Showing 117001 words to 120000 words out of 150033 words

Chapter 40 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

ta soma karatun azkar Lokacin gari yayi haske mami se baccinta take hankali kwance kamar ba ita ce ta gama kuka jiya ba Ita dai farha jingina kanta tai da Jikin gado Hawaye duk ya bushe a idanunta wajan shiddan safe mami ta farka idanu jajir ta dubi farha cikin mamaki.
"Farhan wai baki bacci jiya bane ni dai duk tashin da zan sena ganki a zaune kina sallah?"
Farha bata ce komai ba mami ta tashi ta shiga banɗaki ta jima aciki sannan ta fito tazo ta shinfiɗa darduma a ƙasa tana sallah Bayan ta idar wayar ta ke ringing taje ta ɗauka ta zauna a bakin gado.
"Hello mama ina kwana"
Shuru ne ya biyo baya da alamun na wayar ke magana.
"Eh mama ya kusan ƙarewa kwana biyu ma Kin san muna umara To kuma mun dawo Aliyu ya faɗi yana asibiti nayi zaton Jiya ma zaku zo nan ɗin ai"
Shuru mami tayi can tace

"Ƙaddara mama wallahi ya faɗi to shikenan se kun zo nagode"
Bayan ta gama wayar wadda ta bawa farha tabbacin da mahaifiyarta suke yi tashi tayi ta fita farha ta gyara mata ɗakin wajan ƙarfe tara na safe Mami ta kammala girki ta zuba komai cikin Basket lokacin farha ta gama mata gyaran ɗaki mami shiga tayi ta shirya cikin Jallabiya baƙa tai rolling ɗin mayafin jallabiyar a kanta ta fito tana zabga ƙamshi farha datai tagumi ita ko wankan ma batai ba Tun kayan ta na jiya ne ajikinta Hijabi kawai ta sauya.
"Farhan driver ze kaini asibiti sabida yanzu dana shiga ciki Sadiƙ yayi min waya akan na kaiwa Aliyu abinci sabida Ammi ta tashi yau da rashin Jin daɗi tasha magani bacci take Se anjima zata je wajan shi To ba kowa ni zanje na karɓi Bashir"
Zaraf Farha ta miƙe tsaye tana wasa da bakin Hijabin ta Muryarta kamar zatai wani Kukan tace.
"Aunty mami nima zani"
Mami tayi dariya "To a haka zaki baki wanka ba ki bari anjima seki bi su Ammi" hawaye ne ya shiga ziraro mata wanda bata san da suna zubar ba kafin tace "Ni dai dan Allah zan biki" mami taɗan sha jinin Jikinta kafin ta kalli farha cikin nazari "Farhan badai akan faɗuwar Yaya kike ta kuka tun jiya ba?" Jikin farha yaɗan yi sanyi sabida Kada mami taga zaƙewar ta cikin sauri tace "A,a nima bana jin daɗi ne Kuma sannan Kin san babba kamar shi ya faɗi ai duk mai hankali ze shiga cikin damuwa dole" Mami ta wuce ta ɗauki baske Ɗin tana cewa "Haba nidai nai mamakin Kukan naki To Allah ya baki lafiya Shige Mu tafi" suka fita wajan mota suka shiga driver yaja su zuwa asibitin farha ta matsu suje taga wani hali yake ciki ajiyar zuciya farha ta sauke sanda suka shiga cikin asibitin ba kowa Sabida asibitin mai tsada ne sosai ba Mutane se iya ma'aikata haka suka wuce Ciki adaidai Ƙofar shiga suka haɗu da Bashir Suka gaisa da Mami farha kawar da kanta tayi Gefe.
"Yawwa Aunty mami gwara da kika zo Ni bari nabi driver gida na ɗan kwanta dan Jiya ban yi bacci ba wallahi"
Mami data nuna damuwa ƙarara a gaban Bashir tace.
"To yaya Jikin nashi?"
Bashir yaɗan kalli farha tare da cewa.
"Bai farka ba dai har yanzu amman Likita yace zuciyarsa Normal kawai alluran ne basu sake shiba"
Mami tai ajiyar zuciya tana cewa

