Showing 57001 words to 60000 words out of 150033 words
Chapter 20 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
Allah kada ka ƙara dukan yarannan Kaji"
Aliyu yaja tsaki mai ƙarfi.
"To Limamin shagalallu Bazan Kuma dukan suba"
Daga haka yaja wayar ya kashe.
Sakina matar sadiƙ tai Murmushi tana kallon shi.
"Dady kai da waye ne Kuke ta kai ruwa rana?" sadik yayi dariya.
"Nida Ali ne Ammi ce ta kawo Min ƙarar shi"
Taɗan ja tsaki kaɗan, "Ok shine yake maka tsawa a waya nifa wallahi sam bana Jin daɗin abin da yake maka Ɗinnan Kullum nuna maka nake kaima ka gina kanka kabar zama a ƙasan shi kaƙi kai Kenan Kullum kamar shine babban kai ƙaramin"
Sadik ya haɗe rai tare da cewa.
"Look sakina kin san bana son waɗan nan zantukan yaushe Ali ya taɓa min tsawa Ni ba zaki haɗani da ɗan uwana ba Ina Masa kyakykyawar Fahimta Kuma shima yana Mini"
A Ƙufule ta dire Cup Ɗin hannunta tayi ɗaki fuuu "Allah ya rabamu da Mutuwar Zuciya" ta faɗa da ƙarfi yadda sadik zeji yota.
Sadiƙ damo sarkin Haƙuri juya tea ɗin gabansa yayi yana Murmushi ba tun yau sakina ke Ƙoƙarin Nuna ƙyashi ga Ali ba shikam ba ruwan shi yagama shan tea Ɗinsa yabar Gidan ya tafi office batare daya bi takan sakina ba.
Bayan sun gama waya da sadiƙ ya sauka daga saman gadon ya shiga wanka ya jima acikin Toilet kafin ya fito mintuna kaɗan ya shirya cikin jajayen J.c Rigar Mai dogon hannun ce haka wuyanta a zagaye yake haka wandon shima Dogo ne daga wajan ƙasan ƙafar zagaye da adon fari wanda aka Rubuta Adidas da ƙaton harafi ya feshe jikinsa da turare zeje Filin training ne shine dalilin daya sa ya sanya kayan sedai Koda ya sauko ƙasa yama tarar Rana tayi sosai sai ya Nufi dining abin takaici ba abincin akai gashi yunwa yake ji sosai.
Ya kalli mami dake fitowa se baza ƙamshi take.
"Ina abinci na?" ya faɗa yana kallonta, ta ɗan sosa kai.
"Yaya ashe mai girki tayi tafiya ni ban sani ba amman bani Minti Goma zan dafa maka ko Indomie ce"
Ya ja tsaki yabar mata falon sarai tasan baya cin Girkin masu aiki sannan Idan yace ze Jirata nan ma ɓata masa Lokaci zata yi Part Ɗin Ammi ya nufa duk suna saman dining suna yin Break Bai Ko kalli saitin Su safna ba yaja kujera ya zauna yana gaishe da Ammi ba yabo ba fallasa ta amsa masa su safna dama sun gama suka tashi suka bar wajan itama Ammi da ragowar Haushin sa aranta tana gamawa tabar wajan ya haɗa tea ya ɗebi doyar yana zuba farfesun kifin a gefe Bashir ya shigo suka gaisa Shima yaja Kujera ya zauna yana haɗa tea Fuskar Aliyu a ɗaure yake Break ɗin kamar an masa dole.
Sum sum ta fito daga Kitchen duk Gefen hijabinta ma ya jiƙe tazo zata Gifta Bashir yaɗan ɗaga Murya.
"Zoki zuba min doya"
Aliyu ya watsa mai wani kallo bai ce masa Komai ba.
A hankali ta tako gaban Bashir Hannunta na rawa ta ɗauko plate zata zuba doyar Aliyu ya saka ƙafa ya taka mata tata da ƙarfi ta rintse ido yaɗan saci kallonta kafin yace wa bashir.
"Kai baka da hannu ne?" ya kalleta ba walwala a saman fuskar shi.
"Dallah ɓace min daga nan wurin kai ma tashi ka bani wuri"
Da sauri tayi ɗaki shikuma Bashir ya tashi yana ƙwafa yabar falon jiyay abincin ya fita aranshi duk da yana masifar son doya ya miƙe yabi bayanta zuwa ɗakin.
