki komai ba Ɓata min raina ma da kikai wanda shine dalilin aure na dake bai saka na cutar dake ba"
Ya faɗa with full Confidence, zuba masa ido tayi san kan shi yayi yawa kafin a hankali tace.
"Shi ai laifi tudu ne, Meye dan kaso kanka cuta kuma tana wa nidai na bar mutum da Allah yana madakata yana kallon kowa"
Bakinta ya kama da hannunshi ya matse wanda har hakan yasa ta saki Ƙara yaja leɓanta na ƙasa da ƙarfi.
"Ko kaɗan fatima baki da kunya wannan bakin zan koya masa hankali, shike nan dai koma me zaki ce ki ce I have no problem with that, tunda dai Allah ne me sheda duk haƙƙin ki ina ƙoƙari wurin sauke shi, Har ɗaki na kawo maki abinci amman dan baki da kirki baki taɓa ba yanzu Baki da lafiya na bibiyeki akan mai zakici nan ma ban isa kin gaya min ba, In ma dan kwanan kine bana baki hakkin ki tanan so mamy ce bata nan yau amman ta dawo daga yau zan raba ma ko wacce nata kwanan there is no problem"
Ya faɗa har lokacin riƙe yake da ƙasan leɓanta.
Ture masa hannu tayi da nata hannun ta zumɓura baki gaba


"Kai ne kake tunanin wannan Ni kam na barwa matarka har abada bana buƙatar kwana da ko wani gardi a ɗakina duk da tsoron da nake ji amman na yafe nida nazo zaman wucin gadi wallahi ina samun hanya sedai ka buɗe ido kaga wayam"

Murmushi ya sauke.
"Fatima nine gardin kenan?"
Ya faɗa yana zuba mata ido.
"Oho ma wanda ya tsargu dashi nake"
Ta faɗa tana hararar shi Murmushi ya kuma saki wato yarinyar ba zatai laushi ba rashin kunya a jinin ta yake Ko babba yana shakkar kallon idanun shi ya faɗi magana amman ita hankali kwance lafiyar Allah take maganarta babu alamar tsoro a tare da ita.

"Shikenan tunda kince haka idan ke kin yafe ni ban yafe ba kuma ki fara lissafi tabbas zanzo ɗakin ki kuma zan baki mamaki wannan rashin Kunyar taki sekin yi nadamar yinta"
Ya faɗa yana ficewa daga motar.

Ita mamaki ma ya bata tasan kawai zance ne ta yaya ze iya zuwa wajanta ya kwana yabar matarshi bayan kuma babu wanda yasan shi Mijinta ne da alama har mahaifiyar shi bata sani ba ta fahimci yana shakkar mahaifiyar shi yana gudun ɓacin ranta sosai taɓe baki tayi kome yasa baya son asan ita matar shice oho ko me yasa ya nemi ya ɓoye auren shi da ita Murmushi tayi ganin yadda ya zuba mata idanu ɗazu kamar tsohon maye Shuru da ɗaure Fuska yana masa kyau sedai ta kula baya son rashin kunyar da take masa ita kuma da ita take ɓata masa rai sannan kuma ta lura bamai yawan son magana bane da alamun ma ita ɗin ma da ƙyar yake mata maganar.

Lumshe idanu tayi tana shaƙar Ƙamshin turaren daya bar mata a cikin Motar Allah ya sani tana son wannan bawa nashi ita kanta har mamakin son da take mashi take yi ta zaɓi tana ƙuntata masa ne ta hanyar yi mai rashin Kunya dan ta dinga saka shi magana Kuma duk abin da yay mata bata riƙe shi aranta ba sabida soyayyar shi data makantar da ita tabbas so ɗaya tak tana ma bawan Allah.

"When you finish thinking about me, come out, I'm waiting for you" taji yo muryar shi ya leƙo da kanshi cikin motar dama tasan baze iya tafiya ya barta ba sabida yana tunanin kada ta gudu.
Da sauri ya ɗaga kanshi daga cikin Motar ita kuma ta buɗe murfin ta fito tana ƙunƙuni.
"Nifa ba tunanin ka nake ba ehe ina tuna salim ne bawan Allah me zuciyar zinare yana can ko yana wani hali oho"
Har yayi gaba ya juyo ya saki murmushin daya kassara zuciyarta Kafin yaɗan ranƙwafo Gefen Kunnenta a hankali ya raɗa mata.