"To Alhamdulillahi"
Bashir yaɗan dubi farha.
"Cute babu gaisuwa abin ƴar haka ce Ko?"
Farha batai masa magana ba tabi bayan mami suka shiga ciki Ƙofar ɗakin da yake ciki mami ta murɗa handle ɗin ta shiga farha tabi bayanta sanyi da ƙamshi ne sukai musu sallama A hankali suka ƙarasa gaban gadon nashi..........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 92*

Har lokacin bacci yake yi kwance yake samɓal a kan gadon Jikin shi gaba ɗaya a rufe yake da tattausan Bargo fari tas mami ta aje basket ɗin hannunta tare da zama a saman ɗaya daga cikin dogayen kujerun ɗakin farha kuma bata zauna ba hannu tasa ta dafe gadon daya ke kwancen ta zuba masa idanu bata ko ƙiftawa Addu'a take ta yi akan Allah ya tashi kafaɗun sa.

"Farhan ga wajan zama ki zo ki zauna anan kafin ya tashi naga bacci yake sosai" Cewar Mami farha taja ajiyar zuciya jita ke dama ciwon ya dawo mata shiya sami lafiya Jikinta a saɓule taje kusa da mami ta zauna.

Hannayenta duka biyun ta zube a kumatun ta tare da zabga tagumi ita ko mami wayarta ta ɗauko tana danne danne ɗakin shuru yayi wata nurse ce ta shigo ɗakin bakin ta ɗauke da sallama.

Suka gaisa da mami nurse ɗin ta dubi mami

"Amman ranki ya daɗe doctor yace kada wanda ya shigo wajan shi a bari har ya tashi daga baccin"
Mami tayi wa Nurse ɗin wani kallo tare da cewa "Aini ce mafi kusanci dashi fiye da kowa Kije kicewa Likitan matar shi ce a tare dashi" mami ta faɗa cikin gadara Nurse ɗin bata ce Komai ba ta ƙarasa wajan gadon da yake kwance ta duba shi tayi abin da zatai tabar ɗakin mami taja Dogon tsaki ta cigaba da danna wayar hannunta farha tashi tayi ta fita batare data cewa mami komai ba Mami ta bita da kallo amman setai tunanin ko zaga asibitin zatai shiyasa bata ce mata Komai ba harta ƙullewa ganinta farha bin bayan wannan Nurse ɗin ta dinga yi har zuwa bakin Office ɗin da zata shiga Juyowa nurse ɗin tayi tana kallon farha da sauri farha tayi ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
"Ƙanwata yaya akai?"
Cewar Nurse ɗin farha tai ƙasa da kanta sosai tare da cewa.
"Dan Allah Office ɗin Likitan daya duba wancan marar lafiyan zaki nuna min"
Nurse ɗin tayi murmushi.
"Okay amman yanzu baya nan sabida ba'anan ya kwana ba nasan dai yana hanya can kwanar zaki Miƙe seki hannunki na dama zaki ga office ɗin nashi"
Farha tai mata godiya tabi hanyar data mata kwatancan

Samun kujera tayi a wajan ta zauna zaman jiran Likitan.


A hankali yake motsa bakin sa salati yake yi yana ware idanun shi dishi dishi yake gani maƙogwaron shi ya bushe kanshi se sara mai yake yana masa azababban ciwo ji yake kamar ya rabe Gida biyu ga yatsan ƙafar shi se zugi yake mai kamar ze cire Zazzafan Huci ya saki Yana tariyo abin da ya faru daran Jiya na farko abin da ya ɗaga mai hankali yadda yaga Bashir na ƙoƙarin Cusa kanshi ga lamarin fatima wannan abu ya kaɗa shi wanda tunanin shi ya tsaya ne akan tabbas Bashir son fatima yake gaban shi ya faɗi bai ga laifin bashir ba sabida bashir bai da sani akan alaƙar shi da fatima, A bu na biyu yadda Ammi ta wulaƙanta fatima agaban ilahirin mutan gidansu abin ya ɓata mai ranshi se abu na Uku Shine abin da ita kanta fatima ɗin tayi masa abin ya ɓata mai ranshi a yunƙurin ya tashi ya Bayyanawa Ammi matsayin fatima awajan shi Allah ya ƙaddara masa wannan faɗuwa wadda tasa Numfashin sa ya tafi Hutun wucin gadi wanda bai sake sanin ina kan shi yake ba se yanzu a kuma gadon asibiti wanda shi kanshi bai san Taka maimai awani hali aka kawo shiba Kuma bai san meke damun shi ba yasha fa hannun shi yaji Plastar allura ya taɓa kanshi yaji plasta Ya yunƙura ya tashi zaune da sauri Mami ta ƙaraso tana mai sannu Da taimakonta ya zauna sosai Yana huci dan yadda kan shi kemai Ciwo Abin na dukan shi.