Tana tsaye tana yarfe Jiƙaƙƙen hijabinta ya turo ƙofar ya shigo ciki da sauri tai baya ta ɗauka ko wannan saurayin ne.
Ya jingina da ƙofa bayan ya rufo Ƙofar yana ƙare mata kallo.
"Me kikai yau agidannan?"
Banza tai masa.
Ya daka mata tsawa yana Kuma tambayarta zumɓura baki tayi ta juya masa baya.
"Daga yanzu kada ki kuma shiga kitchen yin wani aiki, sannan kada na kuma ganin wani ya sakaki aiki kinyi idan ba Ammi ba, Kuma kada na sake ganin Bashir ya miki magana kin kulasa"
Ta harare shi kafin tace.
"Nida nazo bauta bani da zaɓin uban gida duk wanda ya sakani aiki yi zanyi kai meye damuwarka, sannan shi wanda kace sunan shi Bashir nina san shima jiya ne kaɗai da muka ci karo da juna ya rungumeni..........
Da sauri taga yayo cikin ɗakin da sauri kanta yayo gadan gadan wanda ta koma bayan wardrobe ta maƙe tana zaro Idanu janyota yayi ƙiii har Tsakiyar ɗakin.
"Amman ban taɓa sanin baki da hankali ba se yau da auren nawa akanki har kika yarda ya rungume ki akan yaya?"
Tsoro yanayin nashi ya bata tai saurin zubewa a ƙasa tana Kuka.
"Nima fa ban sani ba nidai dan Allah kada ka dakeni ni wallahi tsoron ka nakeji wallahi kamin dukan su ni Mutuwa zanyi"
Ta faɗa tana wani irin kuka Muryarshi cike da takaici yace.
"Ai in ke baki mutu ba zaki lalata min aurena dan baki da hankali meye har zaki yarda Jikinki ya taɓa nashi so kike nai Miki duka shima nayi masa?"
Da sauri ta girgiza kai tana zaro ido tana haɗa hannu.
"Good to daga yau kada na Kuma ganin ko hanya kin haɗa dashi in ba haka ba sena miki dukan da zaki kasa gane gidanku shima Kuma ze same nine"
Ya faɗa da wani irin Fushi yabar ɗakin da gudu ta shiga toilet fitsarine na tsoro har ya fara zubo mata sabida bata taɓa ganin yanayin shi kamar haka ba.
Aliyu wajan Bashir dake zaune a falon ya nufa wanda yake ta danna wayar shi da alamun da akwai abin da yake Jira.
"Bashir kada na kuma ganin ka da waccan yarinyar Duk iskancin da kake a gari yana zuwa kunnen mu to ita ba kalar ka bace, idan ka yarda na Kuma ganin Koda magana ta haɗa ku"
Ya ja ƙwafa yabar wajan ya Nufi ɗakin Ammi duk da har Lokacin ranshi a ɓace yake.
Bashir wani basaraken Murmushi ya saki tare da cewa.
"Haba yaya Ali ai wallahi ko zaka kasheni ba zan bar wannan garar ba nasan ba komai ne yasa kake kaf kaf da ita ba dan kawai ƙanwar Musa ce toni kam ba wanda ya isa ya hanani taɓata tare da Ƙudirina na aurenta Very soon"................*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 44*
Ya shiga cikin ɗakin Ammi da sallama cikin bakinshi ya nemi guri ya zauna a ƙasan carpet Ammi bata ko kalli saitin da yake zaune ba.
"Ammi zan ɗanyi tafiya anjima zanje katsina amman ba lallai na kwana ba in kuma na kwana shikenan"
Se kuma ta juyo batare data bari sun haɗa idanu dashi ba tace.
"Me kuma zakai a hanyar katsina kai da kasan yadda hanyar take a yanzu?"
Murmushi yayi.
"Ammi bafa hanyar katsina ba katsina ɗin zani akwai wanda na turawa motoci basarake ne a jahar katsina to ana bikin ƴarshi wancan satin banje ba shine wannan satin zanje nai masa Allah sanya alkairi"
Ammi da duk ranta a jagule yake tunda taji yace ze tafi katsina sabida yadda labarai ke bazuwa na halin da jahar katsina ke fuskanta ta dube shi.
"Nidai dama zaka tura masa saƙon Barka da arziƙi ka rufa Min asiri kada ka tafi katsinar nan"
Shi dariya ma ta bashi uwa kenan duk yadda take jin zafin sa gashi abu kaɗan yazo kuma ya saka ta firgice cikin sanyin murya wadda tai kamar ba tashi ba yace mata.