"Daɗi na dake shashanci in ban da ke sakarai ce, ai ba shi zaki tunani ba iyayen ki zaki tuna da kika bijirema umarnin su sabida haka Think of a situation your parents were in before, sannan kuma ni ba ruwana in kina tunanin wani da aure na akanki ALLAH YA ISA"
Daga haka yayi tafiyar shi ya barta a dashe a wajan Ta faɗi maganar dan ta ƙuntata masa sabida tasan ko wani namiji yana da kishi.
To gashi Ƙilu taja bau ita bata saka masa takaici ba shiya gasa mata magana mai zafin gaske daga ƙarshe ya bita da Allah ya isa, kai wannan bawa yana da abubuwa na bam mamaki idan ya danƙaro maka magana sai ka rantse Goyon gwauro ne wanda Namiji ya raine shi ba mace ba ya iya baƙar magana wadda zata sanyaka kaji takaici kaji damuwa kaji baƙin ciki lallai matar shi tana haƙuri dashi.
Haka taja ƙafafunta da suka mata nauyi tabi bayan shi Tuni ya ɓacewa ganinta sabida yana da sauri sosai bata cimmasa ba se a ƙofar Falon yana ƙoƙarin Buɗewa ya shiga cikin falon Ammi..........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 40*

Fuskar shi ta saci kalla yadda taga ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba gabanta har faɗuwa yayi sosai ya ɗaure fuska ko kallonta kuma beyi ba taga ya buɗe ƙofar ya shiga cikin Falon take masa baya tayi tabi shi ciki Tsayawa tayi daga nesa tana hangen cikin falon wanda shikuma zuwa lokacin Ya riga da shiga ciki har ya zauna.

Jikinta a sanyaye take taka ƙafafunta harta ƙarasa cikin falon kanta a ƙasa batare data kalli mutanan dake zaune a falon ba ta wuce cikin ɗakin ta sum sum.

Aliyu ya kalli Ammi wadda ta ɗora ƙafarta a saman center table Hajjo tana danna mata da ruwan ɗumi.
"Ammi meya sami ƙafafun naki kuma?"
Ya faɗa mata cikin kulawa, Bata kalli inda yake ba ta kauda kanta Hajjo tayi dariya tare da cewa.
"Haba hajiya Ammi Uban ɗakina bai cancanci kiyi fushi dashi ba tunda bashi yakar zomon ba"
Ammi ta ɗagawa Hajjo hannu tana ɗauke ƙafarta Hajjo ta Ɗauki ruwan ɗumin tabar falon, Aliyu ya kuma matsowa gabanta jikin shi duk yayi sanyi murya ya kuma rage wa cikin sanyin jiki yace.
"Ammi badai fushi kike yi dani ba Allah ya baki haƙuri dan Allah ki yafe min ba danni ba"
Ammi dataji zuciyarta tayi sanyi na yadda taga yayi ɗin seta dube shi.

"Daga ina kake da alamun wannan yarinyar tare Kuke, Baba kada ka yaudare ni Ko son yarinyar nan kake nasan halin ka kamar yunwar Cikina"
Shafa kanshi yayi Batare da nuna wani tsoro Ko furgici a maganar ta Ammi ba yace.

"Ammi me kike faɗa haka? nikam ko yarinyar ma da kike magana akanta ban gama gano taba" ya faɗa lokacin da yake Ɗora hannunshi a ƙafar tata yaja yatsan wanda Ammi ta sanya ƙara tana rintse Idanu kawar da maganar yayi yana cewa

"Ammi wai garin yaya ne kika ji ciwo haka?"
Ta yarfe zufar data karyo mata tana kallon shi kafin tace.
"Tsautsayi ne wannan yarinyar bata wanke wa su auta toilet ba to ka gama jibgarsu duk ka jigata min yarana shine ni da kaina naje na wanke Musu harfa na gama ƙaddara Kumfa ta kwashe ni shine na faɗi kaga dai yadda ƙafa ta haye tayi sumtum"
Ammi ta faɗa a zatonta ze ƙara ganin laifin farha yace a sanadin ta mahaifiyar shi ta faɗi ga mamakin Ammi se jin muryar shi tayi yana cewa.

"Sajida safna ku zo nan dan ubanku"

Ya faɗa da ƙarfi kuma babu wasa acikin idanun shi.

