Showing 60001 words to 63000 words out of 150033 words
Chapter 21 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
ɗin daya tashi ta koma ta zauna tana facing mirrow tai masa banza ɗakin yayi shuru har tsawon Mintinu ya rasa me yasa take ɗaure Fuska yau take masifa Duk se yaji ya damu ko wani abun ke damun ta ya Miƙe ya isa gabanta ya kamo hannunta.
"Ni nazo sallama ne zan tafi katsina inna kwana to in ban kwana ba yau zan dawo in sha Allah"
Ya ƙarasa gaban ƙofar ya zaro key ɗin ya cire guda ɗaya ya jefa aljihun sa "Ki dinga saka key a ƙofar nan ban yarda na ƙara turowa naji ta a buɗe ba sabida ɗakin kine kaɗai a falon nan kuma keyn ƙofar babbar falo ya lalace shima zan kawo mai gyara to Kina rufe Ƙofar ki" ya faɗa yana aje mata ɗayan key ɗin a saman madubin ta.
Idanunta ne yaɗan taru da hawaye.
"Katsina kuma? to Allah ya tsare"
Daga haka ta soma ƙoƙarin fita daga ɗakin.
Ya riƙota wannan ne karon farko daya rungumeta ajikinsa ƙamshin turaren shi ya kashe mata Jikinta.
"Menene zaki fita bayan baki Min addu'aba ummmh?"
Ya faɗa Lokacin da yake ɗago kanta ya zuba mata ido lumshe nata idanun tayi sabida ba zata iya jure kallon da yake mata ba gaba ɗaya ya kashe mata jikinta.
Kusanto da fuskar shi yake daidai tata ahankali ya furta.
"I kissed your lips" da ƙaramin sauti yayi mata maganar kamar yana mata raɗar magana, kafin ya tallafo kanta a hankali ya ƙara haɗeta da jikinsa sosai ya ɗora harshen sa a saman idanunta ya shiga zagayewa kafin ya gangaro dashi cikin bakinta Rufe bakin nata tayi gam taƙi Buɗe wa Muryar shi can ƙasa cikin maƙurar buƙata yace "Please fatima" yawani ja maganar kamar ze mata kuka Numfashi mai ƙarfi ta janyo kafin ta Buɗe masa bakin nata ya jefa harshen sa aciki ya soma tsotsar Harshenta da nashi harshen tamkar ya sami alewa har wani tanɗe baki yake kamar maye Goga mata ƙasumbar data cika Masa fuska yake gaba ɗaya tsigar Jikin Farha miƙewa tahau yi tana kuma shigewa Jikinsa kamar wadda takejin sanyi maƙale shi tayi gaba ɗaya ta shige Jikinshi seda ya gaji dan kanshi ya sakar mata harshen nata yaja da baya yana sakin Numfashi itako silalewa tayi ta faɗa saman gado tai ruf da ciki tana Sakin ajiyar zuciya.
Dafe kanshi yayi da sauri yabar ɗakin nata da jajayen idanunshi waɗanda sukai jajir kamar an watsa barkono acikinsu..............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 46*
Ƙarya ne ka gane wani yanayi Aliyu yake ciki sabida kamewar sa haka ya fita yana sauri ya shiga cikin wata farar mota mai kyau da tsari addu'a yayi yana fita daga gidan ya ɗauki hanyar shi, Bayan ya kashe dukkan wayoyin shi sabida Gudun yawan Kira.
Agigice yaya sadiya Yayarsu Farha ta faɗo gidansu farha idanu jajir da alamu ma kanta a juye yake ba itace ta kawo kanta gidan ba aiko tana shiga tsakar Gidan ta zube nan da nan ta soma iska tana buge buge tana Ihu Hankalin Umma a mugun tashe ta fito ta soma kunce goyon bayan sadiya ta ɗauki ƴar tana Ajewa agefe kawu ya fito shima, Suka rufu akanta suna tofa mata addu'a har wajan awa ɗaya tana iskokin kafin su jirge tai hamma ta miƙe tana jan ajiyar zuciya bata ko kalli sai tin kawu ba ta nufi ɗakin umma tana wani irin kuka wanda ta cika gidan dashi tana shiga ɗakin umma ta soma buga ƙafafunta.
