Showing 6001 words to 9000 words out of 150033 words
Chapter 3 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
nafi son fuskata a haka nidai fatana Allah yasa yau na dace dan wallahi har na gaji da zirga zirga"
Ta ƙare maganar tana langwaɓar da kanta kamar wata ƙaramar yarinya koda yake in ba Sanin shekarunta kai ba tabbas zaka ɗauka irin ƴar ƙaramar yarinyar nan ce.
Umma takai duba wajan kofin kokon data ajewa farha wanda bata shaba tace mata.
"Ga kuma kokon naki baki sha ba, kin san dai ba wani kuɗin abinci zan baki ba iyakaci na baki Kuɗin mota daga nan zuwa ƙofar nasarawa nawa zasu kaikin?"
Farha tace.
"Ki bani ɗari biyar inda canji sai na dawo miki dasu, sannan kokon nawa ki rufen inna dawo zan siyo awara wajan Babar su Ruƙayya na haɗa naci yanzu sauri nake kada na makara"
Ta kai maganar tana buɗe handbag ɗinta.
"Kinga umma bani da canji a jakar tawa ma, bari nai sauri zan duba agogo a ɗakin su Ruƙayya tunda ba waya a hannuna yanzu tunda tawa ta faɗa rijiya shikenan"
Umma ta kunce Haɓar zaninta ta ciro Tsohuwar Ɗari biyar ta miƙowa Farha tana ce mata.
"Ni gwarama da wayar taki ta faɗa rijiyar sarai kin san abin magana bayawa kawun ku kaɗan, tunda ya saka dokar hana riƙe waya gwara kin haƙura in kinyi auren kya riƙe ta sannan kuma ki sauri yau karki kai yamma dan jiya baki je Islamiyar dare ba nan yazo kamar zai kawon duka sabida faɗa kin san dai halin sa"
Farha ta rufe handbag ɗinta, Bayan ta saka Kuɗin aciki.
"Umma duk su Ruƙayya da wayoyin su nima Salim yace zai kawon in ya dawo daga lagos nina san zagon ƙasa ake min a wajan kawu ba da ban an kai mai rahoto ba ina yasan ina da wata waya Munafukan banza"
Tana faɗin haka ta sanya kanta tabar ɗakin Ummah ta bita da addu'ar nasara.
Ta ɗaga labulan Ƙofar ɗakin su Ruƙayya Tana cewa.
"Mutanan ɗakin nan suna kusa a duba min agogo?"
Babar su Ruƙayya ta Ɗago kai tana wa Farha wani kallo.
"A,a manyan ma'aikata yau kuma ina aka cillah?"
Sarai farha tasan magana ta gaya mata sabida haka sai tace.
"Alkairi muka nufa kuma dashi zamu dawo ƙarfe nawa?"
Babarsu Ruƙayya ta Cije baki tana cewa.
"Ki shigo ki duba mana sai kace ɗakin baƙon kine"
Farha ta Ƙaraso cikin ɗakin ta kalli agogon dake bangon ɗakin sannan ta ƙarasa gaban madubin Su Ruƙayya ta ɗauki Hoda ta shafa ta fesa turare, dan su Ruƙayya ƴan kwalliya ne saɓanin ita da ko hodar ma sai dai ta bi ɗakunan su ta shafa tasu dan bata da ita sabida kwalliya sam bata dame taba.
"Keko farha ko ɗan caro white ɗinnan na zamani ba zaki siya ki goga ba wannan baƙi naki har yayi yawa ki duba kaf ƴaƴan gidannan Kamannin kawun ku suka ɗauko farare tas kyawawa amman ke wallahi kamar ƴar gudun hijira nina rasa mai salim ya gani a tare dake keba Tsaho ba keba wata cikar ƴa mace ba"
Babar su Ruƙayya kenan mai gaɓa gaɓa ita kai tsaye take Nuna ƙyashinta akan farha kuma duk maganar data fito daga bakinta haka zata faɗe ta babu batun ta tauna ta saɓanin Babar su Hadiza mace ƴar bariki sam ƙaryane ka gane inda ta dosa sai dai farha tana lura da kowacce kawai sai dai ka zauna da mutum ne da halin shi kuma ba komai bane ya tsone musu ido ba illah son da Salim yake mata suna ganin duk yafi mazan ƴaƴan su rufin asiri sai kuma karatun datai musamman wannan aiki da take nema ya tsone musu ido shiyasa ko wacce ta dage sai ƴarta tai karatu sabida suma su sami aiki in sun gama baƙin cikin su ƙiri ƙiri baya ɓuya Wanda suka haɗewa Umma kai su biyun ba'ajin kansu Gwarama ƴaƴan babu ruwansu ta wani bin amman wataran in iyayen suka zugo su haka za'aita bala'i agidan har sai kawu ya tsawatar in kuma aka shirya shikenan.