"Ammi ki kwantar da hankalinki, Ni Birnin katsina zani ba ƙauye ba Kuma in sha Allah yadda naje lafiya zan dawo lafiya, Yana min ciniki sosai ne bazan iya ƙin zuwa yi masa Allah sanya alkairi ba sabida ni a tsakanina da costumers ɗina akwai Girmamawa da zumunci"
Ya faɗa yana kallon ta har lokacin hankalin Ammi be kwanta ba ta kalle shi tana cewa.
"To meya hana tun Jiya ka gaya min nayi addu'a duk da kullum acikin yinta nake ko Jirgi zaka hau?"
Murmushi yayi.
"A,a Ammi mota ce kuma nida kaina zanyi driving In sha Allah, Addu'a kullum muna yinta ba wani abu Khairan In sha Allah"
Tagumi Ammi ta rafka.
Ya miƙe tsaye.
"Ammi zanje na sauya kaya sannan Kuma dan Allah dan Annabi ba danni ba, Ammi adena saka yarinyar can aiki a kitchen in ma hajjo ba zata muku ba ku ɗauki duk me aikin da Kuke so ni zan biya amman itan ce bana son ana saka ta aiki tayi ƙanƙanta da yawa aikin ze mata yawa kada Ƙirjinta ya bude azo ana samun matsala"
Ammi ta tallafe kumatu tana binsa da kallon tuhuma kafin tahau tafa hannu.
"Kai Allah rabamu da Munafuki au ce maka tayi mun saka ta wani abun?Baba zo zauna ka gaya min tsakanin ka da ƴar ficikar yarinyar can nifa na fara zargin ka anya Baba?"
Murmushi yayi tare da cewa.
"Haba Ammi ita ta isa tazo ta gayan ƙananun maganganu ni ai na girmi wannan kawai I noticed kamar Yau ita tayi duk aikin gidannan ne"
Ammi ta hasalo masa tayo caa akan shi.
"Eh ita tayi sabida su safna suna fita makaranta ni kake so na shiga nayi tunda ka dakatar dasu Hajjo ehe nace Ni zanyi ita ƴar maiƙo ta kwanta tai bacci Su suna da makaranta to wa kake zaton ze in ba itan ba sannan ta gama nawa taje tai wa matarka"
Ranshi ya haɗe Ya kuma tsuke Fuska.
"To gaskiya in hakane Kawai Hajjo ta dawo ɗin, Sannan ni ban amince taje Min part Ɗina ba tai aikin iya kacin nan, Sannan kuma Ammi kicire zargina a ranki bani da wata alaƙa da ita in kika cire dalilin Musa yana daraja ni yana girmamani yana ganin Mutuncin kowa nawa to why shi ba zan daraja nashi ba bare ance marainiyace ta yaya bazan ji ƙanta ba Nina san watarana ya Allah zeyi dani"
Ya faɗa yana kallon Ammi yadda yayi ɗin kokai waye ba zaka ce akwai alaƙa a tsakanin shi da ita ba.
Ammi taja ajiyar zuciya.
"To duk naji yanzu tafiyar zakai kaci abincin kuwa?"
Ya ɗan taka yana fita daga ɗakin.
"Eh Ammi kimin addu'a"
Daga haka ya fita daga ɗakin har Lokacin Bashir yana falon zaman Jiran fitowar Farha Aliyu batare daya dubi setin Bashir ba.
"Malam ka tashi ka fita office zaman uban me kake agidan ok kai sedai duk wata ka ɗauki albashi kenan masu wahala suna can suna yi?"
Bashir ya shafa kai yana cewa
"Ba haka bane yaya dama yau zan ɗan huta kaga Jiya na dawo daga Abuja"
Tsaki Aliyu yayi tare da cewa.
"I don't want to come back and see you sitting here without going to the office"
Daga haka ya fita yabar falon Bashir ya kaiwa Iska naushi yana jan tsakin ɓata mai bajat da Yayan shi yayi haka ya Miƙe ya fita yay shirin Office Ko Ammi baiwa sallama ba ya fita a zuciye sanin waye Aliyu in ya dawo Ɗin bai tafi ba komai na iya faruwa.
Aliyu.