Sum sum suka fito daga cikin ɗakin su sabida wunin yau suna ɗaki a kwance Suna ta wa ammi sangarta kala kala batare dasun tausaya mata akan halin da take ciki ba suka zube a gaban sa suna gaishe dashi.
Kawunan su ya haɗe waje ɗaya ya gwara ya sanya ƙafa ya taɗe su a gabansa suka faɗi suna kuka har goshin su ya fashe"Baba meye haka so kake ka kashe min su wai me yarannan sukai maka yau tunda ka tashi kake cin zalin ƴaƴana kada ka bari na maka baki akan su fa"
Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi amman ƙafarta tai mata nauyi sabida targaɗan data ji a yatsanta na ƙafa.

Ba tare daya bi takan maganar da Ammi take mishi ba ya miƙe tsaye ya zaro wata ƙatuwar baƙar waya naɗe ta yayi ya shiga lafta musu a gadon bayan su ba ji ba gani Ihu suke suna kiran "Yaya ba zamu sake ba yaya kayi mana afuwa mun tuba wayyo ammi zamu mutu" wannan ihu shiya fito da Farha daga ɗakinta tsorata tayi ganin yadda yake Jibgar su kamar Allah ya aiko shi da sauri Bashir dake shigowa falon ya ƙaraso wajan Aliyu yana Ƙoƙarin riƙe wayar hannun nashi Aliyu ya tankaɗa Bashir ze zuba masa wayar Bashir yayi tsalle yayi gefe yana yarfe hannu dan har ta same shi.

Sai da yaga sun kasa tashi sannan ya yarda wayar yana huci.
"Dan ubanku daga yau idan kuka sake barin ammi tayi muku wankin banɗaki sena karya ku daku saka mata ciwon ɓarin Jiki gwara na karya ku na watsar ai ba ku kaɗai ta haifa ba duk kuma abin da kuke a gidannan na sani tara ku nake, bakwa ganin mutuncin kowa har wasu na tunanin duk haka muke daga yau na dakatar da Hajjo kune zaku dinga girki na dakatar da mai gyaran falo kune zaku dinga gyarawa in na kamaku da saɓa dukkan sharuɗai na wallahi tallahi"
Ya matsa yatsun sa suka bada sautin ƙass da ƙarfi yayi ƙwafa yabar falon fuww kamar kububuwa.

Bashir da shigowar shi kenan Garin ya wuce daga wajan shima Ɓangaran shi ya nufa wanda yake Kusa da falon Ammi ya aje jakar shi ya shiga wanka batare daya bi takan abin da ya gani ba dan yasan ba mamaki laifi su safna sukai wa Ya Ali, wanda shi kam tsoro ya hanashi magana.

Ammi tallafe kumatu tayi tana jin zuciyarta na mata zafi bada ban kukan uwa bala'i bane ga ɗanta yau dase tayi kuka harta godewa Allah da sauri ta isa gabansu tana ƙoƙarin janyo su jikinta "Ni Ammi kada ki taɓani ai kina kallo yana dukan mu amman baki magana ba kamar tsoron shi kike ji" cewar safna babu wata tarbiya acikin maganar tata Ammi jada baya tayi sabida yanayin safna daya bata tsoro se kuka suke kamar ransu ze fita kafin su Miƙe suna jan ƙafafu sukai cikin ɗakunansu.

Farha da hawayen tsoro ya gama jiƙa mata fuska taja ƙofarta zata koma sabida tuni wani tsoron Aliyu ya cika mata cikinta wannan duka ai idan ita yayi wa shi kawai tata ta ƙare Mutuwa zata yi.

"Zonan munafukar Allah"
Taji yo muryar Ammi wadda take kallonta Jikinta yana rawa ta nufi gaban Ammi ta tsugunna.

Ammi ta dube ta.
"Da ina cikin kwanciyar hankalina baba baya shiga harkar ƙannen shi amman daga zuwan ki zaki raba min kan ƴaƴana munafuka bakar kadara wallahi bana ƙaunar ki mai baƙar fuska da muni kamar daran mutuwa idan ba da ban ta dalilin ki ba ta yaya duk haka zata faru Kuma ki buɗe Kunne da kyau Kijini ba Musa ne ya kawoki gidannan ba Ni ko uban musa ne ba ruwana akan ƴaƴana wallahi ko shi Musan zan iya ɓatawa dashi wannan duk wahalar da baba ya lissafa kece zaki Yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login