"Sannu yaya Allah ya baka lafiya"
Cewar mami ya cije leɓansa na ƙasa Idanunshi sunyi jajir Jijiyar kanshi ta miƙe tai raɗo raɗo.
"Zanyi sallah zona dafa ki"
Cewar shi mami ta kuma zuwa ya dafa ta suka shiga toilet.


"Ƴammata lafiya na ganki zaune kin zuba tagumi" cewar likitan daya ke tsaye akan farha Ta ɗago idanunta ta kalle shi ta soma motsa bakinta alamun gaisuwa ya amsa yana raɓeta ya Buɗe Office ɗin.
Ta bi bayan shi zama tayi a kujerar dake kallon tashi shima lokacin ya zauna yana aje jakar hannun shi "Likita dan Allah meke damun wancan bawan Allah da aka kawo Jiya?" Likitan yaɗan yi mata kallon Nazari tare da cewa "Wai madaki kike tambaya toke mecece ɗin sa?" tayi ƙasa da kanta tare da cewa "Matar shi" Likitan ya saki baki yana kallon ta bai da damar ƙaryatawa dan bai san komai akan Suba yaɗan dube ta a tsanake "Please karki ɗaga hankalin ki ba wata matsala gagaruma bace kawai ajiya zuciyar shi ta ɗan Buga ne se jinin shi daya hau sabida wata ƴar damuwa daya shiga ko kuma wani abu daya gani wanda yaɗan bugi zuciyar shi amman Tun jiya numfashin sa ya dawo kuma Jinin nashi ya sauka se Buguwa da yatsansa da kanshi yayi duk mun gyara masa Yanzu haka Nurse tace bacci yake alluran da mukai masa ne masu ƙarfi" Tuni hawaye ya gama jiƙa gaban Hijabin farha cikin wani irin yanayi take kallon Likitan kafin muryarta cikin Kuka tace "To yanzu wani matakin za'abi don kada hakan ya kuma faruwa dashi?" Likitan yace "Kada ki damu Kawai magani ze dinga sha akan Lokaci Sabida jinin nashi kada ya dinga hawa sannan kuma aguji ɓata masa rai ko yaya duk abin da ze ɗaga masa hankali aguji yi agaban shi ai ita lalura ƙaddara ce wata baka tashi da ita ba seka kwana da ita wata bakai farko da ita ba sekai ƙarshe da ita nidai Inda naji daɗi ma da matsalar zuciyar batai ƙarfi a tare dashi ba" Farha taja ajiyar zuciya Gaba ɗaya ta karaya da lamarin lallai mai rai ba abakin Komai yake ba "To Yanzu wani maganin ya kamata a fara ɗora shi akai?" Cewarta Likitan yace "Duk mun rubutawa Ɗan uwan shi jiya kuma an siyo se a dinga Kula wajan bashi" Godiya tai masa tabar Office Ɗin Likitan ya mayar da ajiyar zuciya yana jin ina ma shine yayi dacen macen da take son shi kamar wannan yarinyar.

Ko gabanta bata gani haka ta nufi Ɗakin da aka kwantar dashi dan ta cika da damuwar lamarin nashi.

Adaidai Lokacin Kuma ya kammala Abin da ze a toilet ɗin mami ta kamoshi mami da taji ƙara kamar an turo ƙofa ta ɗauka ko farha ce cikin sauri tace "Farha ɗan shinfiɗa mana carpet kafin mu fito" duk da halin da yake ciki seda ya dubi mami akaikaice yace "Wace haka?" mami tace "Wannan yarinyar mana ta wajan ammi ai jiya tare muka kwana se Kuka take tama Ƙi bacci se sallah nina ɗauka ma ko akan faɗuwar ka take Kukan dana tambayeta shine tace Itama bata da lafiya ne Da zanzo nan tare Muka zo to naga ta fita ne ban sani ba Ko ta shigo" Ta faɗa sanda suka fito daga cikin Toilet ɗin Aliyu cikin kaɗuwa yace "Kika barta kuma ta fita?" daga haka ya zame daga Jikin Mami Jiri na ɗibar shi ya Nufi wajan abin sallah duk Jikinsa yayi sanyi alokacin farha ta shigo daidai nan shikuma ya tada sallah.

Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye tana Goge hawayenta.
"Farha daga ina kike?" cewar mami.
Sosa kai farha tayi tare da cewa.
"Na fita ne na zauna a waje" ta faɗa tana Kallon yadda yake sallah bayan ya idar ta nemi guri ta zauna wannan karon a ƙasa ta zauna Kusa dashi so take su haɗa ido amman se taga ya kawar da kanshi Gefe.

Ya jima yana addu'a kafin ya miƙe da sauri mami ta zo ta kamashi yadda suka haɗe da juna shida mami se abin yaɗan sosa mata rai da taimakon mami ya koma saman Gadon ya zauna.
"Mami baki zo min da kayana ba wannan sun dame ni wanka zanyi" mami aranta tace ai ko kwaɗo yasha fa ma lafiya wajan yin wanka amman a fili se tace "Na manta amman bari anjima in basu baka sallama ba sena je na ɗauko ma" yaɗan ɓata Fuska "Ni wanka zanyi Kinga kije Ki ɗauko Mini kawai" ya faɗa yana Jingina kanshi da Jikin pillow Ɗin da ke kan gadon


"To bari kayi break" ta faɗa ta shiga haɗa mai tea.
"Ina kwana yaya kwanan Jikin naka?" Yaji Muryar farha amman seyay mata banza yaƙi kulata sema ya Juyar da kanshi Gefe.
"Yaya baka jiba ana gaishe dakai" banza yayi wa mami ɗin itama farha taji wani takaici ya taso mata da ƙyar ta danne ta cigaba da wasa da hijabinta Mami ta tura mai ƙwai da dankali da ruwan shayi Gaban shi ya Tashi zaune Ya ɗauki Cup ɗin shayin

"To sedai nahau napep dan driver yaje kai bashir Gida farha bari naje na dawo"
Cewar mami farha ta Miƙe tsaye "A,a zan biki mu tafi tare kawai" dan ya gama ƙona mata rai yadda ya Nuna halin Ko in kula akanta ai ita jiya ta kasa bacci sabida shi

"A,a ki zauna yanzun nan zan dawo Dana dawo semu koma tare sabida koda Kinje ɗin ma Gidan Ammi ba kowa duk nan zasu tawo" mami ta faɗa tana fita daga ɗakin badan farha taso ba ta Koma ta zauna rannan nata a haɗe ta haɗe fuska babu alamun dariya.

Ɗakin shiru yayi can taji Muryarshi.
"Fatima bani ruwa marar sanyi"
Banza tayi masa.
Ya kuma maimaitawa a zuciye ta miƙe tare da zuwa wajan ƙaramin Fridge ɗin ɗakin ta ɗauko mai gorar ruwan tazo gaban shi ta Miƙa masa amaimakon ya amsa seya haɗa da hannunta.
Ƙoƙarin zamewa take yaƙi bata dama sema cicciɓota da yayi zuwa saman gadon ya direta a saman Cinyar sa.

Taƙi kallon shi a yayin da shi kuma ya zuba mata ido tausayinta yana ratsa mai dukkan Ilahirin sassan Jikinsa.
"Fatima kuka kikai tayi kalla Hijabin Ki duk ya yi jirwaye da ruwan hawaye Koma wanka baki ba"
Ya faɗa a tausashe.
Sabon kukan ta soma yi.
"In banyi kuka ba me zanyi tun jiya kana ta fushi dani"
Da sauri yace mata.
"Ko na mutu baki da asara ay tunda Kin zaɓi kita gasa min magana kamar sa'anki Tunda ba zaki bi yadda nake soba ay shikenan" da sauri tace masa "To ni mai nayi maka Kaga in ma danni ka shiga wannan halin ka fita dan wallahi ciwon nan kaɗai ne ajikinka amman nina fika wahala Jiya ban rintsaba gani nake kamar zan farka ace Min ka rasu" ta faɗa tana Goge hawayenta Kusancin su ne ya daɗu Lokacin daya Ke Kusanto da fuskar shi daidai wajan tata fuskar har ƙasumbar Fuskar shi na gogar tata Fuskar Idanu ya Lumshe yana Fesa mata hucin Numfashin sa.