"To babar su Ruƙayya in dai kawu ne ya haife ni ai shikenan kyau kuma tunda su rukayya nada shi na bar musu suje suyi gasar shi"
Daga haka ta ɗaga labulan tabar ɗakin tana gab da kaiwa soro taci karo dasu humaira Ƙannenta ƴaƴan su babarsu rukayya suna dambe akan kwaɗan kwaki tsaki farha taja aranta tana takaicin wannan ɗabi'a ta yaran gidansu a kullum tana addu'ar Allah ya bata abin da zata wadata gidansu da Abinci.
Har takai bakin titi wannan takaici bai bar ranta ba Suke nan kullum cikin dambe akan abinci kamar wasu mayunwata har ƴan layi sun shaida su tana nan tsaye a bakin titi Allah ya bata adaidaita sukai ciniki dashi akan zai kai ta ƙofar nasarawa akan naira ɗari biyu tafiyar ba wahala sabida babu cunkoso a titi bayan ta sauka ta bashi kuɗin sa ya ciro canji ya bata layin gidan su ƙawarta shema'u ta shiga tana tafe tana sauri haka ta shiga gidansu shema'u ta tarar da ita Itama tana shiri tana ganinta ta washe baki.
"Ƴar halak yanzun nan ya gali yake maganarki dafatan dai kinzo da komai naki?"
Farha tai dariya.
"Da takarduna nake kwana fa a jaka sabida kiran kota kwana, ina mamanku?"
Shema'u tace
"Tana wajan aiki bara na masa magana sai mu tafi"
Shema'u ta faɗi tana ɗaukar mayafinta Jim kaɗan suka fito tare da Ya gali Farha ta rissuna ta gaishe dashi ya amsa yana sakin murmushi suka jera zuwa bakin titi ya samar musu adaidai ta zuwa Inda Gidan rediyon yake a titin audu baƙo way ne A bakin gate mai ɗan sahun ya sauke su suka bashi kuɗin shi, Farha ta kalli saman gate ɗin inda aka rubuta GARKUWA RADIO da manyan harufa ya gali ne agaba su kuma a bayan shi.
Haka suka shiga cikin gidan radion sun jima a zaune kafin suga Md ɗin wanda yace su shigo office ɗin shi bayan sun gaisa ya fara duban shema'u yana cewa yaga takardun nata ta miƙa mai sannan ya karɓi na Farha.
Ya jima yana duba takardun nasu kafin ya dubi Ya Gali.
"Gali kasan fa wannan tashar tamu sabuwa ce gaskiya muna buƙatar gogaggun ma'aikata waɗanda suka san kan aiki su waɗan nan yaran da alamu ma basu taɓa yin harkar ba"
Caraf farha tace.
"A,a wallahi lokacin da muke school an taɓa tura mu gidan radio kuma ba laifi mun sami gogewa a wani ɓangaran"
Md yayi murmushi kafin yace.
"To shikenan babu matsala In sha Allah gobe da safe ku dawo domin muyi muku screening, In mun sami abin da muke nema a tare daku shikenan"
Farha harda zamowa daga saman Kujerar da take zaune.
"Dan Allah ka taimaka mu sami aikin nan musammam ma ni dana ke ta zarya kaga yau zuwa na kusan uku kenan Ban sami ganin kaba, sai yau da Ya Gali yace mu tawo tare dashi"
Daga Md Har Ya Gali da shema'u dariya suka sanya mata sabida yadda tai kamar zatai kuka.
"Karki damu Fatimah Ko?"
Da sauri ta ɗaga kanta.
Sannan Managern director ɗin ya cigaba da cewa.
"Mudai fatan mu wannan tasha tamu ta sami karɓuwa ta ɗaukaka tai suna wannan shine burina"
Da sauri farha tace.