"Yanzu Kawu tsanar taka garemu harta kai haka shine zaka ɗauki farha ka bawa wani wanda bamu san shiba bamu san daga ina yake ba, Wayyo Allah na na shiga uku ƴar uwata"
Yaya sadiya ta faɗa tana wani irin kuka mai ratsa zuciya umma ta zuba mata ido da alamun har Lokacin akwai sauran ƴan wasan ajikinta sadiya tai kuka ta godewa Allah ta koma tai tagumi hawaye yana ta zubo mata umma ta dube ta.
"Wai waye ya gaya miki an bawa wani farha?"
Umma ta tuhume ta sabida tasa gargaɗi kowa akan kada a sanar wa da sadiya sabida matsalar data ke tare da ita.
Ta share hawaye.
"Umma ni kawai Jikina ne ya bani gida ba lafiya, ina zuwa layin nan nai tambaya aka gayan wai an aurar da Farha har yau kusan sati Umma wannan wani irin aure ne aure ba bincike aure kamar na ƴar tsana fisabilillahi me farha taiwa Kawu daze mata haka Ina take da shekarun ma da za'a ce tai Girma batai auren ba"
Tafaɗa cikin Kuka!
Umma ta gyara zama sosai tana cewa.
"Shima kanshi kawun naku abin da yayi ya dame shi dan ko bacci baya samu To sadiya yaya zamuyi farha ta kafe seta auri Mutuminnan Ni kaina bana bacci Kullum zulumina ina yakai mana ita nifa daidai da dangin shi ban sani ba a yanzu ban san ina yakai min ita ba amman ba ita tajawa kanta ba"
Yaya sadiya ta share hawaye! ta shaƙi majina.
"Ni wallahi umma inda ina nan ba mai aurar da ita haka kawai ma ƙila ɗan yankan kai ne"
Umma tayi murmushi mai ciwo.
"Sadiya baki ga yadda ake yada min magana a cikin gidannan ba Wallahi kullum da kuka nake kwana amman ban san abin da Allah ya ɓoye acikin auran nan ba nidai ina mata addu'a kuma addu'ar mahaifi bata faɗuwa ƙasa Banza nasan Allah yana tare da Farha"
Tagumi yaya sadiya tayi tana sakin ajiyar zuciya umma ta cigaba da cewa
"Ta kafe ta nace seta aure shi, Ranar data bar gidannan dagani har ubanta bamu yi bacci ba dan shi ma kanshi hukuncin daya yanke mata yanzu damun shi yake ga lalura kullum yana ɗaki a kwance Matan gidannan kullum cikin min dariya suke suna cewa wai ƴan bokon ƙarshen zamani an ɓuge da auren mafatauci"
Umma ta faɗa da ɓacin rai.
Yaya sadiya ta dubi umma cikin tausayawa.
"Umma haƙiƙa kin mana komai a rayuwarmu kin tsaya mana akan komai namu kinci buri akan farha tayi karatu to kuma Allah seya kawo wannan ƙaddara ina so umma ki cire komai aranki Ki cigaba dayi mata addu'a haƙiƙa addu'arki itace makami agareta addu'arki itace garkuwa a gareta amman duk wannan Kuka baze yi muku ba"
Kawu ne ya ɗaga labulan ya shigo duka jikinsa a sanyaye ya dubi Ya sadiya.
"Sadiya ba laifina bane fatima ita ce ta nace seta auri wannan mutumi ni kuma takaicin ta yasa nace yazo a ɗaura musu aure, kuma an ɗaura ɗin hakan dana yi shine ya tsaya min azuciyata ina ganin kamar nahau dokin zuciya na yanke hukunci acikin fushi sedai hakan danai shine zesa jama'a su ƙi zagina domin kowa yasan ba da san raina yarinyar nan ta kafe ba"
Yaya sadiya tayi murmushin takaici.
"Haba kawu ai yanzu an wuce zamanin burge mutane sabida kome zaka ma ɗan adam bazaka burgeshi ba kamata yayi da yarinyar nan ta kafe seka bi komai a sannu amman yanzu ba yadda zamuyi Allah ya ƙaddara hakan addu'ar dai itace mafita"
Kawu ya goge hawayen shi.