"Kaci abincin se kasha maganin ka"
Ta faɗa tana ɗanyin baya da fuskarta.
Hannunta ya damƙa ya Ɗora a saman Ƙirjinsa a hankali yace.
"Fatima kina jin yadda zuciya ta take Bugawa? Fatima duk rintsi kada Ki kuma furta kalmar zaki rabu dani Kinjii....Ji nake kamar zan Mutu wayyo kaina" ya faɗa Cikin wani yanayi wanda ya kaɗa hantar Cikin farha Kuka tasa tana Kwantar da kanta a saman Ƙirjinsa.
"Me yasa ba zaka gaya Musu matsayina a wajan kaba Me yasa ka zaɓi ka Ɓoye aure na dakai Dan Allah kayi wani abu akan hakan" ta faɗa Cikin Kuka

"Fatima Ammi na tsoron ɓacin ran Ammi na nake wallahi fatima ina masifar Gudun ɓacin ran Ammi ne"
Ya faɗa a wahalce zame wa tai zata tashi daga Jikinsa yayi saurin ƙara Rungumota kamar wani ze ƙwace mai ita hannunshi ya zira ƙasan Rigarta.
Yana wani daɗa matse ta ajikinsa.
"Mami tace Min baki da lafiya oya tell me meke damun ki Muji Jikin naki?"
Ya faɗa yana Buga mata Numfashinsa a saman Fuskarta Lumshe idanunta tayi lokacin dataji ɗumin tafin hannunshi a saman Cikinta yana wasa da tsakiyar Cibiyarta.................
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 93*

Jikinta ne ya hau rawa tana wani irin shige masa kamar mai jin sanyi zullewa take tana cusa kanta a cikin Ƙirjinsa a hankali ta riƙo hannun shi dake Cikin rigar tata.
Fuskarta ta ɗago wadda tai kalar tausayi kamar zata yi kuka! ta ce masa "Dan Allah ka dena" Cikin raɗa kuma a hankali yace "Sabida me bayan ni daɗin hakan nake ji" ya faɗa yana Ƙara shigar da hannunshi sosai Ya shiga Murza Ɗan tudun daya ji a ƙasan marartata Huci ta sauke tana kwanciya sosai a jikinsa wani irin wahalallan Numfashi take ja gaba ɗaya ya saukar mata da kasala ajikinta hannu tasa ta kamo fuskar shi ba zato yaji saukar danshin Bakinta a saman lips ɗinsa tana tsotsa a hankali ya Jinginar da kanshi a saman Pillow ya Lumshe idanunshi Ji yake dama zasu dawwa ma acikin wannan yanayi mai wuyar Misaltawa......

"Ammi ya kamata ki kwantar da hankalin ki Jikin Yaya Aliyu da sauƙi sosai dan yanzu haka ma Aunty mami tana tare dashi" cewar Bashir wanda yake tsugunne a gaban Ammi sadiƙ daya Fito cikin shirin tafiya asibitin sabida ya makara sakamakon Rashin baccin da bai samu a daran Jiya ba shine ya dubi Bashir wanda ke gaishe dashi Bayan ya amsawa Bashir ya kuma ce masa "A,a yaya na ganka agida Kuma shi Aliyun da wa ka bar shi ai da kayi min waya dana je in yaso kai seka tawo" Bashir yaɗan sosa kai tare da cewa "A,a Aunty mami taje har da kayan break fast ma shine nace ni bari nazo nai wanka sena koma" Sadiƙ ya zauna a kusa da Ammi yana gaishe ta kafin yace "Okay to yaya ƙarfin Jikin nashi?" bashir yace "Da sauƙi amman har na tawo be farka ba" Cikin wani irin yanayi ammi tace "To kuma shine zaka ce bazan je na ganshi ba wannan wani irin Bacci ne tun jiya har yau Mutum bai farka ba kaga in da wani abun da kake ɓoye Min gwara ka gaya min nasani ni Musulma ce kuma ba mutuwar da ban gani ba tunda naga ta uwata da ubana naga Ta mijina" Ammi ta faɗa tana share hawayen ta! Bashir ya soma rarrashinta "Wallahi Ammi ya sami sauƙi bacci ne kawai yake sabida allurar da akai masa mai ƙarfi ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login