"Wallahi zamu yi iya yinmu ko kasuwa ka turani nikam zuwa zanyi"
Sosai aka ci dariyarta a wajan haka sukai sallama suka baro Office ɗinsa A bakin gate suka rabu Ya Gali ya basu kuɗin adaidaita shikuma ya tafi Inda zashi har suka rabu da shema'u dariya shema'u kewa farha sabida yadda tai ɗin kowa ya gani sai yaci dariya.
Bata damu ba ita dai burin ta Allah yasa ta sami wannan aiki haka ta wuce gida a bakin titi ta sauka ta ƙarasa Cikin layin su da ƙafa ga uwar ranar data ƙwalle sosai. *09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*006*
Idanunta Jajir ta shiga cikin gidansu da gudu ta suri buta tayi cikin banɗaki sai dai taja ta tsaya a ƙofar banɗakin sabida yadda ta tarar da Salima Ƴar ɗakin su Ruƙayya a saman masai tana kashi.
"Dallah ke salima ki maza ki fito kinje kin sami banɗaki kin zauna kamar ɗaki"
Cewar farha tana rawar diskon Fitsarin daya kama mata marar ta.
"Ba zata fito ɗin ba ai ba gidan Babanki bane ke ɗaya aikin banza aikin wofi Baki iska kin takura taba"
Cewar Habiba wadda take bin Ruƙayya tana bakin rariya tana wanki.
Farha dama mai jiran ƙiris juyowar da zatai ta ɗaga bokitin wankin Habiba ta zubar tare da wanka mata mari.
Wata ƙara Habiba ta saka wadda ta sanya sauran matan gidan Yowa kansu nan da nan dambe ya kaure da ƙyar aka shiga tsakaninsu.
Babarsu Ruƙayya data kama habiba masifa ta soma yi tana cewa.
"Ai ba habiba bace takar zomon haka kawai kinje yawon gantalinki kin fake da neman aiki ba nasara shine zaki huce masifar ki akan ƴata to kije Allah ya isa"
Halifa daya shigo gidan ɗan ɗakin su Ruƙayya ne shima kuma yayan farha ne a wajan uba Muzurai yahau yi yana tambayar ƙanwarsa mai akai mata take kuka! ƙarya da gaskiya Habiba take gaya masa nan da nan yayo kan farha wadda tai ɗammara da mayafinta tana girgiza jikinta Duka ya kawo mata.
Tai tsalle tayi baya tana cewa.
"Wallahi Halifa in ka taɓani sai na maka illah danni ba ƴar ɗakin ku bace shine zakuyo min taron dangi toni ɗaya ce amman gayya"
Umma ce ta fito da sauri ta kama hannun Farha sukai ɗaki Halifa na zagin farha Babarsu Ruƙayya nayi Habiba nayi dama haka al'adar ƴaƴan gidan da matan gidan take muddin ana faɗa kowa nasa yake karewa sai dai fa a wajene ƙaryarka ka taɓa guda ɗaya gaba ɗayansu sai sun rufu akanka amman acikin gida kamar zasu kashe kansu.
Huci farha take Tana faman Hawaye dama ita akwai saurin kuka in ranta yana ɓace magana ma bata iyayi har sai ta huce tukunna.
"Nace ki daina shiga sabgar yaran gidannan haka kawai ni ba zaki dinga jamin magana ba in ba dama ki wuce gidan Nafisa kawai ki kwana biyu ni bana son tashin hankali"
Farha taiwa umma shuru sai faman ajiyar zuciya take saki.
Kafin ta miƙe ta koma tsakar gidan fitsarin da yake cinta tayo ta ɗauro alwala ta dawo ɗaki.
Har lokacin Umma faɗa take ita dai ta Shige uwar ɗaka ta shinfiɗa darduma ta tayar da sallah, Kwanciyarta tai tana Jin takaicin abin da Habiba da su Halifa sukai mata.
Har wajan La'asar Umma tana leƙa ta kota tashi sabida bacci ne ya ɗauketa ba itace ta farka ba sai wajan magariba a gurguje tai sallah ta fito rumfar Umma ta tuɓe rigar dake jikinta tai saura daga ita sai under skirt taja shi saman ƙirjinta.
Umma data shigo ɗakin zata ɗauki kuka ta dubi Farha.
"Sai yanzu kika tashi? wai ba na hanaki wannan shigar banzar ba tashi kije ki saka kayan ki Kizo ki alwalar magariba ki shirin makarantar dare"
Turo bakinta tai gaba.
