Showing 93001 words to 96000 words out of 150033 words

Chapter 32 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

Alhaji Hamishi Mutum mai Mutunci da sanin darajar ɗan Adam ya tausaya masa ya tallafi rayuwarshi Tabbas yana da dama baze taɓa barin Zuri'ar Alhaji Hamishi su shiga cikin masifa ba, Dan ita Momcy sanadin wannan matsala Kullum Acikin hawan Jini take idan ta faɗi ta rasu Yaya ƴaƴanta zasuyi Juyi kawai yake a gado da ƙyar yayi wanka yayi sallar Isha'i ya sanya jallabiya baƙa ya fita Ƙasa ya sauka tea kaɗai ya haɗa yasha Ya fita part ɗin Ammi.

Falon Ammi babu kowa bedroom ɗinta ya wuce anan ya sami sadiƙ da Bashir gaisawa sukai ya nemi Guri ya zauna yaɗan kalli Bashir daya ke danna waya.
"Ka shirya gobe zaka wuce Abuja sabida wannan karon kai zaka zauna kaga duk Umara zamu je"
Bashir ya ɓata fuska kamar zeyi kuka.
"Dan Allah Yaya Ali ka barni a kano wallahi takura nake a wani garin"
Aliyu ya harare shi tare da ce mashi.
"In ba zaka je ba kai ta zama"
Bashir fita yayi yana ƙananun maganganu Aliyu yayi Murmushi mai ciwo wani abun idan Bashir yana yi kawai mamaki yake Su da suka taso Tun kafin sukai shi suka san rayuwa.
Hira Ammi suke da sadiƙ wanda Aliyu bai saka baki acikin hirar tasu ba sema Pillow daya janyo ya kwanta Sadiƙ yaɗan dube shi.
"Wai baka da lafiya ne?" Ya ɗan kalli sadiƙ "Me kagani?" Sadiƙ yace "Naga sanyin ka na yau yafi na koda yaushe" Girgiza kai yayi bai ce komai ba.
Har wajan 9:00pm sadiƙ na ɗakin kafin daga bisani yayi musu sallama ya tafi ɗakin sa Ɗakin ya rage se shida Ammi.
"Yawwa dama maganar waccan yarinyar fati, Nayi mata magana akan zata je gida sabida zamu tafi umara tace koda kanta ma zata iya zuwa to Zaka bata wani abunne sabida Guzurin Mota Idan yaso Gobe seta tafi Nace mata ana jibi sallah ta dawo"
Shuru yayi mata kamar mai bacci.
"Baba wai ba magana nake maka ba kayi Min banza"
Ya ɗan ɗago.
"Ammi ni me zan bata babu wani abun da zan bata kawai ta tafin kamar yadda kika buƙata dama ai Koba dalilin Umara ba kina son ta tafi kamar yadda kika gaya min Jiya to kuma ga dalili mai ƙarfi nan ya taso to kinga dole ne taje"
Ya faɗa yana Rintse idanunshi kanshi ne ke sara masa ga gajiya ga bacci ga yunwa.
"Wallahi Baba idan ka cire maganar Umara data taso mana Bani da wata Hujja na tafiyarta ai nai maka alfarma ta zauna har bayan sallah, To ɗa na kowa ne zan barta anan ita ɗaya ne tare da masu gadi hajja tafiya zatai sauran ma'aikata tafiya zasu yi Dukkanmu Umara zamu tafi to dawa zata zauna In kuma kaga zamanta shiyafi alkairi ta zauna Ɗin ai ga ɗaki nan ga kayan abinci da komai"
Bece komai ba tunanin inda ze kai ta yake Yi acikin zuciyarsa dan koya sha giyar wake baze bari taje gidansu ba dan bai shirya hakan yanzu ba.

Miƙewa yayi yana cewa "Haka ne Ammi Duk yadda kikai shine daidai amman zan yi shawara da Musa" daga haka sallama yayi mata yabar ɗakin Falo ya fita ya shiga ɗakin farha Tana nan kwance a ƙasan tiles hatta zanin Jikinta ya kunce daga ita se under skirt se Birgima take tana Lumshe ido yaɗan Gyara tsaiwar shi akanta.