"Ni na bi ƴata da mugun baki lokacin da zata tafi shiyasa har yanzu mafarkin fatima nake ya Allah ka kare min fatima har ga Allah fatima tana cikin jerin ƴaƴana dana fi so amman ɓacin rai ne ya saka nai mata haka Yau gashi ina Fegenki fatima"
Kawu ya fara tari Ya sadiya ta kawo masa ruwa da sauri amman duk da haka tarin bai lafa ba wanda yana yi Guntun jini na fitowa daga cikin hancin sa umma ta ƙwala ƙara matan gidan suka fito Su halifa ne suka samo tasi har ƙofar Gida aka saka kawu aciki suka tafi asibiti.
Babarsu Hadiza tai ɗammara tana kuka ta nufi ɗakin da umma take zaune ita da ya sadiya ta ɗaga labulan.
"To Hasiya burin ki ya cika Kawu ya faɗi ciwo Daman babban burinki ai ya mutu a raba gida to bari Kiji koda ya mutun kece a ƙasa dan kece mai ƴaƴa mata waya sani ma ko baƙin cikin farha ne yakai shi ga fara tarin Jini tana can yawan barbaɗa dan ba namijin daze auri mace irin yadda aka aurar da ita"
Dama Babarsu Hadiza tunda aka aurar da farha take faɗin ƙananun maganganu musamman data ga yadda kawu ya damu Kullum maganar shi daya sani bai aurar da fatima ga wanda bai sani ba.
Yaya sadiya ta miƙe tayo kan Babarsu Hadiza tana huci kana tace.
"Kin manta karon dani ko? har zaki shigo ɗakin mu kina gayawa Uwata maganar banza ke gado ya dama Ko yau kawu ya mutu uwata ba zatai haya ba kuma ƴaƴa mata arziƙi ne ba kowa Allah yake bawa ba Kuma in sha Allah farha tana cikin Ƙoshin lafiya Bayyanarta gareku seta hanaku bacci matsiyata"
Sum sum babarsu hadiza tabar wajan sabida tsoron sadiya Ya sadiya ta azalzali umma akan ta tashi suje asibitin da aka tafi kai kawu umma ta shirya Lokacin yamma tayi amman haka suka wuce asibitin kansu tsaye Wani ƙaramin Private su Halifa suka kai kawu wanda Ya sadiya taiwa Halifa waya ya gaya mata lokacin da suka ƙarasa ma tuni an bawa kawu gado Neman wajan zama sukai Ya sadiya ta dubi halifa "Me suka ce yana damun shi"
Halifa ya sunkuyar dakai ƙasa.
"Wai ciwon zuciya ke barazanar kama shi wallahi yaya sadiya kawu ya saka tunanin auren farha da yayi ne gashi nan ze kashe kanshi abanza ai ba ita kaɗai ya haifa ba"
Halifa ya faɗa cikin ɓacin rai.
Jikin Umma ne yayi sanyi ta fahimci kowa haushin Yadda kawu ke tunanin auren da yayi wa farha yake yi har dare suna asibitin Kafin Suyi wa su halifa sallama su koma gida Ya sadiya tai gidanta umma ma tai gida.............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 47*
Farha ta jima acikin wani irin yanayi tana ta jin kunyar abin da yayi mata lumshe ido tayi tana hango sanda yake kissing ɗinta ta ƙara mirginawa ta janyo pillow lallai namiji bai da kunya ko kunya bai jiba duk girman shi yazo ya wani rungumeta yana kissing ɗinta miƙewa tayi zaune tana Rufe fuskarta da tafin hannunta wani irin Sanyin jiki take ji ga wani irin yanayi dake bin dukkan sassan Jikinta tasan tana masifar son shi Amman ita harga Allah tana jin tsoron duk wani abu daze haɗata dashi dan ita a ganinta ya yi mata ƙato da yawa.