Ya koma part ɗinsa da ike yayi wanka shiryawa yayi cikin wani ubansun Boyel Navey blue wanda yayi masifar yi masa kyau hula da takalmi da agogo same colour ya saka wanda yayi azabar kyau kai kace wajan ɗaurin auren shi zashi ya tsaya yana fesa turare Ya fito daga ɗakin da waya kare a kunnen shi suna magana da Musa Mami tana zaune a falo ta kashe ado Cikin Jan lace riga da skirt.
Da sauri ta taso ta tare shi tana gyara masa lins ɗin gaban rigar shi.
"Yaya kayi kyau sosai"
Ya saki Murmushi ya zauna a saman Kujerar suna cigaba da waya da Musa Mami ta zuba mai ido wannan Mutumin da kyau yake ma sha Allah.
"This look is like you are going to eat me" ya faɗa yana hure mata idanun ta murmushi tai mai.
"Yaya inda zan iya da cinye kan zanyi yadda bamai samun saura"
Murmushi yayi mai tsada yana Kamo kumatunta.
"Ni naga ma kin fara Kumari gaya min sirrin Kinsan Ni ina son mace ƴar lukuta next time gaskiya ƙatuwa zan auro"
Ya faɗa yana mata dariya.
Turo baki tayi tana Ƙoƙarin saka Kuka.
"Haba yaya kalleni fa ƴar cif cif dani, Ni kaɗai nasan na ishe ka ko yaya?"
Ta faɗa tana leƙa fuskar shi Miƙewa yayi tare dayin gaba yana ce mata.
"Kiyi addu'a katsina ta ɗauka"
Daga haka ya fita daga falon yabar mami cikin zulumi da rashin gane maganar tashi............
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 45*
Cikin shiri ya shiga part ɗin Ammi ɗakin ta ya shiga tana zaune saman darduma da alamun sallar walha tayi ta ɗaga hannu tana addu'a suka shafa a tare ya kalle ta da kulawa.
"Ammi na shirya ai min addu' ni zan wuce fa"
Ammi ta ɗan matso gaban shi ta kama saman kanshi ta ɗora hannunta ta jima tana masa addu'a kafin ta ɗauke hannun duk idanunta sun ciko da hawaye ya shiga girgiza mata kai.
"Ammi Don't cry for me addu'ar dai ita ce in kuma bakya son naje na haƙura"
Ta girgiza kanta.
"Kaje Baba Allah ya tsare"
Jikinsa ne yayi sanyi seya hau janta da hira dan ya kawar mata da tunanin da take yi akan tafiyar tashi, Kafin ya miƙe yana cewa.
"Ammi yau ba'a share Miki ɗakin naki ba ga ƙafar taki har yanzu akwai Kumburi"
Bai jira maganarta ba ya hau kaɗe mata zanin gado ya ɗauki abin shara ya share mata ɗakin tas ya Goge ya ɗauko turaren wuta ya kunna mata nan da nan ɗakin yayi kyau, Ya ɗauko man zafi yazo gabanta ya kama ƙafar yana shafawa Ammi ta zuba masa ido kaf ƴaƴanta ba mai biyayyar shi bamai son ta kamar shi tun yana yaro take jin daɗin sa take alfahari dashi Tuno sanda take fita sharar titi tayi wadda kafin ta fita shi yayi asubancin fita ya share mata sedai taga ya dawo da tsintsiya yana shirin fita makaranta ƙwalla ta taru a idanunta bai taɓa mata Musu a dukkan umarninta ba koda hakan ze jefa shi a damuwa yana bala'in son ta da kishin ta wata irin zuciya gare shi ta sadaukai yana son ƴan uwanshi Komai nashi na sune Bai taɓa mata gardama ba se zuwan Baƙar yarinyar can wadda har ya zage yana dukan su safna agabanta tana masa magana bai saurare taba wannan gardama kaɗai taga ya taɓa yi mata wadda ta hassasa Ƙiyayyar yarinyar a zuciyarta mai tsanani.
"Ammi idan kinga akwai damuwa na haƙura na tafi Office Ni dai nasan In sha Allah lafiya zanje na dawo ina Bin hanyoyin da suka fi wannan hatsari Kuma na dawo lafiya, akaf jahohin kasar nan ɗaiɗai kune bana shiga, Kaduna ce kaɗai ma bani da mutane sosai acan amman sauran Jahohin nan duk akwai jama'ata kuma ina kokarin shiga"
Taja ajiyar zuciya.