"Yanzu dan Allah idan sanyin nan yayi maki illah fa?" tashi tayi zaune ta gyara zaninta tana mai sannu da zuwa kafin ta shiga banɗaki ta wanko bakinta yana zaune a bakin gado tazo ta zauna a gaban shi.
"Ina farar?"
Shi yama mance da batun fara sam.
"Na manta wallahi amman zan sa a samo Miki ita kinci abinci?" ta girgiza kai tare da cewa "Dama so nake inna je gida na sa Ikram tai min ɗan malele" da rashin fahimta yace "Wace haka?" ɓata fuska tayi tare da cewa "ƙanwata mana ba gida zani ba Inji Ammi dama kayana suna haɗe" Murmushi yayi tare da watsa mata wani kallo "waye ze kaiki gidan a haka?" ta murguɗa mai baki tare da cewa "Ƙafata mana" wayar shi ya fito yana Dannata idanun shi yana kan wayar yace "Babu inda zaki zan kaiki Gidansu Hanan ki ɗan zauna kafin mu dawo" da mamakin shi seya ga ta ɓata rai tai kicin kicin da fuska "Idan ma ka kaini wallahi bazan zauna acan ba" yaɗan kalleta "Sabida me?" bata ce masa komai ba ya tashi ya buɗe wardrobe ɗinta kaf kayanta ya fito mata dasu ya zuba acikin Trolly ya kalleta "Tashi muje" Hijabi ta saka a fusace tayi hanyar waje Biyota yayi da kayan ta a hannunshi ya rufo Ƙofar Ɗakin nata ya aje kayan ya shiga ɗakin Ammi ya jima aciki kafin ya fito Tana gaba yana binta a baya har zuwa bakin Mota se Fushi take ya Buɗe mata gidan gaba ta shiga ya aje mata kayan a bayan motar ya shiga mazaunin driver Yayi revers ya Nufi gate suka fita daga gidan Se turo baki take yi gaba Ƙiris take Jira ta fashe shi dariya ma ta bashi A wani waje yayi parking ya fita se gashi da fara a ƙatuwar farar roba ya aje mata saman cinyarta yaja Motar suka cigaba da tafiya.
"Kici farar mana"
Hawaye ta soma tana Turo baki.
"Wai zafin rabuwa dani ne yasa kukan ko kuma me?"
Ji rainin hankali ta faɗa a ranta yasan Gidansu hanan daya ce mata shine ya ɓata mata rai sabida tun ranar data ji yana waya dasu a ɗakin ta tashiga tunanin meye alaƙarsu kuma Wacece ita a zuri'arsu amman dan ya rainata shine zece mata zafin rabuwa.
Ɗora hannunshi yayi a saman nata ya shiga matsawa.
"Ni bana son inga kina wannan Fushin Fisabilillahi Na barki ke kaɗai ne agida Ko kuma na barki Kije gidanku a halin da kike ciki ai se a zageni"
Harara ta ɓalla masa.
"To ba a gidan namu ka ɗaukoni ba, Ni wallahi babu gidan wasu da zani ai dama rannan ina ji kana Magana da Hanan ɗin kuma dana tambayi Hajja tace ba ƴar uwarku bace sabida ka rainani bani da daraja a idanunka shine zaka kaini Gidansu Budurwarka ka ajeni"
Seta rushe da kuka, Tunda yake bai taɓa dariya irin ta wannan Lokaci ba dramar Fatima kullum ƙaruwa take yau kuma ta lafta masa Hanan Jiya kuma tace wa Jamila kwartuwa lallai wannan harta fi mami Kishi.
Rage Gudun Motar yayi a hankali ya saka hannun shi ɗaya ya kamo fuskarta ya sa harshe yana lashe mata hawayen nata kafin ya ɗan lashi bakinta yana wani Lumshe ido ji yake kamar ya saki kan Motar ya janyota Jikinsa ya rarrasheta.
Yawun bakinta ta tara ta tofa mai a fuska tana cusa kanta a tsakanin Cinyarta tana wani irin kuka kashe Motar yayi tare dayin parking a gefen hanya ya ɗora yatsansa a wajan yawun nata data tofa masa ya goge shi tare da sanya yatsan a bakinsa ya tanɗe yawun ya ɗagata cak ya ɗora ta a saman cinyar shi.
"Fatima me yasa kike son ɗaga min hankalina ne inda nasan ma zaki shiga damuwa wallahi da fasa tafiyar nan zanyi ina Ƙoƙarin inga ban cutar dake ba amman ke Kullum cikin ɗaga min hankalina kike hanan ce Budurwata zaki bada sheda ne Kinsan yaya nake da ita harda zaki faɗi haka?"
Ya faɗa yana cusa fuskarshi a saman tata fuskar bai bata damar magana ba bakinsa ya Ɗora a saman laɓɓanta yana tsotsarsu kamar alewa ya ɗora hannunshi a saman Kirjinta yana Yamutsa su wani irin yanayi suka shiga mai wiyar misaltawa kafin ya ɗagata ya mayar saman Kujerar data ke kai ya ɗora mata farar a cinyarta ya tada motar gaba ɗaya Jikin farha ya saki wata irin tsumammiyar soyayyar shi ke ƙara nausarta Jita ke idan bashi ba zata iya rayuwa ba ta ko ina Yayi harya zarta tunani Motar shuru ta ɗauka shi bai mata magana ba itama bata ƙara magana ba Bata ɗago kanta ba se a bakin gate ɗin gidan daya ke faman zuba Horn mamaki ne ya kamata lokacin data ɗaga kanta ta gansu a ƙofar gidan Aunty salama.........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*A LOVE STORY 75*