Miƙewa tayi taje banɗaki ta ɗaurayo fuskarta kuma har Lokacin Hannunta akwai ƙamshin turaren shi ɗakin ta akwai ƙamshin turaren shi ta rasa wani irin turare ne yake amfani dashi mai azababban ƙamshi Ƙamshin da baya barin Ka ta daɗi gefen gado ta zauna duk tana jin kewar tafiyar da yayi kuma tana fatan Allah ya dawo dashi lafiya wayar daya bata tana gida cikin ragowar kayanta daba tawo dasu ba jitai ina ma tazo da ita da babu abin da ze hana ta kirashi taji koya sauka lafiya sabida tana jin a labarai yadda jahar katsina ke fama da hare haren ƴan bindiga da sauran su se kuma taji ta kasa samun Nutsuwa har akai azahar tana zaune gajiya tayi da zaman tayo alwala tazo tayi sallah.
Ta miƙe ta fita falo babu kowa a falon ta wuce Kitchen yau marmarin wake da shinkafa take yi sabida ta jima bata ciba ta saba agida koda yaushe umma tana yi musu ta ɗora wake a tukunyar ta duba cikin kayan miya akwai su salak ta ɗiba ta zauna tana yankawa ƙananu ta gama ta wanke ta aje a kwalanda falo ta fita ta ɗauko kayan da suka ɓata na break ta haɗa ta wanke bayan waken ya dahu ta zuba shinkafar Mintuna masu dama ta ɗauka wajan Girkin dan se wajan Biyu da rabi ta kammala ta zuba a flaks ta jera su mai maggi yaji a wasu ƴan kwanuka takai dining ta zuba nata dana Hajja ta fita daga kitchen ɗin Kai tsaye ɓangaran Hajja ta nufa Lokacin da taje Hajja tana wanki a injin wanki Farha tai mata sannu ta shige Ɗakin Hajja ta aje abincin ta fito.
"Hajja kawo na tayaki wankin"
Ta faɗa cikin kulawa.
Hajja ta washe mata bakin ta fal goro.
"To Fati dama na gama ma amman bazan katse kiba ga shanya ta kimin" Farha ta ɗaga Bokitin ta nufi Igiya tana shanyawa hajja kayan nata Hajja wanka ta shiga ita kuma farha ta koma ɗakin hajja ɗin yau ɓangaran ma ba kowa aciki se Hajja kaɗai Hajja ta fito ta shigo ta shirya Ta kalli farha "Yaya kika jere kayan abincin kuma da alama baki ciba?" Farha tayi Murmushi "Hajja ke nake jira ga naki ga nawa" ta faɗa tana buɗe abincin Hajja tayi Murmushi "Ah lallai yau zanci abinci da marmari wake da shinkafa yaushe rabon duniya da ayyaraye su gidannan basa son irin waɗannan abincin kullum se aikin cin nama ni har ya isheni ma" Hajja ta faɗa tana saka hannu ta fara ci itama farha abincin take ci a nutse sedai duk Bata jin daɗin yanayin Jifa jifa gabanta faɗuwa yake ta tsame hannunta ta miƙe tsaye "Hajja zanje na kwanta kaina ciwo yake" Hajja ta bita da kallon tausayi "To ki amshi magani wajan Hajiya Ammi Allah ya sawaƙe" Ta fita ta wanko hannunta ta wuce part Ɗin Ammi ɗakinta ta shiga ta rufo ƙofar da key kamar yadda yace mata ta kwanta bacci ne mai nauyi ya kwashe ta.
Safna tayi tsaki bayan ta buɗe abincin ta nufi ɗakin Ammi wadda ƙafar yau ta saka ta a gaba dan ko falon ma bata fito ba ta tsaya akan ta.
"Ammi yarinyar nan wake da shinkafa tai mana na abincin rana ni gaskiya ammi bazan ciba wallahi"
Ammi ta dube ta.
"To kije ta dafa miki wani abun mana safna rabu dani ƙafata bana jin daɗin ta sam" batare data Ma Ammi sannu ba ta fita ɗakin Farha ta nufa sedai Koda taja akwai Key taja tsaki ta Koma wajan Ammi.