"To shikenan Nima in ƙafar tawa tai min sauƙi zan ɗan leƙa gidan kawu na duba su kwana biyu banje ba ni kuwa mami ta dawo banji ɗuriyarta ba"
Ya kalleta bayan ya miƙe tsaye.
"Eh ta dawo bata zo nan bane?"
Da sauri Ammi tace.
"Zata zo ne hutawa take"
Ya girgiza kai yana cewa.
"Ammi in baki warke ba kada kije ki famo ƙafarki ga inda ma nace kije nan Gidan su Baba kinƙi zuwa anyi rasuwa amman baki je ba Ammi rayuwar ma duka nawa take yau ina Babanmu baya duniya duk wanda ya maka sharri kai bisa da alkairi ƙarshe sharrin nasa akan shi yake ƙarewa duk yanzu ba arziƙin ki suke ciba dan Allah Ammi ki dai na musu haka ko banza ciki ɗaya suka fito da mahaifin mu wannan Jini fa ba za'a iya kwashewa ba"
Ta zuba masa ido.
"To naji baba ku suka zamewa dole bani ba in ka kuma min maganar su Usman zaka fita da ɓacin raina"
Yayi ƙasa da kanshi.
"Allah ya baki haƙuri Ni na tafi"
Ta bishi da addu'a taja ƙaton carbin gabanta tana cigaba da lazumin da take yi.
Direct ɗakin farha ya tura ya shiga.
Tana cikin Banɗaki da alamun wanka take ya janyo stool ya zauna akai lokacin mami ta kira shi awaya kuma adaidai nan farha ta fito daga banɗakin ɗaure da zani ko hijabi babu ajikinta.
"Hello ƴammatana yaya ake ciki?"
Ya faɗa da ƴar tsokanar mami.
Ta karyar da murya tana cewa.
"Nifa ban gane ba wai katsina ka tafi?"
Yayi Murmushi yana cewa.
"In sha Allah ki tanadar min abun daɗi kafin na dawo"
Ta cikin wayar mami tace.
"To Allah ya tsare min kai daga dukkan sharri me zan tanadar maka ɗin?"
Yayi Murmushi "Dukan ki amman kizo ki gaida ammi bata jin daɗi"
Mami tace.
"Subuhanallahi ban sani ba ai jiya ban dawo da wuri ba amman zanzo kai mata sannu"
Yace.
"Ok" yana kashe wayar ya zubawa farha ido tana zaune gefen gado ta yafa wani zanin akan ta ya rufe mata Jikinta tana shafa mai rannan nata a haɗe kamar kace mata ket ta saka kuka.
"Me yasa bakya saka key a ɗakin nan daga an turo ƙofar take buɗewa?"
Tai masa banza ta miƙe ta Nufi wajan kayanta ta ɗauko zata wuce banɗaki ta saka ya taɗota ta faɗo saman Cinyar shi.
"Washh bayana ni ka sakeni"
Ta faɗa tana ƙoƙarin sauka daga saman cinyar tashi.
Yayi mata riƙon tsauri yaɗan kwanto da fuskarsa daidai tata.
"Kawo na sanya miki kayan naki"
Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya harara ta zabga masa ta warce kayan ta shige banɗaki ta jima aciki kafin ta fito har lokacin yana zaune yana aikin danna wayar shi.
Can nesa dashi ta zauna.
"Ya kamata in zaka shigo ɗakin mutane ka dinga neman iso ni har ga Allah ana shiga haƙƙina"
Ta faɗa tana kawar da kanta Murmushi yayi mata tare da dawowa Kusa da ita yana Ƙoƙarin kamo hannunta taƙi yarda ta zame ta zauna a ƙasa.
"Wai meye ne se Guduna kike tunda nazo na fuskanci kamar haushina kike Ji?"
Ƙaramin tsaki tayi wanda ya tsaya mata iya ita kaɗai dan beji taba ta rasa dalilin daya sa taji zafin wayar da ta tarar yana yi kuma ta tabbata da mace yake yin ta.
Ya sunkuyo daidai fuskarta ya ƙura mata ido.
"Naga kin fara haske ko ruwan gidan namu ya amshe ki ne?"
Ta bashi amsa.
"Eh ai wahala ma tana sa hasken dole wai me kake nema ne kazo ka zauna min a ɗaki kuma ni abu zanyi"
Ta faɗa tana matsawa daga setin nashi.
"Tofa Fatima yau kekam lafiyar ki ni kike wa ƙara a kaina?"
Ya faɗa a hankali.
Saman stool