Me gadi ya buɗe musu gate ɗin ya danna hancin motar shi cikin farfajiyar gidan yayi parking a wajan adana motoci ya kashe Motar ya ɗan dube ta fuskarshi cikin damuwa yace mata.
"Nan yayi miki zaki iya zama a gidan ƙanwata salama?"
Ƙasa tayi da idanunta tana jin hawaye na ƙoƙarin zubowa daga cikin su.
"Kin min shuru fatima, Ni akwai dalilin daya sa kika ga bana son na kaiki Gidanku, Amman idan kinga zuwa gidan ku ɗin yafi Miki sena juya na kaiki"
Lokacin da yayi maganar Muryarshi ta ɗan canza da alamun yana cikin damuwa shima.
"Yanzu kuma idan ka tafi se yaushe zaka dawo?"
Ya tsinci muryarta acikin dodon kunnen shi.
"Saura kwana ɗaya sallah Sabida ni sati Biyu kaɗai zanyi a saudia se na wuce Chaina se ana gobe sallah zan dawo In sha Allah"
Ga mamakin sa seya ga ta saka mai kuka! duk seya susuce ya tarairayo ta jikinsa.
"To kukan na menene wai fatima Lokaci ya ƙure kema dana samar Miki Visa ɗin mun tafi tare amman in sha Allah nayi miki alƙwari In Allah yasa kika sauka lafiya zan kaiki"
Da rashin gane abin da yake nufi na in Allah ya sauketa lafiya tace.
"Ni kenan zaka bari anan dan baka sona amman ka tafi da matar so"
Murmushi ya saki.
"Fatima kincika rigima bana son ki ɗaga hankalin ki, Akan tafiyata in ba haka ba zan tafi ne da damuwa acikin zuciyata zaki ƙara mini damuwa akan damuwa dan Allah ki kwantar Min da hankalinki"
Hannunta ta ɗora a saman Gemunshi tana ja tana hawaye.
"Shikenan ka dena min abin da kake min da daddare?"
Dariya yayi lallai akwai Ƙuruciya a tare da fatima Ya fuskanci gaɓuwa ce ajin farko.
"To shikenan kibi ni bashin duk wanda ban yiba idan na dawo zan rama miki" ta wani zaro ido "Tab ai sena Mutu ina zan iya ɗaukar Duka na kwanakin da kayi"
Dariya yayi tare da lakace mata Kumatunta.
"Fatima kenan kina da rikici Allah ya shirya min ke"
Daga haka ya ɗauki robar farar tata "Muje ciki to na tabbata zaki sami Nutsuwa agidan nan sabida Bani da matsala da salama, sannan Kuma ban yarda Ko bakin gate ki fito ba kuma ko falo zaki je ki tabbata Kin saka Hijabi zan bawa Musa Kayan sawa sabbi ya kawo Miki naga naki duk sun miki kaɗan ƴar lukuta ashe zaki ƙiba"
Ya faɗa yana dariya fita tayi daga Motar ta Jingina da Jikin motar ta ɗora kanta a saman motar seta fashe da sabon kuka ita fa da gaske Missing ɗin sa take Jitake kamar suje tare ɗan zaman da sukai dashi ta gano Mutum ne mai haƙuri kawaici tare da kyautatawa duk wanda yake tare dashi.
Ya zagayo gefenta hannu ya sanya ya zabga tagumi ya zuba mata ido.
Tai kuka sosai kafin taji Tattausar muryarshi wadda tai rauni sosai Kamar ba shiba.
"Kinga muje mota kawai na fasa tafiyar Tunda Ranki baya so na haƙura"
Kuma seta ga ya kama hannunta yana ƙoƙarin sakata acikin Motar da alamun da gaske yake mata maganar.
Tirjewa tayi taƙi tafiya sedai kuma bata dena kukan ba.
"Allah in baki shiga mota ba zan ɗaga ki cak na shigar dake, wai ya kike so nayi ne Kince Bakya son gidan su Hanan naƙi kaiki bayan gidan kamar Gidanmu yake tunda Mai gidan uban gidana ne amman kin fassara da wata manufa, Gidan Ammi kuma ba kowa duk ma'aikatan ta tafiya zasuyi na kawo ki gidan salama sabida kaf ƴaƴan Ammi babu wanda yakai ta haƙuri sauƙin kai sanin ya kamata nina tabbata zaki ji daɗin zama da ita ba alfahari ba, to tunda nan ɗin ma bai Miki ba Muje gidan nina fasa tafiyar na haƙura mu zauna tare"
Tunda ya ke maganar Kuka take ba zaka gano a wani yanayi yake maganar ba yanayin damuwa ko ɓacin rai ƙarya ne ka gano yanayin tunda suke dashi bata taɓa Jin yayi doguwar magana kamar wannan ba Ta yaya zata So kanta kawai ya fasa tafiyar sa wadda ya kashe Kuɗi akanta share hawaye tayi ta ɗan dube shi ya ƙura mata idanun shi da suka ɗan kaɗa sukai jajir abin ka da farin Mutum