"Umma ni gaskiya yau ba zani dare ba sabida ban biya kuɗin wata ba, Malam Alhazai duka na zeyi a banza"
Umma tace mata.
"Bana ce zan bada kuɗin ba nidai tashi kije ki alwalar ga abincin kinan yau ko karyawa baki ba"
Tsananin tausayin umma ne ya kama Farha Umma uwa ce Jajirtacciya akan ƴaƴanta Duk wiya bata bari karatun su ita da Ikram ya salwanta saboda tace su Fa'iza basu yi ba dole ta tsaya akan su Farha Ga mazan su Fa'iza bama su ƙarfi bane duk wata fafutuka ta umma akan Ƴaƴan nata take dan wani bin har aike take bawa Farha takai musu gidajen su duk dan asirinsu ya rufu.
Ta fita tsakar gida bayan ta sanya Hijabi ta ɗebi ruwa ta watsa ajikinta sannan tayo alwala ta koma ɗaki taci abinci Tana kammala cin abincin ta fita tsakar gida bakin Murhun da Umma ke fama da wuta duk idanunta sunyi jajir na hayaƙin itace taimakawa umma tai har wutar ta kama sannan ta soma taimakon ta da tankaɗe sabida kwana biyu Kawu ya kawo abin girki wanda umma ce keda girkin a kwana biyun.
Sai da aka kira sallar magariba sannan ta koma ɗaki Lokacin ankawo wutar nepa sallah tayi bayan ta idar tai azkar ta ɗauko Hajabin dare Ta fito taiwa Umma sallama ta fita makaranta Harta mance ma da maganar Kuɗin wata sai da ta dawo ta karɓa sannan ta koma ƙarfe tara ake taso su tana Zuwa bakin ƙofar gidansu taga Salim zaune saman Babur ɗinsa yana zaman jiranta Da murna ta dube shi.
"Yaushe ka sauka bawan Allah? bara naje na aje kur'anina na dawo"
Gida ta shiga ta aje Jakarta sannan ta shaidawa Umma salim ne ya zo Ta ɗauki tabarma ta fita Ƙofar gida a dakalin Ƙofar gida ta shinfiɗa Tabarmar Salim ya zo ya sauna ta gaishe dashi.
Fuska a sake yace mata.
"Ɗazun nan na dawo sai sauri nake nazo naga Farin ciki na!"
Dariya tai tana rufe fuska Harga Allah tana son Salim kodan yadda yake Nuna mata soyayya mai cike da kulawa da tattali.
"Nidai nayi mamaki tunda a lissafi naji kace sai kayi sati naga kuma yau kwanan ka uku"
Murmushi yayi a karo na barkatai.
"Wallahi Farha ba zan iya kaiwa wannan lokacin ba, Shiyasa na dawo ga wayarki ma nazo miki da ita"
Ya faɗa yana ɗauko ledar wayar daga aljihunsa.
"A,a Salim kabar wayar nan kaga waccan ma Kawu sai da yayi faɗa Ka ajemin idan mukai aure ka bani"
Dariya yayi harda riƙe ciki.
"Idan banda abinki in mukai aure ai wadda tafi wannan zan saya miki, Ni zan sami kawu Na bashi haƙuri Ki riƙe wayar saboda tana taimaka mana wajan jin motsin junanmu"
Fafur Farha taƙi amsar wayar kuma ta hana Salim tunkarar kawu da batun ta riƙe wayar sabida tasan Halin kawu akan hakan zai iya saɓa mata.
Hira suke mai cike da so da ƙaunar Junansu Duk kuma maganar bai wuce akan Salim yana son ya turo Iyayen shi a kawo kuɗin auren su ba sai naci yake mata yana Kwantar da kanshi shidai Allah ya ɗora masa soyayyar Farha a zuciyar shi.
"Salim ka min haƙuri Gobe wannan gidan Radion suka ce muje nasan In sha Allah akwai nasara a zuwan namu Kaga zuwa sati na sama sai Muyi maganar zuwan iyayen naka Nafi son na riƙe aikina ne a hannu sabida ina gudun na aureka kace kai baka san zancen aikin ba"
Yadda tace hakan yabi sabida baya son Ɓacin ranta lallaɓata yake yi Sun kai har wajan ƙarfe Goma suna hira kafin ya mata sallama Dubu Biyar ya bata yace tai kuɗin Mota da ƙyar ta amsa ta shiga cikin Gida.