"Ammi akwai key a ɗakin nata" Ammi ta fusato "Ke rabu dani da abin da yake damuna ga ƙafata ga Baba tunda ya tafi nake Kiran shi a kashe ko zakije wajan Mami kiji yo min kota same shi ita" Safna ta turo baki gaba "Ammi lafiya lau sharrin network ne, Ammi rabu da Aunty Mami tunda ta dawo bata neme kiba ai" daga haka fita safna tayi tasan Ammi ba zata saurareta ba hankalin ta a tashe yake har akai Magariba Ammi nata kiran shi bai ɗauka ba Har Bashir ya dawo daga office Ganin yadda ta damu yasa Bashir yay ta bata haƙuri yana kwantar mata da hankalin ta se Bayan sallar Isha'i Aliyu ya shigo gida Ammi ta rufe shi da faɗan me yasa ya kashe waya duk ya ɗaga mata hankali haƙuri ya bata ya Miƙe ya tafi part ɗinsa Mami tayi masa sannu ta gabatar masa da dinner ruwan tea kaɗai yasha ya kwanta bayan yayi wanka.
Damma yayi sallolin shi mami ɗakinta ta kwanta yau dan jiya ta gurzu shiyasa yau ko gigin Nufo inda yake bata yi ba.
Aliyu yaja tsaki ya miƙe ya zira farar jallabiya da slipers ya sauka bayan ya rufo ɗakin shi Ko ina na falon an kashe ƙwai ya nufi sashin Ammi suma da alamun sunyi bacci dan Goma ta wuce ya rufo ƙofar falon Key ɗin daya riƙe na ɗakinta yayi amfani dashi wajan Buɗe Ƙofar Farha tunda ta tashi dama bata fita ba Sallah tayi tai azkar har aka kira isha'i tayo sabuwar alwala tana nan wajan zaune har Lokacin data idar da sallah mafarki tayi wai kawu ya mutu ana ta kuka agidan su Shine fa tunda ta tashi take ta kuka ga gefen mararta ya riƙe ciwo yake mata kuma tasan ba mp ɗinta ne ze zo ba ta zame ta kwanta anan ƙasan carpet Aliyu ya shigo ɗakin da sallama muryar ta a dashe ta amsa mai sallamar bata miƙe daga kwanciyar data ke ɗin ba.
Ya sami gefen gado ya zauna.
"Yaya baki da lafiya ne? kinci abinci?"
Duka ya jefa mata tambayar yana kallonta.
Ta dafa gadon ta zauna tana Share hawayen ta.
"Ni dai dan Allah kaje ka gano min kawu ne ya rasu"
Ya ɗan kalleta da sauri batare daya gano mai take nufi ba kafin yace mata...........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 48*
"Ki min magana yadda zan fahim ceki mana"
Kanta a sunkuye tace masa.
"Dama ina da wani kawun ne wanda ya wuce mahaifina shi nake nufi"
Cikin rashin fahimta yace mata"Ke waye yace miki ya mutu?"
Ta goge hawayen da yake zubo mata.
"Mafarki nayi wai ya rasu ƴan gidanmmu suna ta kuka"
Takai maganar itama Lokacin Kukan ne yazo mata mai ƙarfi"
Aliyu ya zuba mata ido har wani Lokaci kafin muryar shi cikin sanyi yace mata.
"I'm sorry, dreams are not true, kuma sannan kin saka tunanin gidan ma acikin ranki Amman yana nan lafiyan shi ƙalau"
Ta ɗago ta kalle shi.
"Kai tayaya zaka san yana nan lafiyar shi ƙalau bayan baka je ka gano shiba nidai ko ba zaka ba ka barni naje na gano shi wallahi Ko abinci naci tunanin mahaifa na nake Ummata nasan tana can tana tunani na shima kawun daya ce ze bada ni sadaka Ban san wani hali yake ciba ko ya mutu ne Allah ya nuna min acikin mafarkina"
Ya zuba mata ido kaɗan ya kau da kai sabida tausayin ta daya ji ya fara tasiri acikin zuciyar shi.
"Tam naji zanje na duba shi, Shikenan oya dena kukan haka, sannan ni ban maki alƙawarin fita ba sabida ni bana son yawan fita to yaushe ma kika daɗe da zaki ce zakije gida?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta dafe mararta tana rintse ido da kulawa yace.
"To se kuma meye sauran?" kinci abinci?" ta girgiza kanta alamun bata ciba "Kina meye baki ci abincin ba?" ya jefa mata tambayar batare daya tsaya jin me zata ceba ya miƙe ya fita Minti kaɗan ya dawo da tea mai kaurin gaske.
"Ki samu