"Muje to ni tayaya zance ka fasa tafiyarka bayan tun bani ka tsarata"
Ƙin tafiya yayi taga ya cigaba da tsaiwar shi.
"Da gaske nake miki tafiyar ma naji tafita a raina kawai Muje gida"
Maƙe kafaɗa tayi tana tuttura baki gaba.
Ya zuba mata ido gaskiya fatima yarinya ce ɗanya jagab yana ganin shagwaɓa da sangarta kala kala a hankali ya sunkuyo daidai Kunnenta ya raɗa mata.
"Wai kece auta ne a wajan su mama?"
Dariya tayi kuma ga hawaye tana cewa.
"Tab wallahi idan kaga ƙannena ma seka ce min ba yarinya bace Ni su Ruƙayya duk se sun goya ni fa"
Dariya yayi kaɗan yana sa hannu yana share mata hawayenta itama hannu tasa tai ɗage tana Goge mai saman idanun shi hannun nata ya kama ya sanya yatsanta a bakin shi yana tsotsa a hankali ta ɗora ɗayan hannun nata a saman sajen shi tana shafawa se kawai ta faɗa saman Ƙirjinshi ta rungume shi ya sunkuyo Sabida ya fita tsayi ya rungumeta sosai yana buga bayanta.
"Fatima kina sona da yawa Ko?"
Ya faɗa muryarshi tana rawa ta shiga girgiza kanta alamun da gaske tana son shi da yawa dan ita bata cikin masu Ƙunbiya Ƙunbiya duk abin da take so a fili take nuna wa Muryarta na rawa tace.
"Bamma san adadin soyayyar da nake maka, tunda na ɗora idanuna akan ka na kasa samun Nutsuwa duk abin da kai min bantaɓa Jin haushin kaba sabida ka taimaki zuciyata daka aureni koda zakana yanka naman jikina zanji daɗi ne, sabida ina bawa zuciyata abincin ta na fara son ka tun kafin nasan kai waye tun kafin nasan sunan ka tun kafin Nasan Halaiyar ka Ina son ka kai min alƙawari ba zaka taɓa Juya min baya ba sabida in ka Juya min baya wallahi rasa rayuwata Zanyi na rabu da iyayena saboda kai na rabu da masoyin daya soni Don Allah sabida kai nina tabbata akwai wani Ɓoyayyan lamari da Allah ya ƙaddara a tsakanina dakai"
Tana faɗin haka seta saka mai kuka tana cewa.
"Wannan tafiya taka Jin ta nake har raina Wannan tafiya taka batai Min ba amman bazan hana ka tafiya ba, Duk da na fuskanci akwai abin da kake Ɓoye mini a game da Gidanku wanda basu san ka aure ni ba dan Allah kada ka cutar da zuciyata kada ka wulaƙanta rayuwata Aliyu........
Ta kasa ƙarasa maganar sabida kukan daya ci ƙarfinta........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 77*