"Fatimah nifa nagaji da wannan gantalallan zancen naki koki cewa yaron nan ya turo kona sami uban nashi da kaina ai ba baƙona bane ba"
Cewar kawu wanda ya shigo gidan yanzu.
Muryarta cikin tsoro tace.
"Ai abin da yama kawo shi kenan yace in baka haƙuri zasu magana da Baban nashi"
Ta faɗa tana Addu'ar Allah yasa kada Kawu yace ƙarya take.
"To yanzu naji batu danni bana son ai min kallon ƙaranta"
Daga haka ya haska Fitilar shi ya shiga ɗaki saboda Lokacin an ɗauke wuta.
Da sanyin Jiki ta shiga ɗaki umma tana kallonta tace.
"Kin kyauta da kika wa Babanki ƙarya dan nasan ƙarya kike Salim mai jiran ƙiris kedai ki amfani da damarki kada ta wuce ki"
Farha ta kalli umma.
"Munyi magana dashi ai cikin wani satin zasu zo"
Daga haka tai ɗaki ta aje tabarmar Kuɗin ta miƙawa umma.
Umma tabi kuɗin da kallo kamar tana tsoronsu.
"Nifa bana son yawan amsar kuɗin bawan Allan nan taimakon daya miki ma lokacin kina makaranta kaɗai Allah ya saka mai da alkairi"
"Umma tun da shi ya bani yaya zanyi gobe kinga zamu koma screening kinga na sami na zaryar Mota"
Umma ta Ɗaga Filo ta aje kuɗin farha tai Uwar ɗaka ta haye gado ta kwanta bayan tayi sallar isha'i.
*************
Maman mami ta dubi mami bayan ta raka Ammi mota.
"Dole ki kuka Mami nima Dan zuciyata a dake take ne ace sau huɗu kana samun ciki yana ɓarewa babu wani dalili, Ni babban Burina ki haihu da wannan yaro daga nan ƙaryar Hajiya Amina ta ƙare"
Ta faɗa tana cije bakin ta.
"Mama nagaji ne wallahi Nima na matsu na haihu, wallahi duk biyayyar da nakewa Ammi dan dai kawai ban haihu bane Shasha sha suke mayar dani ita da ƴaƴanta nima sai na maida kaina kamar ban san mai nakeyi ba, Amman wallahi da zarar na haihu da Aliyu duk sai na rabasu sai na soke duk wata facaka da suke da dukiyar shi Ta mayar dashi saniyar tatsa duk wata lalurarta akan sa take ƙarewa Hatta Ƴan uwan shi Dashi suke gadara Lamɓo nake musu kada taga ita ta haɗa auren mu wallahi Sabo da kaza baze hana in yanka taba"
Maman mami ta saki dariya.
"To dama mai nace miki, Cewa nai ki mayar da kanki wawiya ki nuna duk abin da yake musu bai dame ki ba har Allah ya baki Ƴaƴa da ɗanta daga nan kashinta ya bushe, Haba Amina kinyi wauta tun da muka taso Mahaifinmu ya fifitaki akaina duk da mune ƴaƴan shi kaɗai a duniya Ya so mahaifiyarki fiye da tawa, Kika fini Da miji kika fini da ƴaƴa to ni kuma nai alƙwarin sai na ƙwace Goriba a hannun yaro Wannan Aliyun da ya zama garkuwarki sai na rabaki dashi wannan shine babban Burin daya sa Nai miki kwanton Ɓauna na Haddasa Auren Mami dashi"
Maman Mami ta faɗa tana wata irin dariya ta basawa.
Mami ta saki murmushi ta koma ta kwanta aranta tana jin soyayyar Aliyu mai tsanani tare da kishin dukkan Biyayya da Hidimar da yakewa Mahaifiyar shi da ƴan uwanshi sun mai dashi kamar bai san ciwon Kuɗin shiba....... *09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*007*
Washe gari Farha da wuri ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ja ta yafa baƙin mayafi ta fesa turare ta ɗauki handbag ɗinta ta dubi Umma wadda ta zuba mata ido tana kallon ta.
"Umma ni zan tafi ai min addu'a"
Umma ta dube ta da kulawa.
"Allah ya bada nasara, yau ma baki