"Yaya a iya sanina ba wata alfarma a tsakanina dakai, Umarni ne kawai zaka ce min nayi abu kaza wanda in dai bai saɓawa Allah ba da gudu zan maka shi"
Salma ta faɗa cike da ƙarfin gwiwa, Aliyu yaɗan share zufar data tsatstsafo masa daga saman Goshin sa sannan yace mata.
"Salama wannan alfarma ta shallake dukkan wata alfarma wadda kike zato rufin asiri ne nazo Kimin a matsayina na ɗan uwanki na jini"
Ya faɗi maganar cikin raunin sa wanda ya bayyana ƙarara, wani irin tausayi ya bawa salma cikin kulawa salma tace masa.
"Yaya kome ye ka gaya min in sha Allahu baka da matsala dani"
Ya gyara zaman shi sosai ya soma yi mata magana.
"Salma ga amanar fatima nan na kawo Miki ita ki kula da ita kamar yadda zaki Kula dasu Safna In sha Allahu da zarar mun dawo zanzo na ɗauketa, sabida tana da lalura dole se an kula da ita sosai tana ɗauke da juna biyu amman bana son ita kanta tasan tana da cikin kuma kema bana son ki sanar da kowa, Ina son dai ki dinga lura da ita idan da damar hakan"
Jikin salma ne ya ɗauki rawa hankalinta yayi masifar tashi"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un" take faɗa a fili wato kowani ɗan adam akwai kalar tashi jarrabawar wato shi tashi kalar jarrabawar kenan to fyaɗe yayi wa ƴar mutane ta sami ciki Kome shi kuma sabida masifar son haihuwa ta Shiga ranshi yaƙi Zubar da cikin

"Amman yaya ban gane me kake nufi ba, Allah yasa ba zargin dana ɗarsa bane a zuciya ya tabbata yaya kada kayi mana haka Idan ma Ƙaddara ce ta faɗa muku Ni zanyi shahadar zubar da cikin kafin duniya ta sani dan na tabbata Ammi ma taji zata iya haɗiyar zuciya ta Mutu"
Salma ta faɗa muryarta tana wani irin rawa Tunda ta soma maganar ya kafeta da idanu Ranshi idan yayi dubu ya ɓaci sedai uzirin rashin sani da yayi wa salma shine yasa yaji zuciyarshi tana ƙasa tana sassautawa daga zafi da ƙunar da take masa.

"Wannan shine Kuskure na farko da zaki a rayuwarki, Koda wasa kada ki gangancin zubar Da cikin dake Jikin fatima dan fatima ba Lalata da ita nayi na mata ciki ba, Cikin jikinta na sunna ne Nine Mijinta wanda shedu da sadakina suka tabbatar da hakan"
Wata irin hantsila salma tayi ta Dafe ƙasan carpet ta zaro ido Jikinta yahau rawa lallai biri yayi kama da mutum, shiyasa lokacin data masa waya akan ya bata Number ɗin musa yaƙi yace kada ta bari ta tafi se gashi yazo.

"Yaya Ban gane ba wannan wani irin aure kayi wanda kaf ɗinmu bamu sani ba dan bani tunanin Ammi ma tasan wannan yarinyar matarka ce, Yaya mai yasa kayi hakan wanda ka san Wannan aure akwai matsala gagaruma acikin sa Wanda kuma gashi tun kafin aje ko ina rabo ya shiga tsakanin ku da ita"

salma duk ta faɗi maganar a hargitse.
Ya zuba mata ido yana jin dama bai gaya mata ba domin ya hango ruɗu kala kala a cikin idanunta koda yake dama haka ƴa mace take tana da ruɗewa ba kamar namiji ba wanda shine ze tsaya ya saurare ka har ma kuyi magana ta fahimta.
"To salama na ɗauki kayata na juya kenan dama wannan dalilin ne ai yasa nace Miki alfarma nake nema a wajan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login